Matsalolin ma'aurata

#Matsala #1
#Dacewa
Babbar matsala ta farko da ake samu a Rayuwar Aure shine idan ya kasance ka auri macen da bata dace da kai saboda daya daga cikin wadannan dalilai:
1. Macen da aka aura maka ita ba dan tana sonka ba, sai san anfi qarfinta a gidansu.
2. Macen da ka aura wacce ka tabbata dan abin duniya (kudi, suna, sarauta dss) ta aure ka.
3. Macen da kaima ba dan soyayya ka aure ta ba sai dan sha’awa, kyawunta, dangantakarta dss
4. Macen da kake tunanin ta aure ka ne kawai saboda bata da wani zabin.
5. Macen da bata gama yin hankali ba.
Wadannan da ma sauran dalilai da yawa wanda sukan kawo rashin dacewa tsakanin ma’aura suna kawo babbar matsala a Rayuwar Aure, wanda yawanci sai bayan anyi auren ake gane haka, lokacin da an riga an makara da ayi wani gyara akai. Saboda haka ina kira garemu ‘Yan Mata da Samari mu daure mu yaqi zuciyoyinmu mu auri masoyan da muka tabbatar zabin zuciyoyinmu ne kuma sun dace damu domin samun ingantacciyar Rayuwar Aure!
#Halayen Boye
Samari da ‘yan mata kowa yana iya qoqarinsa wajen ganin ya nunawa masoyinsa halin kirki a lokacin neman aure. Daga cikin matsalolin da ake samu a cikin Rayuwar Aure musamman a farko-farkonta shine a lokacin da ma’auratan suka fara gane halayen juna na gaskiya, wadanda a lokacin da zumar soyayya take dibarsu basu san dashi ba, hakan yakan kawo canji ga irin girma da mutuncin da ma’auratan zasu dinga bawa junansu, musamman idan akayi rashin sa’a daya daga cikinsu ya zamo yana da wani hali na qyama wanda da yake boyewa.
Shawarar da zan bayar anan shine sai mu dinga kulawa sosai a lokacin neman aure, samun kusanci da mutanen gidan masoyan namu ta hanyar qannenshi/ta da abokanshi/qawayenta zai taimaka wajen sanin wanda/muke tare dashi/ita da irin halayensu.
Gaskiya dokin qarfe, idan ka zamo mai gaskiya da halin qwarai to ba ka da tsoron komai a tare dakai!
#Matsala #3
#Mulkin Gida
A duk inda taro ya kai mutum biyu to ya kamata ace akwai shugaba wanda za’a iya cewa shine babba, haka ma a Rayuwar Aure dole a samu jagoran tafiya. Sanin kowa ne cewa a Addini da al’ada miji shine yake da mallakin gida, shi yasa ma ake kiransa da MAIGIDA.
Daga cikin matsalolin da akan samu daga wajen wadansu matan shine wai su baza su bari wani ya dinga nuna iko akansu ba, suna ganin idan suna bin maigida sahu da qafa kamar sun fado, za’a mayar da su kamar bayi! Wannan batu kuwa ba haka yake ba, dole ne mata kuyi haquri da yadda addini da al’ada ta tsara akan cewa maza sune shugabanni a Rayuwar Aure, ta haka ne kawai zaku iya cika haqqoqin auren da suke kanku; har ma ku zamo masu biyayya ga mazan auren naku, sai Allah ya baku lada.
Duk macen da take ganin ba zata iya yiwa namiji biyayya ba saboda tana ganin itama ta waye to lallai kuwa fitina baza ta taba qarewa a gidanta ba, irinsu ne zaka ga ko da Allah ya basu zuriyya to haka suma ‘ya’yan zasu taso irin halin mahaifiyar tasu. Saboda haka ina kira ga MATA IYAYEN GIDA da ku daure kuyi biyayya ga mazan aurenku dan samun ingantacciyar Rayuwar Aure, mu kuma maza muji tsoron Allah kada muyi amfani da wannan dama mu cutar dasu matan auren namu. Allah yasa mu dace baki daya.
```Wasu Abubuwan 12 Da Mata Suka Tsana A Lokacin Jima'i```
☛ a dinga kulawa da wanna Domin a gyara irin wanna matsala a cikin al'umma mu na aure.
Sau tari, maza magidanta sukan yi wasu abubuwan da matansu suka tsana ko suke ki a yayin da suke gudanar da jima'i, sai dai kuma kadan ne daga cikin matan sukan iya fitowa fili su nunawa mazajen nasu rashin
jin dadinsu ga irin wadannan dabi'on ko halayen.
Ire-ire wadannan halayen na wasu mazan yakan kuntatawa mata, hakan kuma yakan yi sanadiyar samar masu da rashin gamsuwa a lokuta da dama yayi gudanar da jima'i da mazajensu.
Ga jerin wasu abubuwan 12 da mata suka tsana kamin, lokaci da kuma bayan kammala jima'i.
☛1-Rashin Tsafta-
Wasu mazan basu iya tsaftace jikinsu kamin su tinkari matansu da jima'i. Ana samun wasu mazanma a lokacin da suka shiga wankasu na jima'i, basa kula da mahimman wuraren da ya kamata su tsaftacesu da kyau ganin mahimmancin su a lokacin gudanar da jima'i.
Wurare irin su baki, hamata, matsaimatsi, da kuma 'ya'yan maraina, wurarene da mata suke matukar son ji da ganinsu a tsaftace a duk lokacin da mazansu suka tinkaro su a jima'ince.
Don haka rashin tsaftacesu, yakan hana mace samun jindadi kamin da kuma lokacin gudanar da jima'i.
