Yar jami'a 4

'YAR JAMI'A 006 .
Ina so kisan wani abu baba mak'asudin zuwan mu gidan nan ba don komai bane illah mu nema wa tsoho lafiya,babu yadda za'ai muna ji muna gani mu kai shi inda zai wahala,tunda mu musulmai ne,bisani ma wannan jikarsa ce,maganar asibiti kuma da kika baba shekara nawa kuna zaune gida ana yin na hausa,wane sassak'e da mad'acin ne ba'a bashi yasha ba?ina ce duk an gwada amma jikin jiya i yau,kinga kuwa bazamu zuba ido ace haka za'a barshi cikin wahala ba dole a samu abin yi!kuma ina ganin son da zaki nuna wa tsoho shine ki barshi muje mu jarraba na baturen ko Allah yasa a dace! . . Jimm baba yagana ta d'an yi uwa mai nazarin wani abu kowa ita yake jiran jin abinda zai fito daga bakinta,kwatsam suka fara jin k'uhul...k'uhul...k'uhul....alamun k'arar tari na tasowa daga d'akin dake gefensu,cikin sauri baba yagana ta mik'e suka rufa mata baya sukai cikin d'akin! Kwance suka iske shi yana yunk'urin mik'ewa amma ba hali don wani matsanancin rawa da jikinsa ya soma va shiri sameer ya k'ara suka dashi bai jira cewar suba yadda yaga jikin tsoho na gyargyarwa ya sungume shi yayi yayi waje dashi,haka suka k'ara d'ungumowa gaba d'ayansu suka yo waje banda kuka da kururuwa babua binda baba yagana ke sumbud'awa" . . . Abakin k'ofar zaure ne suka ci karo da malam sale mai shago wanda kukan baba da ya jiyo yasashi shigowa ba shiri,ganin yadda aka fito da tsoho ranga-ranga yasa shi shima kwarma uban salati ya ja gefe ya tsaya,ba wanda ya iya bi ta kansa suka haura sukai waje,cikin aljihu sameer ya fiddo key ya mik'a wa beauty nan ta bud'e motar ,gidan baya sameer ya zauna shi da tsoho d'an ladi na k'ok'arin turo kai ciki ya dakatar dashi yace a'a ka zauna gida ka kula da baba yanzu zamu dawo,badan yaso ba haka d'an ladi ya ja gefe yayi turus! Juyawar da sameer zai yi ne kicib'is suka had'a ido da beauty dake gefen baba tsaye hannu rike da mukullin mota"cikin tsawa ya furta mata" ke dalla malama ki shiga ki drivern namu kikai tsaye akan mu kamar sanda,ba ta bi ta maganar saba duba da yadda jikin tsoho ta tsananta ta nufi driver seat da sauri ta shiga ta kunna motar,ta nufi asibitin dake k'auyen! Da idarsu asibitin waje beauty ta samu ta aje motar wanda har lokacin numfashin tsoho ya kasa dai-daito cikin sauri sameer a bud'e k'ofar ya d'akko tsoho suka fito beauty na take musu baya,cuncurundon jama'a kad'ai kake hangowa ta ko'ina acikin asibitin ga hayaniya na mutane duk inda ka juya mara lafiya ne zaune,abinka da ba'ai saba shiga waje haka ba kafin kace me duk sameer ya rikice ya rasa ina ma zai yi dashi,waje ya gano gefe da wata mata dake goye da yaro ba kowa cikin sauri ya isa wajen ya zaunar dashi juyowa yayi ya kalli beauty rai b'ace yace ki kula dashi ina zuwa kuma banda nuna hali!yana kai wa nan sameer ya sakai yayi gaba" sakayau beauty ta bishi da kallo fuska yamutse uwa mai shirin kuka ta shiga zancen zuci"toh wai shi wannan me ya d'auke ni akuya ko kuwa tunkiya da duk inda naje sai na bi maza?ba takai ga baiwa kanta ansa ba ta jiyo tarin tsoho ba shiri ta katse guntun tunaninta ta nufi wajensa ta na mai sannu! Bai wani jima da tafiya ba sameer sai gashi ya dawo gefensa wani matashi da alama likitane sai wasu samari suma dai cikin fararen kaya dake nuna jami'an lafiya ne,ko da suka k'araso samarin nan cikin sauri da nuna gogewar aiki haka suka janyo gado a wani d'aki dake gefe damu suka d'aura tsoho suka nufi can wani sashen na asibitin,biye muke binsu har suka isa wani b'angare da hayaniya ta tsagaita a wajen,office dake ciki suka nufa muna k'ok'arin biyo su ciki likitan dake biye damu ya d'ago musu hannu badan sunso ba dole yasa suka dakata anan! Waige sameer ya shiga yi ko ya samu wajen zama can ya hango wasu kujeru da basu wuce 4 a jere a k'arshe wajen ba take ya nufi wajen yazauna itako beauty ta shiga sintiri tana kai kawo a wajen! . . Har kimanin minti 30 babu alamar motsi ko fitowa daga ciki! gajiya beauty tayi da zagayen dole ta nemi gefen wata window dake nan ta jingina tana kallace-kallacen jama'ar waje! Can suka fara jiyo taku na tahowar mutum ido duk suka k'ura wa k'ofar sai gashi d'aya daga ciki samarin nan ya fito hannunsa d'auke da takarda!mik'ewa sameer yayi da sauri ya nufoshi inda itama beauty ta yo kansa tana fad'in dan Allah malama ya jikin nasa?bai iya tanka mata sai ma kallo da yakai ga sameer yace yallab'ai dr.ya rubuto allurai da ruwa da za'a siyo,karb'ar takardar sameer yayi k'ok'arin yi sai yaji yace dashi,a'a yallab'ai ai wannan aikin ba naka bane kadai bayar a siyo,lummm sameer ya d'anyi sai kuma can ya wuce gaba yace muje toh wajen! tafiya suka shiga yi har sun kai k'ofar barin wajen sameer kamar wanda yayi mantuwa ya juyo ya kallo beauty wacce itama dai su take kallo yace toh sai ki samu waje gashi can ki zauna a bar lek'en taga don babu abin gani kuma dai a kama kai don nan gidan HIV ne,yana kaiwa nan yasa kai ya fice abinsa!beauty dake tsaye hannu sak'ale da k'aramar jakarta bata ankara ba taji wasu zafafan hawaye sun fara kwaranyo mata a fuska wanda sam batasan dalilin hakan ba! . . Kusan minti biyar kenan da fitar su sai gasu sun shigo rik'e sa ledoji biyu,office d'in saurayin ya shige shi ko sameer ya dawo nan ya nemi waje ya zauna! Kawo lokacin beauty na zaune saman kujerar ta duk'e kai k'asa tana nazarin halin da tsoho ke ciki, Sallama har sau biyu sameer yayi amma ina beauty tayi nisa a tunani"wasu dai anyi asarar kud'in tara wallahi ace sallamar ma basu iya amsawa ba"furucin da beauty kenan ta tsinta daga sameer hakan ya tabbatar mata da sun dawo don haka ta d'ago kai tana kallonsa"kafin daga bisani ta saki doguwar tsuka had'e da tab'e baki ta d'aura k'afa d'aya kan d'aya ta juya masa gyeya! Dariyar k'arfin hali sameer ya saki mai cike da tuhuma sannan ya furzar da wani zazzafan iska waje yace"Wato in aka ce dai akuya wallahi an gama da kai,don kuwa ita ko ina sai ta nuna halinta sai dai in bata samu waje ba! Bai kai ga sauke lumfashinsa ba kamar wacce aka mintsina beauty ta juyo a kufule ta shiga gyad'a masa hannu taba magana"kai malam shiru-shiru fa ba tsoro bane gudun magana ne,ko dan kaga tun d'azu ina raga maka shiyasa kake ganin kai ka isa,toh wallahi ina yi maka kashedi na k'arshe ka fita a harkata tun kafin na nuna maka kaina a zahiri" A razane sameer ya mik'e tsaye ya dafe k'irje had'e da fad'in wa iyazu billahi yanzu banda wannan munanan ayyukan da kika shahara dau kina so kice min har akwai wasu na xahiri?ehh toh lallai ke tashin shuri ce don daga gani bade rainon mutim basai dai aljani! . Ganin yadda sameer ya samu damar ci gaba da gaya mata magana son ransa yasa itama ta mik'e tsaye ta shiga jijjiga jiki uwa mai shirin dambe kana tace na lura kana wasa dani ko?da sigar ko in kula sameer ya bata amsa da,ni kuwa yaushe zanyi wasa da wacce tayi ikrarin kiran kanta da sunan 'Yar jami'a ai ban isa ba tunda ban tab'a bin wani malami tsoho mai nauyin shekaru ya prof KAS na buk'aci b'ata masa mutunci ba,ban kuma tab'a nuna tsiraici na afili don samun distinction ba kin ga kuwa baxan tab'a had'a kanki da ni ba! Hucin da beauty ke fitarwa kad'ai zai zayyanar dakai irin halin da take ciki na k'unar rai na lura da duk wata gab'a da tabi don taga ta d'au fansa sameer ya kasa bata wannan damar! Awulak'anceta watsa masa wani mugun kallo had'e da sakin wani mugun zagi ta koma ta nemi waje ta zauna jiki ba kwari"abubuwa kala-kala ta shiga sak'awa a zuci ganin yadda ko da sau d'aya zatai nasara akan sameer amma nazarinta ya kasa bata,dole haka ta hak'ura na lokacin ba don ta janye k'udurinta arai ba dai don ta gama da jinyar tsoho tukunna! shi ko sameer lura da yadda ta yi lagwas yayi don haka ya shiga murmushin mugunta ala dole ya iya furta hmm kad'an kika gani yarinya in dai kin ce ke 'yar jami'a ce toh mu masu gyara jami'a ne kuma dole ki ladabtu ko