Mijina sirrina 1

 **Based on a true life story**

    _*NA​​*_
*_​​UMMI A'ISHA​​_*
*_DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN K'AI,Rabbishrahli sadri, wa yassirli amri, yafqahu qauli.._*
*1*
~~~ "Oyoyo yaya kabeer...,oyoyo yaya kabeer.."
Wannan shine ihun da yaran dake zaune cikin tsakar gida suna wasa suketa faman yi daidai lokacin da suka ga shigowar matashin saurayin wanda ke sanye cikin farar shadda kansa babu hula sai yar kyakkyawar suma da ya dan ajiye,
Fuskarshi dauke da murmushi ya rungume yaran wadanda akalla zasu kai su kimanin guda hudu,
Daga inda take acikin kitchen ta sake lab'ewa saboda bata son ya ganta duk da sanin cewar dominta yazo gidan, sadadawa tayi ta buya a bayan fridge gamida leka kanta ta window ta yadda tasan bazai iya hangota ba,
Ganinshi tayi rike da hannun Amira da waleeda kannenta sannan ga amir da husna atsaye sai faman jajja masa riga suke suna tsalle,manyan chocolate samfarin coconut chocolate ya debo daga cikin aljihunsa ya mimmikawa yaran,
Sunkuyawa yayi wurin Amira saboda itace babba tafi su husna wayo,
"Amira ina mama?"
"Tana falon abba?"
"Yaya NADIYA fa?"
"Tana kitchen mama tasata aiki.."
Murmushi yayi ya mike saboda yasan aduk inda take taji shigowarsa shiyasa ta gudu ta buya,
Yana rikeda hannun su Amira ya bi hanyar da zata sadashi da falon Abba,
Sai da ya tsaya yayi sallama mama ta amsa ta bashi izini sannan yasaka kai ya shiga cikin falon,
Mama yasamu zaune kusa da abba suna yin hira gefe daya kuma kwanukan abincine da abban yaci kasancewar bai jima da dawowa daga wurin aiki ba,
Su walida da amira na biye dashi har cikin falon sai da suka rakashi ciki sannan suka ruga da gudu suka fita,wuri yasamu ya zauna kanshi a kasa saboda kunya da kuma girmamawa,
Ganinsa yasa abba sakin fara,a tareda mikewa daga kishingiden da yake ya gyara zamansa yana murmushi,
"Kabeeru yanzu kake tafe? Barka da zuwa.."
Cikin jin kunya da sose sosen keya kabeer ya daga ido ya kalli Abba,
"Ehh wallahi abba, shigowata kenan dama nazo ne in gaisheku saboda kwana biyu ban samu damar shigowa ba.."
Murmushi Abba yasake yi ya kalli kabeer din,
"Haba kabeer har yaushene rabonka da gidan, nazaci ai jiyane kawai baka zoba amma ai shekaran jiya ma kazo kodai ka manta ne?"
Maganar da abba ya fadice tasa mama tsoma bakinta tana dan murmushi amma fuskarta babu yabo babu fallasa,
"To ai Alhaji tunda yasaba zuwa kullum jiya kuma baizo ba ai dole yaji kamar yafi sati daya rabonsa damu"
Dariya abba yayi yakoma ya kishingida yana kallon kabeer wanda ya gyara zama yafara gaisar da mama,
Shiru falon ya danyi nawani lokaci saboda shi kabeer nauyin mama da abba yakeji yanzu sam baya iya sakewa yayi hira dasu yanzu kamar da,
Ganin yanata zaune shiru sai dai dan lokaci zuwa lokaci abba yana sakoshi cikin zancen da suke yi da mama yasashi mikewa,
"Abba bari naje waje.."
"To kabeer tafiya zakayi?" Abba yafada yana gyara zamanshi,
"A'a ba tafiya zanyi ba waje zanje"
Fita yayi daga cikin falon cikeda kunya, yana fita abba ya dubi mama yana fara,a,
"Nasan dama ba tafiya zaiyi ba wurin mutuniyar tasa zaije.."
Shiru mama tayi batace komai ba saboda ita kwata kwata bata son wannan maganar saboda wani dalili wanda ta barwa zuciyarta ita daya amma idan hali yayi zata bayyanar dashi ga abban shima yaji, ganin taki zancen yasa abba barin maganar ta hanyar shigo da wani zancen daban domin ya fahimci duk lokacin da zaiyi magana makamanciyar wannan wadda ta shafi kabeer da nadiya mama bata bada goyon baya.
Yana fitowa daga falon abba cikin kitchen yawuce, a bakin kofar kitchen din ya tsaya saboda ganinta da yayi tsaye tana mopping bayan ta kammala share cikin kitchen din,
Yarinyace yar budurwa wacce bazata wuce shekaru goma sha biyar aduniya ba, tanada hasken fata amma ba farace can ba, tana sanye da atamfa kalar koriya dinkin riga da zani, daga inda yake yana iya hango gashinta dake nannade cikin dan kwalin dake daure akanta,
"Sannu da aiki.." Yafadi yana murmushi har lokacin yana tsaye akofar kitchen din,
"Sannu da zuwa yaya kabeer" tafada ahankali sannan maganar ma tayi tane cike da kunya,
"Yawwa sannu sarki aiki.."
Tunowa da tayi cewar bata gaidashi ba yasata saurin dan rissinawa,
"Yaya kabeer ina wuni?"
"Bazan amsa ba har sai kin jiyo kin kalleni ido da ido.."
  Murmushi yasaki bayan ya furta mata hakan saboda yasan ba karamin aiki ya hadata dashi ba domin kunyarshi da takeji bazai taba barinta ta iya hada ido dashi ba...

_*2*_
~~~Jin abinda ya fada ya sata sake sinne kanta kasa tana kallon tiles din dake malale a kitchen din,
"Bazaki gaida ni ba kenan in tafi ko?" Kabeer ya fada har lokacin fuskarshi tana dauke da murmushi,
"To ba na gaisheka ba kaki amsawa" nadiya tabashi amsa tana mai sake juya masa baya dan kar yaga fuskarta,
"Nadiya kenan wai wannan kunyar yaushe zaki dainata ne? Kullum idan nazo sai ki gudu ki buya alhalin nikuma saboda ke nake son zuwa gidan nan, duk ranar da ban gankiba idanuwana radadi da zugi suke yimin, kuma nazo sai ki hanawa idanuwa tozali da kyakkyawar fuskarki? Uhm nadiya? Dan jiyo mana.."
Badan taso ba ta dan jiyo dakyar tana kallon kasa,
"Kinga kyankyaso nan a bayanki.."
Tun kafin ya karasa maganar ta dako tsalle tabar wurin sai gata a bakin kofar kitchen din kusa dashi, dariya ya fara yimata domin dama yasan tana mutukar jin tsoron kyankyaso shiyasa lokuta da dama yake tsoratata dashi,
Ganin yanata dariya yasata gane cewar ba dagaske yake ba,
Fuska ta bata, "yaya kabeer ashe dama tsokanata kake?"
Dariya ya sakeyi ya daga mata gira,
"Wasane matar yaya kabeer.."
Hannuwa tasa ta rufe fuskarta cikeda kunya domin kowa adangi da haka yake kiranta tun tana yar jaririya har ta girma, kowa matar kabeer yake cemata,
"Yau ina ka bar hular taka ka taho haka?"
Sai da ya dan matsa kusa da ita sannan ahankali yace,
"Wai duk zumudin zuwa ganinki ne yasani manto wayata da hulata adaki har sai da nazo nnpc sannan na ankara.."
Dariya itama tafara yi masa, yayinda shikuma ya tsaya yana kallon yanda kumatunta ke lobawa, hakan ba karamin burgeshi yakeyi ba,
"Kici gaba da dariyar bana son ki daina"
Tsagaitawa tayi daga dariyar da takeyi,
"Yaya kabeer na kawo kayi min assignment din biology? Skeleton teacher dinmu yace mu zana nikuma ban iya drawing ba"
Makale kafada yayi,"nima ban iya drawing ba.."
"Please yaya KB"
Jin abinda tace yasashi kallonta tareda sakin wani tattausan murmushi,
"Dauko nayi miki"
"Yawwa yaya kabeer thanks.."
Rabawa tayi ta gefenshi ta wuce fuskarta dauke da murmushi, juyawa yayi ya bita da kallo, yanzu SS 2 take a secondary school alla alla yake ta kammala domin so yake ya zama mijinta sirrinta,
Yana nan a tsaye har ta fito hannunta rikeda pencil, cleaner da note book dinta sai kuma modern biology, tsayawa tayi ta bayanshi tana kallonshi domin a zahirin gaskiya yayi mutukar tsaruwa sam bashida makusa ko kadan.
Babu zato ya jiyo nan tayi gaggawar dauke idonta daga gareshi,
"Yaya KB gashi.." Tafada cikeda jin kunyarsa domin tasan yagane kallonsa ta tsaya yi,
Hannu ya mika ya karbi books din hannunta sannan ya sakar mata wani murmushi, ahankali ya furta,
"Ki ware idanuwanki ki kalleni son ranki kidaina kunya saboda nidin nakine...."
Fuskarta ta rufe da hannayenta ta juya ta nufi cikin kitchen tana cewa "kai yaya kabeer.."
Murmushi yayi kawai ya nemi wuri ya zauna kan wani dan dakali dake zagaye da wasu flowers wanda yake opposite da kitchen din,
Zana mata skeleton din yafara yi yayinda ita kuma ta kafeshi da ido tana daga cikin kitchen din bayan ta kammala mopping din da take yi,
Kallonshi ta tsaya take tayi ko kiftawa batayi,dago kanshi yayi da niyyar yi mata magana nan ya kamata tana aikin kallonshi,
Saurin kawar da kanta tayi ta juya zata koma cikin kitchen nan yayi gaggawar dakatar da ita,
"Nadiya zo nan.."
Tana rufe da fuskarta ta karasa gabanshi ta tsugunna,
"Meye kike satar kallona?? Ba nace miki idan kina son kallona kawai ki kalleni kanki tsaye batare da kunya ba..?"
"Nifa ba kai nake kalloba yaya kabeer" tafada muryarta na rawa dan jin kunyarsa,
"To naji, idan nazana miki skeleton din ai basai nayi miki labelling ba ko?"
Kai ta daga masa batare da tayi magana ba,
Murmushi yayi yaci gaba da zanen, "to bani labari inji.."
"Yaya kabeer nikuma wanne labari na iya bare in baka?"
"Ko na makarantarku ma idan kika bani ina so.."
"Ai makarantarmu babu wani labari acikinta"
"Kedai kawai bakya son ki fada min labarin makarantarku..."
Kafin ta bashi amsa mama ta zo daf dasu zata shiga kitchen domin dora tuwon dare, batare da mama tayi magana ba tasaka kai ta shige cikin kitchen,
Ganin mama yasa hirar tasu takare sai aikin murmushi da suke aikawa junansu,
Littattafanta ya mika mata ya tashi tsaye yana yimata wani murmushi wanda ita kadai ce ta fahimci sakon da yake son isar mata,
Kitchen yabi mama yayi mata sallama ya wuce batare da yayiwa nadiya magana ba amma kuma yana ta kokarin aika mata da sakon bankwana ta cikin idanuwansa sai dai ita ta kasa kallonshi, tana tsaye tana satar kallonsa har ya fice daga gidan,wucewa tayi ta nufi dakinsu itada su amira,
Akan gadonsu ta zube tana mai tuno yaya kabeer acikin zuciyarta duk da cewar har yanzu bai bude baki ya furta mata kalmar so ba amma tasan soyayya suke yi a boye ita dashi batare da sun bayyanawa junansu sirrin dake cikin zuciyoyinsu ba.


