Gidan Aure

Zaman Aure: Jan hankali ga sabuwar amarya
Zaman auren kusan ya fi kowanne zama dadi, haka kuma ya fi komi wuya, domin Hausawa ma suna fadar zo-mu-zauna-zo-mu-saba!
Aure idan zamansa ya yi dadi za ka ga ana jin dadi, ana sam barka tsakanin amarya da ango da mahaifan ango da mahaifan amarya. Har ma ana gasa wurin kyautata wa kowane bangare, kowa zai rika kokarin ganin ya kyautata wa wani bangare domin nuna masa jin dadinsa da godiya a kan diyaucin da aka nuna masa.
A wannan lokacin za ka sami ango yana wani haske, yana ciccika, yana kasaita tamkar wani basarake, ko wata agwagwa. Yayin da ita kuma amarya za ka ga tana sheki da wani irin kumbura tamkar kazar Turawa. Haka za ka ga tana wani irin annuri da sakin fuska. A wannan lokacin ko iska ta kada sai ta yi masa dariya, to, balantana wani ya yi mata magana ta wasa ko ta zolaya. Shi ango kada ma ka tona bangarensa, domin shi kam wannan zarafin ya koma wani dan karamin tauraro ko kuma ya koma tamkar mota kirar sabuwar shekara.
AssalamuAlaikum?
Wa’alaikus-salam!
Barka da wuni?
Barkadai!
Kai jiya na hadu da Ibrahim yayan Suwaiba!
Masha Allahu! To, ya gane ka kuwa?
Eh! kwarai kuwa ya gane ni sossai.
Kai amma wadannan bayin Allah suna da  kirki.
Wallahi haka ne, kuma dattijai.
Ai wani ya gaya mani cewa, idan mutum ya sami suruki kamar Alhaji Abdullhamid, hakika ya yi arziki.
Muhammad, wannan ita ce dalilin da ya sanya iyayenmu ke ba mu shawara, idan za mu yi aure a kan mu auri ’yar dattijai.
Wannan tana daya daga cikin hirar da za ka ji ana yi daga bangaren ango, idan suka hadu da wani daga ’yan uwan amarya. Wanda kuma hakan ne zai faru idan ana hira a bangaren ’yan uwan amaryar idan sun hadu da na angon.
Yayin da su kuma abokan ango za su dinga zolayar ango a kan cewa, wallahi wane ka canza, ka yi kiba, ka koma dan lukuti da kai. Abu sai ka ce agwagwa. Ko kuma wani ya ce da ango wallahi wane ban zaci cewa za ka yi kiba ba, amma kuma yanzu sai ga shi ka yi kiba, ka yi fari, ka yi haske da kyal-kyali, kai amma Suwaiba ta iya kiwo. Duk wadannan su suke nuna cewar aure ya yi kyau, an samu zaman lafiya kamar yadda ake so da buri.
To, amma idan aure bai yi kyau ba, zaman lafiya bai samu ba, to, wannan ba sai na yi bayani ba; domin duk abubuwan da na zayyano a baya, to, sabaninsu ne zai auku. Idan an hadu za a rika cin mutuncin juna da yi wa juna muggan kalamai da habaici, wani lokaci har da zagi. A wannan lokacin amarya za ta koma tamkar kazar da kurdumu ya kama, ko itaciyar da tsawa ta fado a kanta.
Ango kuwa kada ka so ganinsa a lokacin, domin ya koma tamkar akuyar mayya, ko tamkar wanda yake da sabon hauka, kowa yana nesa-nesa da shi, to, balantana wani ya yi masa maganar fara’a ko zolaya idan dai ba wanda ke son cin zarafinsa ba ko idan dama shi makiyinsa ne.
To, wai duk mene ne ke kawo hakan? Zaman lafiya da rashin zaman lafiya. Wasu sukan dora alhakin abin kawai a bangaren mata, ko kuma bangaren iyayen ango. To, amma dai ni zan dora alhakin duk wani abu da ya faru a zamantakewar su haujin mata da mijin, wani lokacin ma namijin ya fi laifi a wannan bangaren amma dai laifi kowa da irin nasa.
Mafita: Bayan an yi aure an gama biki da karbar gaisuwar ’yan uwa na nesa da na kusa, wadanda ke zuwa domin yin addu’a da sanya albarka. Kowa zai watse, za a bar mutum biyu da abu biyu. Su ne amarya sai ango sai kuma halayen amarya  da halayen ango. To, a wannan lokacin ya kamata idan son samu ne, ango zai zauna da amarya su fuskanci juna. Ta wannan wurin za su tattauna a kan muhimman abubuwan da za su kawo musu jin dadi da albarka a zamantakewarsu. Kuma a nan ango ne ya kamata ya yi wa amarya wa’azi a kan ta ji tsoron Allah a kan zamantakewar aure.
A nan angon yana iya ya dan gutsura wa amarya wani abu daga sirrin rayuwarsa na yadda yake son amaryar ta kasance da yadda yake son ta yi ma’amala da shi da mahaifansa da sauran ’yan uwansa da sauran jama’a. Kuma zai iya dan bayyana mata wasu daga ’yan ka’idojinsa ko abubuwan da yake so. Haka babu laifi idan ya tambaye ta a kan abubuwan da take so, ko kuma abubuwan da ba ta so. Idan an bi wannan hanyar, in sha Allahu abubuwan za su tafi cikin tsari, da kuma samun salama da zama mai inganci tsakanin ango da marya.