kin k'i ko ki so!daga haka shima ya nemi can nesa da ita ya zauna tare da janyo waya a aljihunsa ya shiga yin game na zima revenge ko ya samu sauk'in rai! Haka sukai zaune har wajen azahar kafin nan dr ya fito hannunsa rik'e da wani abin kwajin numfashi ya nufosu,ko da sameer ya hangoshi tashi yayi fuska a sake ya nufi wajensa yana fad'in dr. Ya jikin nasa?murmushin k'arfin hali ya saki kafin nan yace c'mon down prince ba wani abu ne na tada hankali ba jimawa da yayi a gida ba tare da an kawo shi asibiti ba shiya haddasa masa hawan jini amma yanzu cikin ikon Allah mun samu munyi controlling nasa sai dai tarin da yake ne wannan sai a hankali kuma ana shan magunguna,yanzu haka yana ciki ya samu sauk'i sosai don nayi masa allurar bacci zaku iya shiga ku ganshi in har jikin naga ba matsala zuwa yamma kafin na tashi a aiki na sallame ku! Amsa masa sameer yayi da toh sannan ya k'ara gode masa da namijin k'ok'arin da yayi yabar duk wani aiki nasa yayi nasu!musabaha suka yi kafin ya basu izinin shiga ciki shiko ya wuce waje,jami'an lafiyar da suke tare suka mara masa baya! . Duk bayanin dr. a kunnen beauty ake yi duk da tana can zaune amma hankalinta na kansu haka bata jira cewar sameer ba duk da tasan ba wani abu zai ce mata ba yana shiga d'akin ta biyo bayansa ta shiga!kwance suka iske tsoho yana bacci hannunsa d'auke da ledar k'arin ruwa da aka saka masa,cikin sauri beauty har tana bige kafad'ar sameer ta k'ara gefen gadon ta rik'o hannunsa cike da tausayin halin da yake ciki ts shiga rero kuka!. Cike da b'acin rai sameer ke binta da wani wulak'antaccen kallo shi ala dole ta buge masa jiki gashi yak'i jinij yaga mace tana kuka balle wannan daya lura kamar ita jin dad'in kukan ma take,tsawa ya daka mata a tsawace yace dalla malama ki wa mutane shiru uban me akai miki da zaki cika mana waje da k'ara?wannan shegen kukan naki ai se ya tashe shi" Bata iya tanka masa ba beauty illah tsagaitawa da kawai ta iya yi da kukan!ta nemi waje gefe dashi ta zauna ta k'urawa tsoho ido, a sukwane shima sameer ya koma can baya ya jingina da bango tare da hard'e hannayensa biyu a k'irjinsa cike da damuwa ya ke kallon yarda robar ruwa ke d'iga cikin kwaroron robar hannunsa! . . . Har wajen k'arfe d'aya na rana tsoho na kwance bai tashi ba,jin kiran sallah na tashi daga cikin masallacin ya baiwa sameer damar fita ya barsu anan,yana sa kai ya fita beauty ta waigo ta k'are ma wajen daya tsaya kallo nan ta saki wata doguwar tsuka tare da fad'in"aikin banza ai na zaci bara kaje sallar ba gafin mu zaka zauna yi ka wani kafe mutane da ido uwa soja gona,tsukar dai ta kara saki don yadda duk take jin ta atakure ita bata saba wannan zaman ba musamman ma na asibiti ga yunwa data fara addabarta,k'are ma wajen kallo tayi tas taga dai babu wani abun ci a wajen balle tai tunanin ci,ga babu bayi da xatai alwala ballantana daddumar sallah cike da b'acin rai beauty ta shiga gunguni wanda ita kanta baza ta tantance abinda take fad'i ba do takaici! Tana haka taji an turo k'ofa an shigo, sanin wanda zai shigo yasa ko takan k'ofar bata bi ba da mamakinta sai ta ji muryar mace,hakan ya bata damar d'ago kai ta kalle ta" Sannu dai" jami'ar asibitin ta fad'a, yawwa sannunmu,bata k'ara tankawa ba matar ta shiga jere mata kayan dake d'auke a hannunta,ledojine guda hud'u bak'ak'e sai sallaya da hijabi data mik'a mata sannan ta iya cewa dama yallab'ai ne yace a kawo miki kuma in kina son wani abu ga d'aki nan na kusa da wannan kina fita daga hannunki na dama sai ki min magana"murmushin karfin hali da jin dad'i beauty ta sakar mata don ko ba komai tasan dai abinci ke cikin ledojin nan don haka ta ce toh nagode amma ina bayi yake?hannu jami'ar takai ga wani labule da ke manne a saitin gadon tace gashi nan madam"madam kuma? Abinda beauty ta furta kenan a ranta,toh me yace musu game da ni?kar dai fa ya gaya musu wani abu na b'atance don k'aramin aikinsa ne?ciskune fuska tayi na dole ba don taso sunan ba tace ok zaki iya tafiya yanzu,da haka jami'ar ta fice tare da janyo mata k'ofar! . . Bayin ta nufa ta d'oro alwala ta fito,inda ta aje hijab d'in je ta janyo ta ta saka dogone har yana d'an ja mata k'asa,haka ta janyo sallayar da shirin sallah sai kuma tayi turus tana bin d'akin da kallo ?can kuma ta nisa tace wayyo ni ina ne yanzu kuma gabas d'in?ganin ba fahimtar hakan zatai ba yasa ta yanke shawarar zuwa ta tambayo matar,aje sallayar tayi ta doshi k'ofa don fita,tana murd'a k'ofar taji an murd'o ta daga waje an turo,saurin matsawa da baya tayi don kar ta bige,har ya shigo kallo,sameer kallo ya bita dashi cikin hijab kwanan sha'awa kamar tayi ta zama kullum haka sai kuma can ya basar ya juya kai gefe cikin izzah ya jefota da tambaya,ina kuma zaki?ita madai kauda kai gefe tayi uwa bazata amsashi ba sai kuma can ciki-ciki tace gabas zan tambayo,kamar be jita ya tab'e baki yayi mata nuni da hannu,kalli nan! Kallo ta kai wajen,bai k'ara tanka mata ba ya nemi guri ya zauna! Bango ta kai wa harara beauty kamar yana kallonta ta juya ta zare sallayar cikin fushi ta shinfid'a ta fara sallar! . . Tana idarwa kenan ta fara azkhar ta ji k'arar wayarta cikin jaka,kallo ya bita dashi sameer ya na jiran yaga cikin biyu wanne zatai azkhar ko waya,da mamakinsa sai yaga ta share wayar taci gaba da addu'ointa,k'arar da cikinta ya bayar da k'aramin sauti yasa ta dole badan taso ba tsagaita adduarta ta shafa,wani abu ta ji ya tsaya mata a rai kuma gashi dai tana son janyo ledojin abincin amma kunya ta hanata don yadda k'afafunsa suka tokare ledar" jim ta d'anyi tana nazarin abin amma lura da yadda yunwa ke nuk'urk'usarta yasa ta dole ta maze had'e da tsuke fuska uwa wata 'yar dambe ta saka hannu ta shiga janyo ledojin,karaf ledar k'arshe ta buge masa k'afa, ai kamar jira yake sai ji kai d'asss.. ya kai ma hannunta duka da k'arfi,ledar beauty ta saki a razane ta d'ago kai ta kalle shi,me kuma nai maka?cike da mamaki take tambayar,mugun kallon nan dai nashi ya k'ara jefo mara ya galla mata wata harara yace"ehh lallai kam tunda kin maida tab'a jikin namiji abincin ki ai baza ki san me kikai min ba,toh wallahi na bar kyaleki kina tab'ani kina cin na jaki banza akuya,zunbur beauty ta shiga yi har tana hard'ewa da hijabin jikinta ta mik'e tsaye ta kama k'ugu ta rik'e tana wani karkad'e-karkad'e tace kasan Allah wannan abin naka ya ishe ni ehe,don ba jaka aka kawo maka ba,mutum sai bala'in naci da shishshigi idan baka son alak'ata dakai tun farko wane karanbanin yasa ka neman tahowa dani? Me yasa baka jefar dani a hanya na san inda dare yayi min ba?ko an gaya maka bani da wajen zuwa?meya hanaka zaman wajen da ka dawo yanxu tunda ban kama hannunka nace zo zauna kusa dani ba?toh dan haka malam kasaurara min ko na ci uban.....ba ta k'arasa k'arshe zagin nata se ji kake fau..fau..fau wasu zafafan mari har biyar da sameer ya sauke mata a fuska,bai jira wani abu ba yayi wulli da ita gefe har tana karo da bango ya zari sallayar dake shinfide a k'asa ya shiga jibgarta da ita,kiciniya suka shiga yi sosai dukkan ninsu a wahalarce musamman beauty dake kwance k'asan tiles jiki duk shatin duka,shiko haki ya shiga furzarwa na wanda bai saba shan wahala irin hakaba! Ganin yadda ta galabaitu yasa sameer dakatawa da dukan yayi cilli da sallayar gefe ya nunota da yatsa yana maida haki yace"wallhi duk randa kika kuskura kika k'ara magana irin wannan sai kin raina wa aya zak'inta mutuniyar banza kawai,har ni zaki kalli mahaifina ki zaga wanda ya bani cikakkiyar kulawa da tarbiyya?toh baki isa ba wanda duk kike tunanin ya tsaya miki shima bai isa ba,da kuma kike cewa na takura miki,eh naji na takura miki don bazan zauna ina kallo karuwa ta lalatamin rayuwa ba,don haka ki kama kanki! Yanda take kwance k'asa tana maida numfashi haka ta shiga nuna kanta da yatsa tace,ni ka kira da karuwa?karuwa fa?k'ok'arin