☛2-Wasanni Motsa Sha'awa-
Wasu mazan sam basu da al'adar motsawa matansu sha'awarsu ta jima'i ta hanyar wasannin motsa sha'awa, yadda zai sa mace sha'awarta ya matsa sosai ta kuma ji ta kamu da bukatar mijinta.
Mata da dama sun koka ta yadda mazansu da sun tashi gudanar da jima'i dasu sai dai kawai su musu hawan kawara ba tare da motsa musu sha'awa ba, wanda hakan yasa mata da suke fuskantar irin wannan matsalar suke tsanar yin jima'i a lokuta da dama. Mata suna sha'awar ayi musu wasanni da dama kamin a soma gudanar da jima'i dasu.
☛3-Rashin Maida Hankali-
Mata sun tsani a lokacin da za a soma ko ake jima'i dasu hankalin namiji ya koma wani wajen. Mace na bukatar ganin mijinta ya tattara hankalinsa gaba daya a kanta kamin, lokacin ko bayan kammala jima'i da ita.
Don haka ne mata suka tsani namiji yana amsa waya ko kallon talabijin, ko kuma yin wani batun da bashi da alaka da abunda suke gudanarwa a wannan lokacin.
Dole muddin namiji yana son ganin ya gamsar da matarsa, to ya maida hankalinsa gaba daya a kanta a yayin da yake tare da ita.
☛4-Lokacin Yin Jima'i- Kashi 80 cikin 100 na mata sunfi sha'awar a yi jima'i dasu ne a lokaci suke da sha'awar yi ba a lokacin da basu da sha'awa ba.
Mata sun tsani namiji ya tilastasu yin jima'i ba tare da suna da bukatar yin shi ba a wannan lokacin.
Don haka yana da kyau maza suyi la'akari da lokacin da mace take sha'awar jin jima'i da kanta, domin ta hakan ne maigida zai iya samun biyan bukatar da za a sakar masa jiki sosai. Gani a akwai wasu lokutan da mace batada sha'awar jima'i a rayuwanta.
☛5-Yanayin Kwanciya- Duk mace tana son mijinta ya saduda ita da yanayin da yafi mata dadi kuma yake sauki da saurin gamsar da ita.
Mata sun tsani mazajensu su kwanta dasu a yanayin da basu jin dadinsa wanda hakan yake sa mace ta tsani gudanar da jima'in ko kuma ta kasa samun gamsuwa.
Don haka yana da kyau maza su kula kuma suyi la'akari da yanayin kwanciyar da mace ta tsana da kuma wanda tafi sha'awa a yayin jima'i.
➜6- Sauke nauyinka a kanta-
Maza musamman masu nauyin jiki, sukan cutar da matansu a lokacin da suka sauke nauyinsu akanasu a yayin gudanar da jima'i. Hakan na hana macen ta samu sararin sarrafa jikinta yadda take bukata.
Maza masu tunbi ko girman jiki su rika amfani ne da yanayin kwanciyar jima'in da bazai takura matansu ba.
➜7- Saurin Zuwan-
Dukkannin mata sun tsani mazansu suyi zuwan kai da wuri a yayin gudanar da jima'i, wanda hakan yana matukar cutar da mace a rauyuwar, don haka wasu matan suka gwammace zama da rashin jima'i maimakon yin jima'in da namiji mai saurin zuwa.
Dole ne maza masu irin wannan matsalar suyi kokarin ganin likita domin samo magani.
➜8- Yin Shuru- Mata suna son jin namiji yana sumbatu a lokacin da yake saduwa dasu.
Mata sun tsani mazansu na saduwa dasu
suna gum da baki tamkar kurma. Don haka yin sumbatu a yayin jima'i da mace, yana kara mata kwarin gwaiwa dama gamsar da ita a wasu lokutan.
➜9-Rashin Alamta Zuwan kai- Mata sun tsani mazansu suyi zuwan kai ba tare da sunyi musu wata inkiyar da zata nuna masu cewa suna kan hanyar zuwa ba.
Alamta zuwan kai wajen namiji a yayin saduwa da matarsa itama yana kara mata wani jin dadin. Yana da kyau namiji yayi nuna wani alamin a lokacin da yake kan hanyar zuwa da kuma bayan zuwar tasa.
➜10- Saurin Tashi- Mata sun tsani namiji da zaran ya biya bukatarsa yayi saurin tashi daga jikinta.
Mace tana bukatar tabbatar da cewa na
miji yana tare da ita koma yana cikinta bayan ya biya tasa bukatar. Domin a wannnan yanayin tana iya samun gamsu idan mai gida ya rigata.
➜11- Zuwan kai a waje- Mata sun tsani namiji yayi zuwan kai a wajen farjinsu ba a cikinsa sai dai idan ita ce ta bukaci yin hakan saboda wasu dalilai.
➜12- Rashin Sadarwan Jima"I- Maza da dama basu da al'adar yin sadarwan jima'i da matayensu kamin, lokaci da kuma bayan kamala kwanciya irin na jima'i. Yana da kyau kasan abunda matarka takeso ko ta tsana a lokacin gudanar da jima'i.
Wannan tattaunawar zai baiwa mace daman bayyana maka abubuwan da ke mata dadi a lokacin wasannin motsa sha'awa, lokacin gudanar da jima'i da bayan kammala shi domin ka kaucewa abunda bata so ka kuma inganta abunda take so.
*SIRRIN MAZA*
Hakika namiji yana da wani sirrin Wanda ba kowacce mace ta San wadannan sirrin ba Sai wacce Allah ya sanar da ita, shi namiji ya kasance Mai tsanani son karairaya, rangwada, kissa,shagwaba, da kalaman soyayya, duk macen data San wadannan kuma take aikatasu hakika zata zama tauraruwa a zuciyar mijinta.