Sai dai kuma koda an sami matsala alhali kuma duk an zauna an tsara abubuwan da ya kamata a yi, to, ko shi bai kamata a yi harkar dabbobi ba wajen warware matsalolin ko ganin cewa kowa ya ji a jikinsa. A’a shi ma akwai matakan da ya kamata ma’aurata su bi domin ganin an sami maslaha da zaman salama  ta wannan bangaren.
Idan ana samun matsala tsakanin ango, ko tsakanin mahaifan ango wadanda su ne watakila za ki zauna da su, to amarya, za ki zauna ki yi duba da nazari a kan abin da ya kawo ki, wato zaman aure ne za ki yi, za ki zauna da wanda ba ki taba rayuwa ta wuni daya da shi ba, yau shi za ki zauna karkashinsa. Yakan yiwu tauraruwarku ma ba daya ba ce, ke ra’ayinki daban ra’ayinsa daban to, a nan ya kamata ke ki ajiye ra’ayinki, ki kulle shi cikin zane, ki boye shi, sai ki rungumi ra’ayi da dabi’un mijinki, wanda ta wannan hanyar idan har halayen ba kyawawa ba ne; za ki iya ki canza masa su daga baya amma kuma sai kin nuna goyon bayansa sa’annan zai saurare ki har ya fahimci nasiharki.
Amarya ta dubi tarbiyya da ilimin da aka koyar da ita daga makaranta da kuma daga iyayenta da masu yi mata tarbiyya, duk ta tara wadannan abubuwan ta biya adashinsu. Ma’ana, yanzu ne za ta biya mahaifanta adashin da suka zuba mata na tarbiyyar da suka yi mata. Kuma a nan za ta biya malamin da ya koyar da ita addini da sauran al’amurran duniya.
Idan har zaluntarki ake yi daga bangaren miji ko mahaifansa ko ’yan uwansa to, kada ma ki kai karar su wajen mahaifanki, a’a zauna da su ki ci gaba da kyautatawa a gare su da yi musu abin da duk kika san zai kyautata rayuwarsu ko da ba su yaba miki. A’a, shi Allah da kike yi dominSa yana nan yana ganin ki, yana yaba miki kuma yana ba ki lada kuma ko-ba-jima-ko-ba-dade sai Allah Ya nuna gaskiya tsakaninku kuma Allah Ya sanya soyayya da fahimtar juna tsakaninku.
Hausawa dai sun ce, komai ya baci hakuri ne babu! Ni kuma zan ce,  komai ya baci maganinsa Allah!
Inaga kafin mu shiga cikin gidan aure, zaiyi kyau mu fara gabatar da wasu shawarware ga ‘yan’uwa, wa’danda zasu taimaka matuka wajan rage matsalolin dake faruwa a gidajan auranmu.
Kasancewata mace zan fara da gabatar da shawarar dana samo daga wajan Malamina (Mal Umar Ya’akub) ga ‘yan’uwana mata….
Shawara ta 1
YAYA ZA KI ZABI MIJIN KI
Ki kyautata zaben mijin ki, ki sani rayuwar aure ba ta dawwama sai da fahimtar juna da soyayya, sanna kuma kina daukaka shi fiye da kowa, shima yana fifitaki fiye da kowa
Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam yace a lokachin da yake koyawa budurwa yadda zata zabi mijinta abokin rayuwar ta
“Idan wanda kuka yadda da addinin sa da halayyar sa, ya zo muku toh ku aura masa, idan baku aikata ba barna da fasadi mai girma zai faru”
Wani mutum ya cewa Imam Hasanul basari: hakika ina da yarinya wacce na fi son ta cikin mutane
Wa kake ganin ya kamata na aura masa ita?
Sai yace
Ka aurar da ita ga wanda yake kiyaye dokokin Allah madaukakin sarki
Idan yana son ta zai girmamata
Idan baya son ta ba zai zalince ta ba
An fadawa wani mutum mai hikima: Wane yane neman auren wance
Sai yace
Shin mawadachin hankali ne da addini?
Sai suka ce: eh
Sai yace: ku aura masa ita
Ana bada labari cewa Nuhu dan Maryam alkalin garin Marwi yaso ya aurar da yar sa
Sai ya nemi shawarar makwabchin sa wanda bamajuse ne
Sai yace: tsarki ya tabbata ga Allah ana neman fatawa a gun ka kuma kai ne kake tambaya ta?
Sai yace: dole sai ka bani shawara
Sai bamajusen yace: Hakika kisrah sarkin farisa ya kasance yana zabar dukiya
Sarkin Rumawa kuma Qaisar yana zabar dagantaka da nasaba
Shugaban ku Annabi Muhammad sallallahu alaihi wa sallam yana zabar addini
Sai ka duba dawa za kayi koyi.
Ke ma dawa za kiyi koyi?
Wa zaki zaba a matsayin mijin ki?
Mai kudi?
Ko Dan dangi?
Ko mai addini?
Shawara ta rage taki ya yar uwa musulma
Allah ka azurta yan uwan mu mata da mazaje nagari
 