mik'ewa zaune tayi amma ina jikin yayi tsami dole ta komar da kai ta kwanta k'asa wasu mugayen hawaye suka shiga anbaliya a kuncinta! . . . Yarda take maida hak'i na kuka haka sameer ke maida hakin wahala suna haka sai rurin waya ya k'ara tasowa daga jakar beauty,sai alokacin ta tuna da d'azu an kirata tana addua haka da janjiki ta isa gaban jakar ta sa hannu ta fito da wayar,lambar zee-zee ta gani rass gabanta ya fad'i ba tare da wani dalili ba,d'aukan kiran tayi ta kara akunne tana fad'in hello"murya k'asa-kasa beauty ke amsa ta can kuma kome zee-zee ta gaya mata sai cewa tayi what??kina so kice min yau akayi test d'in?toh ba cewa akai se last week ba?har nawa akayi?biyu?wanne da wanne?sir p... maganarta yayi dai dai da kallon sameer wanda ke zaune gefen tsoho ya dafe kai da alamar damuwa tare dashi,a sanyaye ta k'arashe wayar sukai sallama da beauty duk jiki ba kwari,tana kashe wayar ta k'ara sulalewa k'asa ta kwanta,tunani kala-kala tun tana iya danne zuciyarta har ta gaza a fili ta shiga dukan tiles din dake shinfid'e k'asa tana fad'in mugu,mugu,azalimi wallah Allah sai ya sakamin! . Tana cikin wannan hali taji daga sama rurin wayar sameer dole ta tsagaita da kukan ta maida kanta ta had'e da gwiwoyinta, zaro wayarsa sameer yayi daga aljihu ya amsa kiran bai wani jima ba ya gama wayar,wata lambar ya shiga laluba beauty na kwance taji cikin wayar yana fad'in kamal yanzu za'a zo a kawo maka test d'ina pls ka adana min kafin na dawo! Da haka suka ci gaba da hira har ya gama,aje wayarsa ke da wuya yaji alamun motsi daga bayansa,da sauri ya juya idonsa ya ci karo da tsoho dake kwance yana k'ok'arin tashi,k'arasawa sameer yayi ya tallabo shi yana tai masa sannu,wanda hakan ne ya tabbatar ma da beauty cewa tsoho ya tashi ,a hankali ta d'ago ta zauna,dishi-dishi haka ya shiga bud'e idonsa har Allah ya saka ya bud'e su gaba d'aya,alama ya fara nuna masa da yana buk'atar ruwa don haka cikin sauri sameer yayi waje don kiran dr. Sameer na fita tamkar ya baiwa beauty damar k'arasowa wajen tsoho ne cikin jan jiki haka ta k'araso suna had'a ido suka sakar ma juna dariya haka ta rungume shi da haka ta hau masa sannu!suna haka sai ga sameer ua shigo tare da dr.dole ta basu guri dr yayi 'yan bincike-bincikensa ya gama da yake ruwan hannunsa ya kai k'arshe zare masa yayi kafin nan ya rubuta masa magunguna yace su zauna nan ya k'ara samun k'arfin jikinsa zuwa anjima sai a sallame su!dad'i sosai ya lullub'e jn yadda cikin k'ank'anin lokaci tsoho ya samj sauk'i,takardar maganin dr. Ya mik'a wa sameer sannan ya basu waje,ledae dake aje sameer ya hau bud'ewa har ya gano wacce ke dauke da ayaba,hannu yakai ya d'ebk yadawo gefen tsoho a hankali ya shiga bashi yana ci har ya gama dai tsoho ba emm ba em em duk tunani ya gama cika game da dabuwar fuskar daya gani tare da jikarsa amma lura da yadda beauty ta kasa sakin jiki suyi hira sosai kamar yadda suka saba sai yayi zaton ko kunyar had'uwarsu da sirikinsa yasa ta shiru(loh tsoho bai sai su beauty duka aka sha ba)da haka ya kauda tunanin a rai"! . _4:30 na yamma:_ . Tsaye suke bakin asibitin rike da takardar sallama inda sameer ya rik'o hannun tsoho duk da jikin da kwarinsa sai dan bashi kulawa kawai,ita ko beauty tafe take nik'i nik'i da ledoji ,baya ta bud'e ta shiga inda sameer ya sanya tsoho gaba ya zagaya ya shiga motar suka fita a asibitin! . Tun saka kan motar sameer a layin tururuwar jama'a kad'ai kake gani ta ko ina ana biye dasu ana ihu na farin cikin tsoho ya dawo,yara ko se d'ane motar suke da yake yamma tayi duk wasu magidanta sun dawo k'ofar gidan tsoho mak'il yake haka suka tsaida motar,inda da kyar Sameer ya iya bud'e wa tsoho k'ofa ya fito dan jama'a,k'ok'arin bud'e marfin motar beauty ta hau yi don ta fito taji an buge hannun daga waje,sanin waye yasa bata ma bi takai ba da sauri ta bud'e k'ofar ai ko yayi saurin maida marfin motar ya kulle kafin ya fidda tsoho yasa mata lock,tururuwar taron jama'ar data gani shi ya hanata magana dole ta koma ciki tai zaune ta bi su da ido har suka shige cikin gida!don tasan sarai sameer na iya dizgata gaban bainar jama'a! . . Juyi da murna babu irin wanda baba yagana batai ba,sam zama ya gagareta,d'akko wancen aje wannan shine kad'ai aikin kai kawo da take wa sameer sai da ta tabbatar ta cika masa gabansa taf da kayan abinci da fura sannan ta iya samun waje ta zauna,baba yagana sameer ya kalla yace baba wai ina d'an ladi kuwa?nisawa tayi kafin nan tace ai d'an ladi ya tafi gona tun bayan tafiyarku watakil ma yanxu duk inda yake yana hanya,wani abu zai yi?a'a dama maganin tsoho zai rakani na siyo cikin gari"sameer ya fad'a" K'aramin murmushi baba ta saki sannan tace ai ban baka labari ba d'azu bayan tafiyarku drammer aka sha ni da shi,wai ala dole anyi masa haramiyar jin rab'ar mota,da gunguni haka ya fita ko ta kansa ni kam ban bi ba ina tunanin yadda tsoho zai samu lafiya duk na gama tada hankali,tunani ya kasa yarda cewa zai dawo da rai sai gashi ya shigo da k'afafunsa kai amma fa mungode da wannan taimako naka! Ba komai baba ai yiwa aki ne yanxu dai ki sama wa tsoho wani abu yaci kafin ya dawo mu siyo maganin"haka baba ta amsa da toh ta mik'e ta nufi cikin uwar d'aka! . . Hankali kwance sameer ya gama cin tuwon alkama miyar gyad'a da baba yagana tai masa ya bishi da fura wacce tasha kindirmo,ya jingina kenan da bango yana son abincin ya ratsa masa yaji maganar d'an ladi yana shigowa" Maimakon ya shigo da sallama sai 'yan wake-wake da yake sakin kamar d'an makid'i har ya zauna dariya kawia sameer yayi masa sannan yace,har ka dawo daga gonar?banza yayi dashi kamar be ji shiba da haka sameer ya ci gaba,dama kai nake jira ka dawo muje mu siyo wa tsoho magani a mota,da jin haka cikin sauri dan ladi ya waigo yana kallon sameer yace wai da gaske kake zaka shigar dani mota?gyad'a kai sameer yayi da zummar eh,ai lokaci d'aya d'an ladi ya saki fuska hira ta b'arke tsakaninsu ta inda yake shiga bata nan yake fita ba,har da alk'awarta wa sameer yau zai had'a masa taro mai kyau a dandali suje kallo,da haka dai sukai ta hira,sai can da hira ta nisa d'an ladi ya waiga ya kalli sameer yace wai kuwa ina hajjo?sakin baki sameer yayi cike da kid'ima bai jira basa amsaba ya mik'e ya zuri takalmi da sauri yayi hanyar zaure". Koda ya isa gaban motar kwance ya Taradda beauty sai had'a zufa take kana ganinta kasan ta galabaita,cikin sauri ya bud'e k'ofar ya shiga lek'enta!.. . . Lura da alamun bacci da ta shiga yi na wahala yasa sameer bubbuga gefen kujerar yana fad'in ke!ke!firgigit beauty tayi ta mik'e zaune kana ganinta kasan ta wahala,fuska cuskune ta kallo shi babu ko kwakwkwaran nauyi a jikinta ga tsamin duka da jikinta ya riga yayi,koma wa da baya yayi sameer wanda hakan ya bata damar fitowa a motar a daddafe ta maida k'ofar ta rufe,cikin sanyin jiki haka ta shiga tafiya sai yaji duk babu dad'i abin bai masa ba,amma dole ya dake ya kallota ta wutsiyar ido yace ke!kike wani cilla k'afa uwa summy cillare(Loh) in zaki saki jiki gara ki saka in ko ba haka ba na fasa kwai yau kowa na k'auyen nan ya san halinki,da sauri beauty ta d'ago raunannun idanunta ta kallosa cike da takaici,murmushin mugunta ya sakar mata had'e da kashe mata ido d'aya yace kinsan dai xan iya don haka sai ki zab'a yana kaiwa nan yayi gaba abinsa ya shige ciki ya barta nan tana jan jiki uwa wacce kwai ya fashe wa a jiki! . . A cikin zaure beauty ta tsaya nan ta k'ara gyara jikinta sosai,cikin k'arfin hali kuma ta saki fuska ba yabo ba fallasa ta nufi cikin gida,Da sallamarta ta shigo tsakar gidan babu kowa sai k'arar muryar d'an ladi dake tashi duk ya karad'e gidan da surutu shi ala dole labari yake ba sameer,muryar beauty da yaji yasa shi tsagaitawa da hirar ya juyo baki a washe yana kallon k'ofa,har ta k'araso wajen sameer bai d'ago kanshi daga duk'en da yayi ba tun jin sallamarta,cikin k'arfin hali beauty ta kalli d'an ladi tace ina tsoho yake,yana d'akinsa"d'an ladi ya bata amsa,bata k'ara cewa komai ba ta sa kai ta wuce su zuwa d'akin,yadda ta gifta ta gaban sameer haka ya d'ago kai ya bi bayanta da kallo,k'arewa tafiyar kallo yayi sam babu wani alamar sauyi ko canji daga tafiyarta,murmushin gefen kunci sameer ya saki a kasalance ya raya a zuciyarsa"lallai yarinyar nan a iskanci ita yarinya ce har da take tsoron k'aramin k'auye kamar wannan susan sirrinta,toh ko dai tsoho ne bata so ya sani? Bai kai aya a tunanin nasaba yaji an tab'o shi a kafad'a,a d'an tsorace ya juyo,lafiya dai ko bak'on birni?tambayar da d'an ladi ya jefo masa kenan,gudun kar d'an ladi ya fahimto abinda yake kallo yasa shi kauda kai gefe ya d'an ja numfashi yace ai da kaga na kau da kai ba wani abu nake mazari ba illah b'aci da rai na yayi ace yadda kake suburbud'amin wannan labari ka kasa bani labarin budurwarka?