Kalaman So

SAKONNIN SOYAYYA GUDA 10+
NA ‘DAYA.
Ke kamar hasken wata ki ke mai hasken da ke haske idaniya, haka kuma kalamanki tamkar siga suke ma’abocin za’ki, tabbas kin yi kama da kanki hakan ya sanya na ji ina son ki.
NA BIYU.
A lokacin da kika ji kina son wani, to yi maza ki adana sunan shi a cikin d’aya daga cikin kogunan da ke a cikin zuciyarki, domin kuwa ita zuciya takan iya raunata a koda wane lokaci amma shi kogon zuciya ya kan kasance tare da ajiyar da aka yi a cikin shi har abada. Ina fatan zan kasance ni ne wanda za ki adana a ma6oya mafi sirrinta soyayya da masoyi? Ina son ki.
NA UKU.
Sauda yawan lokaci idanuwana sukan yi kishi da zuciyata!!! Kin kuwa san mene ne dalili? Saboda a koda yaushe kece abu mafi kusanci da zuciyartawa su kuma idanuwa kin kasance mai yin nesa da su. Ina son ki sosai da zuciya d’aya.
NA HU’DU.
Na kasance ma’abocin soyayya zuciyatama ta gaskata hakan, lokaci na shud’ewa soyayyar ki na k’aruwa a cikin zuciyata, a lokacin da ki ke cikin farin ciki kyakkyawar fuskar ki na bayyanar da murmushi mai taushi da tausasa zuciyar ma’abocin kallonta, kece wadda na ke so a cikin zuciyata babu wata da zata iya canja matsayin ki a wajena. Ina k’aunar ki.
NA BIYAR.
SO tamkar rayuwane, ba ko yaushe yake zamowa abu mai sauki ba haka kuma ba a koda yaushe yake wanzar da farin ciki ba, to amma mene ne zai sa matsawar muna raye da rai da lafiya za mu yanke alakar soyayya a tsakanin mu? Har zuwa yau babu kamar ki a cikin zuciyata domin kuwa jin muryar ki a kullum na rubanya adadin soyayyar da na ke yi miki a cikin ko wane dare ko safiya. karda ki rabu da ni dan Allah, domin hakan zai iya sanyawa na zamo mutum mai rauni a rayuwata.
NA SHIDA.
SO tamkar kurbar ruwan shayi yake mai tsananin zafi, a karon farko zaka kasance cikin shaukin begen shi wanda daga bisani kuma zai k’ona maka harshe na tsawan lokacin da zaka shafe kana yin jinyar shi.
NA BAKWAI.
Soyayyar da na ke yi miki tamkar tafiyace mai nisa da na fara yinta wadda bata da lokacin yankewa har abada. Na san burina zai cika matsawar ina tare da ke domin kuwa dukkanin burina yanzu bai wuce na samun ki a matsayin matata uwar ‘ya’yana ba. Ina son ki fiye da gwal ko kud’i.
NA TAKWAS.
Karda ki fadawa kowa kalaman sirrin bude soyayya da kawancen dake tsakanin mu, domin kuwa a dukkan lokacin da kika furta wadannan kalaman sirri ga wani wato “INA SON KA” hakan na nuni da cewa zai yi amfani da shi wajen bude mana akwatin soyayyar mu ta sirri wanda hakan zai bashi damar yi mana gagarumar sata har ya yi sanadiyar raba ni da ke har abada. Ina son ki.
NA TARA.
Na yi shiri tare da niyar turo miki da dikkanin soyayyata amma sai dai wanda zan turo da sakon nawa gare ki ta hannun shi ya bayyana hakan a matsayin wani babban abu da zai gagari bil’adama d’auka, amma karda ki damu zan zo nan bada dadewaba domin ki tabbatar da abun da na ke fad’a gaskiyane dama an ce zuwa da kai ya fi sak’o. Ki huta lafiya farin cikin zuciyata. Ina son ki.
NA GOMA.
Abba ne zaune a kan wata farar kujerar roba cikin wani lambu mai d’auke da korayen ciyayi da ni’ima mai dad’i, wajen da ya zamo masa wajen hutawar shi a dukkan lokacin da ya fita wajen aiki bayan ya yi aikin ya gaji nanne inda ya saba zuwa ya kirawo matar shi a waya domin jin halin da ta ke ciki tun bayan auren su wanda hakan ba karamin burge matar tashi yake yi ba sannan kuma yana k’ara soyayyar shi a cikin zuciyarta.
Yauma dai kamar kullum, ya fito da wayar ta shi daga aljihu ya shiga kiranta, kamar jira ta ke yi dama bugu d’aya ta d’aga, bayan sallama sai kuwa ya shiga cewa da ita
“Matata Uwar ‘ya’yana maganin kukana, Salimat a baya kafin mu yi aure na yi tinanin cewa bayan mun yi aure ba zan ke samun kulawa da tarairaya tare da kalaman soyayyar nan ta ki masu dad’i ba, na yi zaton komai zai canja kamar yadda na ke gani a wasu gidajen auren ashe mu ba haka abun ya ke ba saima abun da ya ci gaba ya kuma sauya sabon salo mai dad’i, Salimat ina son ki, koda aiki nake yi yadda zan dawo gida na tarar da ke kawai na ke yin tinani, kuma koda abinci zan ci ina ci ne kawai saboda na rayu amma ba wai dan ina jin dadin shi ba, ina son ki sanar da ni abun da zan taho miki da shi idan zan dawo gida ki kuma kular min da kanki har zuwa lokacin da zan dawo kulawar ki ta dawo hannuna.


