Lafazin so

ALAMOMIN GANE MASOYIYA TA GASKIYA
A lokacin da kake ‘ko’karin gano matsayinka a zuciyar budurwarka shin tana son ka ko akasin haka da akwai bu’katar ka nazarci wasu abubuwa wad’anda wasu sun kasance waiwaye ne wasu kuma suna kan faruwa.
*FARKON HA’DUWAR KU.
*YANAYINTA DA KUMA HALAYYARTA.
FARKON HA’DUWAR KU
A yayin gabatar da soyayyarka gare ta ka yi amfani da salo ne mai karsashi wato sai da ka gama jan hankalinta da ra’ayinta a kan ka sannan ka bayyana a gareta da lamari na soyayya?
Furta kalaman amince wa na soyayya ga wanda suke so abu ne da mata suke jin kunyar furta wa a karon farko ga samarin na su, sai dai duk da haka zata ke nuna maka alamun tana son ka kuma zata ke nuna maka wasu alamomi da suke nuni da SO.
Salon da kake bi wajen gudanar da soyayyar ta ku shi ne sikelin auna ci-gaba ko ci-bayan soyayyar ta ku, misali a lokacin da kuke tsaka da soyayya sai ta samu wani da ya fika iya kalaman soyayya da barkwanci da rashin yawan mita da dai duk wani salo mai burge wa to babu shakka ko kafi ‘karuna dukiya zai iya d’auke hankalinta da ga kan ka, sai dai ta tsaya da kai dan kud’inka. A saboda haka akwai bu’katar ka kasance mai sabunta salonka na soyayya tun daga kan kalamai da yanayin yadda kake bata kulawa da sauran su lokaci bayan lokaci.
A dukkan lokacin da ka bu’kaci mace ta baka amsar amince wa tana son ka sai ka ga ta yi murmushi ko ta kasa furta hakan a karo na farko to hakan yana daga cikin alamu na SO domin kuwa wanda ake so ake jin kunya.
Karda ka damu da sai ta furta maka kalmar tana son ka kai dai lura da wad’annan abubuwa kamar haka;
*Sau nawa kake kira kafin ta amsa? Idan har da so zata amsa a kira na farko idan kuma bata amsa ba zata amsa a kira na biyu har ta baka uzurin da zaka gamsu na dalilin rashin amsa kiran, idan har bata amsa a kira na biyu  ba sai ka bar kiranta haka idan har da so zata kira ka da zarar ta ga kiranka da ta rasa har ta baka uzurin kare kai.
*Matu’kar tana son ka za ta kasance mai kar’bar shawarar da duk ka bata kuma za ta kasance mai son abun da kake so.
*A duk lokacin da ka je wajen ta zance za ta fito cikin farin ciki kuma ba zata nuna ‘kosawa da jin firarka ba matukar ka iya zance har zuwa lokacin da za ku yi sallama.
*Idan har ka saba kiran ta a waya matu’kar ta damu da kai idan ka kwana biyu baka kira ta ba to za ta kira ka ta ji ko lafiya, idan ma bata kira ba saboda wani dalili bayan ka kira za ta yi kalamai na nuna ta yi kewar ka.
*Idan har tana son ka a kullum za ta ke ‘ko’karin yin abun da zai faranta ranka, za ta ke ‘ko’karin guje wa abun da zai sa ka yi fushi.
*A lokacin da soyayyarku ta yi nisa zata iya bayyana maka wasu sirrikanta da suka shafe ta.
*A lokacin da ka nuna ‘bacin ranka a kan wani abu da ta aikata da ba dai-dai ba, a yayin baka ha’kuri da shawo kan ka za ta iya zubar da hawaye.
*Zata ke ‘ko’karin bayyana ka ga ‘kawaye da kuma ‘yan gidansu.
*Zata ke ‘ko’karin turo maka da kalamai na soyayya.
*Zata kasance mai tambaya a dangane da ‘yan uwa da kuma abokanka da ma dai duk wani da ta san kuna a tare.
*Za ta ke damuwa da damuwarka.
Irin wad’annan abubuwa da sauran ire-iren su duk zai kasance ta na nuna maka su.
YANAYINTA DA KUMA HALAYYARTA.
Akwai bu’katar ka fahimci yaya yanayinta da kuma halayyarta suke,
*Shin tana da jan aji ne da yawa? wanda hakan ka iya sawa ko tana son ka ba zata amince da kai a karon farko ba har ma za ta iya yin wasu abubuwa da zaka iya tinanin wula’kanci ta yi maka, amma da sannu matu’kar ka iya allonka za ka wanke.
*Tana da kunya ne? ta yadda ba za ta iya sakin jiki da kai ba a karon farko kuma bayan tana son ka, idan ka yi ha’kuri da sannu soyayyarka za ta cire mata wannan kunyar da take ji a kan ka domin kuwa idan aka juri zuwa rafi da sannu tulu yake fashe wa.
*Koda a ce bata da son kud’i farkon soyayyar ku sai ya kasance ka fara yi mata kyaututtuka to da sannu idan ka matsa da yi mata kyauta son abun hannunka zai rinjayi son da take yi maka na gaskiya, an dai kuma ce kyauta tana ‘kara soyayya, amma kuma komai ya yi yawa to zai kawo matsala.