Babu KO shakka wadannan kam Na Daga cikin abubuwa mafi muhimmanci dake taka muhimmiyar rawa wajen sace zuciyar namiji ,ya kasance kin tanadi wani suna Na musamman da Zaki dinga kiran mijinki dashi kamar
● sweety
● honey
● darling
● Abin kaunata
● farin cikin rai Na.
Magana ta gaskiya a wannan fannin a nan ne aka yiwa matan hausawa nisa , don da yawa sune basu dauki hakan a wani Abu Mai muhimmanci dake Iya jefa tsantsar sonki a zuciyar mijinki ba.
Dole a matsayin ki Na macen da ke son ta mallaki mijinta saifa ta dage wajen Iya kalaman soyayya don sune masu kwantarwa da namiji hankali koda kuwa an bata masa rai KO hankalinsa ya tashi.
Sannnan yana Daga cikin namiji ki Iya gabatar da zahirin soyayya, hakika tsakaninki da mijinki bafa jin kunya, ki Saki jikinki ki nuna masa soyayya, domin duk wani hade-hade da manne-manne da zakiyi idan Har baki Iya kalaman soyayya ba da ita kanta soyayyar to gaskiya da sauranki.
Misali idan ya kasance Ku biyu ne akayi sa'a baki iyaba KO kuma kice kina jin kunya Amma ita abokiyar zamanki ta Iya Sai kiga yana zumudi a duk lokacin da akace yaune ranar kwananta.
Don haka dole Sai kin dage kin jajirce kin Iya salo-salo Na soyayya.
Sannan Daga cikin sirrin namiji a wajen jima'i karki zauna shirim baki tabuka komai, ya kasance kema kanki kina gabatar da salo Na shagwaba da duk wani yanayi da zai Iya Saki nuna masa cewa kefa kina jin dadin wannan jima'i dashi.
RASHIN SHA'AWAR NAMIJI A WAJEN MACE 
NEMI ILIMI KAFIN AIKI DASHI RAYUWAR MA'AURATA
Dukkan mace matar aure ko budurwa data samu kanta a yanayi na rashin sha awar namiji to gaskiya ta hadu da kalubale a bangaren zaman aure Zata fuskanci rashin kulawa a wajen mijinta musamman idan ya fahimci batajin dadin saduwa dashi ballantana ace tanada kishiya shiyasa mata masu dabara basa nunawa namiji suna cikin wannan halin kokarinsu su gamsar dashi da abinda yakeso Hakika wasu matan tun suna yan mata suke kashe kansu da shan wasu magunguna marasa inganci da sunan ya rage musu sha awa wasu har jar kanwa suke jikawa da lemon tsami sunasha don ya rage musu sha awarsu kuma wannan duk kuskurene idan har bazaki iya azumiba to ki ajiye burin rayuwa kiyi aure domin ita Sha awa ajikin mace ko namiji ba cuta bace amma rashinta kuma cutace bazaki gane hakanba saita faru dake koda yake namiji be cika damuwa don bashida sha awar maceba amma kuma matarsa zata rasa kulawa To idan akace rashin sha awa ga mace ko rashin jin dadin jima i to ya hada abubuwa da yawa amma masana sirrin jima i suna takkaita bayanin gida uku kamar haka.

(1) akwai wacce tana sha awar namiji hasalima ko zancen jima i tayi da namiji koda a wayane ko a chat zataji farjinta ya jike alamun sha awa zata bayyana a fuskarta zataji sha war namiji ya sadu da ita amma da zaran na miji ya saka azzakarinsa a farjinta saita rasa ina dadin yake ita wannan tana bukatar kyakyawar kulawar soyayya a wajen mijinta ya kamata mijinki yasan hanyoyin Wato sarrafa mace da sanin wurarenda mace takeso namiji ya taba ajikinta musamman lokacin jima i kuma soyayya itama tanada muhimmanci awannan lokacin wato tana saka mace jindadin jima'i.

(2) sannan akwai wacce ita kuma kwata kwata bata sha awa ita ko za ayi wata daya ko biyu ba a tabataba batada matsala idan kin samu kanki acikin wannan halin akwai tambaya akanki kina mafarkin namiji? kinada jinnu ma ana suna tashi? idan duk babu daya to kici gaba da shan maganin karin sha awa amma wanda zaki hada da kanki wannan duk muna bayaninsu apost to idan kuma kina mafarki ko kinada jinnu suma suna daukewa mace sha awa ta zahiri saboda surinka saduwa da ita amafarki sannan zasu iya barin mijinki ya rinka jin dadinki idan sunga dama shima su hanashi saiya rinka jinki salam kamar ba maceba ko kuma su hanaki ni ima lokacin saduwa saiki bushe sai anyi da karfi ta shiga gaskkiya wannan matsalace kuma wani lokacin sihiri akeyiwa mace hakan take faruwa kiyi kokari ayi miki rukuya wacce ta dace da sunna kema kici gaba da addu a kuma kina kwaciya da alwaa idan zaki kwanta ki karanta wasu ayoyi daga cikin qur ani sannan kina share shimfida kafin kwanciya kuma keda mai gida ku rinka addu a kafin ku fara jima i insha allahu zakiyi mamaki

(3) haka kuma akwai mace wacce tana sha awar namiji amma ta fiso ya saka mata yatsa a farjinta tafi jindadi idan ya saka mata azzakarinsa sai taji dadin ya ragu kuma irinsu zaka samesu da bushewar. farji to irin wannan itamma tana bukatar kulawa ta musamman daga wajen mijinta sannan kada kiyi. wasa da gyaran jiki da kuma tsaftar farji to amma inaso ki gane shifa jin dadin jima i ya danganta dagake wato ina nufin yaya sha awarki take yawan sha awarki shine yawan jindadinki yana iyakasancewa haka allah ya haliccceki dama sha awarki gajeriyace ba iirin ta sauran mataba sai kiji kawarki tana baki labari jin dadinda takeyi a wajen jima i to zai iya kasancewa dama ta fiki sha awa ko kuma tafiki samun kulawa a wajen mijinta kinga kada kice dole sai kinji dadi irin nata....