KALAMAN SOYAYYA.
(Domin Samari Da ‘Yammata Da Ma’aurata)
NA SAMARI DA ‘YANMATA.
Na Maza:
KIN ZARCE SAURAN MATA.
Ina neman wata kalma wadda babu wanda ya santa. Ina neman wata kalma da zan furta miki cewa…..ke ta daban ce, ke kyakkyawa ce, kin zarce sauran mata. Zuciya ta da taki ba za su ta6a rabuwa ba har abada. Ina son ki.
SINADARIN RAYUWA TA.
SO shi ne abun da ya dun’kule zuciyoyinmu waje guda har muka tsinci kanmu a cikin soyayya, ina fatan ba za ki bari wani d’an ‘karamin abu ya zo ya raba tsakaninmu ba? Ina son ki. Ke tamkar gishiri ce a cikin rayuwa ta, idan na rasa ki zan yi rayuwa ne da babu armashi a cikinta. Ki Huta Lafiya.
ZAN SO KI JI.
Da akwai wasu tarin tsintsaye da suke wuni suna tattauna batutuwa a kan irin matsayin da na baki a cikin zuciya ta. Zan so ki ji irin abun da suke cewa, domin kuwa a lokacin ne za ki tabbatar da irin son da nake yi miki. Ina Son Ki!
KE CE MURMUSHI NA.
Da akwai miliyoyin furanni a cikin lambun masoya a wannan duniya. Da a ce zan tsunko kowanne fure na baki shi a hannunki, hakan bai isa ya bayyanar da adadin yadda nake son ki ba. Ke ce murmushi na, kuma ke ce farin-ciki na. Ina Son Ki.
SONKI NA MOTSAWA A ZUCIYA TA.
Da akwai wasu lokuta da nake zubar da hawaye saboda ke, na san za ki ce saboda me?…..Da akwai wani lokaci da yake zuwa na ji tamkar na yi fikafikai na tashi sama…..Kin kuwa san duk saboda mene ne? Saboda motsawar sonki a cikin zuciya ta da tsintar kaina a cikin matsanancin shau’ki a dukkan lokacin da na ji muryarki ko na tina da ke…..Ina fatan za ki amince mu rayu a tare har abada. Ina Son Ki!
HMM!! KI YARDA DA NI.
A dukkan lokacin da dare ya yi, ki d’aga kanki sama ki kalli sararin samaniya, za ki ga wani tauraro yana saukowa izuwa gare ki, karda ki yi mamakin me ya sa haka ya faru? Ki yarda da ni, hakan zai iya faruwa a zahiri domin kuwa ni ma na yi hakan har ta kai ga na same ki. Hmm! Ki Huta Lafiya.
INA SON KASANCEWA A TARE DA KE HAR ABADA.
A lokacin da na samu soyayyarki sai na ji tamkar ni ne na fi kowa sa’a a duniya. A dukkan sanda na rintse idanuwa na sai na hango ni tare da ke muna tafiya a bisa gajimare. Idan na kwanta bacci sai na yi mafarkin mun zama mata da miji. Ina sonki, tare da son kasancewa a tare da ke har abada. Ki Huta Lafiya.
A CIKIN IDANUWANKI AKWAI WANI SIRRI.
Sama cike take da taurari masu hasken da ke haske duniya a cikin kowanne dare. Amma haske mafi haskaka fuska da yaye duhun zuciya, na gan shi ne a cikin idanuwanki. Ki Kula Min Da Kanki. Ina Son ki.
HARSHEN ZUCIYA.
Furanni na furta kalmomin yabo a kanki a dukkan lokacin da na shiga lambu mai d’auke da ‘korama gami da korayen ciyayi da bishiyu masu d’auke da tsintsaye. Sukan rera baitukan yabo a gare ki, cikin harshen da zuciya ce kawai ke iya fahimtarsa. Ina Son Ki.
BA ZAN IYA RAYUWA IDAN BA TARE DA KE BA.