*3*
~~~Note book dinta ta bude tafara kallon zanen skeleton din da yaya kabeer yayi mata, gefe daya kuma kamshin turarenshi ne yake tashi daga cikin littafin,
Bin zanen kawai take yi da kallo tana murmushi wanda ita kanta bata san ko na menene ba amma kuma zuciyarta tafi aminta da cewar kawai na tsantsar farin cikine,
"I love you yaya kabeer.."
Tafadi ahankali tareda lumshe idonta,waleeda ce ta shigo cikin dakin da gudu,
"Yaya nadiya kizo inji abba.."
Ajiye littafin tayi ta dauki hijabinta ta fita saboda al'adar abbansu ce haka duk lokacin da ya dawo daga office ko kasuwa to tattara yaranshi yake yi a falonsa suyi hira masu wasa suyi wasansu yana zaune yana kallonsu masu karatu kuma suyi har lokacin sallar magrib yayi a lokacin ne kowa zai dauro alwala yajasu jam'i, haka sallar isha ma, wannan dalilin ne yasa su nadiya basa fita ko ina idan ba makarantar islamiyya ko boko ba sannan hakan ya haifar da shakuwa mai karfi a tsakaninsu dashi,
Ahankali ta tura kofar falon abbansu ta shiga, kishingide ta sameshi yana kallon labaran yamma a tashar AIT, can gefe daya kuma Amira ce da amir suke rubuce rubuce ajikin littafinsu na makaranta da alama home work suke yi, sai husna da walida daketa aikin mammatsa game wanda duk karar game din ta cika cikin falon,
"Sannu da hutawa abba.." Nadiya tafada tana kokarin zama kusa da abban nasu,
"Yawwa nadiya, kabirun har ya tafi ne?"
"Ehh abba ya tafi yanzu bai jima da tafiya ba.."
Shiru abban yayi ya maida hankalinsa ga kallon labaran da yake yi, ita kuma nadiya wurinsu Amira taje tasa ido tana ganin yanda suke yin home work din har mama ta shigo ta iskesu.
  K'arfe 9 nadare bayan su nadiya sun kammala cin abincin dare mama tace suje su kwanta domin har waleeda da husna sunyi bacci su amir ne kawai idonsu biyu,
D'aukar husna nadiya tayi zuwa dakinsu ta kwantar da ita akan katifarsu sannan ta sake zuwa ta dauki waleeda taje ta kwantar da ita su Amira suna biye da ita, gyarawa amir wurin kwanciyarsa tayi ya kwanta sannan itada Amira suka haye gadon dake cikin dakin suka kwanta,
Wayar mama dake ajiye a karkashin pillow dinta ta zaro ta yiwa yaya kabeer plashing, kusan kullum haka suke raba dare suna hira a wayar mama amma ita maman sam bata taba sani ba ita dai kawai tasan nadiya bata taba barin wayarta ta huta mutukar tana gida sai dai idan makaranta ta tafi to lokacin ne wayarta zata samu lafiya.
Ko minti biyu da yi masa plashing din bata yiba ya kirata,da murmushi akan fuskarta ta daga wayar,
"Yaya kabeer kaje gida lafiya?"
"Lafiya lau nadiya, yasu mama?"
"Suna nan lafiya"
"Ya kunya?"
Dariya tasa saboda jin abinda ya fada,
"Yaya kabeer kenan kaima ai ya kamata ka rinka jin kunyata.."
"Saboda me?.. "
"Saboda na cancanci hakan.."
Murmushi ya saki kafin ya bata amsa,
"See you, idan a wayane kibi ki isheni da surutu amma idan nazo sai kiyi shiru ki kasa magana kamar wanda zan kamaki"
Itama dariyar tayi, "to ba kaine ba"
"Nine me?"
"Kaine idan naganka sai naji nakasa yin maganar.."
Dariya ya sake yi, "nadiya kenan.."
"Meya faru yaya kabeeru?"
Murmushi yayi saboda jin ta kirashi da kabeeru,
"Kin ganki ko? Bakinki ya iya fadin kabeeru sake fada naji"
"Yaya KB.."
Dariya suka yi dukkaninsu musamman ma shi kabeer din wanda yake cike da nishadi cikin wannan dare,
"Yaushe zaka zo? Zaka zo gobe?"
"Yaushe kike son kara ganina? Duk lokacin da kike son sake ganina zanzo.."
"Koda kuwa yanzu ne?" Ta tambayeshi tana murmushi,
"Yes even now i shall come if you wish..."
"To ina jiranka idan har dagaske kake zaka zo din"
"Dagaske kike kina son ganina yanzun..?"
"Kaji yaya kabeer da dawasa nake? Dagaske nake mana"
K'arar bude kofa ta jiyo hakan yasata saurin dakatar dashi,
"Ina zaka zo da tsohon daren nan?"
"Sabon dare dai ba tsohon dareba,wurinki zanzo ki ganni"
"To yi zamanka na hakura da wasa nake yi.."
"Inama kiyi dagaske kigani idan zanzo ko bazan zoba"
"Yaya kabeer kenan ai nasan zaka zo"
Murmushi yayi, "to yaushe zan kawo miki budurwata ne ku gaisa?"
Jin abinda yafada yasata mikewa da sauri bayan zuciyarta ta harba, nan taji wani shiru ya ziyarci cikin kunnenta duhu ya mamaye ganinta yayinda bacin rai ya lullube zuciyarta gaba daya.  

*_4_*
~~~Hannu tasa ta danne zuciyarta gudun kada ta faso ta fito waje,
"Nadiya... Yanaji kinyi shiru ko bazaki gaisa da budurwar tawaba?"
Ajiyar zuciya ta ajiye ahankali, dakyar ta iya sassaita tunaninta tayi magana ahankali,
"Yaya kabeer me zai hana ingaisa da ita idan har ka kawo min ita?"
Dan murmushi yayi mai kayatarwa kamar yana gabanta tana kallonshi,
"Ina fata dai har zuciyarki kika fada ma'ana da zuciya daya.."
"Yaya kabeer kenan.."
"Nadiya kenan, nadiya yanmata"
Murmushin dole tayi kafin tayi magana,
"Yaya kabeer nafara jin bacci gashi kaga gobe zanje school"
"Nadiya nifa da wasa nake yimiki banida wata budurwa so karki dauka dagaske ne.."
Duk da cewar taji dadin maganarshi amma sai ta basar,
"Kaji yaya kabeer da wani zance, to idanma dagaske ne ni ba abin in tayaka murna bane??
Sanyayyen murmushi ya saki,
"Hakane to balle ma ba dagaske bane da wasane"
Itama murmushin jin dadi da farin ciki tayi,
"Shikenan tunda kaji tsoro ka sauya magana.."
Yar dariya yayi wadda har tana iya jiyo sautinta,
"Nayarda naji tsoron..."
Juyi nadiya tayi taja bargo ta dan rufe rabin jikinta,
"Yaya kabeer zan barka haka yanzu saboda kasan gobe zan je makaranta"
"To ya nadiya babu komai, Allah ya kaimu goben sai kin jini" yafada cikeda tsokana,
"Ok tom bye bye" tabashi amsa bayan ta lumshe idanuwanta, katse wayar tayi lokacin da taji yace "bye bye good night and have a nice sweet dream"
Addu'ar kwanciya bacci tayi ta shafe jikinta, da tunanin kabeer bacci yayi awon gaba da ita.
  Washe gari da misalin karfe biyu nadiya ta dawo daga makaranta dama ba makarantarsu daya dasu amir ba su akusa da gida suke ita kuma nadiya makarantarsu da dan tazara da unguwarsu, a gaggauce ta shiga gida tana shiga tasan cewar yaya kabeer yana gidan saboda taji kamshin turarensa sannan ta hango takalmanshi a kofar falon mama dan haka bata bari kowa yaji dawowarta ba ta wuce dakinsu ta ajiye school bag dinta ta fito ta shiga kitchen,
Abinci ta zuba ta zauna tana ci kamar ance kalli window tana kallon wurin tayi ido biyu dashi tsaye yana kallonta yana yi mata murmushi,
Sunkuyar da kanta tayi tadaina cin abincin, murmushi kabeer yayi ya saki karfen dake jikin window din,
"Kici abincinki dama kawai nazo ganinki ne, bari natafi inyaso sai nadawo da yamma lokacin kin gama laumar.."
Bai jira abinda zatace ba ya juya yawuce, murmushi tayi ta tashi ta leka sai da ta tabbatar da cewar yatafi baya gidan sannan ta koma ta dauki abincinta ta nufi dakin mama tana tafe tana cin abincin,
A falo tasamu mama tana shirya husna da alama wanka tayi mata,
"A'a kekuma yaushe kika shigo? Jibeki kina tafiya kina cin abinci, keda zaki yiwa wani fada amma kece meyi"
Zama nadiya tayi saboda mama kamar yayarta take sam batayi kamada mahaifiyarta ba kai idanma ba sani kayiba zaka zaci ya da kanwa ne domin kamar yadda abba yake jansu ajiki haka itama maman ke jansu ajikinta musamman ma nadiya domin kowanne abune yake damunta to ita take fadawa sannan idan shawarane ma da ita take yi,
"Hajiya mama kenan wallahi wata yunwa na debo kuma ina zuwa sai na iske yaya kabeer agidan shine nagudu kitchen na buya acan nazuba abincin nafara ci, yanzu kuma da ya tafi shine nadawo nan dan kisan nadawo.."
Tsayawa da shafa man da take yiwa husna mama tayi tana kallon nadiya,
"Nadiya wai menene tsakaninki da kabeer ne?"
Nadiya jin maganar tayi tazo mata a bazata dan haka tayi shiru tagagara bawa mama amsa wanda har sai da mama ta maimaita mata tambayar sannan tayi gaggawar zakulo amsa ta bawa Maman,
"Mama babu komai kawai zumunci muke yi tunda ni yar uwarsa ce shi dan uwanane"
"Nasani nadiya, amma bayaga wannan bana son wani abu ya hadaku muddin ba zumunci bane"
"Amma mama saboda..."
Katseta mama tayi bata barta ta karasa abinda take son tambaya ba,
"Ya isa haka bana son tambaya, ki maida hankalinki kawai kici abincin da yake gabanki"
Shiru nadiya tayi taja abincin taci gaba da ci tana ta sakar zuci saboda bata san dalilin mama na rashin son wani abu ya hadata da yaya kabeer ba amma
Koma dai menene sannu ahankali zata tambayi Maman....