NAU’O’IN GWAJE-GWAJEN LAFIYA KAFIN AURE
Masana sun bayyana cewa ana yin gwaje-gwajen lafiya ne kafin aure a kan nau’o’in cututtuka guda biyar:
1. Gwaji don tabbatar da ku6uta daga cututtukan da ke qetare mai shi zuwa waninsa a dalilin mu’amala ta jima’i (Sexually Transmittable Diseases – STDs), kamar:
HIV,
Hepatitis B,
Hepatitis C,
Gonorrhoea,
Syphilis.
2. Gwaji game da rukunin kwayoyin halitta (genes) don sanin Genotype din masu niyyar yin aure a matsayin “AA”, “AS”, ko “SS” don tabbatar da ku6uta daga cututtukan da ke bin hanyoyin jini wajen yin naso da shafar abokin zama ko ‘ya‘yan da za a haifa kamar cutar Anaemia (sickle cell disease).
3. Gwaji don gane rukunin jini: ‘A’, ‘B’, ‘0’ ko ‘AB’, da danginsa na Rhesus factor (positive, ‘+’ ko negative, ‘-‘). Kasancewar bincike ya nuna cewa macen da ke qarqashin dangin jini na Negative idan ta aure wanda ke qarqashin Positive, tana iya fuskantar hatsarin yawan zubewar ciki ko mutuwar dan da ke cikin mahaifa (intrauterine death). Gudanar da irin wannan gwajin na da muhimmanci.
4. Gwaji don tabbatar da rashin aibobin da ke sa a kai ga raba aure a tsakanin miji da mata, kamar cututtukan da ke iya jawo rashin haihuwa, da kuturta, da wasu nau’o’in cutar daji (cancer) masu hatsari, da cutar qoda.
5. Gwaji game da cututtukan da a ke gado, wadanda aka ce a yanzu adadinsu ya kai 8000. Irin wadannan cututtuka sun hada da ciwon hauka, da ciwon ido da ‘ya‘ya ke iya gado daga iyaye kamar glaucoma.

HUKUNCIN GUDANAR DA GWAJE-GWAJEN LAFIYA KAFIN AURE

Kusan dukkan malamai a wannan zamani sun hadu a kan muhimmancin gudanar da gwaje-gwajen lafiya kafin aure don kaucewa wasu cututtukan da ke yin karan-tsaye ga dorewar aure, ko su sabbaba cuta ko naqasa ga ‘ya‘yan da za a haifa. Amma sun yi sa6ani game da wajabcinsa a kan wadanda ke son yin aure. Wasu malamai na ganin cewa Hukuma ko iyaye na iya wajabta gudanar da gwaje-gwajen lafiya a kan wadanda ke son yin aure, wasu malaman kuma na ganin kawai a bar mutane su za6i abin da suke so, ba tare da an wajabta masu ba.
Daga cikin masu ganin wajabcin gudanar da gwaje-gwajen lafiya kafin aure akwai: Muhammad Az-Zuhailiy, da Naasir Al-Maimaan, da Usaamah Al-Ashqar. Waxanda ke ganin halascin gudanar da gwaje-gwajen ba tare da wajabci ba sun hada da: Ibn Baaz, da Abdullah ibn Jebreen, da Abdulkareem Zaydaan, da Muhammad Ra’afat Uthmaan.
Allah ya shiryar da baki daya akan bin Sunnar Manzon Allah da tafarkin magabata na kwarai. Amin

TO YAYA MACE ZATAYI TA ZAMA ME SHA AWA?
da farko kada kibari mijinki ya fahimci bayajin dadinki ya kamata ki daure ki rinka nuna masa jindadinki koda kuwa ba dadinsa kikejiba domin duk lokacinda mijinki ya fahimci kina saduwa dashine adole bakyajin dadinsa to tabbas akwai matsala shi namiji yanaso yaga matarsa tanajin dadinsa hakan yana sawa yaji baya bukatar karin aure kuma zaki shiga zuciyarsa sosai Sannan ki tabbara bakida ciwon sanyi (infection) shima yana iya hana mace ni ima ko jindadi duk maganinda tayi zai iya zama a banza dole sai kinyi kokarin magance wannan matsalar Sannan ki kasance me amfanida man ayu me kyau (original) shima yana karawa mace jindadin jima i zaki shafashi a gabanki bawai cikin farjinkiba zakiji Sha awar namiji sosai Sannan zaki iya samun danyen zogale ki markadashi saiki tace wannan ruwan ki zuba masa kanunfari da zuma kinasha safe da yamma Sannan idan kinada tabbacin aljanune suka hanaki Sha awa ko kuma sihiri akayi miki ga yanda zakiyi Kisamu man habba da man zaitun sai kiyi musu rukuya a ciki kuma ki karanta ayatush-shifa da allahumma rabban-nasi da bismillahi da kula’uzai da kul-huwa kafa uku-uku saiki dinga shafawa kuma kina sha safe da yamma sannan kuma ki samu turare mai kanshi wanda kansinsa yake da dadi sosai shima kiyi masa rukuya a ciki saiki dinga shafawa a wurare talatin na jikinki wuraren kuma sune kamar haka:-
1-Kan gashin giranki
2-Ramin kunnuwanki
3-Kofofin hancinki
4-Kan nonuwanki
5-Kan farjinki da kan dubura sannan sai kan yatsun hannayenki guda goma da kan yatsun kafafuwanki guda goma sai ta kwanta kuma duk lokacinda zaki kwanta ki kwanta da alwala sannan kina share shimfida haka zatayi kullum har kwana goma ..