A mafarki da kuma a cikin soyayya babu abun da ba zai iya faruwa ba. Ina son ki sosai hakan ya sa nake ji tamkar ba zan iya rayuwa idan ba tare da ke ba. Ba na fatan rasa ki a rayuwa ta, domin kuwa a dukkan lokacin da na rasa ki, na tabbatar da rayuwa ta za ta shiga garari. Ina Son Ki kuma ba zan ta6a canjawa a kan hakan ba.
Na Mata:
INA SONKA MASOYI NA!
Tsuntsaye na bu’katar fukafukai domin tashi, kifi na bu’katar ruwa domin ya yi rayuwa, ni kuma ina bu’katarka domin na yi rayuwar farin-ciki. Ina son ka masoyi na!
MU KASANCE A TARE.
Ina son jinka a kusa da ni, ta yadda numfashi na da naka zasu gauraya, ta yadda zan ke juyo sautin bugun zuciyoyinmu na fita a tare. Mu kasance a tare har abada. Ina Son Ka!
INA FATAN MAFARKI NA YA ZAMA GASKIYA.
A kullum na kwanta bacci, na kan yi mafarkin ka zama uban ‘ya’ya na, ni kuma na zama mata a gare ka. Sai dai na san iya mafarki ba zai wadatar da ni ba a bisa kulawar da nake tinanin samu daga wajenka. A saboda haka nake fatan mafarki na ya zama gaskiya watarana. Ina Son Ka!
MASOYI NA.
Ina Son Ka, zan kuma ci-gaba da sonka tun daga futowar rana har izuwa fad’uwarta a cikin kowace rana har abada. Ka Huta Lafiya.
KA ZAMA RUHI NA.
Ina fatan ka fahimci manufa ta? ina fatan ka gane nufi na a kanka? Zan rayu ne cikin sonka har zuwa ranar ‘karshe, saboda kai ba saurayi ne kawai a waje na ba, ka zama ruhi na, sonka na yawo ne a cikin jinin da ke gudana a jiki na. Ina Son Ka!
NA MA’AURATA.
Miji:
INA SON KI!
Ba zan iya musalta adadin yadda sonki yake lunkuwa a zuciya ta ba a cikin kowace rana. Ina son ki matata. Babu wani abinci da yake yi min dad’i a baki na matu’kar ba ke kika girka shi ba. Ina nan tafe izuwa gare ki da shirin zuwa cin abincinki mai dad’i. Ki kula min da kanki.
ZUCIYA TA NA CIKE DA KEWARKI MATA TA.
Mata ta uwar ‘ya’ya na. Na kan yi kewarki sosai a dukkan lokacin da na duba gefe na ban gan ki ba. kamar kullum, yanzu haka ina zaune cikin tinaninki. Zuciya ta na cike da kewarki, zan samu sassauci ne kawai idan na ji ki a kusa da ni. Ki kula min da kanki har zuwa lokacin da zan dawo kulawarki ta dawo hannu na. Ina Son Ki.
BA NI DA KAMAR KI.
Na futo wajen aiki hakan na nufin mun yi nesa da juna. Amma ina son, ki san da cewa, a duk inda nake, a duk inda na shiga, ba zan rabu da tinaninki a matsayinki na mata ta da nake matu’kar so da ‘kauna ba. Ina nan tafe a hanya zuwa gare ki. Ki kasance mai tina cewa, ba ni da kamar ki. Ina Son Ki.
Mata:
INA ALFAHARI DA SAMUNKA.
Hasken idaniya ta, annurin rai na. Miji na, uban ‘ya’ya na. Tabbas samun miji irinka shi ne abun da mata da yawa suke fata. Na same ka hakan ya sanya nake jin tamkar na fi kowace mace sa’a a duniya. Ina fatan dawowarka gida lafiya, miji na abun alfahari na.
KAI NE NAKE GANI NA JI SANYI A ZUCIYA TA MIJI NA.
Ina fatan kana nan lafiya miji na? Ina nan zaune cikin gida amma zuciya ta tana tare da kai. Kai ne kawai nake gani na ji sanyi a cikinta. Ina nan ina jiran dawowarka gida lafiya. Ina son ka. Ka kula min da kanka.


