Mijina sirrina 2

*13*
~~~Jan hannunta mama tayi zuwa cikin dakinta suka zauna agefen gado,
"Nadiya idan da wani abu ki fada min saboda bazai yiyu haka kawai babu dalilin komai ki sauya ra'ayinki akan kabeer ba bayan kuma ada babu wanda kikeso kamarsa,
Idan kawayene suke zugaki to ki sani zasu kaiki ne kawai su baroki, idan kuma kuruciyace ke daukarki to kisani zaki cuci kanki wanda bazaki gane hakan ba sai nan gaba zaki fahimci cewar kin yiwa kanki illah domin Allah ya baki dama ya zabar miki miji nagari wanda ya dace dake amma kinki amincewa,
Idan kuma fada kukayi dashi to ki sanar min sai nakirashi naji menene ba'asi daga karshe na daidaitaku domin daga ke har kabeer ni dayane awurina babu banbanci.."
Tunda mama tafara wannan maganar nadiya tafara zubar da hawaye wanda bata san dalili ba, jin mama tayi shiru yasata yin magana cikin kuka,
"Mama nidai kawai yanzu bana sonsa ne wallahi nafasa aurensa.."
"Nadiya kin taba ganin anfasa aure babu dalili? Karfa ki manta yau saura watanni biyu kacal ki kammala karatunki kuma kin sani kina gamawa ko wata daya bazaki kara agidan nan ba za a aurar dake saboda kece kika nuna haka tun farko, tun da fari ke kika nuna aure kikeso idan kin gama secondary har abbanki ya ji ya kuma yarda dan haka yanzu bakida bakin da zakice kin fasa"
Kukan nadiya ne ya karu,
"Mama wallahi nidai nafasa auren yaya kabeer, ni bana sonsa yanzu"
"Ai nadiya ko bakya son kabeer yanzu tunda ada kin soshi dole ki aureshi, idan har abbanki ma yaji wannan maganar to kisani sai ranki ya baci dan haka ina mai shawartarki da kiyi gaggawar watsi da wannan hudubar ta shaidan.."
Mama na kaiwa nan ta mike tayi ficewarta saboda ita atunaninta kawaye nadiya tasamu a makaranta suke hure mata kunne dan haka tayi komawarta kitchen taci gaba da aikinta tabar nadiya nata faman kuka,
Har mama tagama tuwon abba yadawo nadiya na daki tanata faman kuka, sai da abba ya tambayi mama cewar ina nadiya sannan ta tuna ashe tabarta adaki nan ta tashi taje dakin nata tana shiga ta sameta tanata kuka bata daina ba,
"Ke har yanzu kukan kike yi? To kici gaba dayi karki daina". Mama tafada tareda sake fita takoma wajen abba,
Tun daga nan nadiya ta sauya kwata kwata, gaba daya haushin yaya kabeer takeji idanma yazo gidan bata saurararsa har sai idan mama na wurin, ko waya yanzu ta daina yi dashi idanma ya kira bata dauka dama kuma wayar mamace ita bata da waya har yanzu,
Gaba daya abinda ke faruwa Mama tasani amma har yau shi abba bai saniba shima kuma kabeer gidansu basu saniba, yayinda ita kuma nadiya tafara rubuta jarabawar fita domin har sun fara practical,
Lokacin da abba yaga sun fara practical tuni yabada order din gado tun daga kasar Italy, kaya aka kawo shiryayyu kama tun daga kan gado, kujeru, dining table da sauran kayan kawata gida hatta kayan kitchen an siyo, nan hankalin nadiya ya tashi saboda ganin wadannan kayan dan haka ta saka mama agaba tana yimata kuka akan ita wallahi yanzu bata son yaya kabeer karatu zatayi, da abin ya ishi mama sai taje ta fadawa abba tace ga nadiya can tasata agaba tana yimata kuka akan wai bata son aure karatu take so,
Amir abba ya tura ya kirata ta shigo idanuwanta jajur alamun tasha kuka ta koshi,
"Nadiya meyake faruwane? Naji mamanki tace kinzo da sabuwar magana"
"Abba ni yanzu nafasa auren yaya kabeer karatu nakeso"
"Ai nadiya ko agidan mijinki zaki iya yin karatu har kikai matsayin professor dan haka kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki kinji, shi aure baya hana karatu sannan karatu baya hana aure za a iya hada duka biyun, kabeer yayanki ne ba bare bane dan haka bazai cutar dakeba"
"Abba ni kawai auren ne yanzu bana so"
"Nadiya kefa da kanki kika kawo min kabeer kikace shi kikeso nikuma nabashi ke tareda yimasa alkawarin aure sai yanzu kuma yaji na canja magana? Ai aure tsakaninki da kabeer babu fashi, insha Allah kina gama makaranta da sati biyu zan daura miki aure akaiki dakin mijinki kamar yanda nayi alkawari ko bayan raina kar afasa"
Hawayene suka cigaba da ambaliya akan kumatun nadiya nan Abba yace tatashi tatafi, tashi tayi tafita taje taci gaba da kukanta adakinta,
Tsakanin d'a da uwa sai Allah nan itama mama taji hankalinta yatashi dan haka tabi bayan nadiya, adaki ta isketa tana kuka dan haka tazauna akusa da ita ta dafata,
"Nadiya kiyi shiru kinji, ki saurareni kiji abinda zan fada miki, tun farko nadiya kece kikace kabeer kikeso wanda nikuma banso hakanba saboda wasu abubuwa da na hango amma ganin hankalinki ya karkata akansa yasa na amince saboda ki samu abinda kikeso, to yanzu idan muka Mara miki baya muka hanaki auren kabeer duniyace zata zagemu, shi kansa abbanki indan har na goya miki baya zaiga laifina, zaice saboda kabeer ba dangina bane shiyasa nake kin aurenku dashi,
Dan haka ki nutsu kiyi hakuri kibarwa Allah ikonsa kedai kawai kici gaba da addu'a kinji"
Tashi zaune nadiya tayi tafara share hawayen fuskarta tana kallon mama......

*14*
~~~Kallon mama tayi bayan ta share hawayen dake gudana akan fuskarta, sannan ta bude baki dakyar tace,
"Shikenan mama naji nayarda zan auri yaya kabeer kamar yadda kukeso.."
"Ai bamu mukeso ba nadiya, kece kike so bawai auren dole zamuyi miki ba, yau da ace bakece kika fito kika nuna kabeer a matsayin wanda kikeso ki aura ba to da ko yace yana sonki bazan goyi bayan abashi aurenki ba mutukar bakya sonshi, to amma BAKIN ALKALAMI ya bushe dan haka kiyi hakuri ki rungumi kaddara saboda kabeer shine mijinki..."
Jijjiga kai nadiya tayi, "to mama, amma gaskiya yaya kabeer yanada wata dabi'a wacce kowacce macen kirki bazata so mijinta ya kasance haka ba, yaya kabeer shegen son kula yan matanshi yayi masa yawa baya minti biyar sai kinji mace ta kirashi nikuma abin yana bani haushi"
Dafa kafadarta mama tayi tana murmushi,
"Haba nadiya, yanzu dama akan wannan zaki fasa auren kabeer? Ai wannan duk abune mai sauki da zarar kunyi aure duk zai manta da wadannan yan matan suma kuma zasu daina saurararsa su daina kulashi indai sukaji cewar yayi aure, wannan ba komai bane face halayya da dabi'un matasan zamani yawanci haka suke sai kiga wani ma yatara yan mata fiyeda goma kuma kowacce yana ikirarin cewar budurwarsa ce sonta yake.."
Murmushi nadiya tayi na karfin hali, itama Maman murmushi tayi ta mike tsaye amma duk maganganun nan tayi sune kawai saboda ta kwantarwa da 'yarta hankali,
"Ki saki ranki kinji karki sake nuna masa damuwarki ko bacin ranki akan haka, sannan tun daga yanzu ki zama mace mai daukar mijinta a matsayin sirrinta wacce bata fallasa asirin mijinta, ki koyi rufawa miji asiri kinji, bawai komai zaka rinka fada wanda ya shafi mijinka ba, shi aure da kike ganinsa nadiya zallar hakurine acikinsa dole sai ka koyi hakuri ka ji kaki ji kagani kaki gani sannan dole sai ka zama mai kawaici da mantuwa kar kayita tara laifukan da ake yi maka mutukar zakayi haka to bazaku taba zama lafiya da abokin zamanka ba domin koda yaushe mai laifine awurinka.."
"To mama"
Juyawa mama tayi ta fita, tabbas maganganun mama sun saukar mata da nutsuwa da kwanciyar hankali nan da nan ta nemi damuwarta ta rasa nan tafara harkokinta kamar yadda ta saba ta dauko comprehensive book dinta ta bude domin karantawa bayan taje sunci abinci da mama da kannenta,
Waleeda ce ta shigo da gudu tana rikeda wayar mama a kunnenta,
"Yaya kabeer ga anty nadiyan.."