 
*5*
~~~Bata kara bi takan maganar ba suka cigaba da hirarsu ita da maman har ta kammala cin abincin da takeyi ta tashi tabar falon ta koma dakinta tana rikeda wayar mama, lafewa tayi akan gadonta suna yin waya da yaya kabeer, sun dauki lokaci mai tsawo kafin suyi sallama nadiya ta tashi ta shiga wanka ta fito ta shirya tasaka uniform din islamiyyarta domin karfe uku suke tafiya su dawo karfe shida na yamma,
Hannen kannenta ta kama suka yiwa mama sallama suka tafi, sai da misalin karfe shida da yan mintuna suka dawo, dawowarsu tayi daidai da zuwan yaya kabeer shi da wani abokinsa,
Nadiya bata bari sunga fuskarta ba tafara gaidasu,
"Baiwar Allah ya kiketa boye kaine kamar marar gaskiya,kodai bakida gaskiya?" Abokin yaya kabeer din yace da ita,
"Kabarta kawai musty domin yar kauye ce" yaya kabeer yafada cikin barkwanci da tsokana, ita dai nadiya shiru tayi musu tana jinsu sai dai ta lura wannan abokin na yaya kabeer wanda aka kira da musty sai faman binta da kallo yake, duk inda ta waiga sai taga yanata kare mata kallo,
Ganin haka yasa ta takura ta shige gida yayinda yaya kabeer ya mara mata baya,
A soron gidan suka tsaya kowannensu fuskarsa dauke da murmushin kauna,
"Yaya kabeer ina ka samo wannan abokin mai shegen kallon tsiya?"
Dariya maganarta ta bashi dan haka ya fara darawa yana kallonta,
"Wai musty? Abokinane unguwarmu daya sannan tare muka yi karatu dashi"
Dan karamin tsaki taja, "Allah na tsani mutum ya tisani agaba yayita kallona"
"To yanzu dai nayi laifi tunda har na kawo wanda yayi miki abinda bakya so, ayi min afuwa..."
Murmushi tayi, "ni ai ba laifi nace maka kayi minba amma dai wannan abokin naka gaskiya ya fiya kallo da yawa"
"To ai nabaki hakuri"
"Nahakura"
"To zan iya tafiya?" Yace da ita cikin tsokana,
"Zaka iya mana yaya kabeer..."
"To fara shiga gida nagani"
Wucewa tayi tana murmushi ta shige cikin gida sannan shima kabeer din ya juya yafita.
Fuskarta dauke da fara'a ta shiga cikin gidan, zaune ta tarar da mama da kannenta tana yimusu shari'a wanda kusan kullum aikin kenan amir da amira kamar zasuga hanjin cikin junansu,
"Ke kuma a ina kika tsaya su Amira suka rigaki shigowa?" Mama ta tambayeta idanuwanta akanta,
"Mama yaya kabeer ne ya tsayar ni wallahi.."
Shiru Maman tayi ta mayar da hankalinta gasu amir taci gaba da yimusu sulhu, yayinda ita kuma nadiya ta ajiye jakar islamiyyarta ta shiga kitchen domin ta jiyo tuwon da mama keyi ya fara kauri alamun ya kama,
Itace ta karasa girkin sannan ta fito daidai lokacin abbansu ya dawo nan kuma dukkaninsu suka dunguma zuwa falonsa kamar yadda suka saba.
   Tunda musty abokin kabeer yaga nadiya yaji ta kwanta masa arai domin yarinya ce mai hankali sannan kuma mai nutsuwa gata da kunya da ganin girman nagaba, gani daya da yayi mata yasashi kamuwa da sonta dan haka batare da ya shawarci abokinsa kabeer ba ya samu mahaifinsa yayi masa maganar nadiya domin shi dagaske yake sonta bada wasa ba sannan son aure yake yimata ba na yaudara ba shiyasa ma yake son mahaifinsa yaje ya tambayo masa aurenta,
Aranar da ya sanar da mahaifinsa aranar yaje ya samu baban nadiya daf da lokacin sallar magrib, kasancewar abba mutum ne mai karrama bako sai da ya karrama baban musty sosai ya fito musu da ruwa sukayi salla kamar dama sun san juna sannan baban musty yafadawa abba abinda ke tafe dashi,
Shiru abba yayi kafin ya cewa baban musty zai tambayi nadiyan ko tasan musty din inyaso duk yadda sukayi da ita zai kirashi a waya ya fada masa, anan suka yi exchanging din phone numbers dinsu abba ya shiga gida,
Lokacin da yashiga falonsa nadiyan ya samu ita da mama suna cin tuwo tare, su kuma yaran an zuba musu taliya suna ci,
Sai da abba ya bari sun gama cin abincin sannan yayi gyaran murya yace,
"Nadiya zo nan"
Kusa dashi ta koma ta zauna, "gani abba"
"Bakon da nayi dazu saboda ke yazo.."
Ras,ras gaban nadiya ya fadi saboda bata san abinda tayiba,
"Abba laifi yace nayi masa?"
Murmushi abba yayi,
"Ba laifi kikayi masa ba nadiya, yazo nemawa dansa aurenki ne, sunan yaron wai Mustapha abokin kabeeru ne yayanki"
Ba karamin faduwa gaban nadiya ya sake yiba, nan fuskar musty ta bayyana acikin zuciyarta lokacin da ya kafeta da ido yana yi mata wannan kallon kurullar....

 

*6*
~~~Shiru nadiya tayi saboda bazata iya fadawa abba cewar yaya kabeer take so ba,
"Nadiya ya naji kinyi shiru ne?"
Muryar abba ta dawo da ita cikin hayyacinta,
"Abba babu komai.."
"To Mustapha dai ya turo mahaifinsa tunda babu wata matsala zan sanar dasu inyaso yafara zuwa har kusamu ku daidaita"
"To abba" ta fada kanta akasa, ita dai mama tana zaune tana jinsu amma har akayi aka gama batace ko uffan ba,
Mikewa nadiya tayi ta fita zuwa dakinta gaba daya tama rasa abinda yake yimata dadi acikin zuciyarta, gashi bata son fadawa yaya kabeer domin gudun sakashi cikin damuwa,please call me ta tura masa nan take ya kirata,
"Yaya kabeer yau ban ganka ba"
"Nidinma yau ban samu ganin fuskar gimbiya nadiya ba amma nasan dalili.."
"Wanne daliline?" Ta tambayeshi cikin dokin jin abinda zai fada,
"Yau naje unguwa ne sai dazunnan nadawo shiyasa ban shigoba, amma gobe sammako zan dako da sassafe inyi karin kumallo da kyakkyawar fuskarki"
Dariya abinda yafada ya bata dan haka tafara dariya,
"Kaji yaya kabeer da abin dariya sai kace wani abinci da zakace zakayi karin kumallo da fuskata"
"Ni ai kinfi abinci, da ace za a ajiye min ke inyita kallonki to da na tabbata bazanji yunwa ba.."
Wata dariyar ta sake yi har tana kokarin fadowa daga kan gadonta,
"Yaya kabeer zaka sa cikina ya fashe dan dariya gashi dama naci tuwo na koshi dayawa.."
"Wai wai, wai, overfeeding kikayi ai? Oya tashi ki fara exercise ina jiyoki daga nan"
Tashi tayi tana dan murmushi,
"Allah yaya KB jina nakeyi nagaji nidai ban son exercise dinnan.."
"To yi tsalle guda goma ina kirga miki, oya fara"
Tsalle tafara tanayi yana kirga mata har sai da tayi guda ishirin sannan ya barta takoma saman gado ta kwanta tana haki,
"Washh, yaya kabeer wlhi kabani wahala da yawa"
"Waye yasa kici abinci yayi miki over?"
"Kaine.."
"A'a ni karki yimin sharri.."
Murmushi tayi kafin tabashi amsa wayar tayi shutdown, komawa tayi ta kwanta tana cikeda farin ciki.
Kamar yadda kabeer yafada kuwa da safe sai gashi yazo lokacin ko school su nadiya basu tafiba, asalima lokacin suke shiryawa, kanta babu ko dan kwali tana cikin kitchen tana cin soyayyen dankalin da mama ke soyawa sai gashi ya shigo, ba karamin mamaki nadiya tayiba domin ta zaci wasa yake yimata da yace zaizo da sassafe ya ganta,
Dan tsananin kunya kasa gaisheshi tayi tana jinshi da mama suna gaisawa daga nan yawuce ciki falon abba,
Bata bari yaji fitarta zuwa makaranta ba ta zare jiki tagudu.
  Abangaren Mustapha kuwa ba karamin dadin labarin da mahaifinsa yazo mishi dashi yajiba musamman ma da yaji cewar ba ayiwa nadiya mijiba asalima ko tsayawa da samari bata fara yiba,wanka ya dauka ya shirya ya fito ya nufi gidansu nadiyan,
Tana falon abba tana yiwa su amir homework yaro yayi sallama yace wai nadiya taje inji Mustapha, kamar bazata yi motsiba har saida taji mama tayi magana sannan ta tashi tafita zuciyarta babu dadi,
Tsaye ta sameshi ya saka hannuwanshi acikin aljihu yana yimata murmushi sai dai ita ko kadan bai burgeta ba, sallama tayi masa ya amsa cikeda kulawa nan suka gaisa yafara koro mata jawabi,
"Nadiya wato tun ranar farko dana soma ganinki Allah ya jarrabi zuciyata da sonki da kaunarki saboda yabawa da nayi da hankalinki da nutsuwarki,ina fata zaki bani hadin kai har nakai ga cimma burina da muradina na mallakarki..."
Saida taji yayi shiru sannan tayi magana,
"Yaya Mustapha nagode da soyayyar ka agareni,hakika duk Wanda yace yana sonka to ya gama yimaka komai kuma bakada kamarshi,to amma nikuma inada wanda nakeso"
Cikeda mamaki ya kalleta saboda shidai mahaifinsa yace mahaifinta ya sanar dashi babu wanda yake zuwa wurinta,
"Kina da wanda kikeso? Waye?"
"Yaya kabeer ne abokinka"
Jin abinda tace yasashi yin shiru nawasu yan lokuta kafin daga bisani ya kalleta,
"Shikenan nadiya nagode da kika fada min gaskiya baki rufeni ba, kuma nayi farin ciki da jin cewa kabeer ne wanda kike so domin mutumne shi mai kyakkyawan hali da dabi'a mai kyau, Allah ya tabbatar da alkhairi"
Sallama yayi mata ya tafi nan itama ta juya ta shiga cikin gida tana dauke da farin cikin cewar tagama da babin Mustapha..


