Karin magana 2

51. Abin Allah! Budurwa da jika.
 
52. Abin Allah, na Annabi ne.
53.Abin aro, ba ya ado.
 
54.Abin aro, bai rufe katara.
 
55. A bin ba zai yiyu ba, auren mage da bera.
 
56. Abin ba'a ne? An ce da kare mai sunan maza.
 
57. Abin banza, hanci ba kafa.
 
58. Abin biki, na biki ne.
 
59. Abin cikin kwai, ya fi kwai dadi.
 
60. Abin da aka gasa, shi ya ga wuta.
 
61. Abin da aka shuka, shi yake tsira.
 
62. Abin da Allah ya yi, Annabi sai ceto.
 
63. Abin da babba ya gani daga zaune, yaro ko ya hau rimi ba zai linkaye shi ba.
 
64. Abin da baki ya daura, hannubai iya kwancewa.
 
65. Abin da dama ta jure, hagun ba ta jure ba.
 
66. Abin da kamar wuya! Gurguwa da aure nesa.
 
67. Abin da ke ga amarya, shi takan ba ango.
 
68. Abin da ke gidan Sarki, akwai shi a kasuwa.

68. Abin da ke gidan Sarki, akwai shi a kasuwa.
 
69. Abin da kunya, uwar 'ya ta cinye suruki ran aure.
 
70. Abin da mutum ya shuka, shizai girba.
 
71. Abin da ruwan zafi ya dafa, in aka hakura ruwan sanyi ma ya dafa.
 
72. Abin da wancan ya ce shi na ce! Kirarin mai tsoro.
 
73. Abin da ya ba ka tsoro, wataran shi zai ba ka tausayi.
 
74. Abin da ya ci Doma, ba ya barin Awai.
 
75. Abin da ya ci ungulu, ba ya barin shaho.
 
76. Abin da ya dami mutum, da shi yake mafarki.
 
77. Abin da ya kewaye gida, gidan zai shiga.
 
78. Abin da ya kora bera wuta, ya fi wutar zafi.
 
79. Abin da ya taba hanci, ido saiya yi ruwa.
 
80.Abin da ya zo, shi ake yayi.

81.Abin daga Allah yake! Matar takaba ta yi ciki.
82.Abin dariya! Yara sun tsinci hakori.
 

83. Abin duniya mene ne? Kaza ta jawo muzuru kwanan gida.
 
84. Abin duniya mene ne? Sarkinfawa da kyautar kaho.
 
85. Abin fada, na mai baki ne.
 
86. Abin majinyaci, na mai magani ne.
 
87. Abin mamaki! Ciyawa da cin doki.
 
88. Abin mamaki! Kare da tallan tsire.
 
89. Abin mamaki! Kurege da fada wa zomo dadin kanzo.
 
90. Abin mutum, abin wasansa.
 
91. Abin na yi ne! An biya wa zawara hajji.
 
92. Abin nema ya samu! Matar falke ta haifi jaki.
 
93. Abin sai ido! Bebiya ta auri makadi.
 
94. Abin shanya, ba a hana rana.
 
95. Abin su na 'yan dangi, bare ina ruwanka?
 
96. Abin tsana! Amarya a kan kare.
 
97. Abin tsoro! Kura a rumbu.
 
98. Abin wani da wuya, nemi naka.
 
99. Abin wani, bai yi wa wani magani.
 
100. Abin ya zo daidai! Mai ido daya ya leka buta.
follow me on facebook follow me on twitter follow me on instagram

Fitattun labarai

Habiba complete hausa novel

Alqawarin da ciwo

Amfanin cin qafar kaza

Budurwar Roba

Amfanin lemon tsami

Afanin Zogale

Adam A. Zango

Amfanin namijin Goro (bitter kola)

Tona asiri

Yanda zaka duba sunanka a Npower