Karbar wayar tayi tana murmushi,
"Yaya KB"
"Ranki ya dade, haka akeyi kuma gaba daya sai kibi ki manta da kabeer dinki? Anya kuwa kinyiwa yayanki halacci?"
"Haba yaya kabeer ni na isa, waneni da mantawa da yayana, mijina sirrina..."
Yanda tayi maganar ne yasashi yin dariya,
"Kajita kamar gaske alhalin kin manta dani asalima fushi kikeyi dani bayan nikuma baki sanar dani laifina ba"
"Yaya kabeer kenan wannan maganar ai tawuce so karma kace zaka tadata.."
Ajiyar zuciya ya saki mai mutukar karfi,
"Wato nadiya nikaina ban san irin son da nake yimiki ba shiyasa da kika juya min baya gaba daya hankalina ya kasa kwanciya.."
"Ayya yaya kabeer ai nace maka yawuce ko"
"Nagode matata, yanzu me kike shirya mana nadangane da hidimar bikinmu?"
"Yaya kabeer ai shiri yana wurinka sai yadda kace.."
"A'a yadda kikace dai gimbiya.."
Murmushi tayi saboda yaushe rabonta da su zauna suyi waya ta minti biyu da yaya kabeer,
"Yanzun me kakeyi ne?"
Kin ganni adakina na tura A'isha taje ta kawo min abinci.."
"Allah sarki gwauro.." Tafada cikin tsokana,
"Gwauraye dai har dake ai ko ke ba gwauruwa bace?"
"Gaskiya ba ita bace.."
"Nima ai ba gwauron bane tunda inada matata nadiya saura lokaci kankani ta zama mallakina nakaita gidana, nakaita dakina...."
Katseshi tayi ta hanyar cewa,
"To ya isa yaya kabeer basai ka lissafa ba"
Dariya yayi, "shikenan tunda kin hanani fadar sirrin zuciyata.."
"Ba hanaka nayi ba amma basai ka fada ba dai, yanzu kabani labarin abinda kake shirya mana na biki"
  Sun dade tare awaya suna tattaunawa har zuwa wani lokaci, koda gari ya waye ma shine yazo ya kaita makaranta domin ranar tanada paper,
Daga nan komai yaci gaba da tafiya yadda akeso domin sun shirya yanzu maganar bikinsu kawai suka saka agaba,
Kamar da yanzun ma koda yaushe kabeer yana kan hanyar zuwa gidansu nadiya,
Ita kuma nadiya yanzu gaba daya kanta ya dauki zafi saboda jarabawar da takeyi gashi gida sai shirye shiryen biki ake tayi mama kullum cikin fita take tana zuwa siyayyar abubuwan da ba asiya ba,
Suma gidansu kabeer din ba abarsu a bayaba wurin shirye shiryen bikin domin har sun kammala hada lefe akwatuna bakwai masu tsananin kyau da tsada,
Saura paper biyu nadiya ta gama jarabawarta aka kai lefenta, sai kawai dawowa tayi daga makaranta ta tarar da kaya makota sun shiga sunata gani,
Mamakine ya kamata saboda yaya kabeer ne fa ya daukota daga makaranta ya kawota gida amma shine bai fada mata ba?
Ai mutane naganinta suka hau guda suna cewa "ga amarya ga amarya.."
Ko takan kayan bata bi ba tawuce daki tana kokarin cire takalminta,
Dakin mama taje ta dauki wayarta ta kira kabeer,
"Yaya kabeer shine ko ka fada min ankawo kayan nan ko? Sai kawai zuwa gida nayi natarar mutane na kallo"
"Yi hakuri mantawa nayi, haba yanmata na ai kin san dai haka kawai bazan ki fada miki ba"
"Shikenan dai nagode"
Katse wayar tayi tatafi taje tayi wanka ta shirya, bata samu damar ganin kayanba sai da dare yayi bayan ankaiwa abba yagani,
Komai da aka saka acikin akwatinan sunyi mata domin babu na banza gaba daya masu tsadane.
Haka aci gaba da shirye shirye shiryen biki, musty abokin yaya kabeer shine babban abokin ango dan haka shine akan komai,
Ayanda angwayen suka tsara za agudanar da kamu da walima sai dinner aranar da aka daura aure bayan ankai amarya dakin mijinta, ita dai nadiya duk abubuwan da suka shirya bata da matsala domin yanzu bikin saura sati biyu saboda yaune zata zana jarabawarta ta karshe,
Kayan taya murna sosai yaya kabeer ya hado mata su greeting card, calendar, memo, key holder, handkerchiefs da sauran kayayyaki tududu wanda har mama sai da tayi masa fada tace shi da hidimar biki take gabansa meya aikeshi wannan aiki,
Aranar da su nadiya suka gama jarabawar tun daga ranar kawayenta yan class dinsu suke zuwa su rakata rabon iv card domin har yaya kabeer ya buga ya basu,
Shirye shiryen da ake gudanarwa agidansu nadiya sai wanda yagani domin gaba daya angyara gidan anyi sabon fenti abba ya zubawa mama sabbin furnitures nadiya nagani ta hau dariya tana cewa,
"Mama Ashe kema kin zama amaryar tunda harda sabbin kaya"
"Ahh nazama kam, gani uwar amarya sannan kuma amarya.."
Kullum musty ne ke kaisu rabon iv card din itada kawayenta har suka kammala nan kuma tafara sintirin zuwa gyaran jiki wurin kawata KHADIJA SIDI domin kwararriyace wurin fito da amare,
Cikin kwana biyu kacal da fara gyaran jikin nadiya tayi kyau tayi sumul fatarta ta sake gyaruwa ta dawo kamar bayan kwado dan tsananin laushi da taushi....

*15*
~~~A daren ranar kabeer yazo gidan, ganin nadiya yayi gaba daya ta sauya masa kamanni saboda tsananin kyawun da fatar jikinta tayi, gyaran jikin ba karamin karbarta yayiba ya fito da ita sosai sai kace balarabiya,
"Yan matana.. Irin wannan kyau haka, ai da ahanya na hadu dake sai kiwuce nawuce domin bazan iya ganeki ba... Wow"
Murmushi nadiya tayi, "kai yaya kabeer harda su tsokana haka"
Sajen dake kewaye afuskarshi ya shafa yana cigaba da kallonta tacikin hasken kwan lantarkin da ya haskesu,
"Allah ba wasa ba kin sauya min gaba daya, kinyi wani irin kyau Wanda ada banma san kina dashiba sai yanzu nagani"
"Ohhh yau dai yaya kabeer tsokana yakeji dan haka bari nayi shiru nabarshi yayi tsokanarsa yagama"
"A'a babu wani tsokana fa"
Dariya tayi ta kalleshi, "yawwa namanta ban fada makaba su zarah maina suna nemanka saboda wai hall din da kukace za ayi dinner acan ba lallai ya isa ba.."
"Jama'ar taku har nawace da bazai isaba? Zai isa harma yayi saura kudai kawai ku zama ready.."
"Shikenan to zamu zama ready din kamar yadda kace"
Murmushi yayi ya dan matsa kusa da ita, "har kin fara kamshin amarcin ne? Naji sai wani rikitaccen kamshine yake faman tashi.."
Juyawa tayi tawuce tana dariya tana fadin "yaya kabeer kaganka ko... Hmmm"
Tun daga wannan ranar basu sake haduwa sunyi mintuna biyar atare ba saboda gaba daya abubuwa sunyiwa kowannensu yawa musamman ma kabeer,
Tun ana saura kwana biyu biki gidansu nadiya yafara cika da yan uwa musamman ma yan uwan mama wadanda suka zo daga kura domin mama haifaffiyar garin kura ce,
Aranar musty yazo yakai su nadiya kunshi da saloon, basu suka dawo gidaba sai dare lokacin har yan jere sun dawo sunata faman koda gidan da irin daular da aka ajiye aciki,ita dai nadiya najinsu batayi koda tari ba saboda dama kabeer ya nuna mata gidan awaya lokacin da yayi yayi da ita suje tagani taki sai ya dauko mata hoton gidan awayarsa yakawo mata tagani, gida kam ya tsaru babu karya kamar a turai domin gidane irin tsarin na turawa.
Saura kwana daya afara shagalin biki mahaifiyar kabeer ta aikowa da nadiya wani kayataccen leshi mai tsadar gaske a dinke tace tasa ranar kamu, ita kam nadiya koda yaushe aranta tana jin cewar tayi sa'ar uwar miji mai sonta da kaunarta,
Ranar kamu ba karamin kyau nadiya tayiba tafito sosai domin wani leshi ne ajikinta golden da gwaggwaro shima golden sai takalmi da jaka,
Nadiya tayi kyau iya kyau nan aka kwashesu zuwa wani hall wanda acan za ayi shagalin kamun, daf da za atashi angwaye suka zo nan kabeer yakasa rufe bakinsa sai fara'a yaketa faman zabgawa yasha wani yadin boyel brown da hula sai kamshine yake tashi ajikinsa, hotuna kam da video sun shasu babu adadi har su kabeer din suka tafi nan taron ya watse kowa ya koma gidansa yayinda su nadiya da sauran dangi sukuma suka koma gida.