*7*
~~~Hankali kwance nadiya ta koma gida taci gaba da gudanar da harkokinta, soyayyarsu itada yaya kabeer kuwa kullum sake yin gaba take tana kara kulluwa, koda yaushe suna makale awaya suna hira, sannan kusan koda wanne lokaci yana gidan mutukar nadiyan tana nan.
   Tunda nadiya ta sanarwa da mustapha cewar tanada wanda take so yaji hankalinsa ya dan tashi amma idan yatuno da cewar kabeer ne wanda take so din sai yaji ranshi ya danyi fari saboda yasan kabeer zai riketa riko na gaskiya wannan dalilin ne ma yasashi sanarwa da mahaifinsa yanda suka yi da ita, shima mahaifin nasa baiyi k'asa a gwiwa ba ya kira abban nadiya ya fada masa abinda yafaru gudun kar aga musty din yadaina zuwa bayan kuma manya sun shiga, shiru abban nadiya yayi saboda shidai a iya saninshi nadiya bata da wani saurayi amma tunda yaji haka to ya zama dole ya tuntubeta da zarar ya koma gida.
  Kamar yadda al'adar gidan take yauma zaune suke dukkaninsu a falon abba suna kallon tashar mbc drama, rage karar volume din tv din Abba yayi yace,
"Yawwa nadiya kafin na manta zo ina son magana dake.."
Kusa da mama ta dan matsa tana kallon abba,
"Nadiya yaron nan mustapha da yazo wurinki yace kince masa kinada wanda kikeso hakane..?"
Kai ta dagawa abba, "hakane Abba"
"To waye?" Abba yasake tambayarta, kamar bazata yi magana ba dan kunya ta daure tace,
"Abba yaya kabeer ne"
Shiru abban ya danyi fuskarsa dauke da murmushi,
"To kira min kabeer din, dama yau ai naga baizo gidanba"
Tashi tayi ta fita tana cikeda murna, wayar mama ta dauka ta kirashi,
"Yan mata.."
"Yaya kabeer albishirinka?"
"Goro" yafada yana murmushi,
"To kazo abba yana kiranka"
"To ai baki fada min albishir din da kika yimin ba"
"Idan kazo zakaji"
"To gani nan zuwa"
Katse wayar tayi ta koma falon abba tana jin kamar ta daka tsalle dan tsananin murna,
Tana shiga falon abba ta dan saci kallon mama nan taga fuskar Maman babu walwala sosai amma dai batayi magana ba,
Nan kuma taji ranta ya dan sosu saboda tasan bacin ran mama yanada alaka da maganarsu itada kabeer tunda tun jimawa Maman ke yimata gargadin cewar karta bari soyayya ta shiga tsakaninta da kabeer,
Tana ta tunanin abinda zaije yazo aranta taji sallamar yaya kabeer nan tayi hanzarin jan hijabinta ta rufe fuskarta saboda kunya sai dai amma tun kafin ya karaso kamshin turarensa ya rigashi karasowa,
Cikin nutsuwa yayi sallama ya shiga bayan abba ya amsa masa, nan kuma su amir sukayi kansa suka cuccukumeshi domin yasaba basu sweet duk lokacin da yazo,
Yau dinma saida yabisu ya basu daya bayan daya sannan suka kyaleshi ya nemi wuri ya zauna, cikeda girmamawa ya gaisheda abba da mama,
"Kabeeru dalilin da yasa kaji nace kazo shine nadiya ce tazo min da wani zance cewar kai da ita kuna son junanku hakane?"
Sunkuyar da kai kabeer yayi cikeda kunya yace "hakane abba"
Dan fara'a abba ya fadada cikeda jin dadi yace,
"To kabeeru babu shakka naji dadin wannan labari domin hakan zai kara dankon zumunci da aminci a tsakaninmu domin nadiya yar uwarkace, sannan ni mahaifinka ne ako ina zan iya tsayawa in nema maka aure bare agidana,dan haka ni a matsayina na mahaifin nadiya nabaka ita a matsayin matar aure ko bana raye ban yadda nadiya ta auri kowanne namiji ba face kai har sai dai idan kaine ka sauya akalarka, dan haka abinda nake so dakai shine da zarar ka koma gida ka sanarda yaya cewa ga abinda mukayi dakai saboda sonake yi nadiya na gama makaranta ayi bikinku da ita batare da andauki dogon lokaci ba"
Ai kabeer najin abinda Abba yace yaji kamar an yimishi bushara da gidan aljanna, nan wani dadi ya rufeshi zuciyarsa ta samu wata nutsuwa mai kayatarwa tuni yafara yiwa abba godiya,
"Abba nagode madalla, Allah yasaka da alkhairi, Allah yabar zumunci abba.."
"Babu komai kabeer ai duk abinda nayi maka kaina nayiwa domin kai d'anane halak malak"
Saida kabeer ya sake jaddada wata godiyar sannan ya tashi ya fita, cikeda jin kunya nadiya tabi bayanshi, tana zuwa tsakar gida kuwa ta iskeshi lafe ajikin bango dama ita yake jira ya harde hannuwansa ajikin kirjinshi,
Kallonshi tayi yasha gaye cikin wata rantsattsiyar purple colour din shadda galila wacce tasha dinkin buba dan haka ba karamin kyau yayiba,
"Yanzu kaji albishir din da nayi maka dazu?" Tafada cikeda murmushin kunya,
"Naji wannan dalilinne ma yasani shirya baki tukwici, rufe idonki"
Rufe idonta tayi tana murmushi, "yaya kabeer Allah dai yasa nima chocolate din zaka bani irin wacce kabawa su amir..."
Bata iya karasawa ba saboda jin lebenshi akan nata, take jikinta yafara rawa tayi gaggawar bude idonta, nan ta juya zata gudu yayi saurin rikota,
"Ai abba yace yabani ke ko baya raye nine mijinki, tsananin farin cikine yasa kikaga nayi miki haka so karki fassara ni da wata manufa, ko ba komai dai kin san ni yayanki ne dan haka bazan taba cutar dakeba"
Har lokacin bata iya yin magana ba saboda tsantsar kunyar da ya haddasa mata,
"Yaya kabeer nidai.."
Hannunta ya rike ya matsa kusa da ita tareda leka fuskarta wadda ta kawar gefe guda,
"Kedai me?"
"Nidai kasani jin kunya"
Murmushi yayi ya mike tsaye yana kallonta zuciyarsa cikeda farin ciki...


*8*
~~~ "Wai kina nufin haka zamuje gidan kina yimin wannan kunyar?"