(kwana ba sai a mota ba)bud'e idonsa sameer yayi da sigar son jin wani abu ya k'ara langwab'ar da kai gefe sannan yace toh ko dai baka da ita ne? . . K'afa d'an ladi ya d'aga sama ya dire a kan tabarma sai kuma ya kwashe da wata irin muguwar dariya mai cike da mamaki,sai da yayi ma'ishiyarsa sannan ya d'ago kai a gadarance yana wani faffad'a kafad'a yace Wato d'an birni ni d'in nan da kake gani na duk ranar da naje dandali sai 'yan mata sunyi fad'a akai na,shiyasa kaga samarin garin nan duk kishi suke da ni don mero 'yar gidan mai gari wancan satin da naje dandali baka ga yadda take nuna kauna k'arara akai na ba,har wani kod'a ni take wai tana son tsagun fuskata,amma ni duk basa gabana ,jin maganar d'an ladi na k'arshe yasa sameer k'are wa bak'a k'irin d'in fuskar d'an ladi mai cike da tsagu kallo,jinjina kai yayi cike da mamaki,ganin yadda d'an ladi ke ta faman kod'a kanshi ba ji ba gani,surutan 'yan mata barka tai yasa shi d'aga masa hannu yace toh suda sarkin magana yanzu dai gaya min wace zab'inka acikin nasu?cikin sauri d'an ladi yayi hanzarin kai hannunsa ya rufe fuskarsa shi ala dole yaji kunyar tambayar" Murmushi sameer ya saki ganin yau ya had'u da wani garan yace sai kuma can yace haba d'an ladi meye na rufe fuska kuma kai dai gaya min ko wace zan baka shawarar yadda zata so ka fiye da tunaninka, jin haka tuni d'an ladi ya zare hannunshi yace wai da gaske?eh mana kai de gaya min,turo baki gaba d'an ladi yayi uwa mai shirin surb'ar koko yace bawata bace illa haj...hajj...sai kuma yayi shiru! haba kai kuwa meye haka ka fad'i sunan sosai mana ni ban gane wannan yaren ba, jin hak a kunyace d'an ladi ya nok'e kai ciki-ciki yace ni fa hajjo nake so tun dana ganta d'azu" . Hahahahahahahahaha!wata irin muguwar dariya sameer ya saki wacce shi kansa bai ma san lokacin data kwace masa ba don kid'ima da abinda yaji,ido waje ya zaro yana fad'in wace hajjon?ba dai hajjo ta birni ba?washe baki d'an ladi yayi don jin dad'in yadda sameer yayi saurin gano shi yace alqur'an ka gano ni sarkin wayo!k'ara kecewa sameer yayi da wata muguwar dariya ta k'eta ganin bazai iya dai-daita kansa da dariyar ba yasa shi mik'ewa da sauri ya kamo hannunsa yana fad'in kaga taho muje a siyo maganin,a can ma tattauna komai,ba shiri d'an ladi ya mik'e ya bishi sukai waje! . . Tun bayan shigar beautu d'aki hira kawia suke da baba yagana don abincin ma kasa cinsa tayi don yunwar taci ta har ta cinye,duk da kuwa ta jin zugin jikinta,a tsammaninta su sameer suna zaune a tsakar gida,shiko tsoho na kwance yana bacci tun bayan abincin da baba yagana ta bashi,jin kiran sallah da baba yagana tayi ya sata mik'ewa da sauri tana fad'in yau naga yarinyar kawai duk na biye miki da hira gashi ko abinci ban aje miki balle na baki ruwan wanka,dariya beauty ta saki sannan tace ai dama ba sona kike ba yanzu dai bara nai sallah sai ki bani jagolgolon da kike yiwa tsoho na ci,dariya duka suka saki kafin nan baba ta fita ta barta anan! . Gyalen data yale kanta dashi shi ta cire ta k'ara gyara tukkuwar gashin kanta sosai sannan ta janyo wani k'aramin d'ankwali data gani nan gefen shinfid'ar tsoho ta d'aure kanta dashi ta nufi tsakar gida!wayam taga wajen babu alamar mutum wanda hakan ya tabbatar mata cewa su sameer sun tafi sallah ne!k'aramar tsuka ta saki cike da b'acin rai ta furta d'an masifa kawai mutum kamar maye se shiga harkar mutum gaskiya ya kamata ko ba komai na gaya wa daddy abinda duk yake faruwa tunda nan ummah bata nan balle ta tsawatar min in ma dawowa zai yi gara yayi amma duk mutanen nan biyi sun takura wa rayuwata kamar ni kad'ai ce mutum a duniya?wata tsukar ta k'ara saki cike da cin haushi haka ta nufi bakkin tijiya da zummar kafin tai bacci daren yau zata sanarwa dady duk kan abinda ke wakana bayan tafiyarsa,butar dake gefe sanye da ruwa ta d'auka ta nufi bayi! . _8:00p.m na daren ranar!_ . Ruwa ta watsa beauty ta shigo d'akin baba yagana wanda ke jere da na tsoho,zaune ta isketa saman gado tana k'idayar kud'i, eyyeemba su baba an yi arzik'i irin wannan kud'i ince dai kayan d'aki zaki saya mini dasu?tayi maganar tana yarfe ruwan hannunta,dariya baba yagana ta saki nan ta d'ago kai tace mata toh sarkin son banza wannan ba kud'in tsoho bane balle a jere miki d'aki da kumbo wannan kud'in dashi ne da muke yi jiya aka kawo min d'ibata ko k'idayasu banyi ba don dama na maganin gargajiyar tsoho nake tari sai gashi yaron kirki yazo ya share mana hawayenmu,abinda shekara da shekaru ake magani yau lafiya gobe babu amma kiga jikinsa yau har da cin abinci da shigowa gida da k'afafunsa aiko lafiya ta samu,jinjina kai beauty tayi had'e da tab'e baki ta kauda kanta gefe,tana rayawa azuciyarta"lallai baba baki san wanene shi ba da har kike yabonsa mutum mugu azalumi wanda babu tausayin 'ya mace a zuciyarsa,da har zai mun dukan ajali kusa! . Gafaranku dai masu gida,maganar d'an ladi kenan wacce ta dawo da beauty cikin hayyacinta ta k'arasa shigowa da sauri ta nemi gefen gadon kusa da baba yagana ta zauna! Waige ta shigayi ko ta samu abu ta rufe jikinta don zanin atanfar baba yagana ne d'aure a k'irjinta,sai alokacin ta tuna da akwatin kayanta na motar sameer da suka zo basu fito da kayan su ba haka suka tafi asibiti,bata an kara ba taji an yaye labule sama, cikin rawar jiki,ido na kyarma ta d'ago ido sama me zata gani?d'an ladi rik'e da hannun sameer tsaye a bakin k'ofa!yarda ta matsar da kwayar idonta akan d'an ladi sai gashi ta kasa sauke idonta daga kallon da suke mayarwa da juna ita da sameer!ko wannen su da abinda zuciyarsa ke raya masa,cikin k'arfin hali da mazantaka sameer yayi saurin sunkuyar da kansa gefe tare da jan hannun d'an ladi cikin zafin nama yace fito nan waje musha iska mubarsu ciki!bai jirayi amsar d'an ladi ba sai ganinsa d'an ladi yayi an finciko shi da k'arfin tsiya tsakar gida,inda farin wata ya haske su! . . Duk kan abin nan daya faru akan idon baba yagana dake rik'e da kud'i a hannu ta tsaya da k'idaya tun shigowarsu!juyowa tai sosai ta fuskanci beauty wacce ke zaune kanta a duk'e ta zuba wa zanen ledar tsakar d'akin ido,wanda ita kanta bata san dalilin yin hakan ba taji baba ta dafo kafad'arta! Da yake hankalinta ya d'an gushe zuwa tunani sai ya zamana a tsorace ya d'ago kai ta kalli baba!murmushi mai cike da fassara baba ta saki sannan ta saukw ajiyar zuciya ta kira sunanta!hajara! Beauty ta amsa kanta na k'asa! Allah yasa ayi damu! Me za'ayi daku baba?ido waje ta d'ago kai tana tambayar,jin baba tayi shiru tana dai 'yan murmushin nan nasu na manya da suka san me duniya ke ciki!nan ta ci gaba da magana Allah kuwa baba ki yara da n... bata iya sauke lumfashin ta ba baba ta tsayar da ita ta hanyar nuna ta da yatsa tace kul hajara naji kince wani abu!ki tashi ki shirya ki sallah kawai shi ya fi miki ga kuma tuwonki can rufe a tasa!daga haka baba yagana ta mik'e ta maida kud'inta ma'ajiyarsu tayi waje abinta!