  Washe gari da misalin karfe 2 aka daura auren kabeer da nadiya akan sadaki dubu 30 kamar yanda waliyyinsa ya bayar wato mahaifin nadiya, shikuma mahainsa yayiwa nadiya walinci, ana tashi daga wurin daurin aure suka wuce wurin walimar da abokanshi suka shirya masa nan akaje aka debo su nadiya ita da kawayenta,
Yau dinma nadiya ba karamin kyau tayiba cikin wani jan leshi gashi an lullube jikinta gaba daya da lifayya wadda daga ganin adon dake jikinta kasan naira tayi kuka,
Wa'azi aka gudanar awurin walimar sannan akaci aka sha, ango shima ba abarshi abaya ba wurin zuba kyau domin wata lafiyayyar farar shadda yasha wadda taji dinki mai tsada,
Karfe hudu aka tashi daga walimar aka maida su nadiya gida, suna zuwa gida suka tarar da har anfara harhada kayan da za akai nadiya dasu domin abba yace ana yin sallar mangariba aje akaita,
Ai kuwa nadiya najin haka sai kuka nan mama tazo ta kama hannunta suka nufi falon abba,
Nan suka zauna tanata gursheken kuka,
"Nadiya kiyi hakuri kidaina kuka kinji domin kowacce mace hakace take faruwa da ita arayuwarta mutukar wannan ranar tazo, nidai abinda zance miki shine kiyi hakuri kibi mijinki sau da kafa kiyi masa biyayya,ki zama mace tagari mai rufa asirin mijinta, ina miki addu'ar Allah yabaki rayuwa mai dadi agidan mijinki yasa ta silarshi ki shiga aljanna, Allah yayi miki albarka"
"Amin amin, sannan kuma banda kazanta nadiya, banda rashin kunya, banda biye makota ana gulma, banda tona asirin miji, duk abinda yasaki kiyi abinda ya hanaki ki hanu, Allah yayi miki albarka yabaki yaya nagari" mama ta dora bayan abba yagama, nan mama ta kamata ta maidata inda ta daukota, da kuka da komai nadiya tasamu tayi wanka ta fito ta shirya lokacin har yan daukar amarya sunzo dan haka babu bata lokaci aka fita da ita aka saka a mota aka nufi gidan mijinta da ita lokacin ba afi karfe 7 nadare ba,
Suna zuwa kuma aka fara shirye shiryen tafiya dinner, angama shiryata kenan ango ya shigo cikin wani sky blue din yadi marar kauri, itama kuma dama shigar blue tayi nan suka bada kala,
Sai faman murmushi yake yimata amma ita duk idonta yayi ja saboda kukan da tasha gwanin ban tausayi, hannunta ya kama suka fita yana yimata magana ahankali,
"Menene yasaki kuka yanmata na? Ko kukan rabuwa dasu mamane? Kiyi hakuri kinji ai baku rabuba zaki rinka zuwar musu.."
Ita nadiya dai bata yi magana ba saboda tasan tana bude bakinta to fashewa da kuka zatayi dan haka taja bakinta tayi shiru,
Iya kawatuwa wurin dinner din ya kawatu yasha decoration  blue colour,nan aka fara gudanar da abinda za ayi gadan gadan,
Daga nadiya har kabeer sunsha ruwan nairori wasu ma masu yimusu likin ita nadiya ba saninsu tayiba kawai dai tasan gayyar kabeer ce musamman ma wasu yanmata wadanda suka daddage sunata zubar musu da ruwan nairori,
Karfe 12 aka tashi daga dinner din aka kwashi mutane zuwa gida, nadiya ita da kawayenta suna motar musty shine yakaisu gida yana zuwa yace kawayen su fito zai mayar dasu gidansu nan suka yi masa caaaah wai bazasu tafiba sai anbasu kudin siyan baki, cheque din 20,000 ya rubuta musu yabasu sannan suka yarda suka hakura suka fito bayan sun gama tsokanar nadiya wacce ke lullube ta tukunkune agefen gado tana risgar kuka...

*16*
~~~Sai da akayi kamar mintuna ishirin da tafiyarsu zarah maina tafara jiyo karar mota alamun yaya kabeer ya karaso gidan,
Sake gyara mayafinta tayi ta lulluba tana sauraren shigowarsa minti kadan kuwa sai gashi ya shigo hannuwansa dauke da ledoji manya guda biyu,
Ajiye ledodin yayi ya karasa wurinda take ya zauna akusa da ita yana murmushi,
"Yanmata nah.."
Shiru nadiya tayi takasa ko motsi ganin haka yasashi dagota zuwa jikinsa,
"Kidaina kukan haka kinji? Maza tashi kije kiyi alwala kizo muyi salla"
Batayi musuba ta mike taje ta shiga toilet din dake cikin dakin tayi alwala tafito tazo ta iskeshi yana jiranta nan yajasu salla sukayi sallar nafila raka'a biyu kamar yadda sunnah ta koyar,
Ledodin da ya shigo dasu yajawo ya bude ya fito da gasasshiyar kaza da snacks da drinks masu mutukar sanyi, "yan matana jeki kitchen ki dauko mana flate da wuka da cups.."
"Yaya kabeer ban san inda kitchen din yakeba.."
Jin abinda tace yasashi murmushi ya tashi dakansa yaje ya dauko yadawo ya zauna,
"Ga kaza zoki ci kinji yanmata na"
Duk da cewar nadiya najin yunwa sosai amma sai taji bazata iya cin kazar ba saboda kunyarshi dan haka ta jijjiga kai cikin dashewar murya tace,
"Nakoshi.."
Jan kazar yayi gabansa ya zage yafara cin abarsa batare da ya sake magana ba nan nadiya ta sake jin daci aranta saboda halin ko in kular da ya nuna mata,
Tana kallonsa yagama cin kazar ya dauki juice yasha ya mike,
"To tashi muje ki kwanta.."
Tashi tayi yabi bayanta zuwa kan lafiyayyen Italian bed din da aka kafa mata acikin dakin.
***
  K'arfe 8 nasafe nadiya ta farka duk jikinta sai faman yimata ciwo yake saboda gajiyar biki wacce ta hadar mata da gajiyar da yaya kabeer ya tara mata adaren jiya,
Dubashi tayi amma baya cikin dakin nan ta yunkura dakyar ta sauka daga kan gadon ta shiga toilet tasamu tayi wanka ta fito in banda yunwa babu abinda takeji nan tayi salla ta shirya ta zauna tayi tagumi tana jiran dawowarsa amma shiru babu alamunsa,
Ganin har karfe goma da rabi tayi bai dawoba gashi tana jin rsananin yunwa yasata tashi taje ta dauko guntun snacks din da ya bari adaren jiya tafara ci tana ci tana hawaye saboda bakin cikin rashin ganin yaya kabeer,
Ita abinda yasata kuka ma shine yasan irin yanayin da yatafi ya barta aciki maimakon ya tsaya ya tarairayeta yabata kulawa ya taimaka mata ya nuna mata soyayya kamar yadda kowacce amarya take samu daga angonta washe garin ranar da aka kaita amma ita yayi tafiyarsa yabarta bata samu wannan kulawar ba,
Sannan ko acikin littattafan da take karantawa tana jin irin zumudin da angwaye keyi tareda nunawa amarensu soyayya amma ita sam bata samu haka ba, da kuka tagama cin snacks din ta tashi tafita tana tafiya dakyar, gidan tabi ta ga yanda aka tsarashi dan kyau kam gida yayi kyau sai dai fatan Allah yasa tasamu farin ciki mai dorewa acikinsa,
Ganin dagaske yaya kabeer baya cikin gidan yasata komawa falo ta zauna zuciyarta nata tunanin inda yatafi, "kodai abinci yatafi siyo mana?"
Nan ta zauna ita kadai har yan gidansu suka zo su waleeda da yan uwan mama, ananne ta dan sake taji dadi ana jimawa kuma sai ga yan gidansu yaya kabeer dauke da kulolin abinci,mintuna kadan sai ga kawayenta suma nan taji tasamu saukin damuwar dake addabar zuciyarta,
Gidanta cika yayi sosai da mutane nan kawayenta suka sata ta sake yin wanka tasha kwalliya domin yan unguwa sai shigowa ganin amarya suke yi,
Wuni guda cur babu kabeer babu alamunsa sannan ko waya bai yimata ba dadi daya taji shine kawayenta da kannenta har dare suka kai agidan sai daf da sallar isha sannan suka tafi, nan kuma tsoro ya tisata agaba sa'arta daya ma da akwai wuta,
Atsorace taci gaba da zama acikin gidan har karfe 9 nadare sai lokacin taji karar mota alamun dawowar yaya kabeer....