2 KI YI ADO DA KWALLIYA SABODA MIJIN Ki
Ki kasan ce kamar wata kyakyawar fulawa ma abociyar kyau da daukar hankali tare da kyakyawan kan shi ga mijin ki
Ki fuskan ce shi da mafi dadin kamshi da mafi kyawun tufafi
Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam yace:
“Mumini bai amfana da komai ba bayan kiyaye dokokin ubangiji mafi alkhairi gare shi sama da mace ta gari, idan ya kalle ta zata faranta masa rai”
Nana Aisha ta ce: mata ku kwadaitu da yin kwalliya ga mazajen ku
Idan kina da miji kike so kiyi masa magana toh kiyi ta a mafi kyawun yadda take
Umamatu bintul Haris tana yiwa yar ta nasiha yayin auren ta tace:
Kar idon sa ya ga mummunan abu daga gare ki
Kar hanchin sa yaji kanshi daga gare ki sai mafi dadi
Abdullahi bn Ja’afar yana yiwa yar sa nasiha yayin auren ta
Kwalliya ta zama dole a gare ki
Ki sani kuma hakika mafi kyawun kwalliya shine kwalli
Kuma mafi kyawun turare shine ruwa (yana nufin ki sance mai yin wanka a koda yaushe, saboda idan babu wanka toh kwalliya da turare basu da amfani)
Wata mahaifiya tana fadawa yar ta a lokachin auren ta
Kar ki yarda ki bar yin kwalliya
Sai yar ta ta ta kasan ce tana yiwa mijin ta kwalliya har ta wuce shekara 70 a rayuwar ta
An tambayi wani mai hikima akan wacece kyakyawar mace
Sai yace:
Itace wacce take samun damar isuwa ga idon mijin ta da hanchin sa da zuciyar sa
Asma bn Kharija alfaza’riy ya aurar da yar sa
Yayin da zai mika ta ga mijin ta, sai yace da ita:
Kar ya ji shin shi ni komai daga gare ki sai mai kyau
Kar yaga komai sai mai kyau.
Yar uwa ta musulma Ko kina kwalliya domin mai gidan ki Shugaban ki Jagoran ki
Ko kuma ballagaza ce ke kazama a cikin gidan ki
Ba kya yin kwalliya da ado sai zaki biki da unguwa ko kasuwa ko asibiti
Ya kamata mu gyara domin mu samu cikakken cigaba a cikin gidajen mu
3 KAR KI CUTAR DA MIJIN KI
Miji na kwarai Ni’ima ne, ki kiyaye shi, shine hanyar ki ta samun farin cikin duniya da lahira
Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam yana tsoratar da mace mai cutar da mijin ta, yace:
Mace ba zata cutar da mijin ta a duniya ba, har sai matar sa daga cikin HURUL IN ta ce:
Kar ki cutar da shi Allah yai wadaran ki, hakika akwai abun da zai shiga tsakanin ku, ya kusa ya rabaku ya zo gare mu
Annabi Dawood ya ce
Macen da bata gari bace a gurin mijin ta, kamar abu mai nauyin gaske ne a gun tsohon mutum
Luqmanul hakim ya fadawa dan sa