Murmushi ta danyi "wai yaya kabeer ni duk ba wannan ba yaushe zaka zo muyi hira irin wacce muka dade ba muyiba?"
Daga kai yayi yana kallon sararin samaniya alamun tunani fuskarsa kuma kunshe da murmushi,
"Uhmmm, ina jin zanzo a weekend saboda ranar ne banida aiki da yawa sannan kema kina gida.."
"To Allah ya kaimu, yanzu dai bari nakoma ciki saboda kai naga kana cikin farin ciki.."
Dakatar da ita yayi ya hanata tafiya,
"Ina kuma zakije bayan akwai labarai da yawa da nake burin ji daga gareki"
"Labari kuma yaya kabeer? A wannan daren?"
"To da sai awanne daren?" Ya tambayeta yana murmushi,
"A'a yaya kabeer karfa ka sauya min maganata zuwa wata daban"
Murmushinsa ne yasake karuwa, "kaji min yarinya da wayo, wai ke waye ya koya miki wayone? Ni ban taba ganin first born mai wayo irin nakiba"
Dariya tayi ta rufe fuskarta, "har nakaika wayo? Kaima fa first born dinne amma kafini wayo ma"
"A'a ban fiki wayoba zadai muzo daya, musamman ma tunda zuciyoyinmu sun kasance guda daya, sannan nan bada dadewa ba zamu zama abu daya..."
Dariyace ta kwace mata nan tayi baya da sauri tana dariya,
"Nidai yaya kabeer natafi da wannan sai anjima.."
Shima dariyar yayi ya daga hannu alamun bye bye yana cewa,
"Ok bye yanmatan yaya kabeer"
Har taje daf da dakin mama dariyar take, a kofar daki taga mama tsaye fuskarta babu walwala sannan da alama ita take jira,
"Mama..."
"Zo nadiya" Maman ta fada idonta har ya danyi ja saboda bacin rai, jiki asanyaye nadiya tabi bayanta zuwa cikin bedroom dinta domin basu tsaya a falo ba,
Zama mama tayi agefen gado itama nadiyan ta zauna,
Kamo hannuwan nadiya mama tayi tana kallonta,
"Nadiya nasan ke yarinyace karama wacce bata gama sanin rayuwa ba, wadda hankali bai gama ratsata ba, wacce bata san rayuwar aure ba, wacce bata san irin gwagwarmayar da kowacce mace keyi agidan aurenta ba, bawai ina son rabaki da kabeer bane nadiya a'a sai dai ina son kisani shi auren zumunci yafi komai gyara zumunci idan har yayi dadi amma yafi komai b'ata zumunci mutukar baiyi dadiba shiyasa zakiga tun farko ban so soyayyarku da kabeer ba saboda kabeer dan dakinane akwai zumunci mai karfi tsakanina dashi haka iyayensa, bana son azo ayi abu ba aji dadinsa ba zumunci ya baci.."
Gaba daya jikin nadiya yagama yin sanyi saboda jin abubuwan da mama ta fada dan haka take taji jikinta ya fara yar rawa,
"Mama kiyi mana addu'a kawai akan Allah yasanya albarka acikin al'amarin amma ni sam bazan iya rabuwa da ya kabeer ba saboda nafara sonsa tun ban san wacece niba.."
Shiru mama tayi tana kallonta batare da tace komaiba, ita akwai abinda ta dade tana hangowa wanda ita nadiya ko kadan bazata iya hangoshi ba domin akwai kuruciya atattare da ita sosai saboda gaba daya yanzu bazata wuce shekaru 15 ba aduniya dan haka yanzune tafara saninma menene rayuwar,
"Shikenan nadiya tunda kin kasa fahimtata shikenan bazan hanaki abinda kikeso ba Allah ya sanya alkhairi da albarka acikin tarayyarki da kabeer"
Idanuwan nadiyane suka ciko da kwalla nan tayi saurin tashi ta fita saboda sai take jin kamar yanzu ne zata tafi tabar mamanta da yan uwanta,
Duk da cewar mama sunyi haka da nadiya bata iya hakura ba tashi tayi taje ta iske abba a falonsa yana zaune shida su amir da waleeda nan ta tashesu tace sutafi dakinsu suje su kwanta,bayan fitarsu ta samu wuri ta zauna kusa da abba,
"Abban nadiya wata magana nake son muyi dakai amma ta fahimta, dafarko ina son ka fahimceni ka gane cewar ni bawai bana son kabeer ne ko kuma yana da wani mummunan tabo awurina ba, kawai nidai bana son maganar aurensa da nadiya ne saboda auren zuminci bashida alfanu mutukar ba ayi daceba amma idan har aka dace yayi dadi to zumunci yana sake kulluwa,
Ban so lokaci daya farat daya ka amince ka bawa kabeer nadiya ba saboda gaskiya nidai auren zumunci baya daya daga cikin abinda nake son yiwa 'yayana.."
Abba bai tanka ba har saida yaji tayi shiru alamun ta gama sannan yafara magana da tausasashiyar murya,
"Haba hajiya bilkisu, ai kabeeru dan dakinki ne, kin sanshi kin san halinsa sannan kin san ko wanene shi tun yana yaro dan haka bakida kokwanta acikin halayyarsa, kuma insha Allah wannan auren akwai alkhairi acikinsa ba kadanba da yardar Allah sai kowa yayi alfahari dashi kedai kawai kiyi musu addu'a kuma ni ina ganin da ace mu dauki nadiya mu baiwa wani wanda bamu saniba, bamu san asalinsa ba bamu san halinsa ba bamu san ko waye shiba gara mu baiwa na gida wanda muka san tushensa muka san komai nasa.."
Jijjiga kai mama tayi alamar gamsuwa da bayanin da yayi mata sai yanzu ta danji ta samu nutsuwa akan zancen,
"Shikenan to Allah ya tabbatar da alkhairi"
"Yawwa hajiya bilkisu addu'ar da zamuyi kenan, kinga yanzu tana aji biyar next term zata shiga aji 6 nan da wata shekarar insha Allah zamu yi bikinta mu kaita gidan mijinta, amma kafin nan ina so nayi miki albishir da cewar keda ita yar taki na biya muku saudiyya zakuje ku sauke farali sannan ku iyo addu'a akan Allah ya basu zama lafiya da zuri'a dayyaba"
Murna ce ta kama mama saboda jin albishir din da abba yayi mata nan ta hau fara'a tana mai yimasa addu'ar Allah ya kara masa budi acikin harkokinsa...