*17*
  
~~~Tashi tsaye tayi ta karasa bakin kofar falon domin taroshi amma koda taje sai tayi turus saboda ganin irin kallon da yayi mata,
"Yaya kabeer sannu da zuwa.." Tace dashi jikinta asanyaye,
"Yawwa..." Shine kawai abinda yace yabi ta gefenta yawuce batare da yasake koda kallonta ba,
Tamkar gunki haka nadiya ta zama sai ido da tabishi dashi,
Abubuwa biyune suke daure mata kai ahalin yanzu, nafarko fitar sassafen da yayi ko tashi bai bari tayiba sannan tunda ya fita bai dawo gidanba sai yanzu, sannan yanzun ma da yadawo babu fara'a babu magana mai dadi kenan da saninsa yatafi ya barta yayi biris da ita ko waya bai yimata yaji yanda ta wuni ba tunda yafi kowa sanin acikin yanayin da yatafi ya barta,
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un..." Shine kawai abinda ta iya furtawa taje kan kujera ta zauna hawaye nata faman ambaliya akan kumatunta,
Tunani daya takeyi Allah yasa ba irin wannan mummunan zaman zasuyi ita da yaya kabeer ba, burinta daya Allah yasa bazai sauya mata daga yaya kabeer dinta mai sonta mai kaunarta mai damuwa da ita akoda yaushe ba,
Kukan zuci taci gaba dayi har na tsawon wani lokaci nan ta tashi ta bishi cikin daki ga mamakinta akwance ta sameshi yanata faman daddanna wayarsa wadda da alama chaten yakeyi,
A dan nesa dashi ta zauna tana kallonsa,
"Yaya kabeer lafiya kuwa yau ka tashi tun sassafe ka fita baka dawoba sai yanzu..?"
"Lafiya lau" ya amsa mata atakaice,
Dan shiru tayi nawani lokaci sannan tasake magana,
"Yaya kabeer ga abinci can nakawo maka?"
"Ke dan Allah ki kyaleni idan ina jin yunwar ai zan fada miki haba, ke wacce irin yarinyace kin tisani agaba sai surutu kike yimin? Kin tambayeni ina natafi dasafe kinzo kuma kina sake yimin nonsense question.."
Binsa da kallo kawai nadiya ta tsaya yi saboda yadda ya fututtuke yana balbala masifa kamar wacce ta watsa masa wuta, ko a mafarki akace mata yaya kabeer zaiyi haka bazata taba amincewa ba amma sai gashi azahiri tagani,
"Allah yabaka hakuri yaya kabeer.." Tafada idonta cikeda kwalla,
Tashi tayi tawuce taje ta dauki zani ta shiga bathroom tayi wanka ta fito tazo ta shirya tasaka kayan bacci ta kwanta,
Bata san iya adadin lokacin da ya kwashe yana chaten dinsa ba.
  Yauma kamar jiya haka tasake tashi da ciwon jiki, jikinta duk yayi tsami amma koda ta duba gefenta sai taga wayam babu yaya kabeer babu alamunsa,
Zama tayi akan gadon tana tunani, to wannan wacce irin rayuwace? Dama haka auren yake? Miji sam bazai zauna agidansa tare da matarsa ba,
Nan da nan hawaye suka fara zubowa daga idanuwanta ita sai yanzu tagane dalilin mama da kullum idan tatashi yimata fada akan aure take cemata tayi hakuri domin gaba daya auren babu komai acikinsa face hakuri to dama wannan hakurin ne?
Share hawayenta tayi ta tashi ta dingisa zuwa cikin toilet tayi wanka tafito tayi salla ta shirya ta fita falo gidan babu komai na abinci sai ko danye sannan gas dinma ba aduro ba gashi babu kalanzir idan risho tace zata kunna, in banda yunwa babu abinda takeji,
Tana zaune afalo taga an kawo wuta nan taje ta jona electric cooker ta dora indomie ta dafa ta zo falo ta zauna taci tana gamawa ta tashi ta gyara gidan tasake yin wanka,
Tana daki tana kwalliya taji sallamar yan gidansu nan tafita cikeda murna domin su waleeda ne da sauran yan biki sukazo yimata sallama saboda ayau zasu tafi,
Ba karamin dadi tajiba nan ta hanasu waleeda tafiya tace sai yamma tayi hakane saboda tana son ta ragewa kanta zaman kadaicin da zata yi, daidai lokacin sallar azahar suma kannen kabeer suka zo gidan, nan suka zo mata da abinci wainar shinkafa da miyar agushi wai inji mama,ita dai nadiya tasan tayi sa'ar uwar miji amma abisa dukkan alamu batayi sa'ar mijiba,
Nan suka wuni dasu fati da su husna kannenta sai mangariba sannan suka tafi ai kuwa suna tafiya ta shiga damuwa domin gidan tsitttt yake sai ita kadai kwal kamar mayya.
Yauma kamar Jiya yaya kabeer bashi yadawo gidan ba sai da misalin karfe 10:30 lokacin nadiya har bacci ya dauketa akan kujera tana zaune ta kifa kanta akan hannun Kujerar da take kai....

*18*
~~~Sai da yafi minti 20 da dawowa sannan nadiya tafarka nan tsoro ya sake kamata domin duk a zatonta bai dawoba amma kuma tana jiyo kamar motsi acikin dakinta,
Tashi tayi tanufi hanyar dakin tana magana "waye..?"
Shiru taji dan haka ta sadada ta shiga, tana shiga taga yaya kabeer ne yake tsane jikinsa yafito daga wanka,
"Yaya kabeer kaine kadawo ashe.. ?"
"Nine" yabata amsa, sanin yanda suka yi jiya yasata yin shiru bata sake magana ba, nan itama taje tayi wankan ta shirya ta kwanta,
Tunani ne ya mamaye zuciyarta saboda gaba daya yaya kabeer ya bata mamaki bata taba tsammanin cewar irin wannan rayuwar zasuyi dashiba, ita a zatonta irin rayuwar soyayyar da ake rubutawa acikin littafi zasuyi ashe abin ba haka bane sai yanzu tagane cewar rayuwar datake karantawa a littafi tasha banban da abinda ke faruwa azahiri amma ita bata fahimci hakanba sai yanzu,
Da wadannan tunanin bacci yayi awun gaba da ita, kasancewar tasamu tayi isasshen bacci yasata tashi da wuri domin ta riga kabeer tashi, Salla tayi ta zauna tana karatun alqur'ani har yaya kabeer din yatashi,
Gaisheshi tayi bayan ya idar da salla nan yace ta dora masa ruwan zafi tace babu gas kuma babu kalanzir,
Fita yayi can sai gashi da gas din da kayan tea yazo ya ajiye mata nan taje ta kunna wuta ta dafa masa ruwan zafin sannan ta dafa ruwan tea, wanka yayi ya fito yasha tea din akaro nafarko da yaci wani abu agidan,
Yana kammalawa ya kada rigarsa yafita bai sake waiwayar gidanba hatta kayan miya sai aike yayo mata,
Jalop din taliya da shinkafa tayi ta zuba a food flaks ta ajiye taje tayi wanka, tana fitowa taji wayarta na kara nan taga mamace murna sosai ta shiga yi ta dauka suka gaisa nan mama ta harhadata dasu waleeda dasu amir suka gaisa sai da suka gama gaisawa da kowa sannan mama takoma gefe,
"Nadiya ai babu matsalar komai ko? Naji tunda aka kaiki baki kiraniba sannan baki kira abbanki ba"
"Ehh mama wallahi wayar tawace babu kudi.."
Dan dam mama tayi sannan tace "to shikenan, ina kabeer din ko ya fita?"
"Ehh ya fita mama"
"To shikenan, ayita hakuri dai nadiya, zaman aure dan hakurine Allah yabaku zaman lafiya"
"Amin mama" nadiya tafada tana hawaye domin ita yanzu sai take jin cewar rayuwar gidansu tafi ta gidanta dadi domin da agidane da tuni yanzu tana can cikin kannenta yan uwanta suna wasa da dariya wani lokacin ma harda mama da abba acikin wasan amma nan gashi tazo rayuwarta atakure,
Sai da suka jima da mama suna hira sannan sukayi sallama ta ajiye wayar tazauna agefen gado tasha kukanta ta koshi ta share hawayenta tasoma shiryawa lokacin ba afi karfe 2 narana ba, tana gab da kammala shirinta taji karar shigowar text nan ta dauka ta duba tana budewa taga mamace ta turo mata katin waya har na dubu daya,
"Allah sarki mama.." Tafada idonta cikeda kwalla,
Falo ta koma bayan tayi salla tajona kayan kallo ta kunna tafara kallon wata tasha, tunowa da tayi cewar tana karantawa acikin littattafai tana jin irin yanda mata ke kulawa da mazajensu yasata daukar wayarta ta kira yaya kabeer,
Kamar bazai dauka ba sai kuma taji ya daga,
"Hello nadiya.."