Ya kai da na ka kiyayi mace wacce bata gari bace, saboda rikicew ce kafin shekarun tsufa, ka kiyayi lalatattun mata, saboda babu abinda suke bari sai alkhairi
Wani mutum na kwarai ya auri wata mata, ta kasan ce tana cutar da shi da magana, tana wulakan ta shi, sai ya kyale ta ya tafi zuwa wata hasumiya a cikin wani dutse yana bautawa ubangijin sa, har ya mutu
Kuma bai bar komai ba na kayan duniya, sai wani karamin akwati
Sai aka kawo wa matar sa akwatin
Yayin da ta bude shi
Sai ta samu karamar takarda a ciki an rubuta
Kar ka auri macen da take cutar da kai da harshen ta da ayyukan ta
wani mutumin qauye ya auri wata mata sai take cutar da shi da harshen ta da ayyukan ta
Sai yayi mata waka
Jaki ya tafi da babar amru****bata dawo ba jakin ma bai dawo ba
Ya yar uwa ta musulma babu ke babu cutar mijin ki da ayyukan ki ko maganganun ki
Saboda wadda bata cutar da mijin ta Annabi ya fada a kan ta
Duk matar da mijin ta ya mutu yana mai yadda da ita ta shiga aljanna
Toh idan kuma ya mutu bai yadda dake ba fah
Ina zaki shiga
‘Yan’uwa zamu dakata anan sai in Allah ya kaimu mako na gaba.
4. KI KASAN CE KAMAR HAAJARA WAJAN IMANI
Imani shine rai na rayuwa, duk family din da basu da imani kamar ganye ne a cikin gagarumar iska, ki gin arayuwar ki ta aure akan imani mai karfin gaske wanda baya rawa, ki kasan ce a cikin imanin ki kamar Sayyada Haajara Allah ya kara mata yarda
Yayin da Annabi Ibrahim aminchin Allah ya tabbata a gare shi, tare da sayyada Haajara da ‘dan ta da take shayarwa zuwa garin makkah, ya bar ta a wanna wajan wanda babu ruwa babu abinchi, babu wanda aka saba da shi, babu makwabchi
Yayin da yayi niyyar tafiya sai tace masa
Ya Ibrahim ina za ka tafi
Ka bar mu a wanna filin wanda babu mutum a cikin sa kuma babu komai
Ta maimaita masa wanna maganar da yawa
Shi kuma ko juyowa gun ta ba yayi
Sai tace: Allah ne ya umarce ka da haka
Sai yace: eh
Sai ta fada da zuciya mai cikakkiyar imani: toh tabbas ba zai tozartar damu ba
Wani mutum daga cikin magaba ta na kwarai, salihin bawa, ya tafi zuwa jihadi ya bar matar sa da ‘ya ‘yan sa babu kudi,
Sai a ka cewa matar sa yanzu zaki kyale shi ya tafi kuma baku da kudi?
Sai ta fada da imani: miji na ba kowa bane sai mai kawo abinchi (dan aken da ake aiko shi ya kawo abinchi) ban cewa shi mai azurtawa bane
Idan dan ake ya tafi toh mai azurtawa baya manta kowa.
Ya yar uwa ta musulma, ke ma kina da irin imanin nan
A wani matsayi kika dauki mijin ki
Kai azurtawa ko kuma dan aike