SAKONNIN SOYAYYA MURMUSHIN MASOYA.
TA ‘DAYA.
Ina son dukkan taurarin da suke bisan sama, amma ba za’a hada son da na ke yi musu da kuma na wadda ta ke a cikin idanuwan ki ba, ina son ki.
TA BIYU.
Lokaci yana nan zuwa da zaki mallakawa wani zuciyar ki, ina mai yin kira a gare ki da ki tabbatar da cewa kin mallakawa wanda ba zai raunata zuciyar ki ta hanyar yaudara ko cin amana ba, saboda ita zuciya d’ayace babu wadda zaki dauko ki sauya a lokacin da bakin ciki da damuwa suka mamaye zuciyar ta ki.
TA UKU.
Yanzu haka ina cikin farin ciki, shin kin kuwa san mene ne dalili? Hmm saboda na kasance mai sa’a, kin kuwa san tayaya? Saboda Allah ya na so na, kin kuwa san me ya sanya na ce haka? Saboda ya ba ni wata babbar kyauta, kin kuwa san mene ne? Ba komai ba ne ba face KE masoyiyata, ina son ki.
TA HU’DU.
A koda yaushe lokaci tashi yake yi tamkar tsuntsu, amma ita soyayyar mu kullum ginuwa ta ke tare da kara samun wajen zama a cikin zuciyoyin mu karda ki manta da ni ki kasance mai yin tinani na kamar yadda nima na kasance a ko da yaushe.
TA BIYAR.
Abun da na ke ji a dangane da ke gaskiya ne kema na san kin san da haka cewa ina son ki, a duk lokacin da kika bar ni ba zan iya motsawa ko da nan da can ba, wannan shi ne abun da zai faru da ni a duk lokacin da na rasa ki.
TA SHIDA.
SO tamkar wata sarkar zinari ce da ta d’aure zuciyoyin mu a waje guda, a dukkan lokacin da kika tsinka waccan sarka tofa ki tabbatar da cewa tamkar kin kore farin ciki ne daga cikin zuciya ta.
TA BAKWAI.
Salim ina son ka, me ya sanya ka ke yin kokwanto a bisa kalmar so da na furta a gare ka? Tabbas kaine mutum na farko da haduwa da shi ya kore min bakin ciki, ya wanzar da farin ciki a zuciya ta ya yalwata murmushi a saman fuska ta hakane dalilin da ya sanya na ke kiran ka da SADAUKI. Salim, ka yi nasara ka yi nasarar jan ra’ayin soyayya ta a kan ka kaine na mallakawa linzamin zuciyata, kaine mutum na farko da na taba furtawa kalmar SO kuma a yanzuma zan kara mai-maitawa a gare ka ina son ka. Ka amince mu yi tsaftatacciyar soyayya. Sai yanzu na gano cewa a duniya babu abun da ya kai samun masoyi dad’i, a duk lokacin da na rasaka ban san halin da zan shigaba, daga karshe ina mai sanar da kai cewa buri na yanzu bai wuce na ganin ranar da zaka zamo ango ni kuma na zamo mata a gare ka ba, ina alfahari da kai a duk inda na kasance, ka huta lafiya daga mai son ganin farin cikin ka a koda yaushe. SALIMAT.