Jin ya ambaci sunanta yasanya ta mamaki domin ada yanmatana yake kiranta amma yanzu tadawo nadiya,
"Yaya kabeer kana inane?"
"Ban gane ina inaba, sai kace wani yaronki zaki wani tambayeni ina ina? Menene? Me zanyi miki?"
Jikinta ne yafara rawa saboda jin masifar da yake yimata,
"Babu komai dama dai bugowa nayi inji lafiyarka.."
Bai sake bata amsaba ya katse wayar Kitttt,
Har lokacin da ya kashe wayar jikinta rawa yake domin fada yake yimata bil hakki da gaskiya,
Tagumi tayi tana rike da wayar tagagara koda motsi tana tunanin yanda yaya kabeer ya zama ahalin yanzu.
Wuni tayi acikin damuwa abincin ma bata iya ciba saboda ita kadaice masu zuwar matan ma yau babu wanda ya lekota dan haka tawuni sukuku har dare sai wurin karfe goma yaya kabeer ya dawo,
Sannu da zuwa tayi masa taje ta kinkimo abincin data dafa ta kawo masa,
"Yaya kabeer ga abincin.."
"Ke kinci?"
"A'a kai nake jira.."
"To danme zaki jirani? Agidanku mahaifiyarki tare kikaga sunaci da mahaifinki? Nace agidanku haka akeyi? Karki sake wani jirana akan abinci, idan kin dafa kayanki kici kawai basai kin jiraniba kin gane?"
Tsallake abincin yayi ya wucewarsa zuwa cikin daki yabarta sakare tana hawaye, jan abincin tayi ta dan tsakura a flate tafara ci tana hawaye har ta gama.
  Washe gari da sassafe yace taje ta dafa masa ruwan wanka zai fita, nan ta shiga kitchen ta dauki ashana kenan ta hango wani murgujejen bera nan ta yarda ashanar tayi daki da gudu domin tana tsananin tsoron bera,
"Menene?"
"Yaya kabeer bera ne acikin kitchen din.."
"Akan beran zaki fasa dafa min ruwan wanka? Ke wacce irin sakarya ce marar sanin abinda ya kamata? Look kinga nifa bazan dauki wannan sakarcin na banza da wofiba..."
Bathroom ya shige ya doko kofar yanata bala'i, falo ta koma ta zauna, tana zaune ya fito cikin shirinsa nafita yasaka kai yafice bai ko kalleta ba.........


*19*
~~~Bin bayanshi da kallo tayi sannan cikin damuwa tace,
"Adawo lafiya"
Bai amsata ba ya karasa ficewa, haka nadiya ta zabga tagumi tana tunanin makomar rayuwarta.
  Cikin wannan hali suka yi sati biyu koda yaushe idan kabeer yasa kafa yabar gidan da safe baya dawowa sai karfe 10 nadare, tunda akayi bikinsu basu taba zama da nadiya sunyi hira na minti daya ba, sai dai idan har fad'a zaiyi mata,
Koda yaushe ita kuma tana kokarin nuna kulawarta agareshi domin tana yimasa waya taji yanda ya wuni wani lokacin ya dauka yana tsaki wani lokacin kuma yaki dauka,
Tana zaune taci kwalliya amma gani daya zaka yimata kasan cewar akwai abinda yake damunta yaya kabeer ya shigo, lokacin karfe 5 na yamma,
Abinci ta kawo masa ya zauna ya danci ya tashi ya shiga cikin daki, wayarsa da yabari afalon ne tasoma kara nan nadiya ta dauka da niyyar kai mishi ai kuwa sai gashi ya fito, fautar wayar yayi yafara yimata fada,
"Uban waye yasaki ki daukar min waya? Danme zaki taba min waya? Karki kuskura nasake ganinki kin taba min wayata..."
Yana gamawa yawuce fuuhhhhh yakoma daki mintuna kadan yazo yawuceta yabar gidan daga nan bai sake dawowaba sai 11 nadare.
  Haka rayuwar nadiya da yaya kabeer ta kasance koda yaushe babu dadi, tsakaninta dashi babu kulawa, babu magana mai dadi, babu tausasawa, babu nuna soyayya babu komai, kullum cikin yimata fada yake, idan ta kirashi awaya ya hauta da fada idan bataci abinciba ta jirashi yazo yayita fada da haka har suka debe watanni biyu da bikinsu, mai karatu acikin watanni biyun nan nadiya bata da wani labari mai dadi wanda zata bayar dangane da rayuwar aure, ko kadan bata san dadin aureba sai sabanin haka,
Kasancewar bata cikin kwanciyar hankali yasata ta rame ta kanjale domin kullum cikin kuka da damuwa take, lokacin da takai kimanin watanni uku babu kadan mama tazo mata,
Tsayawa mama kawai tayi tana kallonta saboda ganin irin yanda ta rame ta zabge, ita mama da atunaninta zata zo ta iske nadiya tayi kiba ta hada jiki amma sai taga sabanin haka sai dai batayi magana ba domin tayi zaton ko dai har nadiyan tasoma laulayi ne,
Nan mama ta kusan wuni agidan amma abin mamaki harta taho bata ga kabeer ya koma ba,duk sai bata kawo komai aranta ba saboda tasan irin soyayyar dake tsakanin kabeer din da nadiya.
  Acikin satin da mama tazo itama maman su yaya kabeer tazo taga gida, sosai mamanshi keson nadiya domin har kayan makulashe ta kawo mata irinsu alawar madara, gullisuwa, tsami gaye,yashin madina, hanjin ligidi da sauransu haka ta kawo matasu cikin leda viva,bata jima dayawa ba tatafi,
Tun daga nan nadiya bata sake ganin kowa nagida ba sai dai mamanta kullum tana kiranta su gaisa da ita sannan ta hadata da kannenta su gaisa haka kuma duk satin duniya sai mama ta turo mata kati na dubu daya ko na 750 dama shi yaya kabeer babu ruwanshi da batun wayarta ko wani abin bukatarta kullum da safe da zarar ya kada rigarsa yafita sai dare.
  Haka nadiya taci gaba da zaman hakuri zaman da babu komai acikinsa face damuwa da bacin rai har ta debe watanni shida lokacin dai ya kaita gidansu sau daya haka itama yakaita tagaida mamanta sau daya daga nan sai dai su waleeda suzo mata a weekend su wuni shiyasa har burin zuwan weekend take domin abba yana kawo mata su, duk ranar da suka zo wuni take cikin farin ciki shiyasa bata barinsu su tafi sai dare yayi.
Cikin wannan yanayi nadiya tafara amai wanda abisa dukkan alamu na laulayin cikine, kabeer ko ajikinsa babu abinda ya dameshi,
Lokacin ma da ya shigo ya isketa tana aman kallonta yayi yace,
"Ke cikine dake ko?"
Daga nan bai sake magana ba yayi tafiyarsa yawuce ciki yabarta tana faman kwarara amai,
Satinta biyu tana zazzabi atafe daga karshe zazzabin ya kwantar da ita, nan ya dauketa yakaita asibiti likita yana dubata yace cikine da ita na wata biyu, ga mamakinta sai taga yana murna harda bawa likita tukwici, daga nan ya daukota suka dawo gida bayan ya biya ta kasuwa ya siyo mata fruits su lemo da ayaba da makamantansu,
Tunda suka dawo gida kuma yarage fada da masifar da yake yimata yafara dan kula da ita, komai tace tana so baya k'i shiyasa lokaci kankani tayi kyau tayi kiba saboda hankalinta ya dan fara kwanciya,
Yanzu abu dayane ke damunta shine wayar da yaya kabeer ya tsiri yi acikin kowanne dare, koda yaushe ta bude idonta sai tajiyoshi yana waya, kusan kwana yake yana yin waya da wadda bata san ko wacece ba, bayaga haka kuma ko wacce safiya ta Allah sai yafita da sassafe yana tafiya inda bata san ko inaneba,
Wannan dalilinne yasa yau ta daura aniyar tambayarshi inda yake zuwa, tana kwance afalo ya shigo lokacin misalin karfe 9 nasafe, akusa da ita ya zauna nan ta yunkura ta tashi dakyar,
"Yaya kabeer wai ina kake zuwa da sassafe ne?"
"Nadiya shamsiyya nake zuwa nake kaiwa makaranta, baki Santa ba ko? Yar kanwar mamace to shine aka kawota gidanmu dan tayi karatu.."
"Amma yaya kabeer fisabilillahi sai kaine zaka rinka kaita makarantar? Kullum fa da karfe 6 kake fita, haba dan Allah, gaskiya nidai wannan abun yana bata min rai.."