5 KIYIWA MIJIN KI MURMUSHI
Murmushi alama ce ta sabawa, ki sanya shi akan leban ki domin mijin ki ya gani duk lokachin da ya kalleki
Manzaon Allah sallallahu alaihi wa sallam yace: “Kar ku raina ko wani irin aikin alkhairi, ko da ka hadu ne da dan uwan ka da sakakkiyar fuska”
An tambayi wani MIJI:
Menene abinda yafi faranta maka a gun matar ka
Sai yace:
Fuskar ta mai walwala da dariya, nishadin ta, tare da cikakken farin cikin ta
Dayan kuma yace: Dukkan gajiya ta tana tafiya yayin da mata ta ta fuskance ni ta na mai dariya
Na ukun yace: Murmushin mace ga mijin ta rabin farin ciki ne, daya rabin kuma yana daga yalwal da take gidan ka
Wani talakan Mabarauchi ya rayu da matar sa a cikin farin ciki da jindadi, yana kuma daga al’adar matar sa tana yiwa mijin ta ban kwana a safiya yayin da zai tafi aikin sa, tana mai murmushi kuma ta tare shi da yamma tana mai murmushi, ya kasance kuma yana son wanna abun, shi yasa ma ya nema daga gare ta ta cigaba da wanna halin na ta a duk sanda ya gan ta
Yayin da mijin ta ya mutu sai ta daukarwa Allah alkawari ba za ta kara yiwa wani murmushi bayan mijin ta
Ta rayu tsahon rayuwar ta tana mai azumin murmushi
Ya yar uwa ta musulma shin ke wa kike yiwa murmushi
Mijin ki
Ko kuma ko wani shashasha, soko
6- KI NEMI YARDAR MIJIN KI
Yardar mijin ki itace mabudin farin cikin ki, kiyi kokari ki rabauta da yardar sa, saboda shine hanyar ki zuwa gidan aljanna.
Manzan Allah sallallahu alaihi wa sallam yace: Duk matar da mijin ta ya mutu yana mai yarda da ita zata shiga aljanna
Annabi Dawood yana cewa: mace ta gari hular sarki ce wadda aka yi mata ado da zinare, duk lokachin da mijin ta ya gan ta tana sanyaya masa idanuwan sa
Sata mata ta ga mijin ta a cikin mafarki bayan rasuwar sa, yana zaune a kofar wani daki wanda yake a kulle daga cikin dakunan aljanna,
Sai ta tambaye shi na waye wanna
Sai yace: wanna dakin na ki ne, babu wata da ta taba shiga cikin sa, saboda na mutu ina mai yarda dake
Wata mata ma’abociyar addini da halaye na gari ta auri wani mai kudi dan kasuwa
Ta kasance tana himmatuwa wajan yi masa hidima kuma tana kin yin barchi saboda mijin ta
Sai yayi rashin lafiya wata rana
Sai ta zauna a wajan sa ta sunbatar hannusa da kafar sa tana kuka saboda ciwon dake damun sa
Sai aka ce da ita: me isa kike aikata wadanna abubuwan
Ki saukakawa kan ki mana
Za ki iya halakar da kan ki
Sai tace: ina aikata haka saboda yardar miji na tana bakin kofa cikin kofofin aljanna, bana so a haramta min shiga
Ya yar’uwa ta musulma, anya kuwa kina yiwa mijin ki hidima da aikace aikace
Shine yake fara yin barchi ko kece
Anya kina damuwa da damuwar sa
Inajin dai yan aikin gida ne suke kula miki da miji
Sune suke masa girki
Su share masa dakin barchin sa
Su wanke masa kayan barchin sa
Su kawo mai ruwan da zai sha
Su dauko masa jakar sa idan ya dawo daga aiki
Anya kuwa kina son ki shiga ALJANNA