'YAR JAMI'A Part 007 .
Cikin sark'ak'iya tare da b'acin rai haka beauty ta mik'e ta shiga zagayen d'aki kai kawon da take ne ba tare da samun wata mafita ba yasa ta tsagaitawa da zagayen nan ta shiga laluben d'akin,a saman wata ghana most go taga sallaya tare da hijab ai kuwa cikin sauri ta janyota ta zunbula har tana jan k'asa nufo k'ofa tayi da niyyar fita,amma ina tana kaiwa bakin k'ofa sai tai turus ta tsaya jin sautin hirar da suke a tsakar gida shi ya bata raunin gwiwar fita,ta d'an jima nan tsaye sai kuma can dabara ta fad'o mata labulen k'ofar ta janyo ta bud'e shi kad'an ta lek'a kanta ta shiga magana da k'ara tana cewa"d'an ladi ka je mota ka duba jakata na ciki ka d'akko min! . Hira suke sosai abinsu su sameer su kaji kamar daga sama ana magana!jimmn sameer ya d'an yi kad'an kafin nan ya tuna ashe kayansu na mota!d'an ladi ne ya fara cewa murya k'asa"d'an birni kaji wai jakar gimbiya na mota,murmushi sameer ya saki da jin kalmar gimbiya sai kuma yace toh je ka d'akko mata!kallo ya watso masa yace ai kasan ban iya aiki da na'urar bud'e mota ba!auff ashe fa haka ne muje toh,haka suka mik'e sameer na gaba yana biye dashi suka fita ba'a wani jima ba sai gasu da kaya nik'i-nik'i sun shigo,mai makon jakar beauty ta kasance a hannun d'an ladi sai gata a hannun sameer,yana k'ok'arin wucewa d'akin baba da k'aramar jakar sameer don ya kai mata sameer ya tsaida shi yace a'a wannan fa malam tawa ce kai min ita d'akin ka bara na mik'a mata tata!toh kawai d'an ladi yace ya wuce, shi ko sameer ya nufi k'ofa, a bakin k'ofar shima dai ya tsaya amma bai kai ga d'aga labule ba,wanda har lokacin beauty na tsaye wajen sai dai ta saki labulen ta jingina da bango ta ji sautin magana! Tabbas mai hali baya tab'a canja halinsa,a gaskiya dai anyi asarar shekaru,girma ya fad'i,wallahi ina mamakin kasancewarki tsatson wannan dangi na mutunci da girmamawa,sai dai kuma ta wani fannin ba laifi bane don naga haka don ko 'YAR JAMI'A shahararriyar karuwa ce!mai neman maza,wacce bata son kamun kanta ba,wacce take ikirarin kanta da beauty ma'ana kyakykyawa ko?toh Allah dai ya raba mu da kyawun d'an miciji!ameen! Yana kaiwa nan da maganarsa sameer ya wulla mata jakar ciki da k'arfi har ta kai ga buge k'afarta!amma ba yadda ta iya dole ta toshe bakinta da rad'ad'd'in da k'afarta ta bayar lokaci d'aya! Sameer ko daya wurga mata bai zame ko ina ba daga nan sai d'akin d'an ladi,itako beauty abinka da wacce rai bai saba b'aci haka ba komai ace dady sai ya zamana sabon abu a wajenta,haka ta daure ta ja k'afar da tuni dama ta gama tsami don dukan da ta sha da rana a asibiti,ta k'arasa gefen akwatin ta bud'e wata doguwar rigar kalar ruwan toka(ash)dai ta k'ara janyowa ta zura da yake duk dogayen rigunan ta kwaso don tasan halin tsoho sarai tun tana yarinya ba'a shigo masa ita gida da k'ananan kaya! Haka ta kammala shiryawarta tsaf tayi sallah sannan ta ci tuwo,Alhamdullah ta fad'a bayan ta gama cin abincin, duk da ba wani cin kirki tayi masa ba!abinka da ba'a saba ci ba! Tana k'ok'arin hayewa gado ne taji muryar baba yagana tana fad'in toh ina kuma kuke shirin fita haka,ko wacce amsa suka bata sai ji tayi tace toh ku jira ku kai min kifin rijiyata yawo tun zuwanta ba inda ta lek'a, Kafin ta iya wani kwakwkwaran motsi ina har baba ta shigo,yi tayi kamar bata ji shigowarta ba ta ci gaba da hayewa gado,ke meye haka kuma hajara?bacci tun yanzu?ai kuwa baki isa ba tasowa zaki ku tafi,kai baba mu tafi kuma ina? Fuska sake baba yagana tace dandali mana kije kisha kallo in da rabo sai ki sama wa d'an ladi mata daga nan ma! Don naga da alama ruwan ido ya masa yawa!cuskune fuska beauty tayi kamar me shirin kuka tace dan Allah ni dai su je kawai gajiyar hanya tayi min yawa gobe naje ni,had'e girar sama data k'asa baba yagana tayi ta matso saitin kunnenta tace mata kaga ja'irara banza mara wayo,ki shigo da yaro santalele fari sol wannan k'auyen ko kishinsa bakya yi ai ya ci ace duk motsinsa kuna tare,haka d'azu fa ina kallo suka fito ko ki bi su,saurin katseta beauty tayi ta shiga bubbuga k'afa na shagwab'a tana cewa ni wallhi baba yagana ki shiru don tsakaninmu ba dangin iya bana baba kawai had'in ummah ne tace ya rako ni! Janyo ta baba yagana tayi cikin fushi ta tsaya k'em a tsaye sannan tace toh yi maza zura takalmin ki mu wuce,yadda taga baba tayi fuska ba annuri yasa ta tilas ta zuwa suka fito daga d'akin a jere da juna! . A daddafe beauty ke binsu da kallon mamaki, to shin me d'an ladi ya shirya musu haka?kallo takai ga inda su d'an ladin suke nan taga sameer tsaye gefen dama sai wani matashi wanda da alama shine d'an mai garin, a hankali ta k'arasa inda suke badon taso ba haka ta koma gefen sameer ta tsaya don ta tabbatar ta tsaya d'ayan gefen sai ya mayar mata da magana! Tun tsayuwarta a wajen wasa ya fara kad'e-kad'e da wak'e-wake ke tashi sosai,a inda ko wane makad'i ke baje irin nashi basirar a salo na gargajiya,murna da farin ciki sosai kake iya ganowa a fiskokin kowane saurayi dake wajen inda kuwa 'yan mata ke cikin fili suna taka rawa d'an ladi da d'an mai gari sunai musu lik'i,wayarsa sameer ya fitar daga cikin aljihunsa a yayinda ya shiga vedio ya hau yo saboda wannan shne karonsa na farko da yaga abun gargajiya irin haka,sai ya zamana abin ya k'awatar da shi nesa ba kusa ba,beauty dake gefensa tana tsaye jugum tana binsu da kallo sosai ta shagala da kallo bata ankara ba taji an janyo hannunta cikin tsakiyar fili,d'ago kai tayi don taga wacece ai kuwa tayi ido hud'u da wata matashiyar bafulatana fuskarnan cike da fara'arta ta shiga juya mata hannu da nunin su yi rawa,duk da yadda rawa da wak'a suka zama jiki a wajen beauty sai gashi yau ta tsinci kanta da jin kunyar hasali ma duk sai take jin nauyin kasancewarta a filin,haka bafulatanar nan ta ci gaba da juya mata hannu amma sam tak'i yadda ta taka,ganin haka d'an ladi jiki na rawa yayo kanta ya shiga yi mata lik'i,can gefe guda kuma ya hango sameer tsaye sai d'aukar su yake a waya ai da saurinsa ya k'arasa ya kamo hannunshi sameer na kaucewa amma ina sai da ya kawosa cikin fili,kunya ya aje gefe sameer ya kamo hannun d'an ladi suka sha rawarsu suna yiwa juna lik'e,haka dai sukai ta sharholiyarsu a ranar abinda aka jima ba'a yi irinsa a dandalinba,sosai daren ya k'awatu ga kowanne saurayi da budurwa,ba su suka tashi a dandali ba sai 12:30,da haka ne kuma kowa ya kama hanyar gida inda su sameer suma suka nufo gida,beauty kuwa anyi k'awa bafulatana don har k'ofar gida ta rakota anan sukai sallama ta kuma shaida mata sunanta ladiyo! suna shiga kai tsaye d'akin tsoho duka suka wuce,beauty da ge gaba ita ta fara shigewa ciki inda ta iske d'akin cike da mutane har kawo wannan lokacin ga tsoho na kishigid'e gefe yana dariya wanda hakan ya nuna abin dariya akayi,sallamar tace ta katse su don haka suka juyo baki d'aya zuwa ga k'ofa,a d'an razane beauty ta ja da baya sanadin fuskar data gani yana dubanta,jiki na gyarma ta zube k'asa ta shiga gaisuwa,Alhaji ina wuni? Fuska d'aure wanda ta kira da Alhaji ya amsa da lafiya lau! ya wajensu ummantaki? Duk suna lafiya!sannan ta iya gaishe sauran bak'in dake wajen wanda da alamun Alhaji ne da iyalansa suka shigo don dattijuwar mace ke gefensa da matashin yaro!baba yagana ce ta katseta da tambayar ina kika baro mazan kuma? Nan ta amsata da gasu nan tsakar gida tsaye!bata kai ga rufe baki ba Alhaji ya jefota da tambayar ke wane maza kuma?yarda take mutuwar tsoron Alhaji yasa ta kasa basa amsa sai baba ce ta tari numfashinsa da cewa loh ai su d'an ladi ne sai kuma bak'on da suka taho dashi daga birni,bara na kira ku gaisa,nan take ta kwala musu kira suka shigo cikin girmama wa dukkan ninsu suka gaisheshi kafin nan tsoho cikin murya k'asa-k'asa yace sannu dai d'an nan naga magunguna dazu bayan fitarku yagana ta kawo min kuma nasha