Amfanin lemon tsami

1-GYARA FUSKA, ana Amfani da Lemun Tsami wajen kauda Kurajen Fuska, Fimfus, da Kyasfi, Yana sa fuska ta kara kyau. Yadda ake amfani da shi, Araba 1-2, rabin za'a goge Fuska dashi, za'ayi Haka na wasu lokuta, Amma a kiyaye Idanu, kuma kar a shafa a shiga rana se an wanke tukuna.

2-DATTIN HAKORA DA WARIN BAKI, Ayi amfani da Burushin wanke Baki da ruwan LEMON TSAMI a wanke Hakora Zasu fita kar, Baki zai bar wari, amma kar arika wankewa akai-akai
sai lokaci-lokaci saboda zai iya raunana karfin hakora.

3-WARIN QASHI (HAMMATA) idan Ana fama da ciwon warin Qashi, ko rashin tsaftace Hammata yadda ya kamata, Idan an shafa LEMUN TSAMI a Hamata zai kauda wannan warin.

4-RAGE KIBA DA TIMBI (TEBA) wanda ke buqatar haka, ya samu LEMON TSAMI daya a ruwan sha da bai wuce kofi daya ba, lokaci-lokaci, kiba da tai6a zasu sa6e.

5-RAUNI (CIWO), sabon raunin da bai wuce Hankali ba, da zarar an matsa mai LEMON TSAMI zai kame ya warke.

6-RAGE SHA'AWA, ana shan LEMUN TSAMI da Lipton dan rage sha'awa.

7-MAQYAN-QYARO, ana goge maqanqaro da LEMON TSAMI akai-akai zai mutu.

8-AMOSANI, ana goga LEMUN TSAMI a kai bayan an aske gashin kan.

9-QARNI, ana amfani da LEMUN TSAMI wajen kawar da karnin kifi. AMMA A KULA, idan mace ta yawaita amfani da Lemon tsami to zai rage mata sha'awa. Haka mata masu ciki kada su yawaita amf a ni da Lemon tsami. Masu Gembon ciki wato Olsa, su ma su
kula wajen shan lemon tsami. Amma dukkan wadannan zai musu illa ne in sun sha a ciki ba wai shafawa ba.

YADDA AKE AMFANI DA LEMON TSAMI WAJEN GYARAN FATA

Lemon tsami da zuma; Ki debi rabin cokalin ruwan lemon tsami da kuma rabin cokalin zuma sai a kwaba su, daga nan ki shafa a fuskarki na tsawon minti 15, sannan ki wanke da ruwan sanyi. Idan kina da fata mai gautsi to za ki iya hadawa da man zaitun. Lemon tsami da nono; Za ki hada rabin cokalin ruwan lemon tsami da rabin cokalin nono (amma an fi son kindirmo) sai ki kwaba sosai. Bayan haka, sai ki shafa a fuska


follow me on facebook follow me on twitter follow me on instagram

Fitattun labarai

Habiba complete hausa novel

Alqawarin da ciwo

Amfanin cin qafar kaza

Budurwar Roba

Afanin Zogale

Adam A. Zango

Amfanin namijin Goro (bitter kola)

Tona asiri

Yanda zaka duba sunanka a Npower