Shawarwari 60 Ga Mata Don Inganta Zaman Aure
Wadannan shawarwari 60 ga matan aure domin samun zamantakewa mai inganci, da aure mai albarka. An dai san cewa mace ita ce ginshikin aure, ita ce ke iya tattalin gidanta har mijinta da sauran iyalin gidan za su sami kwanciyar hankali. Muddin kuma aka sami akasi har mace ta yi sake ba ta iya tattalin gidanta yadda ya dace ba, hakika za ta rasa gano kan yadda rayuwar aurenta za ta kasance. Ba don komai ba, sai domin gidan baki daya zai rasa alkibla sahihiya.
 
Ga shawarwarin kamar yadda wani manazarshi ya fito da shi, ya aiko mani, ni kuma nake son ‘yan’uwana mata su amfana da su. Ga su nan kamar haka:
 
  • Abu na farko da ya kamata mace ta yi a daidai wannan tsarin shi ne, ta rike wa mijinta amana.
  • Ta yi masa biyayya a kan duk abin da ba sabon Allah ba ne.
  • Ta kula da dukiyarsa
  • Ta kula da Sallah a kan lokaci. Da addu’ar zaman lafiya a kullum ta yi Sallah.
  • Ta girmama shi a gaban idonsa.
  • Ta kare girma da matsayinsa a bayan idonsa.
  • Ta so abin da yake so,  ko da ba abin so ba ne a wajenta ba.
  • Ta ki abin da yake ki, ko da ba abin ki ba ne a wajenta.
  • Ta damu da duk abin da ya damu da shi.
  • Ta kau da kai daga duk abin da mijinta ya kauda kai daga gare shi, muddin bai saba Shari’ah ba, ko da tana matukar kaunar abin.
  • Ta yi fushi, da dukkan abin da ya yi fushi da shi don Allah.
  • 12.Ta yarda da duk abin da ya yarda da shi, don Allah.
  • 13.Idan ya ba ta kadan, ta ga yawansa
  • 14.Idan ya ba ta da yawa ,ta yi godiya ga Allah, sannan ta yi masa fatan alheri.
  • 15.Ta farka daga bacci kafin ya farka
  • Sai ya yi bacci kafin ta yi
  • 17.Ta yi hakuri idan ya yi fushi
  • 18 Ta yi taushi idan ya yi tsauri
  • 19.Ta lallashe shi idan ya hasala
  • Kada ta nuna raki a gabansa
  • Kada ta yi kuka alhali yana dariya
  • Kada tayi dariya alhali yana kuka
  • Kada ta tsaya kai da fata sai ya yi mata wani abu
  • Kada ta matsa masa da bukatu
  • Kada ta rika ganinsa kamar yaron gida
  • Kada ta rika yi masa gyara barkatai, ba tare da basira ba.
  • Kada ta rika kushe tsarinsa, ko da baya kan tsari mai kyau. Sai ta yi amfani da hikima ta gyara masa.
  • Ta rika zuga shi a gaban danginta
  • Ta rika girmama shi a wajen kawayenta
  • Ta rika nuna masa abu mai kyau
  • Ta rika boye abu mummuna
  • Idan ya kawo wata damuwa gare ta, ta taimake shi ta yadda za ta iya, don ya samu ya warware matsalar.
  • Idan ya nuna ba ya son wani abu, to ta gaggauta dainawa.
  • Ta kwantar masa da hankali a lokacin damuwa.
  • Ta sassauta masa idan yana cikin bakin ciki.
  • Ta tsaya da jinyarsa idan yana rashin lafiya.
  • Ta taimake shi lokacin da yake neman taimako.
  • Idan yana cikin kunci ta sassauta bukatunta, sannan ta kame kai daga hangen na hannun wasu.
  • Ta yi masa rakiya lokacin fitarsa, ta tare shi a lokacin da ya dawo.
  • Ta tausasa harshe a lokacin da take magana da shi.
  • Ta zama mai tsaftar gida iya iyawarta.
  • Ta tsara dakinta sosai yadda zai birge mijinta.
  • Ta yi masa bankwana a lokacin balaguro.
  • Ta yi ado karshen lamba a duk lokacin da ta san yana nan, ko ma ba ya nan.
  • Ta rika bayyana halaye masu kyau ga mijinta.
  • Ishara ta ishi mai hankali da ta kula da tattalin gidanta a koda yaushe.
  • Ta bayyana kanta a matsayin mace
  • Ta iya murmushi da lafazi mai kwantar da rai
  • Ta cika zuciyarsa da sonta da kwalliyarta
  • Ta yi kokarin jan hankalinsa da abin da yake so.
  • Ta mayar masa da kyakkyawa idan yay i mata mummuna.
  • Ta yafe masa idan ya munana mata.
  • Ta karbi uzurinsa, ko da sau dari ne a duk rana ta Allah.
  • Kada ta yi sallar Nafila sai ta sanar masa.
  • Kada ta dau azumi sai ya sani.
  • Kada ta fita daga gida sai ya sani.
  • Ta iya girki kala-kala don mayar da yawu.
  • Kazantar jiki ta dade tana kashe aure, don haka tilas ta girmi wannan.
  • Kada ta shigar da wani cikin lamarinsu, sai bukatar hakan ta taso.
  • Kada ta nemi saki ko rabuwa haka kawai, sai da hakkin Allah.
Allah ya zaunar da mu lafiya da iyalanmu baki  daya, amin summa amin.
follow me on facebook follow me on twitter follow me on instagram

Fitattun labarai

Habiba complete hausa novel

Alqawarin da ciwo

Amfanin cin qafar kaza

Budurwar Roba

Amfanin lemon tsami

Afanin Zogale

Adam A. Zango

Amfanin namijin Goro (bitter kola)

Tona asiri

Yanda zaka duba sunanka a Npower