Karin magana 5

  • Tsohon doki ya fi sabon takalmi
  • Mu gamu a ka, jakin kuturu ya shiga tofa
  • maganar wofi, zakara ya taka wuka 

  • Masoyin kwa’do ba na kifi ba ne.
  • Wanda za a kashe don an karairaya shi ba kome.
  • Kowa ya yi maka kan kara, ka yi masa na itace.
  • Da kunne ya ji, da jiki ya tsira.

  • Kome tsawon hannun mutum ba ya cude bayansa.
  • Mai ido daya ba ya gode Allah sai ya ga makafo.
  • Hakurin kaya sai jaki.

  • Tsattsagar hakori ta kan kawo jini.
  • Ganin gida kare ya kan zagi kura amma ba a daji ba.
  • Kowane mutum a dakinsa yaro ne.

  • Hakorin dariya shi ya kan yi cizo.
  • Abin da baki ya daura hannu ba shi kwancewa
  • Wanda bai gode wa Allah ba, ya gode wa azabarsa.
  • Allah na taimakon wanda ya taimaka kansa.
  • Ba a aron bakin mutum a ci masa albasa.

  • Akwiya ta yi wayo da yankekken kunne.
  • Talaka ba aboki, ko ka so shi, ran biki ka ki shi.
  • Matsiyaci abokin sarki.
  • Duk nisan jifa, kasa zai dawo 

  • Abokin cin mushe ba a ɓoye masa wuƙa.
  • Da babu gwanda ba dadi, sarki akan jaki 
  • A yi, a gamma, ta fi takamma, gobe a koma

  • Hakin da ka raina shi kan tsole maka ido.
  • Ruwa ba ya tsami banza
  • Kada gammo ya birkice mai dammi
  • Idan gamba tana da dadi a nono, nono ma yana da dadi a wuri'n gamba

  • Aboki barawo, barawo ne
  • Ba na fassa randa'n daki ba, na waje ba ta shigga ba.
  • Idan dei a chini ba a seyer ba, kaza ta fi doki.
  • A buggi karfe da saura'n zafi, in ya fuche sai a wahalla
  • In rana ta fito tafin hannu ba ya kare ta.
  • barkar mu da Sallah

  • soyyaya gamuwar jini
  • mhm inji matar barawo
  • mummunan kare sai cizo ba haushi
  • gindin banza matar gardi ta haifi allo

  • garin masoyi ba ya nisa
  • daga gani sai kai ya kumbura
  • ba na fiye ki ba an che da karuwa "hawo gado"
  • azaba miya ba daddawa
  • abin na yi ne an biya wa bazawara hajji
  • araha maganin mai wayo
  • mai karambani shi yake biyan bashin kakarsa
  • dabara ta fi karfi
  • ba a hada gudu da susar duwawu

  • bari kula da samun dangi
  • saurin fishi shi ya keh kawo da-na-sani
  • so hana ganin laifi
  • Dama dama kibiya a ido 
  • da jini a tsoka saidai rashin tsagawa 
  • duniya ba ta auren rago

  • zama da madaukin kanwa shi ya ke kawo farin kai
  • sai bango ya tsage kadangare ke samun wurin shiga
  • idon da ya ga sarki ba yatsoron galadima
  • gani ba chi ba neh

  • ashin sani makaho ya taka sarki
  • mukami bebe da rediyo
  • rijiya ta ba da ruwa guga ya hana
  • bakinsa, ba kamar tsuliyarsa ba.
follow me on facebook follow me on twitter follow me on instagram

Fitattun labarai

Habiba complete hausa novel

Alqawarin da ciwo

Amfanin cin qafar kaza

Budurwar Roba

Amfanin lemon tsami

Afanin Zogale

Adam A. Zango

Amfanin namijin Goro (bitter kola)

Tona asiri

Yanda zaka duba sunanka a Npower