Mikewa yayi yashiga cikin daki baiyi magana ba, nan ran nadiya ya baci domin tagane cewar tsakaninsa da shamsiyyan akwai wani abu, tana ganinsa yazo ya sake fita bayan yayi shirin office,
Tagumi ta zabga tayi shiru, wayarta ce ta soma kara nan ta dauka taga bakuwar number ce,
"Assalamu akaikum"
Daga daya bangaren aka amsa sallamarta tana jin muryarsa ta ganeshi ba kowa bane face yaya Kamal dan gidan wan mama wanda suke zaune agarin tofa....

*20*
~~~Nan suka fara gaisawa cikeda zumudi domin rabonta dashi tun tana JSS lokacin da yake zuwa gidansu hutu, Allah ya hada jininta dashi sosai,
Hirace ta barke tsakaninsu nan yafara tambayarta ya rayuwar auren nasu, tsakaninta da yaya kamal babu boye boye sannan ayanda take jin zuciyarta sam bazata ji sauki ba har sai ta amayar da abinda ke cikin zuciyarta dan haka ta fara zayyane masa damuwarta tun daga washe garin ranar da aka kawota har yau,
Hakuri kamal yafara bata cikeda tausayinta,
"Nadiya kiyi hakuri, ki dauki Dangana sannan kisani komai na duniya mai wucewa ne sannan babu abinda yake dawwama a duniya,
Dadi baya taba dawwama haka shima wuya da damuwa basa dawwama,
Farin ciki baya dawwama kamar yanda bakin ciki baya taba dawwama,
Kisakawa ranki cewar ibada kike yi domin zaman aure ibadane haka kuma abayan kowanne tsanani to da akwai sauki haka alqur'ani ya sanar damu,
Kiyi hakuri kici gaba da yiwa mijinki biyayya karki gaji sannan karki daina,
Kidauka cewar bautar Allah kikeyi sannan aljanna kike nema kin san kuwa samun aljanna ba abune mai sauki ba dole sai ansha wahala sai anshiga damuwa,
Haka kuma kamar yadda baki taba fadawa kowa ba saini to kiyi hakuri kisake daurewa karki fadawa kowa wannan maganar domin sirrinki ne keda mijinki ta shafa kinji..?"
"Naji yaya kamal.."
Nan yaci gaba da bata shawarwari akalla sai da suka shafe awanni yana yimata nasiha gamida bata hakuri tareda tausar zuciyarta akan taci gaba da jurewa gamida hakuri,
Ko ba komai taji dadin shawarwarin da yaya kamal yabata tareda bada hakuri domin idan abu yana damunka kasamu wanda ka fadawa har yabaka hakuri dadi kakeji koda bai baka komai ba.
  Nan taci gaba da rainon cikin da yake tareda ita shikuma kabeer bai fasa halinshi na daka sammako ya fita da sassafe ba wai shamsiyya yar uwarsa yake kaiwa makaranta sannan ga wayar dare da ya kware akanta kamar gwauro marar iyali,
Juyi nadiya tayi nan tajiyo muryarsa kasa kasa afalo yana maganganu ahankali wanda daga ji wayar tasa yake yi, yunkurawa tayi ta tashi dakyar ta fita falon nan ta hangoshi akwance cikin kujera kamar ba dareba sai wayarsa yake,
"Yaya kabeer..."
Juyowa yayi tareda katse wayar yana cewa "i will call you back latter..."
Tashi yayi yana kallon nadiya,tamkar zai hauta da duka haka yayi yabude babin masifa,
"Menene? Acikin tsohon daren nan zakizo kina kirana, me zanyi miki? Ba tambayarki nakeba, nace uban me zanyi miki, wannan wanne irin rashin mutunci ne, da rana ba abar mutum ya hutaba haka da daddare ma baza abarshi ya hutaba.."
"Haba yaya kabeer, yanzu me yayi zafi da zaka fara fada da daddaren nan, ni idan nice na bata maka rai kayi hakuri, gani nayi abinda kake yi bai daceba sannan bai kamata ba, ya za ayi ni ka baroni acikin daki sannan kazo nan ka zauna kana waya, idan wayarka zakayi ai sai kayi da rana tun kana waje amma bawai sai kadawo cikin gida..."
Katseta yayi cikin wata irin tsawa,
"Ke karki kuskura kiyi min iyayi kin gane ko,kece ma zaki tsara min yanda zan rinka gudanar da rayuwata?, saboda gaki uwata ko? To bari kiji.."
Bai karasa ba yaga ta rike cikinta tareda faduwa akasa nan da nan yaga tafara murkususu jini yana bin kafafuwanta, iya tashi hankalinsa kam ya tashi domin yana mutukar son cikin dake jikinta nan yaji ya shiga rudu,
Dakyar ya iya kokarin daukarta yakaita cikin mota yanufi asibiti da ita wanda yake can gaba dasu kadan,
Cikin wani daki aka sata nan likitoci suka yi cahhhh akanta suna dubata daga karshe dai sunaji suna gani babu yanda zasu iya cikin dake jikinta ya zube,
Kabeer yayi mutukar bakin ciki lokacin da yaji cewar cikin ya zube, nan ya zauna acikin asibitin har gari ya waye sannan ya tafi gidansu yaje ya sanarwa da mamanshi, hankali tashe mama ta bishi zuwa asibitin bayan tasaka A'isha ta hadowa nadiya tea da sauran kayan karyawa,
Tunda mamanshi taje itace take kula da nadiya domin tana mutukar sonta ko kadan bata son damuwarta shiyasa kullum cikin yimata hidima take, karfe 8 daidai yaje ya dauko A'isha da shamsiyya zuwa asibitin ita nadiya sai yau taga shamsiyyan ma domin akomai tasan tayiwa shamsiyyan nisa amma da yake namiji ba dan goyo bane shine yaya kabeer yake neman fifita shamsiyyan akanta,
Nan sukayi mata sannu mama ta taimaka mata ta tashi ta hada mata tea sannan ga farfesun kayan ciki da soyayyen kwai ta bata taci takoma ta kwanta, sai da wurin karfe 11 sannan yaje gidansu nadiya yafada nan mama ta rude ta shirya tatafi asibitin amma da taje sai taji hankalinta ya kwanta saboda tasamu maman kabeer na kula da nadiya,ita nadiyan ma lokacin bacci takeyi, nan su mama suka shiga gaisawa tareda jajantawa juna.
Kwanan nadiya takwas a asibitin aka sallameta bayan anyi mata wankin ciki nan Maman kabeer tace maman nadiya tatafi da ita Gida tunda likitoci sunce ta dan samu hutu banda aikin wahala, ita abinda yasa bazata tafi da nadiya gidanta ba tasan idan sunje bazata sake kamar gidansu ba amma idan gidansu ne zatafi sakewa,
Nan mama ta yarda suka tafi da nadiya bayan sun biya ta gidanta sunje sun daukar mata kayan sawarta, komawar nadiya gida ba karamin kwanciyar hankali ta samuba domin cikin sati biyu tayi kiba tayi kyau jikinta ya dawo saboda mamanta tana mutukar kula da ita sannan babu abinda takeyi daga kallo sai ko taci abinci ta kwanta, gashi yanzu babu damuwa babu bacin rai bp dinta ma da yahau ya sauka, babu abinda takeyi ko mama tagani tana aiki idan tace zata tayata sai taki, sai dai ta zauna tayita kallo idan kuma su husna sun dawo daga makaranta suyita hira suna sata dariya domin suna nan har yanzu da halinsu na sa'insa, idan yamma tayi kuma abba yadawo to bazai shigo haka ba sai ya tahowa da nadiya wani abu na kwadayi, yana dawowa kuma zasu tattara su koma falonsa hatta abinci tare za ahadu aci, ana ci ana hira shiyasa nadiya ta kwammace gara rayuwar gida sau dubu data gidan aurenta.
  Yaya kabeer ma yana zuwa dubata lokaci zuwa lokaci sannan yana kawo mata abubuwan bukata, har nadiya ta Karaci zamanta agidansu tafara shirin komawa gidanta bata taba fadawa mama matsalarta ba ko kuma damuwarta ba duk da tasan tana cikin damuwa sannan babu wanda yafi cancanta da jin damuwarta sama da mahaiifiyarta amma bata taba sanar da mama ba, tasan ita babu wani jin dadi ko farin ciki kwaya daya da zata iya fada wanda tasamu agidan aure to ina dadin ma yake auren dako amarci ba asamu anyiba matsalolin rayuwa suka taru suka yimasa illa,
Watanta biyu agidansu sannan takoma gidan yaya kabeer bayan abba ya bata kudi har dubu hamsin yasaka mata acikin account yace idan tana da damuwa sai ta dauka tayi amfani dashi,
Tunda ta koma gidan yaya kabeer yasamu abinda yayi missing shikenan suka dawo yar gidan jiya, baya zama agida idan yafita tun safe sai dare, baya zama suyi hira da ita to bai zauna agidan bama bare suyi hirar, wayar cikin dare, fita sassafe kai shamsiyya makaranta, ita dai nadiya kawai zaman hakuri take nan tasake rarramewa, damma dai yaya kamal dan uwanta yana kiranta awaya koda yaushe yana kwantar mata da hankali, da haka kwanaki masu yawa suka shude nan tasake samun wani cikin tafara laulayi ganin haka yasa yaya kabeer fara bata yar kulawa saboda cikin da yake jikinta,
Kamar wancan lokacin yanzun ma tayi kiba tayi kyau saboda hankalinta ya dan kwanta, sannan kuma fitar da yakeyi sassafe zuwa kai shamsiyya makaranta ahalin yanzu yadaina wayar tsakar daren ce dai har yanzu yanayi,
Daga mamanta har Maman shi kowacce na taka muhimmiyar rawa wurin ganin sun bata kulawa domin kullum cikin yimata aiken kayan dadi suke, haka kawai zataga mamanshi ta aiko A'isha kanwarshi ta kawo mata abun kwadayi, ko kuma taga Amira kanwarta mama ta aikota, yanzu bata da damuwa sosai saboda shima yaya kabeer din yarage masifar da yake yimatay,nan hankalinta ya kwanta tayi kyau sosai kowa yaganta yanzu yasan tasamu kwanciyar hankali sabanin da.