kamar yadda kayi mata bayani,ubangiji Allah yayi maka tukwici da gida ln aljannah yasa kaima kasamu mai yi maka!d'aki kowa ya amsa da ameen! Alhaji ne ya nemi su tashi su tafi tunda ya zama kamar al'ada duk dare sai sun raba hira a gidan k'anin nasa!haka sukai sallama suka fita har Alhaji ya kai bakin k'ofa ya juyo ya kalli beauty ake zaune manne da bango yace zuwa gobe sai ki shigo da bak'on naki waje na ina nemanku!mutuwar zaune kusan beauty tayi don da an auna jininta awannan lokacin babu shakka ya daskare!tsawa ya doka mata sosai yace baki jini bane, asukwane ta amsa da toh sannan ya fita! Mtsss kai Allah dai ya shirya wannan muguwar zuciyar taka wallahi ace mutum zafi kamar zaki,tsoho yayi maganar yana k'okarin mik'e,da sauri beauty ta taso ta fad'o jikinsa ta shiga rero kuka don tasan yadda ya yink'ura d'in nan wajenta yake son zuwa,babin lallashi da bada hak'uri sabo tsoho ya bud'e inda duk suka zama 'yan kallo a d'akin!can beauty ta tsagaita da kukan ta d'ago kai tana ajiyar zuciya tace wallahi tsoho shiyasa ko ummah tace nazo bana son zuwa kai kana sona amma Alhaji baya sona kullum fad'a se duka!janyota tsoho ya kuma yi ajiki yace yi hak'uri mutuniyar maza ce yagana ta kai ki d'aki kiyi bacci gobe in jiki na ya k'ara sauki zaki sha labarai!murmushi beauty ta sakar masa sannan ta tashi ta bi bayan baba yagana suka fita,inda suma dai su d'an ladi sukai bankwana dashi suka nufi d'akinsu! . _Karfe 07:00 na safe!_ Zaune take beauty ta gama cin karin kumallo kenan bayan wanka data gama,tashi tayi ta janyo wata jar doguwar riga mai ratsin fari a ciki ta saka kayan masha Allah abinka da farar mace sun karb'i jikinta ainun,k'aramin gyalen kayan ta yale kanta dashi kamar yadda ta saba ta shirya tsaf,baba yagana dake kwance saman gadonta na k'arfe tace sai ina kuma?fari beauty tai mata da ido tace sai d'akin tsoho kema dai kinsan wannan kwalliyar tsoho ce!dariya baba yagana ta kwashe da ita sannan tace ja'irar banza kya dai gyara zancen naki,don kin rai nani zaki ce haka mana tunda jiya da murnarki kika dawo daga dandali,toh kar dai ki manta da zuwanku gidan Alhaji,lokaci guda beauty ta d'aure fuska ta juyo ido narke tace dan allah baba yagana ki wani abu akai wallahi ni bana son zuwa don nasan tabbas fad'a kawai zan sha kinsa fa halinsa!fuska baba ta yamutse da jin maganar beauty sannan ta iya cewa toh ni me zance akai bayan kinsan halin kayanki,yanzu dai tsoho bacci yake don tun safe ya ci abinci yasha magani ya kwanta,ki tashi ki yiwa bak'onki jagora ki tafi can gidan tun safe kafin ya fita gona don kinsan ya d'akko zafin gona kanki zai huce!dariya duka suka saka tare sannan beauty ta zari takalmi da jakarta tayi waje! Tsaye take beauty bakin k'ofa ita bata shiga ba kuma bata koma d'aki ba,can dai ta lura tsayuwar nan ba yi mata zatai ba dole ta matso daf da k'ofar ta manne jiki da bango murya k'asa-k'asa tayi sallama,d'an ladi ne ya amsa mata amma da mamaki sai gani tai sameer ya bude labulen k'ofar ya fito,kallo d'aya yayi mata ya kauda kai,ita d'in ma dai kauda kan tayi k'asa tana son gaishe shi amma tana tsoron dizgi,dole ta iya bakinta ganin bata da niyyar magana yasa shi tamke fuska a kasalance yace zaki iya wucewa mu tafi ko?ba tare data tanka masa ba beauty ta shige gaba abinta ta nufi hanyar fita waje,bin ta tayi a baya,haka suka yi ta tafiya da yake safiya ce babu duk jama'a sai harkokinsu suke yi haka har suka isa k'ofar gidan, anan ne kuma ta ta tsaya a tafiyar ta juyo ta kalleshi tace nan ne gidan!wani kallon raini sameer ya fara binta dashi kafin yace in nan ne gidan ni zan shiga nai miki iso ki shiga kome?ta ji haushin kalamin nasa sosai duk da dama tasan bai zama lallai ya bata kyakykyawar amsa ba haka ta saka kai gaba ta shige gidan!kusan minti uku da shigarta sai gashi ta fito tace da sameer wai yace ka shigo! Kallonta kawai yayi ba tare daya ce uffanba, da haka ta fahimci abinda yake nufi ta shige ciki shi ko yabi bayanta! Alhaji na zaune tsakar gida rike da ludayi a hannunsa sai gabansa da kwanon koko ya cika shi taf,a hankali yana surb'ar kayansa yana had'awa da k'osai ya ji sallamar sameer!ludayin hannunsa ya maida cikin kwanon lokaci guda kuma ya shiga gyara babbar rigar dake sanye jikinsa,zama na kamala da manyance Alhaji yayi kafin yayi wa sameee iso daya zauna dama dashi,k'ok'arin zama beauty tayi kafin kace wani abu Alhaji ya da mata wata uwar tsawa ke shige ciki ki baiwa mutane waje, jiki na gyarma haka beauty ta afka cikin d'aki!kallon sameer Alhaji yayi akaro na farko ya sakar masa murmushi inda sameer ya sunkwi da kai cikin jin kunya a ladabce ya gaishe sa,amsa Alhaji yayi da fara'arsa har yanayi masa tayin koko,cikin dariya sameer ya amsa masa daya gode,shiru ya biyo baya na 'yan wasu lokaci sannan Alhaji ya nisa yace yaro ya sunanka?cikin nutsuwa ya amsashi da sameer! Jinjina kai Alhaji yayi na gansuwa da hakan kafin yace toh malam sameer tak'aitaccen tarihin rayuwarka nake son ji,sannan ka sani a hira dani ba'a k'arya don haka sai ka kiyaye,tom sameer ya amsashi sannan ya k'ara gyara zama sosai ya shiga motsa leb'ensa! . Da farko dai sunana Sameer Al-qaseem maji dad'i ni haifaffen garin yola ne mahaifina Alh.Alqaseem maji dad'i ya kasance k'asaitaccen d'an kasuwa a garin yola gashi kuma d'an siyasa,bayan sarautar gado da muke da ita ta maji dad'i da aka nad'a masa,hakan ne yasaka bayan zab'en da akai shekara uku baya muka dawo garin abuja da zama sakamakon zab'arsa a kujerar senator da akayi,mu uku ne a gurin mahaifina,na kasance babba sai k'anne na biyu mata aysah da salaha wanda duk suna zaune yanzu haka da mahaifana a garin abuja suna karatu,ni kuma nayi karatuna tun daga matakin karatu na primary kawo yanzu dana kamala jami'a nake bautar k'asa da nake yanxu a garin kano,gaba d'aya nayi a garin abuja wajen yayan mahaifina Alh.Aliyu maji dad'i da yake shi can yake zaune sai ya zaman to tun tashi na babana ya maidani wajensa saboda Allah bai bawa matarsa haihuwa ba sai dai in anyi hutu naje wajensu!bayan karatu na kuma a b'angaren kasuwancu yayan mahaifina tare muke harkokin company d'insa dani yanzu haka jira yake na gama bautar k'asa d'ina takaddun company daya bud'e min yana nan a garin lagos inda zan fara jan ragamar kula dashi dazarar na gama bautar k'asa! Wannan dai shine tak'aitaccen tarihin rayuwata! Ajiyar zuciya ta gamsuwa da abinda ya fad'a Alhaji yayi,yadda ya lura da tsantsar hankali da nutsuwa irin ta sameer yasa shi umartarshi daya rubuta masa lambar wayar mahaifin nasa dana yayan mahaifinsa a takarda,haka kuwa akayi sameer ya janyo wani k'aramin memo daga aljihunsa na gaba tare da biro ya rubuta masa,karb'a Alhaji yayi ya linke takardar ya zura a aljihu,da haka suka shiga 'yan k'anan hirarsu wacce duk bayanine akan sameer da zuriyarsa! . Duk labarin nan da sameer ke labartawa Alhaji akunnen beauty dake mak'ale baki k'ofa tana jinsu da yake d'akin bak'i ne sai ya zamana babu kowa ciki,shiru ya biyo baya nan take kuma ta shiga nazarin rayuwar sameer da yadda taji tsantsar nasaba da girma irin na gidansu,lallai wannan mutumin mai girma da karamci ne dole ya ki ni da duk wata halayya tawa toh yanzu da ace yana nan akai birthday d'ina inda muka sha rawa da maza a lokacin ai da bansan daga jiya zuwa yau wane irin zagi da tozarta zansha ba!tana cikin wannan tunane taji kamar daga sama Alhaji yana magana,lallai indai wannan itace rayuwarka ka tashi gidan girma da mutuntaka kuma ka dace duk inda kaje kaga abu kuma har ka yaba dashi toh abaka,don haka yanzu inaso ka gaya min gaskiya domin Allah daga saninka da hajara zuwa yau wane irin halayya ka fahimta tattare da ita! K'ululu.....k'arar cikin da sameer ya bayar kenan don shi kam anyi masa tambaya mai matuk'ar tsauri wanda shi kansa bai ma san ta ina zai fara ba inda akan rayuwar beauty ne,a