MAGANIN BUSHEWAR GABAN MACE
gamai samun daukewar ni'ima da rashin sanin dadin aure ko rashin nishadi to amarya ko uwar gida ga yanda zaki magance wadannan matsaloli cikin sauki, sai ki samu:
-aya
-zuma
-dabino
-garin sallaja
sai ki markadesu ki tacesu sai ki rinka diba kadan-kadan kina hadawa da zuma da garin habba kadan kina sha safe da yamma, wadda batayi aure ba kada tasha.mijinki zai ji kin canza sosai.
● SINADARI MA 'AURATA:●
shi wannan wani sinadarine mai albarka wanda ake yi masa lakabi da sinadarin ma'aurata, kuma yana jimawa a jiki, sannan yana kara kuzari kuma yana karawa mace martaba ga mijinta, zaki samu:
-furen zogale
-zanjabil
-habba
-garin raihan
sai ki dakesu guri daya sudaku dakyau sai rinka diban karamin cokali kina hadawa da zuma kina safe da yamma shima wannan sai mai aure amma idan kin kusa yin aure zaki iya yin wannan hadin.
HADIN MATAN MASAR DA MATAN SUDAN:
ko shakka babu shi wannan hadin matan masar da matan sudan,da matan jordan suna yinshi yana kara ni'ima musamman yana gyara aure, kuma yana kara dadi wurin saduwa yana kuma sa nishadin masoya, sannan kuma zaki zama yar gaban goshi
-kankana mai kyau
-zuma
-raihan
sai ki yayyanka kankanar ki zuba a kofi, ki saka zuma da madarar ruwa da garin raihan sai ki rinka sha safe da yamma.
RASHIN SHA'AWA:
akwai matanda basayin sha'awa ko basa jin dadin saduwa ko ni'imarsu ta dauke, to yanda za'a magance wannan matsala shine sai kisamu
-zangarniyar zogale,da ya'yanta gadaya
-karanfani
-citta
-masoro
-da kinba
sai ki dakesu guri daya su zama gari,sai ki rinka shan wannan hadi a shayi safe da yamma,ki gwada ki gani, yana kara dadin da mai gida zai gamsu sannan kuma zaki rinka cin dabino(ajuwa) mai kyau tare da kwakwa zaki sha mamaki.
NI'IMA SINADARI MAI DADI
ga wani hadi na musamman dan karin ni'ima da nishadi da dadi
-ya'yan zogale
-kankana
sai ki dakesu guri daya suyi laushi sai ki rinka sha da nono safe da yamma.
DON FARIN CIKIN MA'AURATA.
shi wannan wani hadi ne da akeyinshi dan farin cikin ma'aurata, kuma yana sa asamu nishadi da kuma karin ni'ima da dadi, yanda akeyi shine za'a samu
-kankana mai kyau sosai( a yayyankata)
-ya'yan zogale
-kumasoriyya ta asali
-ayaba mai kyau sosai
ya'yan zogale da kumasoriyya za a dakesu da kyau suyi laushi, sai ki rinka diban karamin cokali na garin maganin kina hadawa da wancen kankanar da ayaba da madara ta ruwa, sai ki yamutsasu ki rinka sha, sau biyu a rana safe da yamma
sannan kuma in zaki kwanta da daddare sai ki hada farin miski da zuma farar saka da man zaitun mai kyau ki rinka shafawa a gabanki,zai kashe kwayoyin cututtuka da gamsar da maigida da nishadi.

DON MAGANCE ZAFIN SADUWA:
wannan wani hadi ne da akeyi don magance zafin saduwa ko rashin sha'awa ko daukewar ni'ima
-dabino
-garin ridi
-garin habba
-da garin raihan
sai a samu zuma lita daya a hadasu wuri daya a rinka sha cokali daya a ruwan shayi safe da

*MATSALOLIN MAZA RAUNIN AL'AURA:*
namiji da yake fama da raunin al'aura ba'a cewa ya sha magani kaza, sai anyi masa bincike guda uku,
1 a duba a gani baya da ciwon sugar?
saboda cutar sugar tana sabbabar da raunin al'aura.
in yana da ciwon sugar a kwai maganin da zaiyi amfani da shi.
2 sai a duba yana da basir?
In yana da shi akwai hanyoyin da ake bi a magance shi.
3 a duba a gani baya da gajiya da talauci? ko yawan aiki ko damuwa domin shima yana kawo raunin al'aura saboda hankalin bai natsuba balle yayi sha'awa.
*KA DAURE KAYI WADANNAN MAGANIN MAIGIDA*
ciwon sugar
○ man hulba
○ zaitu ( jonifer oil )
○ habba yar'algeriya ,
○ zaitu lauz
sai a hada su waje daya kafi ya kwanta da dare da awa daya zai samu madara musamman na luna, sai a dumama su tare da zuma sai a gauraya shi a sha.
da safe kafin a karya, za'a dace insha Allah.
inda kuma babu ciwon sugar yana son ya samu kusancin matansa sai ya samo hulba tare da matan zasu sha tare kafin su kwanta da awa daya wanna yana taimakawa.
damuwa sai a rage ta sosai da shan sugari duk.
*MU GYARA KUSKUREN MU MA'AURATA*  
Akwai abubuwa da yawa wadanda Ma’aurata suke aikatawa a lokacin Jima’insu. Kuma wadannan abubuwan suna da illoli masu yawa dangane da lafiyarsu jikinsu ko addininsu.