  Cikinta yagirma ya shiga wata bakwai sannan yayi kato kamar wadda zata haifi yaya hudu, karfe biyu da rabi na dare ta farka tana jin yunwa da kishin ruwa dama tunda cikin yafara girma take tashin dare cin abinci da shan ruwa, yaya kabeer tajiyo afalo yana aikin wayar tasa ta dare kamar yadda ya saba, nan ta yunkura dakyar ta fita falon ranta idan yayi dubu ya baci take zufa ta rufeta jininta yahau mutuka saboda dama ta dade da kamuwa da hawan jini nan hawan jinin ya tashi jikinta yahau rawa,
"Yaya kabeer..."
Takira sunanshi cikin radadin ciwo, saurin tashi yayi ya katse wayar amma kafin yakarasa wurinta har ta sulale ta yanke jiki tafadi cikin daukewar numfashi.......


*21*
~~~Arude yaje inda take yafara jijjigata yana kiran sunanta,
"Nadiya, nadiya, nadiya.."
Jin bata amsaba sannan da alama bata yin numfashi yasashi cikin sauri ya mike ya fita arude domin dauko ruwan sanyi saboda abisa dukkan alamu suma tayi,
Bude idonta tayi tabishi da kallo domin dama suman karya tayi masa saboda taga alamun idan har batayi masa hakaba bazai daina wannan mummunar dabi'ar ta wayar dareba,
Tana jin alamun tahowarsa tayi saurin rufe idanuwanta tareda dauke numfashinta,yana zuwa ya kwara mata ruwan sanyi nan ta saki ajiyar zuciya da karfi ta bude idanuwanta cikin alamun galabaita,
"Nadiya ko zamu tafi asibiti..?"
Kai ta girgiza masa tana kallon duk yanda yabi ya rude domin ko kadan baya son ya sake rasa cikin dake jikinta,
"Bani abinci naci yunwa nakeji"
Cikin hanzari ya tashi yaje ya kawo mata ta karba ta fara ci, tun daga wannan lokacin tasamu yadaina yin wayar dare sannan zuwa kai shamsiyya makaranta ma da yakeyi yanzu yadaina saboda baya son asake samun matsala kamar yanda aka samu a wancan cikin,
Cikin kankanin lokaci nadiya tayi kyau tasake yin kiba saboda yanzu bata da matsalar komai kabeer yana kula da ita haka mahaifiyarsa itama tana iya bakin kokarinta wurin faranta mata rai.
  Har cikin nadiya ya shiga watan haihuwa kabeer bai sake yimata wani abu wanda zataji daci acikin ranta ba domin yana mutukar son cikin dake jikinta,
Cikin dare nakuda ta kamata nan yashiga firgici ya kinkimeta suka tafi asibiti gaba daya yakasa samun nutsuwa yayi nan yayi can har aka samu ta haifi yaranta yan tagwaye mace da namiji, murna awurin kabeer abin ba acewa komai, kasa tafiya yayi sai acikin mota ya kwana, gari yana wayewa kuwa yaje yakaiwa su mama labari kafin kace wani abu tuni har asibiti ya dinke da yan uwa yan gidansu da yan gidansu nadiya, jariran tubarkalla bul bul dasu kyawawa domin yaya kabeer shima ba baya bane awurin kyau haka nadiya,
Kwanansu biyu a asibiti aka sallamesu suka koma gida, kayan da kabeer ya hado shida mahaifiyarsa abin ba amagana domin sun jibgowa mai jego ita da jariranta kaya na kece reni,
Abban kabeer da abban nadiya tare  suka zo ganin jariran anan suke tambayar kabeer sunan da zai sawa yaran yace sunan mahaifiyarsu abban zaisa da sunan mahaifinsu wato usman da Habiba nan su abba suka yita sawa yaran albarka dasu kabeer din,
Adaki yasamu nadiya ya fada mata yanda sukayi dasu abba nan itama tabada goyon baya tace sai su rinka kiran yaran da nabeel macen kuma nabeela,
Shagali iya shagali kabeer yayishi awannan haihuwar, komai da nadiya ke bukata itada yaranta ya tanadar musu, ranar suna aka nadawa yara sunan Habiba da usman,
A washe garin suna kuma aka tafi da nadiya gida domin mamanta ta kula da ita tunda haihuwar farice sannan yara biyu,
Tunda ta koma gida ta sake samun kwanciyar hankali, yaya kabeer yana zuwa kusan kullum yana ganinsu ita da yaranta dahaka har suka yi watanni biyu agida a lokacin ne abba yace zaman ya isa haka ya kamata su koma gida nan nadiya ta hada komai nata ta shirya kabeer yazo ya dauketa suka tafi.
  Komawarta gidanta nan ma babu wani bacin rai ko tashin hankali zamansu suke yi da kabeer lafiya babu wata matsala, dan uwanta kamal kuma kullum cikin kiranta awaya yake yana tambayarta yanayin zamansu da kabeer kullum hakuri da nasiha yake yimata yana nuna mata cewar shi zaman aure ibadane dan haka dole akwai jarrabawa acikinsa.
  Kwantar da hankalinta tayi taci gaba da kulawa da yaranta har suka yi watanni a lokacinne kuma kabeer ya bijiro mata da maganar kara aure.....


*22*
~~~Tashin hankali sosai nadiya ta shiga lokacin da taji cewar yaya kabeer zai kara aure nan kuma tabi tafara ramewa amma mamanta da yaya kamal koda yaushe cikin kwantar mata da hankali suke suna cewa ai babu komai tadaina damuwa,
Cikin dan takaitaccen lokaci ya hada kaya ya kai gidansu yarinyar nan manya suka shiga ciki yaci gaba da zuwa wurinta suna soyayya, sunan yarinyar munnira tana zaune acan wata unguwa wai ita hammaga,
Daurewa nadiya tayi ta kwantar da hankalinta ta yakice tunanin abin aranta ta rungumi yaranta fadeel da fadeela wanda ahalin yanzu sun soma girma,
Neman aurensa yaya kabeer yasa agaba amma kuma dayake munnira ba matarsa bace sai ta kwanta rashin lafiya mai tsawo har Allah ya karbi ranta nan yabarwa gidansu kayan da ya kai mata yace bazai karba,
Daga nan kuma haka rayuwa taci gaba da juyawa har yasake haduwa da wata budurwa mai suna kareemat itama kuma da gaske yake sonta bada wasaba,
Koda ya sanar da nadiya hankalinta ba karamin tashi yayiba domin bata san wacce irin mace zai auro ba saboda tana tsoron sake shiga damuwa kamar lokacin baya,
Neman aure dagaske yaya kabeer yake yinsa domin baya son adauki dogon lokaci ba ayiba wannan dalilinne ma yasashi tura magabatansa da wuri,
Nan da nan yafara gyaran gida sannan yafara kokarin hada kayan lefe ita dai nadiya tana zaune tana ganin ikon Allah amma tayi kokarin boye masa damuwarta,
Lokacin da yagama gyara gidansa tsaf sai ya hadowa nadiya kayan fadar kishiya akwatuna uku ya iyo mata cikeda kaya ya kawo,
Sai da yafara kaiwa mamansa tagani nan taketa fada saboda ita sam bata son yayiwa nadiya kishiya saboda bataga laifin yarinyar ba yarinya mai hakuri da biyayya da ganin girman nagaba,
Haka ya debo kayan ya kawowa nadiya tana kitchen tana aiki,
"Ga kaya can nakawo miki.."