SAKONNIN SOYAYYA ABINCIN ZUCIYA.
ALMARA A SOYAYYA.
A duk lokacin da na zauna zuciyata tana rada mini cewa, ranar da aka haifeki ta kasance rana ce da aka yi ruwan sama a cikinta, ammafa ba ruwane irin wanda kowa ya sani ba. Walkiya zata bayyana a sararin samaniya tare da k’ara mai shiga kunnuwa da ratsa zukata a ranar da kika bar duniya, ammafa wannan duk hasashen zuciyata ne. Kina da kyau da kyawun kallo. Ina alfahari da samun ki.
KARDA KI NISANCE NI.
Abun da nake ji a dangane da ke tabbas gaskiya ne kuma kema na san kin san da haka, ina matukar son ki. A duk lokacin da kika yi nesa da ni, nima ba zan iya sake ci gaba da rayuwa a cikin walwala ba, amma na san ba zaki taba bari hakan ya faru ba, ke kadai ce a cikin zuciyata. Ina son ki.
SON KI KULLUM NA KARUWA A ZUCIYA.
Ina musanta cewa ina matsantawa a soyayyar ki amma zuciyata ta tabbatar da hakan, lokaci na wucewa soyayyar ki na karuwa a cikin zuciyata. Kina da tattausan murmushi, kin kasance ma’abociyar kyakkyawar fuska, ina mai tabbatar miki da cewa babu wata da zata iya maye gurbin ki a cikin zuciyata. Ki huta lafiya.
SOYAYYAR MU TA HAR ABADA CE.
Idan mutanen da muke so suka guje mana, mu kasance masu son su a cikin wuya ko dad’i hakan shi ne zai kara kusanta mu da su. Gidaje na rushewa, mutane na mutuwa amma soyayyar mu ta har abada ce. Ki kwana lafiya.
AMMA DA KAMAR WUYA.
Inama a ce zan zamo hawaye ta yadda zanke kwanciya a cikin idanun ki, kumatunki ya zamo babbar farfajiyar da zanke rayuwa a bisan su, labbanki su kasance nanne wajen da mutuwata zata ke riskata. Ina son ki.
KALMOMI UKU “INA SON KI”
Kalmomi uku na yin sanadin karuwar bugun da zuciyata ke yi, kalmomi uku na sanya kafata karkarwa, kalmomi uku na sanya kaina ya yi ta faman rangaji, bari dai na furta su yau a gare ki ko na huta da azalzalar da zuciyata take yi mini a dangane da hakan, kalmomi uku: INA SON KI!!!
KECE ABAR TINANINA.
Damuwa? A’a sam, tayaya zan kasance cikin damuwa bayan a ko yaushe ke ce abar tinani na? Da ke nake kwana sannan kuma da ke nake tashi a cikin zuciyata. Ina kaunar ki!!
FUREN SOYAYYA.
Idan har ya kasance zan ke samun kyautar furanni a dukkan lokacin da na hadu da ke, to kuwa ni zan kasance mai ziyartar dausayi ma’abocin firanni masu kamshi na mallaka dukkan lokacina na wannan rana domin girmamaki. Ina son ki sosai a cikin zuciyata.
NA MALLAKA MIKI ZUCIYATA.
Ina tsananin so da kaunar ki bayan da kika samu nasarar sace zuciyata. Wannan zuciyar da ta kasance mallakina, ina mai farin cikin na mallaka miki ita a matsayin wata kyauta ta musamman. Na zama mallakin ki. Ki kasance mai ririta soyayyar mu kamar yadda na kasance. Na baki amanar kaina ki amince mu damke amanar juna. Ki huta lafiya.
AMSARTA NAKE JIRA.
Duk da Iskar dake kadawa a wajen lokaci bayan lokaci amma kasantuwata a bakin kogin bai hana gumi tsatstsafowa daga cikin fatata ba.
A zaune nake kan daya daga cikin duwatsun da suke gefen kogin ammafa kaina a sunkuye yake tamkar wanda aka bawa aikin irga korayen ciyayin dake wajen, fuskata cike take da damuwa.
Sautin shigowar sako wayata ne ya sanya na zabura na daukota daga cikin Aljihuna, sunan wadda ta turo da sakon da na gani ne ya sanya na yi murmushi cikin zumudi na shiga karantawa kamar haka ” Dan-Hausa ka yi hakuri a bisa jinkirin da na yi wajen turo maka da amsar sakon ka na ganin na amince da soyayyar ka. Abba a tun ranar da na fara dora ido na a kanka na ji zuciyata ta kamu da son ka, bana iya bacci a kullum idan ban ganka ba, kaine masoyina na hakika tunda har zuciyoyin mu sun aminta da juna. Ina son ka kaima kana sona ina yi maka albishir din ka samu makullin bude DAUSAYIN SOYAYYAr zuciyata, ina kuma fatan zaka kara shiri domin fantsama a cikin kogin soyayya mai dadi. Ina yi maka fatan samun nasara a dukkan al’amuran ka, daga masoyiyar ka SAFIYYAT.” ina gama karantawa ban san lokacin da na yi wani tsalle ba na fada cikin wannan kogin dake gabana saboda tsabagen farin ciki tare kuma da sanyawa a raina wannan shi ne kogin soyayyar da take magana a kai, ina cikin kogin bakina na furta kalmar SOYAYYA! SOYAYYA!! SOYAYYA!!! MAI DADI!