Ga wasu ‘yan kadan Zan lissafo:
1. *RASHIN GABATAR DA WASANNI KAFIN JIMA’I:*
Wannan ba daidai bane domin kuwa Manzon Allah (saww) yace “IDAN ‘DAYANKU YAYI NUFIN KUSANTAR IYALINSA, TO LALLAI A SAMU ‘DAN AIKE A TSAKANINSU”.
Sai Sahabbai suka ce “Wanne irin ‘dan aike?” Sai yace “SHI NE SUMBA (KISS) DA KUMA MUBASHARA (RUNGUMAR JUNA).
Rashin gabatar da irin wadannan wasannin yakan haifar da rashun gamsuwar Jima’i. Shi kuwa rashin gamsuwar Jima’i yakan haifar da matsalolin da zasu kawo rabuwar auren.
Yana daga cikin fa’idodin gabatar da wadannan
wasannin, zai sa Maniyyin ita Macen ya gangaro daga ainihin inda yake, sannan kuma za ta samu cikakkiyar gamsuwa.
2. *KUSKURE NA BIYU SHI NE TSOTSON AL’AURAR JUNA:*
Wannan kuskure ne babba wanda ko dabbobi basu yinsa. Duk da cewa babu wata ayah ko hadisi wanda ya fito karara ya yi bayani akan haramcin wannan, to amma Malamai sun yi sabani sun kasu gida biyu akan hukuncin yin hakan, kuma sun raba hukuncin gida
biyu:
Idan har ya kai ga shan Maniyyi to Malaman Malikiyyah da Hanafiyyah sun ce HARAMUN ne. Domin su a wajensu Maniyyi najasa ne. Kuma bai halatta Musulmi ya shigar da najasa cikin cikinsa ba.
Idan kuma Maziyyi ne aka tsotsa, to dukkan Malamai sun ce HARAMUN ne. domin kuwa shi Maziyyi najasa
ne abisa ittifakin Malamai bai daya.
Idan kuma ba a tsotsi Maziyyi ko maniyyi ba, to Malaman da suke bayar da fatawa a Jami’ar Az’har sun ce MAKRUHI NE.
Wasu kuma irin su Nasiruddeen Albaniy sun ce HARAMUN NE duk da hakan.
3. *KUSKURE NA UKU SHINE YIN SURUTAI A LOKACIN JIMA’I
Shi ma wannan ba daidai bane. Shari’ar addinin Musulunci ta hana mutum ya rika yin magana a lokacin da yake tsirara.
4. KUSKURE NA HUDU SHI NE RASHIN LULLUBE JUNA DA MAYAFI: Shima wannan ba daidai bane. yin hakan ya yi kama da Jima’in dabbobi kenan.
5. *KUSKURE NA BIYAR SHINE RASHIN AMBATON ALLAH KAFIN FARA JIMA’I
Ya kamata Ma’aurata su kula da yin Bismillah tare da karanta addu’ar nan wacce Manzon Allah (saww) yace duk wanda yake karantawa yayin Jima’i da matarsa, to indai aka samu rabo, to shaitan ba zai iya cutar da yaron ba.
Ga addu’ar nan: “BISMILLAHI ALLAHUMMA JANNIBNASH SHAITAN WA JANNIBISH SHAITANA MA RAZAQTANA”.
6. *KUSKURE NA SHIDA:*
idan Miji ya biya bukatarsa, to bai kamata ya gaggauta sauka ba, har sai ita ma matarsa ta biya bukatarta.
7. *RASHIN SAUYA YANAYIN KWANCIYA:*
Shi ma wannan ayar Alqur’ani ta bada damar miji ya sadu da matarsa bisa kowanne irin yanayi. A tsaye ko azaune ko a kwance ko a tsugunne, mutukar dai ba ta dubura
bane. Don haka ya halatta Ma’aurata su rika chanza yanayin kwanciyarsu saboda kara ma juna nishadi.
8. *KUSKURE NA TAKWAS SHINE SADUWA A LOKACIN DA TAKE CIKIN JININ HAILA, KO JININ
HAIHUWA
Allah (SWT) ya ce : “KU NISANCI MATA A LOKACIN HAILA. KAR KU KUSANCESU HAR SAI SUNYI TSARKI”.
9. *KUSKURE NA TARA SHINE SADUWA TA DUBURA:*
Shi ma wannan kazanta ce wacce ko dabbobi basu yi. Manzon Allah (saww) ya ce “TSINANNE NE DUK WANDA YA SADU DA MAI HAILA, KO KUMA YA SADU DA
MACE TA DUBURA”.
*KINA WA MIJIN KI SUMBA KUWA??? (KISS)*
*KISS YANA MATUKAR KARA SOYAYYA GA MA"AURATA* 

Amma a dinga wanke baki sosai saboda tsaro
*Ya ke uwar gida, ko amarya, ko kin san cewa yiwa mai gida ko ango sumba ya kansa hankalinsa ya dawo kanki kuwa.*
*To ki saurara kiji, yakamata kisan cewa sumba (kiss), yana da matukar muhimmanci mara misali a rayuwar aure, wajen kara dankon soyayya tsakaninki da mai gida.*
Dan duk lokacin da zaki yiwa mai gida sumba (kiss), zai ji a ransa ashe baki kyamar sa, kuma baki gudunsa, kema
kuma haka zaki ajeye a ranki in ya yi miki. Kuma yin sumba (kiss), sakanin ma'aurata, watau mata da miji, yana taka rawar gani wajen motsa sha'awan juna, kuma ita sumba (kiss), bawai sai a baki kadai ne kawai ake
yinta ba, ko ina a jikin mijin ki za ki iya yi masa, shima kuma miji zai iya sumbartar matar sa a ko ina a jikinta,
  • kamar su, fuskarta, bakinta, nononta, goshinta, cibiyarta.
Da dai sauran su.