Jin abinda yafada yasata ajiye aikin da take tabi bayansa zuwa falonta nan taga akwatuna masu kyau sabbi dal guda uku, duk da cewar kayan ciki masu tsadane sannan sunada mutukar kyau hakan bai hana hankalinta tashiba,
Zama tayi ta bude kayan tafara gani tana jin wani irin bacin rai acikin ranta tamkar zata fashe da kuka amma sai ta daure ta boye damuwarta tafara yaken dole,
"Naga kaya kam kuma sunyi sosai ubangiji Allah yasaka da alkhairi yasa ayi a sa'a"
Tace dashi tana kokarin hada kayan wuri guda, "amin" yabata amsa yana dauke dasu fadeel,tun da taga kayan kuma sai ta shiga damuwa hankalinta ya tashi nan takira yaya kamal ta fada masa yayita bata hakuri, maman kabeer dinma har gida tazo ta rarrasheta tabata hakuri tace ta kwantar da hankalinta koda ace kabeer ya kara aure to bazata wulakanta ba.
Hakurin tayi ta dauki dangana ta zubawa sarautar Allah ido ta zauna tana jiran ranar da zataji yace ta shirya tazo aje akai kaya amma kuma shiru daga karshe ma sai yazo yace yafasa auren,
Duk da cewar lokacin da yace zaiyi aure hankalinta ya tashi to yanzunma da yace ya fasa hankalin nata ba kwanciya yayiba saboda tasan bazata taba fita awurin mutane ba za aga kamar itace take hanashi auren.
Amma koda ta zauna tayi tunani cewar Allah yasan gaskiya kuma yasan zuciyarta sai kawai ta share abin yadaina damunta nan ta kwantar da hankalinta babu daukar dogon lokaci tayi kiba ta murmure, haka taci gaba da zama tana mutukar kyautatawa yaya kabeer musamman ma yanzu data samu ta yaye su nabeel dan haka ta zage damtse tana kyautatawa mijinta.
Shima yaya kabeer din yanzu babu laifi ya dan sauko yana dawowa gida akan lokaci sannan yana zuwa yaci abinci da rana kuma lokaci zuwa lokaci yana kiranta awaya yaji lafiyarta ita da yara kafin ya dawo gida,
Harkokinsa kuwa koda yaushe sai samuwa suke suna sake budewa domin yanzu yatara kudi wanda shi kansa bai zaci zai mallaki irinsu ba dan haka ya fada harkar business nan yafara fita kasashen waje yana shigo da kaya ko wanne iri na amfanin yau da gobe kafin wani lokacin har yaya kabeer ya zama young millionaire,
Nadiya kam koda yaushe cikin kyautata masa take musamman ma yanzu da taga ya nannemi aure amma Allah bai shirya za ayiba, ita dinma yanzu tayi fes da ita tayi kyau, duk lokacin da yafita saro kaya kasar waje yana kaiwa kamar wata daya acan koma fiyeda haka shiyasa take dauko su Amira su tayata zama kafin ya dawo.
  Haka rayuwar taci gaba da tafiya har tsawon wani lokaci, nadiya nazaune cikin kwanciyar hankali uwar mijinta da danginsa na mutukar sonta ko kadan basa son laifinta, yaranta har sun dan tasa domin yanzu shekararsu biyu da rabi.
  Acikin yawace yawacen da yaya kabeer keyi na fita kasashen waje kwatsam ya hadu da wata Mata ma'aikaciyar gidan wani radio,asalinta yar garin jos ce amma saboda tsabar bariki haka tafito daga gidan iyayenta ta gina gidanta ta tare tana duniyancinta sannan tana fita waje ta ziyarci duk kasar da takeso alokacin data gadama,
Ganin yaya kabeer yasata rudewa nan ta nufeshi tana kwarkwasa tana faman jujjuya jikinta, kamshin turaren da ta saka kuwa kamar zaiyi magana,
Farrr tayi masa da idonta ta kalleshi tana yauki,
"Sunana asabe mc..."
Dagowa yaya kabeer yayi ya kalleta.....

    _Gaisuwa da fatan alkhairi ga dunbin masoya wannan littafin ina gaisheku aduk inda kuke._

  *23*
~~~Cikin yauki da kwarkwasa gamida jan hankali asabe mc tasake magana,
"Haba handsome ya naji Kayi shiru bakace komai ba? Kodai banyi maka bane?
Gaskiya amma idan har kaki kulani bazan ji dadiba.."
Sake kallonta kabeer yayi yana mai kallon irin shigar dake jikinta,
Wani material ne mai shegen kyau gashi daga gani mai tsadane kalar light blue yasha dinkin doguwar riga wadda ta tsaru tamkar yar kanti, ta yane kanta da dan siririn mayafi fari idonta sanye cikin farin face,
"Har yanzu dai banji kace komai ba.."
Dan yake kabeer yayi domin shi ko kadan bai taba ganinta ba sai yau, yau dinma yanzu,
"Gaskiya ka hadu, duk macen data sameka tayi saaaa'a"
Yanda taja maganar daga karshe yasa kabeer zuba mata idanuwanshi yana dan miskilin murmushi,
"Kema kina da kyau ai..." Yafada yana fadada murmushinsa,
"Well.. Tunda har ka yaba dani mai zai hana muyi exchanging contacts so kaga sai mu rinka gaisawa.."
Kabeer baiyi musuba ya bata phone number dinshi ya karbi tata daga nan suka rabu kowa ya nufi wurinda zaije,
Lokacin da yagama harkokinsa zai dawo gida tsaraba ya tulowa su fadeel da nadiya kamar gaske,
Ya dawo ya iskesu lafiya nan kuma yaci gaba da kula dasu, satinshi biyu da dawowa Nigeria yana office a zaune yana aiki wayarshi tasoma ringing yana dubawa yaga asabe mc ce,
"Ranka yadade..."
Yaji muryarta bayan ya daga wayar,
"Yakike..?"
"Ranka yadade kuma haka akeyi daga ranar nan ban sake jinka ba nayi jiran nayi jiran har nagaji naji bazan jureba shine nace bari ni na kiraka na gaisheka"
"To nagode asabe.."
"No ka rinka kirana da mc shine daidai"
"To mc shikenan sai kin jini"
Katse wayar yayi yana murmushi wanda bai san dalilinsa ba,
Haka da yakoma gida ma da daddare sai da asabe mc ta kirashi sannan kuma ta turo masa da wani cool massage,
Tun daga wannan rana take kiransa akalla takan kirashi fiyeda sau biyar arana shiyasa tun baya kiranta har shima yafara kiranta yana mayar mata da reply din text massages din da take turo masa,
Tsawon watanni biyu zuwa uku suka dauka suna waya amma nadiya ko kadan bata taba saniba, wata ranar juma'a kabeer ya kira asabe mc suka gaisa anan ta kashe murya ta marerece tace,
"Gaskiya handsome ya kamata nazo har garinku naganka domin wallahi ina son sake ganin kyakkyawar fuskarka.."
"A'a ai bakece zakizo ba asabe nine yakamata nazo kuma insha Allah zanzo.."
"Yaushe? Karfa kahanani zuwa kai kuma kaki zuwar min.."
"Zanzo, kibari zan sanar dake idan natashi zuwa"
"To ina cikin garin kano dai duk lokacin da zakazo ka sanar dani.."
Sallama sukayi tun daga wannan lokacin kusan koda yaushe asabe bata da magana sai ta tambayar kabeer yaushe zaije wurinta, ganin tanata damunshi akan yaje yasashi shiryawa yayiwa nadiya sallama cewar zaije cikin kano amma bai sanar da ita abinda zaije yiba,
Sabuwar motarshi ya dauka wacce batafi 2 weeks da zuwa ba ya tafi bayan yasha kyau da kwalliya cikin wani sky blue din yadi mai tsada, sai da ya shiga cikin garin kano sannan ya kira asabe mc ya tambayeta unguwar da take nan ta sanar dashi tareda yimasa kwatancen gidan,
Cikin dan takaitaccen lokaci ya samu gidan ya karasa, gidane safe contact mai parts dayawa kusan duk kawayen asaben ne agidan kowacce da part dinta sannan idan tayi bako sai ta saukeshi anan kawai dai gidan yan barikine,
Lokacin da yashiga gidan da wata farar budurwa yafara cin karo tana brush abakin barandar part dinta daga ita sai gajeren wando da yar karamar vest, nan ya dauke idonsa yana jin kamar yakoma kada yashiga amma sai dai sam yakasa komawar haka ya kutsa kai yawuce domin dakin asabe mc shine na biyun karshe,
Wata budurwa yasake gani sun fito itada wani saurayinta suna kokarin rufe kofa nan ya kawar dakai yawuce zuwa sashen asabe,
Sai da yayi knocking sannan ya bude kofar ya shiga nan wani rantsatten kamshin turare wanda bai taba jin irinsa ba ya bugi kofofin hancinsa.....
follow me on facebook follow me on twitter follow me on instagram

Fitattun labarai

Habiba complete hausa novel

Alqawarin da ciwo

Amfanin cin qafar kaza

Budurwar Roba

Amfanin lemon tsami

Afanin Zogale

Adam A. Zango

Amfanin namijin Goro (bitter kola)

Tona asiri

Yanda zaka duba sunanka a Npower