yayinda beauty tuni ta gama daskarewa jikin k'ofa tana jiran shigowar Alhaji tasha duka don tasan yau kam kashinta ya bushe, jin yadda sameer yayi shiru yasa Alhaji k'ara jefo masa tambayar ta wata siga,yace kar ka d'auka na tambayeka haka da wata manufa ne a'a illah dai kawai ya kamata ace kasan wacece hajara sosai don kuwa ni azamana da ita akwai matsananciyar soyayya dana lura a tsakaninta da mahaifinta wanda hakan ya sanya ta sangarta mafi muni,har ya janyo bata ganin kowa da gashi ga shiga mara ma'ana amma zuwansu na k'arshe garin nan na horar da ita mafi k'ololuwa don a lokacin tana gab da fara shigarta jami'a don haka nake rok'onka daka gaya min meke wakana tun yanzu na gyara ta basai tayi aure abin yafi k'arfi na ba!duk da haka shiru sameer yayi don duk wasu k'ofofin kansa ji yayi an gama kulle masa su wai yau shine ake wa tambaya akan beauty haka?kafin yayi wani k'wak'wk'waran motsi suka ji sallama daga waje!tuni sameer ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya don kuwa yasan neman Alhaji akazo yi! Yun k'urawa Alhaji yayi yace ina zuwa daga haka yayi waje!bai jima ba sai gashi ya dawo nan ya nufo sameer ya zauna yace kaga abokin tafiya ta gona wato makwabcina yazo don haka zan baka damarka ka je gida yanzu,bazan d'au lokaci da yawa a gona ba saboda wannan muhimmiyar maganar dazarar na dawo can gidan malam zan nufa sai mu k'arasa maganar tamu! Cike da murnar zuci sameer ya amsa shi da toh Alhaji, Kwalawa beauty kira Alhaji yayi cikin sauri sai kuwa gata ta fito hannu rik'e da takalma don rikita,kallonta yayi yace ki mai dashi gida zuwa anjima zan shigo bai jira cewar taba ya nufi hanyar fita ya fice abinsa bayan daya d'auki kayan aikinsa a gona yayi waje! . Duk da jikinta ya gama bata sameer ita yake kallo a lokacin amma sam ta kasa d'ago kai ta kalleshi balle kwakwakwaran magana, takalmin dake mak'ale a hannunta ta zaro ta saka sannan ta nufi hanyar fita!ba tare da shima ya damu da hakan da tayi ba sameer ya bi bayanta! Shigarsu zauren gidan ne kuma labari ya canja don beauty ta gama fahimtar tabbas sameer zai tona mata asiri dole ya yanke shawarar ta sauke koda kad'an ne daga cikin girman kan da take ji ta nemi gafararsa!don hakan ne kad'ai zai ceceta yau a hannun Alhaji,yanke hukuncinta yayi daidai da tsayuwarta haka kuma sukwane ta juyo har suna kusan cin karo da juna ta tsaya, shima dai tsayawar yayi da sauri ganin yadda jikinsu ke kusan had'uwa yace lafiya dai?? Murya can k'asa beauty ta kira sunansa"ya sameer!! Shiru yayi yana bin ta da wani wulak'an taccen kallo har sai da ta k'ara kiran sunan nasa"ya sameer fa magana nake"anan ne ya iya samun bakin magana ya amsata"ya sameer kuma?yaushe na zama yayanki?ko kuma ince yaushe daddynki ya gaya miki bayan ke ya haifa miki wani d'an uwa sameer? Bata damu da zancen da yake ba haka taci gaba da magana,ya sameer don girman Allah kayi hak'uri da duk wani abu daka sani nayi maka ko kaji labari nayi ma wani wallahi sharrin shaidan ne!!what?? Kinsan kuwa me kike fad'a 'Yar jami'a??shaid'an fa kika ce?yarinya karki kuskura kiyi wa shaid'an k'azafi don kuwa bai miki komai ba!ganin yadda sameer lokaci guda ya tada jijiyoyon goshi yasa beauty sulalewa da gwiwoyi k'asa ta d'ago hannayenta sama tace ba don hali na ba ya sameer don girman mahaliccinka ka taimaka ma rayuwata,wallahi kana son jefa min rayuwata acikin mawuyacin hali! Dariya sosai sameer ya sakar mata har yana sark'ewa,sororo beauty ta bishi da kallo don tasan tabbas hakan zai faru dama!ke malama ki tashi muje ki nuna min hanya na koma gidan tsoho na jira Alhaji acan lokaci na k'ure min!cewar sameer yana gyad'a kai na mugunta!narai beauty ta kuma yi da ido tace haba ya sameer yanzu lokaci kake dubawa ba hatsarin da rayuwata take ciki ba?yanzu ashe yadda kake kiran sunan Allah dama duk a baki ne?ya sameer ka tausaya min mana!ganin yadda beauty ta duk'ufa da rok'onsa yasa shi had'e rai a karo na biyu ya daka mata tsawa"wai ke wace irin mace ce? nace ki tashi muje ko in baza ki ba just tell me sai na nemi mafita ama ba ki tsaya kina min wani zance mara anfani ba! . Ajiyar zuciya beauty ta saki can kuma ta mik'e jiki ba kwari ta kad'e k'asa da ta shafi kayanta ta shiga tafiya,bin ta sameer yayi tayi yana kuma k'ara gane hanya sosai har suka iso,har ta sa kai tana k'ok'arin shiga zaure taji yace ke? Da sauri ta juya kamar dama jira take tace na'am ya sameer!wani irin duka ya kai ma bango a zuciya kafin nan ya d'ago kai da tuni sun rud'e sun ja jur yace ba na ce karki k'ara kirana da ya sameer ba?call me wit my real name sameer don bana karb'ar tuban d'an muzuru,sannan kisani in har kina so asirinki ya rufu sai kin min Alk'awarin zaki sanar min da duk wani labari naki da dalilin da yasa kike wannan mummunan halayyar taki!saurin d'ago kai tayi jiki na b'ari beauty ta amsashi tana nuni da hannu wallahi duk abinda kake son ji zan gaya maka amma ba yau ba sai ana gobe zamu koma kaga yanzu lafiyar tsoho ya kamata mu kula da ita,kai kuma in Alhaji ya kiraka sai kasan abinda zaka gaya masa wannan shine kad'ai alfarmar da za kai min! Kallo mai cike da buk'atar amsa sameer ya jefeta dashi ran nan sam babu alamar annuri haka yasa hannu ya tureta can gefe daya ya shige gida abinsa! . Bai takura mata sameer ba har sai da tayi kukan ma'ishinta don kanta ta tsaya,sannan ta d'ago kai a hankali ta kalle shi,har lokacin sameer kan shi na gareta don haka ya kauda kansa a sanyaye ganin yadda beauty tai narai da ido,murmushin k'arfin hali ta saki mai cike da tambaya sannan ta dai-daita nutsuwarta ta shiga magana,"yau zata zamo rana wacce ban yi tsammanin kasancewarta a rayuwata ba,sai dai ina k'addara ta riga fata,babu yadda na iya dole na bud'e sirrin da bai kamata na bud'e shi ba don kuwa bani da wata mafita,ya sameer kamar yarda kasha kirana da sunan karuwa ban tab'a inkari akan haka ba, don duk wanda yasan hajara da halayya irin tawa dole duk sunan da aka kirani dashi na amsa,sai dai abinda baka sani ba koma ince jama'a basu sani ba game dani shine,wannan d'abi'a dole ta sakani yinta ba don naso ba!don kuwa na samo wannan halin ne" Adalilin principal d'in makarantarmu ta secondary school,da jin haka k'ara gyara zama sameer yayi sosai yana fuskantar ta don jin abinda ta ambata,nan ta ci gaba da magana,eh haka ne magana ta ba k'arya principal d'inmu itace ummul abaisi na duk rayuwar da muka tsinci kanmu aciki,sanin kan kane dai dady bazai sani makaranta mai arha ba,makaranta ta ajin k'arshe wajen tsadar kud'i wanda duk 'ya'yan masau kud'i yawancinsu nan suke yi anan nayi primary don haka bayan na gama na d'ora secondary,anan ne kuma wata rana muna zaune a aji da yake mun zo s.s.s3, bazan tab'a mantawa ba muna karatun geography sai ga discipline master yazo har aji ya kiramu mu uku,jiki na gyarma muka bishi duk mun gama bayarwa dukanmu zaiyi,sai bayan da muka fita ne yake shaida mana cewa principal ke nemanmu,haka ya samu gaba har office d'inta,bayan daya kaimu ne labari ya fara canjawa dayake mace ce principal d'in tana washe baki ganinmu ta shiga zayyana mana buk'atarta ta hanyar wayo da dabara"ta shaida mana cewa yanzu mune ajin k'arshe sannan tasan fatan kowannenmu shiga jami'a nan ta cigaba dacewa ita jami'a ba'a shigarta haka nan sai an shirya haka dai taitayi mana bayani muna ganewa ta kuma shaida mana da tazab'e mu muyi mata wani aiki ne saboda tasan 'yan gidan masu hannu da shuni kamarmu babu zancen takurawa ko matsantawa ta iyaye a tattare damu!bamu gama gane inda ta dosa ba sai da discipline master ya k'ara wayar mana da kai da cewa duk kanmu yana so mu kar muyi applying makaranta d'aya ta yadda zamu cimma burin janyo hanakalin malamai maza,ko wacce d'aliba ta yi k'okarin kawo nata toh darajarta zata k'aru sannan akwai wasu mak'udan milliyoyin kud'i da bayan shekara hud'u