*9*
~~~Nadiya na shiga d'aki ta kifa kanta jikin gado tafara rera kuka ahankali wanda ita kanta bata san dalili ba amma dai tafi zargin cewa na fargabar rabuwa dasu mama ne, shigowar su Amira da taji ne yasata yin shiru ta tashi ta shiga toilet, sai da ta gyara fuskarta sannan ta fito lokacin harsu waleeda sun kwanta,
Itama kwanciyar tayi ta dauki wayar mama dake wurinta tafara yin game, kiran yaya kabeer ne ya shigo nan ta d'aga jikinta a sanyaye,
"Yaya KB ya kaje gida?"
"Ni ai nayi fushi dake, wato ko ki kirani kiji yaya naje gida ko?"
"Ayya haba yaya KB ai kasan dai inada niyyar kiranka kawai dai Allah ne baiyi ba"
Jin yanda ta marerece murya ya sashi yin yar dariya mai dan sauti,
"Dadina dake ba a kada ke a magana mutukar a wayane amma idan a filine kuma kinfi kowa shiru"
"Ai kai dinne yaya kabeer kwarjini gareka, kwarjini kake yimin"
"Wanne irin kwarjini kuma?" Ya tambayeta ranshi cikeda farin ciki,
"Yaya kabeer in tambayeka mana"
"Allah yasa nasani yanmatan yaya kabeer"
Murmushi tayi ta sake makale wayar a kunnenta,
"Yaya kabeer kuma idan muka yi aure shikenan bazaka rinka kawoni gidan mama kullum ba ko?"
Dariya ya fara yi mata saboda jin yarinta afili,
"Haba nadiya kuma idan kikace kullum zan rinka kawoki ai sai su maman ma su gaji dake"
"To yaya kabeer kazo mu zauna agidan su Maman mana gaba daya basai munje gidanmu ba"
"Nadiya kenan, ke karamar yarinyace baki san menene aure ba, ko kin sani?"
"Nasani mana yaya kabeer"
"To fada min menene aure"
Shiru ta danyi tafara tunani kafin tayi magana,
"Yaya kabeer aure shine idan saurayi yaga budurwa yake sonta itama take sonshi sai ayi musu aure.."
"Daga nanfa?" Ya sake tambayarta,
"Sai akaita gidan da ya gina mata, iyayenta su siya mata kayan daki"
"Uhum daga nan kuma fa?"
Dan shiru ta sakeyi sannan taci gaba,
"Sai ya siyo kayan abinci ta rinka yi masa girki tana share gida tana yin wanke wanke"
"Shikenan?"
"Ehh" tabashi amsa tana murmushi, shima murmushin yayi,
"Shikenan kin gama?"
"Nagama mana"
Dariya yafara yi yana dad'awa har na tsawon wani lokaci domin sai yau yagama tabbatarwa da nadiya karamar yarinya ce wadda kuruciya ke dawainiya da ita,
"Ba ayi muku biology ne nadiya?"
"Ana koya mana.."
Shiru yayi saboda baya son yasata taji kunya shiyasa bai son fada mata kai tsaye,
"To tunda baki san menene aureba nabaki assignment ki zauna ki nutsu ki gano min menene aure"
"To yaya kabeer zan yi"
Murmushi ya dan yimata sannan yayi mata sallama,ajiye wayar tayi tanata tunanin maganganun da sukayi da yaya kabeer yanzu,
To ita yanzu tayaya zata samo wannan assignment din da yaya kabeer yace ya bata? Ta raya hakan acikin ranta, gyara kwanciyarta tayi taci gaba da tunani can sai ta tuno cewar yan ajinsu dayawa tana ganinsu suna karanta littattafan hausa sannan kuma tana yawan jinsu suna labarin aure ko labarin soyayya amma ita bata taba tsoma bakinta aciki ba amma itama daga gobe zata fara aro littattafai tana karantawa domin ganin abinda ke tattare aciki,
Sati biyu da kiran da abba yayiwa kabeer mahaifin kabeer suka zo domin su tattauna da abban nadiya.
***
Alhaji Bashar Usman da Alhaji Mu'az usman yan uwan junane ciki daya uwa daya uba daya suna da kanne mata guda uku wadanda yanzu haka kowaccensu tana can agidan mijinta tareda yaranta, Alh Bashar shine babba sai mai bi masa alh mu'az daga nan sai Hajiya Kubra sai haj sa'ade sai yar autarsu hajiya Maimuna,
Asalinsu yan jahar kano ne cikin wata karamar hukuma wacce ake kira da Rano, anan suka taso dukkaninsu sannan har yanzu anan kowannensu yake zaune tareda iyalinsa hajiya kubra ce kadai ke zaune a karamar hukumar sumaila, shi abbansu kabeer yana zaune a tsohuwar G. R. A, shi kuma abbansu nadiya yana zaune a unguwar Rano Quarters,
Alh bashar yana da 'yaya guda hudu biyu maza biyu mata, kabeer shine babba sai Fati wacce ke binsa daga nan sai Muhammad sai autarsu A'isha,
Tun lokacin da aka haifi nadiya yan uwa da dangi keta tsokanar kabeer suna cewa an haifa masa mata, haka itama nadiyan koda yaushe dangi da yan uwa cikin tsokanarta suke suna kiranta da matar kabeer, tun kabeer bai dauki abun da gaskeba har yazo ya fara yarda da abinda 'yan uwa ke fadi tsakaninsa da nadiya,
Ita kuwa nadiya lokacin ma bawani kwakkwaran sani ta yiwa yaya kabeer dinba amma kowa yazo gidan sai taji yana cewa "matar kabeeru" duk sanda aka tsokaneta da wannan sunan kuka take yi domin bata sanshi ba.....


 *10*
~~~~Lokacin da nadiya ta dan fara hankali a lokacin ne ta gane yaya kabeer sai ta tsinci kanta cikin jin kunyarsa, haka kawai take jin kunyarsa sam bata yarda suna haduwa dashi, shikuma gidansu nadiya wurin zuwansa ne koda yaushe kusan kullum sai yaje gidan tun bai fara jin son nadiya ba har yaji yafara sonta lokacin yana makarantar gaba da secondary wato jami'a, da sonta yayi karatunsa yagama yafito yazo ya kama aiki a wani kamfanin turawa dake nan cikin garin rano,
A boye suke gudanar da soyayyarsu ba tare da kowa ya furtawa dan uwansa ba amma su da kansu sun yarda cewa soyayya suke yi.
***
  Abban su kabeer da kanshi yaje yasamu abban nadiya domin kabeer ya sanar masa yanda suka yi da abbansu nadiya, gaba daya iyayen nasu abin ba karamin dadi yayi musuba musamman ma mahaifiyar kabeer domin tana mutukar kaunar nadiya tun lokacin da aka haifeta, kullum ita kenan aiken nadiya tazo tayi mata hutu amma ko sau daya nadiya bata taba zuwaba sai dai lokaci zuwa lokaci suna zuwa agaisa itada mama dasu Amira,
Tunda mahaifiyar kabeer taji maganar auren nan tarasa inda zata tsoma ranta dan dadi, nan da nan tace sai afara tanadi.
Batun soyayyar nadiya da kabeer kuwa abinsu gwanin sha'awa domin suna gudanar da soyayyarsu cikin burgewa da kulawa da juna,
Koda yaushe yana gidan wai zai koya mata karatu amma kuma ba karatun suke yiba soyayyarsu kawai suke yi, yanzu itama nadiyan ta tsunduma harkar karance karancen littattafan hausa dan haka tana karuwa da abubuwa da dama wadanda ada bata sansu ba.
  Term din da suke ciki yana karewa ta shiga SS 3 a lokacin suka tafi aikin hajji ita da mama, ba karamar tsaraba ta jibgowa yaya kabeer ba tayi masa siyayya ta burgewa mai yawan gaske musamman ma turaruka da jallabiyoyi kala kala,
Ranar da zasu dawo kabeer ne yaje airport domin daukosu, tun karfe 6 yake airport din amma jirginsu bai sauka ba sai misalin karfe 9 nadare,
Kallon nadiya kawai ya tsaya yi domin hakorin da tasako ba karamin kyau yayi mata ba, ganin mama nema ya hanashi magana,
Nan ya daukosu suka nufi gida, lokacin da sukaje mama fita tayi tana rike da jakarta nan itama nadiya ta yunkura zata fita kabeer yayi saurin riketa,
"Hajiya nadiya ina kuma zakije bamu gaisa ba?"
Murmushi tayi saboda jin ya kirata da hajiya,
"Inye muga hakorin Allah yayi miki kyau"
Hannu tasa ta rufe bakinta tana dariya, "haba yanmata na mugani mana"
Dakyar ta iya bude bakinta yagani, hannunta ya saki yana murmushi,
"Kinyi kyau sosai"
"Nagode yaya kabeer"
Tare dashi suka shiga cikin gidan yana rikeda kayansu da ya dauko musu daga nan yayiwa mama sallama ya tafi.
  Tunda su nadiya suka dawo kuma kabeer yaci gaba da zuwa gidan koda wanne lokaci,itama mama yanzu ta hakura tana son auren saboda ganin irin gata da soyayyar da Maman kabeer ke nunawa nadiyan sannan dama kabeer yarone mai biyayya
Nadiya taci gaba da zuwa makaranta sannan soyayyarsu da yaya kabeer na tafiya yanda ya kamata sai dai kuma yanzu nadiya ta dan fara d'ar d'ar da auren yaya kabeer saboda wani dalili,
Dalilin kuwa shine ayanda ta fuskanta yaya kabeer yanada yanmata masu yawan gaske, tun abin baya damunta har yafara damunta domin akwai lokacin da suka fita dashi ita da waleeda ta rakasu zai kaita shopping lokacin da sukaje shopping din suna gab da kammalawa wata budurwa tazo anan yatafi wurinta ya barsu nadiya, tun daga irin tsaiwar da sukayi da budurwar zaka fuskanci cewar saurayi da budurwa ne baya ga haka kuma sai kwantar da murya yake yi duk da dai nadiya bata jin abinda yake fada amna tagane cewar hakuri yake bawa yarinyar, anan ya kirgo kudi ya bata yadawo wurinsu nadiya wacce tagama shakar bacin rai,
Ko takansa nadiya bata bi ba taja hannun waleeda suka fita sai shine ya dauko kayan da suka siya bayan yabiya kudin,
Motarshi ya bude ya saka kayan sannan su nadiya suka shiga suka zauna, baiyi magana ba itama nadiyan haka nan yaja motar suka tafi,
Tana kallonsa anata kiranshi awaya yana katsewa daga baya kuma ya dauka yace zai kira anjima,
Wani haushine ya cika mata ciki domin koda yaushe ahaka yake ayita kiransa awaya yana rejecting ko kuma ya dauka yace zai kira ko ba afada mata ba tasan cewa yanmata ne ke kiransa domin yaya kabeer kyakkyawan namijine mai jida kyau da kuruciya sannan ga abin hannu domin aikin da yake yi da turawa yasamu nasibi sosai acikinsa sannan gashi da ilmi wannan dalilin ne yasa yasamu karbuwa sosai ake damawa dashi har kasashen waje suke fita aiki shiyasa kowacce mace zata yi burin mallakarsa,
Babu wanda yayi magana acikinsu har sukaje gida amma kafin su karasa an kirashi awaya yafi sau 30 wanda kusan duk kiran na yanmata ne,
Waleeda yabawa kayan ya rike hannun nadiya tamau tayadda bazata iya kwacewa ba, sai da yaga waleeda ta fita sannan ya sawa motar lock ya kalleta....


