Karin magana 1

1. A daga sama! An yi wa wada kwace.

2. A dauki kare ran farauta?

3. A dauri kashi ko a bata igiya?

4. A aiki kare ya aiki wutsiya?

5. A amshi kadai ne, ba a ga mutuwa ba.

6. A bakin tsoho ne, goro kan tsufa.

7. A bakin wawa, akan ji magana.

8. A bar dariyar mai noma, ko bai sayar ba, ya ci abinsa.

9. A bar ganin allura kankanuwa,karfe ce.

10. A bar kaza, cikin gashinta.

11. A bari ya huce, shi kan kawo rabon wani.

12. A ci a sha, a rage don gobe.

13. A ci ba a sayar ba, kwai ya fi doki.

14. A ci yau a ci gobe, shi ne ci.

15. A cikin ido, ake tsawurya.

16. A haifi da da samu, ya fi a mutu a bar masa gado.

17. A ja mu a kai! An ba uwar makaho kashi.

18. A kashe wuta, tun tana kankanuwa.

19. A lallaba a kai ta, in ta fito muna so.

20. A lokacin da mage na nan, bera ba ya wasa.

21. A mari matacce, don mai rai ya ji tsoro.

22. A nema a samu, arziki ne.

23. A nuna wa na rigingine farin wata?

24. A raba arne da makami.

25. A rabe da alwalar kifi a ruwa?

26. A rabe magirbin yakuwa, da na rama?

27. A rabu a gana, arziki ne.

28. A rama wa kura aniyarta.

29. A rashin kira, karen bebe ya bata.

30. A rashin kula, akan kade kudi.

31. A rashin sani, bako ya sha ruwan wanka.

32. A rika sara, ana duban bakin gatari.

33. A sa a baka, ya fi a rataya.

34. A san mutum, a san cinikinsa.

35. A sayar a fadi, karin wayo.

36. A shekara saran ruwa, sai tambatse.

37. A so kare, har jelarsa.

38. A so uwa, a so 'ya'yanta.

39. A tauna tsakuwa, don aya ta ji tsoro.

40. A taya Allah kiwo, ya fi Allah na nan.

41. A yi a gama, ya fi gobe a karasa.

42. A yi abin da za a yi! Mahaukaci ya dauki rigar kurma.

43. A yi maza, a fidda jaki daga duma.

44. A yi wadda za a yi! Bera ya zubda garin kyanwa.

45. A zaba a gasa, ta hana yaro suna.

46. A zuba wa ungulu kwan zabuwa?

47. Abin kwarai ya saba bacewa an dangana, ba takalmi ba.

48. Abin al'ajabi! Ango ya kwanada kunzugu.

49. Abin aljihu, na mai riga ne.

50. Abin Allah! Budurwa da ciki; gwauro da yaye.
 
follow me on facebook follow me on twitter follow me on instagram

Fitattun labarai

Habiba complete hausa novel

Alqawarin da ciwo

Amfanin cin qafar kaza

Budurwar Roba

Amfanin lemon tsami

Afanin Zogale

Adam A. Zango

Amfanin namijin Goro (bitter kola)

Tona asiri

Yanda zaka duba sunanka a Npower