za'a bata!jin yadda suke jaddada miliyoyin kud'in anan yasaka kowannen mu amincewa,hakan ya saka bamu tashi a wajen ba duk sai da aka bamu somin tab'i na naira dubu d'ari biyu da hamsin!tare da yarjejeniyar ya zama sirri a tsakaninmu,toh tundaga wannan ranar kullum sai mun je office d'in principal bayan an tashi a makaranta ta k'ara wayar mana da kai yadda zamu janyo hankalin malaman jami'a yayin da muka shiga! Hankalin ummah ya fara tashi in ban manta ba tun daga ranar data fara ganin d'abi'u na da tarbiyyata ta canja duk da dama ba wani tsauri nake samu ba tunda dady na nan kuma baya son b'acin rai na,kullum rigimar daddy da ummah bata wuce akai na,haka har mukayi jarabawar waec da neco amma duk ummah ta lura ba wani karatu nake ba illah dai kad'e-kad'e da wak'e-wak'e da suka zama jikina,ga kud'i da nake kashewa baji ba gani,wasu dady ke bani wasu kuma principal ke turamin ta account tunda duk ta bud'e mana account,wata rana dana karb'o kud'i daga banki ko dana shigo gida na taradda dady a parlo dole nima na zauna,dana tashi mik'ewa ne tsautsayi hannun jakar ya bud'e wasu mak'uden kud'i suka zubo,wato a lakacin ba ummah da dady ba harta ni kai na sai da gaba na ya yanke ya soma gyarma,amma da yake dady baya son ganin laifi na sai yayo sauri mik'ewa ya fara kwasar kud'in ya mayar min jaka sannan ya kamo hannu na mukayi d'akina,turani ciki kawai yayi shi kuma ya wuce nashi d'akin a ranar ne ummah ta fara gaba da ni wai na fara samun kud'i daga waje,wanda ni kuma tun daga lokacin na fahimci ummah bata so na,bata son cigaba na arayuwa daddy ne kad'ai ke so na! . Haka rayuwa ta jin dad'i da daula taci gaba da wanzar min har ya kawo lokacin da na samu admission zuwa jami'a ranar ji nayi tamkar na zama millioner gani nake nesa tazo min kusa,da murna haka na kira na shaida musu,wanda suma murnar sukai tayi min! Tun kafin sati d'aya da fara shigowata jami'a tuni na ziyarci duk wani kanti na kaya,mak'il haka na cika drawers dina kaf da k'ananan kaya,takalma da jakunkuna,duk da naso siyan gyale ko da k'anana ne amma principal ta hanani acewarta zasu rage min kwarjini kuma zasu b'oye min kyaun halitta! Shiru beauty tayi da ta kawo nan a hirarta ta kai hannu fuska,mak'alallen wahayen dake shirin sauka a kuncinta ta goge had'e da jan majina!tsintar kanta tayi beauty ta k'in ci gaba da labarin har sai da ya nemi da taji gaba sannan tayi gyaran murya taci gaba! Tun daga ranar dana shiga jami'a tunani na bai wuce ta wacce hanya zan samu na cimma burina cikin sauk'i ba,sai kuwa gashi na samu malam umar,mutum na hannun dama a b'angaren neman mata da kud'i na iya samo kanshi don na sakar masa kud'i iyakar sakarwa kafin ya had'a file guda na duk wasu sirrika na malaman makarantar ya bani,ita kuma k'awata zee-zee tunda na fahimci 'yar abi yarima asha kid'a ne sai na rik'eta na fara sakar mata kud'i don sune matsalarta duk da agidan ma bata tsiraba,mahaifinta mutumin kirki ne ga kula da hak'k'in iyali amma mahaifiyarta 'yar Allah bamu musamu ce,ita dai a bata kud'i shiyasa kullum cikin samari masu mota take wai a haka baban na sa ido kenan! Ina ganin wannan shine abinda kake son ji ko? Tana tambayar ne tare da maida dubanta ga sameer tana kallo!d'ago kai yayi shima dai ya kallota don abinda yake da muradin ji har kawo yanzu bai jiba nan take kuwa ya fara jefo mata tambayoyi! "Daga shigarki jami'a zuwa yau malamai nawa kika had'ata dasu?kuma ke nawa ne sukai anfani dake? A kid'ime beauty ta zaro ido cike da mamakin tambayarsa ta k'arshe inda shima ya zaro mata nasa da zummar eh amsarta yake jira!tab'e baki beauty ta yi sannan ta kauda kai gefe guda cikin murya can k'asa tace mutum goma na kai mata,ni kuma babu,ban gane babu ba?babu me?sameer ya tambaya! sunkwui da kai sosai beauty tayi don tasan bai zama lallai sameer ya yarda da amsarta ba ta k'ara nanata masa da babu d'a namiji ko d'aya da muka tab'a keb'ewa ko ta minti biyar a wajen makaranta dukkan ninsu a waya muke magana bayan na fahimci yanayin mutum toh sai na bashi address nata,wannan shine silar da ya saka ko wane course bana fad'uwa tun shigata jami'a kawo yanzu! Shima prof KAS da kaga abu ya had'amu na zagaya kuma na zagayo na ga babu wata hanya da zan iya samun makin da nake so dole sai nayi masa abinda nayi masa shiyasa hakan ta faru,bata kai ga rufe baki ba wata tambayar tabiyo baya"toh abincin da kike rabawa na stop and chop shi kuma sadaka ce ko kuwa zakkah?kai duk'e tana kallon k'asa tace shi kuma neman suna ne kawai da son shahara don sun tabbatar min hakan zai saka kowa ya san da zamana a jami'a! . Shi kuma kamal dana ganku tare a mota wancan satin darasi yake koya miki? a'a beauty ta bashi amsa sannan tace shima munje can sau biyu! Wani gauran numfashi sameer ya saki mai cike da tuhuma ta b'angare d'aya kuma yana jin dadin yadda yake kallon gaskiya tsagoronta a idanun beauty !dole ya danne yanayin da yake ciki kwallon hannayensa wanda yake wasa dasu ya watsa mata su cikin zafin nama wanda hakan ya matuk'ar raxanata ta d'ago kai a tsorace ta dubeshi"ta mau fuskar nan babu alamar wasa balle murmushi haka ya shiga binta da wani mugun kallo sai can kuma cikin dakewar murya ya shiga magana yana nuna ta da yatsa"kin cuci kanki wallahi,banza, wawuya, asharariya,wacce bata san ciwon kanta ba balle na wasu shin kina tsammanin da haka zaki samu kud'i da wannan mummunar d'abi'ar,amma dai tur da halin kawaliya mace mai neman maza a gari tana kai wa wata can!kin zama akuya mai komai tq samu ya zama nata!don haka ina so ki sani wannan labarin naki karki tsammani abin so ne a wajena,babu abinda ya haifar miki illar tsantsar k'iyayya a fili wanda in kin lura zaki ganta cikin kwayar idanuna!kuma da kike batun kina samun nasara a jami'a toh ki rubuta ki ajiye wannan semester d'in sai kin samu matsala da course d'ina,don na d'au alwashin haka tun ranar da kika tozarta prof a gabana,kika wulak'anta tsohon da bai ji ba bai gani ba!maganata ta k'arshe a wajenk kuma sak'oni d'an ladi ya bani cewar yana sonki da aure,kuma a matsayina na wanda Alhaji yake ganin girma har yakan zauna muyi wasa da raha na furta masa na bashi ke,sai dai kuma kash ina ji masa takaicin namiji salihi zai auri mace mai hali irin naki wacce take wa kanta kirari da 'yar jami'a! Yanda ya gama lura sameer da k'ofofin kan beauty sun riga da dun gama kullewa da munanen kalaman da yake jefarta dasu ga wasu zafafan hawaye da suka kasa tsayuwa a kumatunta ya sashi mik'ewa a fusace har yana buge k'afarta ta hagu yayi gaba ya barta nan jikin bishi cike da damuwa! . Cike da damuwa tare da danasani haka beauty ta mik'e ta nufi gida cikin mawuyacin hali"shiru ta samu gidan wanda hakan ya tabbatar mata cewa tsoho sun fita da Alhaji zagayen yamma don ya motsa jikinsa, bata zame ko ina ba sai d'akin su d'an ladi a ganinta wannan shine mafi kyawun lokaci daya dace ta yi magana da sameer,sallama biyu tayi amma duk ciki babu wacce ya amsa mata,ga kuma takalmansa a bakin k'ofa wanda hakan ya k'ara tabbatar da ita cewa yana ciki,ba ta damu da jin haka ba sai ma kamo labulen d'akin tayi ta rik'e ita bata shiga ba,ita kuma bata lek'a ciki ba ta fara magana cikin murya k'asa uwa mai rad'a"nasan ya sameer duk abinda ka kira ni dashi wallahi na cancanta amma kayi wa girman Allah wannan magana ta zama sirri tsakanina da kai don idan har sirrina ya tonu a gidan nan wallahi na mutu,nasan dai zuciyarka akwai Allah a ciki,kaji k'aina ya sameer tunda kaga dai ban b'oye maka komai game da ni ba,kai ma ka tausaya min!
follow me on facebook follow me on twitter follow me on instagram

Fitattun labarai

Habiba complete hausa novel

Alqawarin da ciwo

Amfanin cin qafar kaza

Budurwar Roba

Amfanin lemon tsami

Afanin Zogale

Adam A. Zango

Amfanin namijin Goro (bitter kola)

Tona asiri

Yanda zaka duba sunanka a Npower