Kuma yin sumba (kiss), alama ce dake nuna irin tsananin son da ma'aurata kema juna.
Ba wayewa ba ne, don matar ka tama sumba, sai kamata kallon yar iska, ko don mijin ki ya miki sumba ki masa
kallon da iska, to wallahi wannan jahilci ne, idan kuna ganin kuma kariya ne to sai a tambayi mallaman addi ni, aji
gaskiyar lamarin.
*DABARA TA ITACE YIWA MIJINA SUMBA(KISS)* 
kamar dai uwar gida ta tambayi marya cewa me kike yiwa mai gida ne naga duk hankalinshi ya dawo kanki sai tace sumba(kiss) saboda haka yake uwar gida yakamata kisan cewa kiss yana da matukar muhimmanci marar misali wajen kara dankon soyayya tsakaninki da mai gida dan duk lokacin da zaki yiwa mai gida kiss zai ji aransa
ashe baki kyamarsa kuma baki gudunsa kema haka zaki aji ranki in ya yi maki kuma yinsa yana taka rawar gani wajen motsa sha'warku, kuma ita kiss nan bawai sai baki da baki ne kawai ake yinta ba ko ina a jikin mijinki zaki iya yi masa, shima kuma miji zai iya kiss matarsa a ko ina ajikinta kamarsu.
NONONTA,
BAKINTA,
FUSKARTA,
GOSHINTA,
CIBIYARTA,
DA DAI SAURANSU;
kuma yana daga cikin manya-manya abubuwanda ke kara dankon soyayya tsakanin mata da miji da kuma motsa sha'awa,kuma alama ce dake nuna irin tsananin son da kikewa mijinki shima kuma haka lalle wannan ba karamar dabara bace,ki jaraba uwar gida zaki dace da yarda Allah.
*ABIN LURA*
mata da yawa suna manta wanna bansan ko kunya bace tasa bata kiss kiss yanada amfani ga miji yar'uwa inda bakiyi ki gwada koda sau daya ne zaki sha mamaki.

●SIRRIN MA'AURATA LOKACIN AURE 
*shawara 1*
Haba maigida ! yanzu in ba ka kwantar wa da Uwargida hankali ba waye zai kwantar mata ?
kana zaman Hira mai shayi abokai.
◾ yan mata
kaji tsoron Allah ka daina aikata wannan dabi'a ka zamo mai walwala da sakin fuska da raha tare da iyalanka.
amma kaje cikin abokanka Ana Washe musu baki ko
yan'mata ,amma ga wacce ya dace ka washewa baki ka rinka saka ta cikin annashuwa.
yawancin mata 80% na yawan hawan jini maza ne
don Allah kubi hanyoyin da zaku zauna da matanku lafiya ka zamo mai ba ta shawara ita ma mai baka shawara. sai a yi ta sha'awa zamantakewar Ku, Ku zama abin koyi a wurin jama'a.
a karshe kuji tsoron Allah kula da matanku , Ku tausaya musu ,sai Allah ya jikan Ku, kuma ya yi musu jagora a dukkan mu'amala.
* shawara ta 2 *
kada ka zagi matarka a gaban ya'yan ka ko yan'uwanka ko a gaban mutane, aikata hakan yakan sa ya'yan cikin damuwa kuma kana zubar mata da mutunci a idon ya'yan ka da yan'uwa ka da sauran al'umma ba laifi ba ne ka yi mata fada amma ba a gaban mutane ba ko ya'yan ka ya kasance idan za Kayi mata fada daga Kai sai ita kuma Kayi shi ta hanyar nasiha ba ka ware baki ba duniya ta ji
musamman ma in tana gidan yawa ko cikin kishiyoyinta wani ma in ya tashin rashin mutuncin sa a gaban akokinsa zai ta hantarar matarsa komai sai masifa da zagi.
 shawara ga mata
karki zamo mace mai yawan rokon maigida ko abokan maigida, hakika roko yana debe kima da kwarjini da mutunci na mutum, hakika akwai matan da mazajensu ba sa kirga kudi ko su ba su ajiyar kudi ma nuna musu alama ta suna da da kusin ba sa yi saboda sun San hali, don haka duk mai Neman fada da gindin zama a wajen maigidanki ta daina yawan rokon mutane.
shawara ga mata
kar ki dogara da abin hannun mijinki kice komai sai mai gida yayi miki, hakika a wannan zamanin ki ka ce haka Zaki yi kina tare da wahala don haka ki dogara da Allah ki wadatu da abinda ke hannunki kiyi amfani da shi kar kici ba shi domin shi ba shi musifa ne babban.
 ALLAH YA RABA MU DA BASHI
mai gida Inda kasan matarka bata Sana'a Kayi kokarin taimakon ta da abinda zatayi koda bata Sana'a amma wasu mazan basa barin matan Sana'a
kuma basa iya dauke musu duk wata bukatar su irin haka sai kaga mace tana hali Mara kyau.

BABBAN SHAWARA GA MATA
⊂( ̄ ̄)⊃GIRKI SIRRIN MATA⊂( ̄ ̄)⊃
ki zamo mai iya girki da kwarewa wajan hada kayan shaye- shayen karki Bari a miki zarra ta bangaren girke-girke ya zamo mai gida ba shi da tunanin ya ci abinci a wajen ke idan mai gida ya gamsu da abincin Uwargida ko yana kasuwa sai yazo yaci idan kuma aikin yayi masa yawa sai ya turo an karbar masa, amma babu kima aga mijinki yana yawo Neman abinci da safe da yamma ya tura nan ya tura
nan, babu kima in baki iya ba ko baki kware ba sai ki nemi masu koya miki girke-girke kwatowa kanki 'yancin a wajan mai gida ki Sani babu wacce tazo da iyawa kowa koya yake don haka kema sai ki koya domin faranta wa maigida .