*11*
~~~D'auke kai nadiya tayi ranta fal da takaici ita yanzu jin yaya kabeer take yafara fita aranta saboda kule kulen yanmatanshi, baya minti biyar sai mace ta kirashi sannan takasa gane alakarshi da wadannan tulin yanmatan,
"Yan matanah.." Muryarshi ta katse mata tunanin da takeyi,
Sam kin juyawa ta kalleshi tayi maimakon hakama sai kokarin kwace hannunta da ya rike tafara yi,
"Juyo mana kiji abinda zan fada miki yanmata na"
Nan dinma dai sake kawar da kanta tayi bata juya ta kalleshi ba ita bakin cikin da takeyi shine yanzu saura yan watanni kadan tayi candy kuma da zarar tagama school bikinsu za ayi ita dashi to haka zaije yana yimata wadannan kule kulen yan matan sai kace wani marar aji?
"Haba nadiya ta, ya kamata ki kasance mai yimin uzuri da afuwa akoda wanne lokaci, dan Allah ki saurareni kiji.."
Jin ya hadata da Allah yasata juyawa ta kalleshi,
"Ina jinka"
"Nadiya nifa wadda kika ganni da ita ba budurwata bace kanwar abokina ce, abokin nawa ma yanzu ba a kasar nan yakeba to shine tace wai in dan taimaka mata saboda sha'anin karatu dalilin dayasa kenan kika ga na dauki kudi nabata amma tunda bakiji dadiba kiyi hakuri.."
Shiru ta danyi na dan wasu sakanni tana nazari, nadiya yarinyace mai wayo da basira da kaifin kwakwalwa shi kansa ya shaida haka sannan gata da saurin gano abu shiyasa wani lokacin har tsoron yimata karya yake yi domin atake zata gane kuma tafada masa sai dai kawai yaji tace "yaya KB nagane logic din.."
Dagowa tayi ta kalleshi suka hada idanu abinda bai taba faruwa ba domin tsananin kunyarsa da takeji baya barinta ta iya hada idanu dashi,
"Yaya KB idan har wannan budurwar kanwar abokinka ce baka da alaka da ita meyasa zaku ware ku koma wuri daya bazaku gaisa ku tattauna agabanmu ba?
Meyasa zaku rinka maganganu kasa kasa alamun bakwa son kowa yaji abinda kuke cewa ciki har dani wacce kake shirin zama MIJINA SIRRINA, ni aganina ai duk wani abu wanda ya shafeka nima ya shafeni babu boye boye a tsakaninmu.."
"Hakane nadiya, amma kisani komai yana son sirri, yanzu yarinyar nan da agabanku ne bazata iya rokona kudin ba saboda bani kadai bane.."
"To amma da kuka gama yaya kabeer meyasa ko gaisawa baka kawota munyi ba a matsayina na kanwarka mai shirin zama matarka sirrinka?"
"Ohhh nadiya kin fiya rigima, ki yarda dani wannan yarinyar banida alaka da ita"
"To naji nayarda amma masu kiranka awaya tun dazu sukuma suwaye?"
Sumar kanshi ya shafa kafin yabata amsa "yan companynmu ne"
"Yan campanynku ne amma shine ka gagara daukar wayar saboda ina wurin?"
"Amma dai ai kinga driving nake ko"
Murmushin takaici ta danyi saboda har yanzu bata yarda da abinda yafada ba, "yaya kabeer gaskiya nidai bana jin dadin wannan abinda kakeyi, idan har zaka aureni to meye naka na kule kulen yanmata? Nasan dama tunda kana da kyau da kudi yanmata dole zasu soka to amma ai wannan ba yana nuna cewar ka sakar musu fuska kayita kulasu ba.."
"Wai nadiya yaushe muka fara yar haka dakene? Kodai wasu kika samu suke zugaki awaje?"
"Ko kadan ba maganar zuga bace yaya kabeer maganace ta gaskiya nidai bana son wannan kula yanmatan da kakeyi"
"Shikenan naji kuma zan kiyaye, shikenan?"
"Shikenan, bude min zan fita"
Juyo da fuskarta yayi yana murmushi,
"To ai baki tabbatar min da cewa mun shirya din ba"
"Mun shirya karka damu"
"To sai yaushe?"
"Sai da daddare idan kadawo"
"To kiyi min dan murmushi nagani mana"
Yanda yayi maganar ne yasata yin murmushin ba tareda ta shirya ba, nan ya bude mata kofar ta fita ta shiga gida, ko mama bata fadawa abinda ya faru ba tabar maganar aranta shi dinma da yadawo da daddare bata nuna masa ba.
  Kwana biyu da faruwar haka yace ta shirya zai zo ya kaita wurin mama su gaisa, nan ta shirya taci ado cikin wani swiss material blue, tasa mayafi da takalmi blue da jaka, ba karamin kyau tayi ba nan yazo suka tafi tareda su husna wadanda zasu rakata dama ka'idar gidan duk inda zataje to dasu husna take tafiya ko walida idan kuma basa nan to Amira ko amir acikinsu wani zai rakata,
Yana driving suna hira har suka hau titin da zai sadasu da unguwar, suna karya kwana sukaga wasu yan mata tsaye a bakin titi su biyu sunci uwar kwalliya, har ya dan gotasu sukaji maganar daya daga cikin yan matan tana tsayar dashi,
"KB, kb, kb.."
Packing yayi agefen titi ya dubi nadiya, "ina zuwa 2 minutes"
Bata cemasa kala ba har yafice tana ganinsu ta cikin mirror shida yan matan sai dariya sukeyi, shida yace tabashi minti biyu saida ya shafe fiyeda minti 15 awurinsu nan ran nadiya yabaci,
Dakyar suka rabu da yanmatan nan yadawo cikin motar yana shafa sumar kanshi,
"Yanmata na kiyi hakuri nasan nayi laifi amma ki yafe min kannen wani abokina ne.."
Ko ci kanka bata cemasa ba saboda shiru ma amsa ce da haka suka karasa gidansu, tun da mama taji sallamar nadiya tafara yimata lale sannu da zuwa, ba karamin dadi nadiyan tajiba domin mama tana mutukar kaunarta kamar zata goyata duk lokacin data ganta,
Kafin wani lokaci ancikata da kayan cima kala kala, mama sai janta take da hira tana tambayarta mutanen gidansu su mama dasu Amira,
Duk kannensa sai da sukazo suka gaggaisheta bayan duk sun girmeta babu sa'anta A'isha ce ma dai zasu danyi kusan sa'anni da ita amma daga Muhammad har fati sun girme mata sosai,