ZUCIYAR DA TAKE SON KA ABAR A BAWA KULAWA CE
¤ Tirsasawa zuciyar ka son wanda ya nuna yana son ka a zahiri babbane ko yaro, talakane ko mai kudi, mace ko namiji, kyakkyawa ko akasin haka.
¤ Bada kulawar ka ga wanda ya nuna maka kulawa.
¤ kasance mai damuwa da damuwar wanda ya damu da kai.
¤ Amsa kiran wanda yake amsa kiran ka cikin gaggawa.
¤ karda ka yawaita yin fushi da wanda yake gudun ya bata ranka.
¤ Rayuwa babu masoyi lami ce tamkar miya babu gishiri take zamtowa.
¤ Kasance mai faranta zuciyar wanda yake kokarin faranta taka zuciyar koda kuwa kai zaka shiga cikin damuwa ne.
¤ Kasance mai kare mutuncin masoyin ka a lokacin da kuke tare ko bakwa tare da shi.


WAKAR MAKAUNIYAR SOYAYYA.
Ni ban san haka soyayya take ba.
Zuciya na k’una tamkar a kan tukuba.
Na kamu da son ta gashi ban santa ba.
Zahirin siffa da hali nifa ban san su ba.
Amma gashi cikin dare begen ta nake.
Ni ‘Dan-Hausa ba’ko ne a soyayya.
Gashi bani da sanin ilimi na soyayya.
Tun a farko na ce ta zo mu yi soyayya.
A zato na ta aminta za mu yi soyayya.
Ashe ni a gare ta tamkar aboki nake.
Bari na baku labarin a inda na ganta.
Amma farko bari ku ji zahirin suffar ta.
Fatarta ba’ka ce abar son zuciya ta.
Ita ba doguwa bace kuma bata da gajarta.
A sauti na murya kullum son jin ta nake.
A yanar gizo-gizo muka had’u watarana.
Na dauketa fiye da sauran mata a waje na.
A kullum tinani nake ina tsawaita buri na.
Dama a ce na bude ido na ganta a gaba na.
Ku sanar da ita ni Abba sonta nake.
Abokaina ina kuke ku zo ku ciro ni.
Na fada cikin makauniyar soyayya ni.
Na rasa tsanin da zana taka ya fidda ni.
Ashe ita a gurin ta abin tausayine ni.
Yau na rasa yadda zana yi kukan zuci nake.
Ya Allah ka fidda ni.
Karda ta cutar da ni.
Harma ka ba ni magani
Sannan ka tseratar da ni.
Zuciya! neman d’auki take.
A yau nai muku bankwana.
Abokai na ce sai watarana.
Ga hawaye fal a idanu na.
Ina neman mai share hawaye na.
Ido na a rufe sai nema nake.
Dama a ce tun farko kin amince.
Da mun sha soyayya a zahirance.
Zan baki kulawa har ki mance,
dikan damuwa a kalamance.
Har yanzu kar ki manta son ki nake.


FARIN CIKI BA YA SAMUWA SAI DA SADAUKAR WA A SOYAYYA.
Duk wata mu’amala tsakanin mutane biyu, madamar za a yi ta yau da kullum, to lallai ne a gamu da ciwonta sannan kuma a gamu da waraka wata rana, kwatankwacin soyayya da ita ma ake gamuwa da hakan a cikin ta. tabbas farin ciki ba ya samuwa sai da sadaukarwa. Zubar da hawaye game da soyayya lallai ne, domin ranar da za ka ga masoyin ka cikin wani yanayi marar dadi kuma ba ka iya magance shi, lallai dole a yi hawaye. Babu yadda za a yi ka yi soyayya ba tare da ka zubar da hawaye ba, madamar dai soyayyar ta gaskiya ce, domin kuwa rayuwa tana tattare da abubuwa biyu ne, bakin ciki da farin ciki. Idan watarana an sha zuma to wata rana madaci ake sha.




follow me on facebook follow me on twitter follow me on instagram

Fitattun labarai

Habiba complete hausa novel

Alqawarin da ciwo

Amfanin cin qafar kaza

Budurwar Roba

Amfanin lemon tsami

Afanin Zogale

Adam A. Zango

Amfanin namijin Goro (bitter kola)

Tona asiri

Yanda zaka duba sunanka a Npower