Karin magana 4


  • wanda Allah ya ba wa hakuri ya fi a zage shi
  • tashin hankali gobarar gemu
  • shegun gari, an iso! kare ya ga kura
  • rashin kunya mace ta auri mace
  • matambayi ba ya bata
  • magana ta kare mata ta che wa mijinta "shege"
  • Idan ana chin baure to a guji tona chikin sa, wata rana za aga tsutsa
  • Idan gemun dan uwanka ya kama da wuta shafa ma naka ruwa
  • in ka ji gudu da labari

  • shimfidar fuska ta fi shimfidar tabarma
  • karamin goro ya fi babban dutse
  • ana yabon ka sallah ka kasa alwala
  • tsoro na daji kunya na gida
  • zuwa da kai ya fi sako
  • kada Allah ya kawo ranar yabo
  • hangen dala ba shiga birnin kano ba ne
  • gaba ta kai ni gobarar titi
  • Allah ya yi abin inji mafadin aurensa
  • a bar kaza chikin gashinta
  • ya da alheri a baya ka tsinche shi a gaba
  • wawa bai san sannu bai san sannu ba sai ya kone
  • uwargida sarautar mata
  • ruwa na Allah, kifi na Allah masu chi ma na Allah
  • mai suna ya san sunan sa
  • mai tsoro ba ya suna
  • fatara mai ta da tsohon bashi
  • tasuniyar gizo ba ta wuche ta koki ba
  • in mutum ya fi ka gona fi shi da taki
  • hannun ka mai sanda
  • ban da tuna baya, gyartai ya ci sarauta

  • dara ta chi gida
  • Wasu basu iya chin dambu da tsinke ba 
  • da kai da kaya duk mallakar wuya ne 
  • da biri ya san ashana, da mutanen kauye sun sha wuta

  • tsalle d'aya, shi ke jefa mutum rijiya
  • duk wanda ya raina tsayuwar wata a sama, ya hau ya gyara.
  • dare rigan mugu
  • ba ka da ta chewa barawo a hanun mata

  • na ji wannan an che da kurma chinye duk
  • mugu shi ya san makwanchin mugu
  • Wanda ya gaji ya mutu
  • yanzu yanzu sai Allah
  • an raba mini hankalina biyu. an che wa rago sha fura ka tafi gona
  • yaushe rabon duniya da da ayyaraye
  • son maso wani koshin wahala

  • so, hana ganin laifi
  • sandan da ke hannun ka da shi kake jifa
  • saki reshe kama ganye
  • laifin dadi karewa
  • kowa ya yi zagi a kasuwa ya san da wanda yake
  • kai da kaya duka mallakar wuya ne

  • fadan da ya fi karfinka sai ka mai da shi wasa
  • don ganin bakin hadari ba a zubar da ruwan buta
  • a rashin uwa a kan yi uwar daki
  • matar wani ba ta wani ba che
  • machi amana na tare da kunya

  • rai ya fi dukiya
  • kai waye kenan bazawara da jaka
  • kai kuma waye kiyashi a jirki
  • iya shege kauri da kare

  • maganar kano larabchi
  • laifi tudu neh sai mutum ya taka nasa ya hango na wani
  • "ga mu ga Allah" bawan sarki ya rasa doki. Da ya samu dokin'sai ya che "ga mu ga sarki"
  • gado ba karambani ba
  • banza girman mahaukachi, karamin mai hankali ya fi shi
  • ba wahallale sai mai kwadayi

  • tabarmar kunya da hauka akan nade ta
  • idan mafadin magana wawa ne majiiyinta ba wawa ba neh
  • idan ka na da kyau ka kara da wanka

  • cin yau ya fi na gobe
  • matar na tuba ba ta rasa mijin aure
  • mai wuri ya zo mai tabarma ya nade
  • son maso wani koshin wahala
  • ina ruwan shege da alheri
  • dole neh tsufa da duwawu
  • karuwa ba ta kiwon kaza
  • ki bai taba zama so ba

  • tsoron Allah a zuchi yake
  • Allah mai halitta jaba ta ga bakin mijinta
  • abokin kirki, ya fi mugun dan uwa
  • yini da malami ya fi shekara da jahili
  • wanda ya isa, ba ya fada          

  • wanda za a ba, ya ce ,'me ya guntsiri nan?'             
  • shashanci gaba da bako                   
  • mhm ma ai magana che
  • murna ta koma chiki               
  • kare na yawo zabuwa na yawo wata rana a gamu                         
  • bahin rijiya, ba wurin wasan makaho ba neh                           
  • duk bakin da ya ci, ya kamata ya gode                          
  • in ka sani, ba ka nuna saninka                          

  • a bakin wawa a kan ji magana                         
  • idan da rabon kunci zai sha mari, Allah ba da hakuri ba ya hana fada                           
  • idan an hana ihu ba a hana aha ba
  • Abida mutum ya shuka .............. in kairan kairan,in sharran sharran
  • idan angulu ta biya bukata, zabuwa ta tafi da zanenta.
  • marasa gaskiya ko a ruwa gumi yake
  • komai wayon amarya, sai an sha manta

  • ko in kula harara a duhu                       
  • karya ta kare bori ya kashe boka                          
  • hankali ke gani ido gululu ne  
  • duniya mai halin dan mangwaro, kana tsotson ta sai ta sunbule maka
  • da alheri kishiya ta hau kura
  • babbar magana, karuwa ta ga gawar soja

  • abun da wuya, kamar tseumi
  • zamani riga ne
  • yin kunnen uwar shegu
  • yaro idan ba ka san gari ba, saurari daka
  • wanda bai ji bari ba ya ji hoho
  • tambarin talaka chikinsa

  • tashin hankali gobarar gemu
  • da babu gwara ba dadi               
  • wake daya shi ya ke bata gari
  • garin neman gira, a rasa ido.


follow me on facebook follow me on twitter follow me on instagram

Fitattun labarai

Habiba complete hausa novel

Alqawarin da ciwo

Amfanin cin qafar kaza

Budurwar Roba

Amfanin lemon tsami

Afanin Zogale

Adam A. Zango

Amfanin namijin Goro (bitter kola)

Tona asiri

Yanda zaka duba sunanka a Npower