SHAWARA GA MATA
ki zamo mace mai riko da addinin musulunci kar ki zamo mai wasa da ibada ki bautawa Allah kamar kina ganinsa ki Sani in kin kasance bakya ganinsa to shi yana ganinki ki maida lamuranki ga Allah karki yi yawan bin  BOKA KO MALAM kamar yadda wasu matan suke yi ko bin bokaye da yan bori yin hakan ba zai Kara miki komai ba asara da tabewa..
DON JAWO HANKALI MAIGIDANKI
madarar ruwa.
ayaba.
garin dabino
garin aya.
idan kika sami madara ta ruwa gwangwani daya, sai ki sami ayabarki kamar manya guda biyu ,sai ki yanyanka ta kananan a cikin madara ruwan , wacce kika sami kofinki kika juye, sannan sai ki kawo garin dabinonki cikin karamin cokali sai ki zuba a hadin madararki, sannan sai ki kawo garin ayarki shima sai ki hada ki gauraya shi sai ki shanye.

GIDAN NI"IMA  DON KARA WA KANKI NI'IMA
 ruwan kankana. kwai. zuma.
idan kika sami kankana Zaki tace ta, ki sami ruwan cikin karamin kofi sannan sai ki kawo kwanki guda daya sai ki fasa shi a cikin kananan, sannan sai ki kawo zumarki cikin babban cokalin biyu, sai ki shanye wannan yan'uwa muddin kuka daure da sha wannan to kuwa ina mai tabbatar muku zaku ga aikin.
SHAWARA GA MA'AURATA MAZA
ka zamo mutum mai nutsuwa kar ka sake ka rinka aikata abubuwan da zasu jawo maka zubewar mutuncinka ya kuma jawo zubewar mutuncin iyalanka kamar shaye- shayen , hakika shaye-shayen yana jawo raguwar kima da kuma yawan alfasha ya kasance ba ka da aiki sai zagi don akwai wadanda zagin ya zama musu Riga ya zame musu jiki, ko zance zasu yi sai sun hada da alfasha kunga ai wannan ba tarbiyar bace ta gari idan baka so ya'yan ka su dauka sai ka daina.
shawara ga ma'aurata mata
kiji tsoron Allah ki kula da mijinki, ki ba shi kulawa ta
musamman ki zama mai tsafta da iya ado, ki zamo mai kisisinar da gwalli, da rangwada duk hanyar da Zaki Bi , ta haka Zaki dauke hankalinsa ya daina kula yan'mata da zawarawa a waje.
amma kin kasa kula da shi kin kasa kula
da kanki, ba ki San me zai ja hankalin mijinki ba, kin zauna daga ke sai dauri iya kirji, ba wankin baki ba gyaran ga shi, ba kula da kafa ba wanki ba wanka ba aski hammatarki bare na gaba ( farji ) dole ki samu matsala don haka ki gyara in kina so ki ga dai-dai.

shawara ga ma'aurata mata
Ki zamo mace ta gari ta kwarai ki zamo mai samawa mai gidanki farin ciki karki sa masa tashin hankali da bacin rai karki zagi mijinki karki yi abinda zai bata masa rai Musamman wajan kwanciya wasu matan suna azabtar da mazajensu ta wannan hanya wata in bai neme taba ba zata Kai kantaba wai ba aji waya gaya miki kyaje wajen Jan ajin matsa sha'awa ko bai niyyar yi ba yaji yana bukarta yayi kuma ta haka hankalinsa zai dawo jikinki ko yaushe yaji yana so ya kasance da ke ki kula garin Neman gira a rasa Ido.
shawara ga maza
ka nemi halali ka ciyar da ya'yanka da iyalanka ,ka sa halali ka tufatar da iyalanka da iyayenka da halali, kada kaci haramun ko kasa haramun ko ka ciyar da ya'yanka da iyayenka da haramun, Ku Sani, haramun tana lalata rayuwa, tare da Hana karbar addu'o'in don haka Ku gujewa duk abinda kuka San zai iya jefa Ku cikin fushin ubangiji.

SIRRIN MIJINKI
DOMIN KARIN NI'IMA
irin wannan hadin shine ake Kira sa maigida kuwwa yana matukar saurin kawowa mace ni'ima.
zogale.
zuma
nono.
ki busar da zogelenki amma ba a cikin Rana ba, ki daka shi Yayi laushi sosai Zaki iya tankadawa sai ki rinka dibar cokali daya kina zibawa a nono ki zuba zuma cokali (³) a ciki ki rinka sha wannan hadin yaaj matukar Kara wa mace ni'ima sosai da lafiya.
GYARAN JIKI
gyaran mace yana matukar muhimmanci a tare da ke yar'uwa kada ki Bari fatar jikinki ta koma tamkar ta wata tsohuwa.
ganyen dalbejiya.
lalle.
zuma.
man zaitun.
sabulun gana.
dudu osun.
ki hada su guri daya ki daka a cikin turmi mai tsafta, sai ki rinka wanke da shi Zaki ga yadda fatarki zata canza.
GYARAN GASHI
wacce gashin kanta ke yawan karewar sai ta samu man dalbejiya ba tare da kin hada masa komai ba kullum da dare sai ki rinka shafawa yana Hana zubewar gashi.


follow me on facebook follow me on twitter follow me on instagram

Fitattun labarai

Habiba complete hausa novel

Alqawarin da ciwo

Amfanin cin qafar kaza

Budurwar Roba

Amfanin lemon tsami

Afanin Zogale

Adam A. Zango

Amfanin namijin Goro (bitter kola)

Tona asiri

Yanda zaka duba sunanka a Npower