Kasa kasa ta kalli kabeer nan taga yamaida hankalinsa kacokan akan wayarsa wanda ko ba afada mata ba tasan chaten yake yi....

 
*12*
~~~Wani b'acin raine ya sake rufe nadiya amma bata bari kowa ya fahimta ba, nan ta zauna agidan har sai da sukayi sallar mangariba sannan tayiwa mama sallama cewar zata tafi tareda fito da sabulun wanka wanda ta kawowa Maman ta bata,
"Ah haba nadiya harda wahala? Ai nice zan baki bake zaki baniba, haba nadiya keda ba ma'aikaciya ba bamai Sana'a ba kuma shine harda dorawa kai wahala?"
Maman tafada zuciyarta cikeda murna, cikin hanzari ta shiga daki ta dauko wata leda ta bawa husna tana fadin,
"To ga wannan babu yawa, agaida mama dakyau dasu Amira nagode madalla Allah yabar zumunci, Allah ya nuna mana wannan lokaci yasa ayi damu, agaida Alhaji dakyau.."
Godiya nadiya tayiwa mama sannan tafita, wani abin haushi kuma tana fita taga yaya kabeer tsaye ajikin motarsa shida wata budurwa wacce bata santa ba,
Kamar tasaka ihu haka nadiya taji ita sai yanzu take gane yaya kabeer, yanzu take fahimtar koshi waye, mutumne shi mai yawan kule kulen yanmata shiyasa har tafara kokarin janye zuciyarta daga gareshi domin gaskiya bazata juri wannan halayyarba,
Fuskarta babu yabo babu fallasa ta karasa wurin ta bude gaban motar ta shiga tana kallonsu ta cikin glass din motar,
"Shikenan zee sai munyi magana kigaida gida"
Yafada tareda bude kofar motar ya shiga,
"Wannan wata yarinyace acan gaba damu kadan to kwana biyu bamu haduba sai yau shine muka tsaya muka gaisa"
Yace da nadiya yana kokarin tada motar,
Ko kala nadiya bata furta masa ba saboda abin yana cin zuciyarta sosai, duk tulin yanmatan nan na yaya kabeer ko mata goma aka bashi damar ya aura tasan sai wasu dole sunyi saura to bare mata hudu kacal aka halasta masa,
Zuciyarta kamar zata fashe dan bacin rai sukaje gida, fitowa tayi zata shiga cikin gida yayi saurin shan gabanta,
"Wai nadiya dan Allah meyasa kike son sauyawa ne daga yanda nasanki zuwa wata tadaban? Meyasa kike son yiwa soyayyarmu illah? Dan Allah nadiya kidaina bata ranki akan duk wata mace da zakiga na tsaya da ita, ki dauka afadin duniyar nan babu wata mace sai ke, kisawa ranki cewar kowacce mace abayanki take, ke kadai nake gani a matsayin matar aurena dan haka ki daina damuwa kina bata ranki"
"Naji.." Shine kawai abinda nadiya tafada ta gegeshi zata wuce nan yayi saurin janyota wanda har sai da tafada jikinsa batare da ta shirya ba nan ya riketa yaki sakinta,
Jinta tayi cikin wani irin sabon yanayi saboda tunda take da yaya kabeer haka bata taba faruwa a tsakaninsu ba tasan dai sau mafiyan lokuta yana rike mata hannu ko yaja hancinta ko kuma yaja mata kunne amma bai taba gwada rungumeta ajikinsa ba sai yau,
Jin tana neman shagala yasata yin hanzarin zamewa,
"Ai nace maka na hakura ko?"
"To ai gani nayi kamar ba har zuciyarki ba shiyasa"
Murmushi tayi masa irin wanda zai tabbatar masa da cewar da gaske ta hakuran, nan ya karasa sakinta ta shiga gida, tun daga lokacin maganar ta wuce awurinta domin adaren ranar ma raba dare suka yi suna hira awaya.
  Haka komai yaci gaba da gudana batare da nadiya ta sake nunawa kabeer damuwarta ba saboda bata son yasata acikin jerin mata masu korafi da rashin hakuri, koda yaushe tana lura dashi domin tana son ganewa ko ya sauya ko kuma yana nan kamar da,
Kamar da din kuwa yake babu abinda ya sauya na daga kule kulen yanmatan da yake yi, wayo tayi masa ta karbi wayarsa aro tace zata kira kawarta nan ta shige dakin mama taje ta fara duban wayar ai kuwa sai da taji kamar zuciyarta zata buga domin bacin rai saboda massages ne na yanmata, da hotunansu kaca kaca,
Shi kansa kabeer sai da jikinsa yabashi cewar nadiya bincike ta tafi yimasa awaya bawai kawarta zata kiraba kamar yadda tace nan ya tashi ya tsaya yana jiran fitowarta Amma shiru sai da ta shafe fiyeda mintuna talatin adakin mama tagama duba wayarsa ciki da waje sannan ta fito, da mamakinsa sai yaga fuskarta asake babu alamun damuwa anan ya danji dama dama saboda watakil zarginsa bai zama gaskiya ba kila ba bincike tayi masa a waya ba,
Bashi wayar tayi suka dan taba hira ya tafi, yana tafiya nadiya taje tasamu mama wadda ke kitchen tana tuka tuwo, tsayawa nadiya tayi abayan mama,
"Mama.."
"Na'am.."
"Mama nafasa auren yaya kabeer"
"Saboda me?" Mama ta tambayeta cikeda razani bayan ta juyo tana kallonta,
"Mama haka kawai"
Rufe tukunyar mama tayi ta juyo tana kallon nadiya har na tsawon wani lokaci,
"Nadiya lafiyarki kalau kuwa? Anya babu abinda yake damunki?"
"Mama lafiyata lau, babu abinda yake damuna, nidai kawai yanzu bana son yaya kabeer abar maganar auren nan kawai ni yanzu karatu ma nake sonyi ina gama secondary zan tafi jami'a"
Tsayawa kawai mama tayi tana kallonta cikeda mamaki domin sam nadiya bata taba nuna sha'awar ta na cigaba da karatu ba sannan tun farko ita ta nace ta nuna kabeer takeso shiyasa itama Maman har ta hakura ta amince ta mara mata baya ta yadda take tayata to amma abin tambayar shine yanzu wanne abu kabeer yayi mata har take neman canja ra'ayi akansa....?
follow me on facebook follow me on twitter follow me on instagram

Fitattun labarai

Habiba complete hausa novel

Alqawarin da ciwo

Amfanin cin qafar kaza

Budurwar Roba

Amfanin lemon tsami

Afanin Zogale

Adam A. Zango

Amfanin namijin Goro (bitter kola)

Tona asiri

Yanda zaka duba sunanka a Npower