SHAWARA GA SAMARI ‘YAN SOYAYYA.
  • Yi ammafani da kalaman soyayya masu dadi da inganci a lokacin da kake gwagwarmayar samun amincewar zuciyar dukkan wata yarinya da ka gani kana son mallakarta.
  • Kasance mai lissafawa tare da tauna dukkan wata magana kafin ka furta ta ga masoyiyarka bayan ta nuna maka amincewarta a soyayyarka.
  • Karda ka kasance mai takura wa tare da matsantawa a kan dole sai ta yi wani abu da ta nuna maka bata son yi a zahiri ko ta nuna maka alamun hakan, domin kuwa hakan zai sanya ta fara gajiya tare da kosawa da kai.
  • A dukkan lokacin da kake son ta yi maka wani abu to ka gabatar mata da bukatar ka cikin siyasa da zolaya amma idan ka nuna mata dole to kuwa ba zaka samu yadda kake so ba idan ka samu an yi ma kenan.
  • Kasance mai yin dukkan wani abu da ka san zai faranta mata ka kuma guji yin dukkan wani abu da ka san zai kuntata mata. Yi mata kyauta a lokacin da bata zaton samun hakan daga wajen ka, yin hakan zai sanya ka burgeta zai kuma kara sanya soyayyar ka a cikin zuciyar ta.
  • Karda ka cika yi mata kyautar kudi ko bata wasu abubuwa barkatai domin kuwa yawan yin hakan zai sanya ka kasa banbance cewa soyayyar gaskiya take yi maka ko kuma kudin ka take so.
  • Mace bata son takura bata son ka fiya maimaita mata abu daya, ba kuma ta son ka cika kushe wani ko wata a gaban ta, bata son kuma a lokacin da kuke tare kake nuna kulawa ko fifiko ko nuna wata ta fita kyau ko wani abu makamancin haka. Mata suna son kake yabon kyawun su.
  • Ka kasance mai bayyana mata cewa ita kyakkyawa ce a duk lokacin da kuka yi waya ko kuma kuke tare, ka ke bayyana mata cewa muryarta na da dad’i sosai kana samun nutsuwa a duk lokacin da ka ji sautin muryar ta, ka nuna mata cewa ta iya kwalliya kuma tana da tsafta.
  • A duk lokacin da kuka hadu ko a waya ko a zahiri ko kuma sako ka tura mata to ka bayyana mata kana sonta kafin ku rabu.

SAKONNIN SOYAYYA NA BARKA DA SALLAH.

FATAN ZAN SAMU ABUN DA NAKE NEMA?
A koda yaushe ina fatan nasara ta kasance a tare da ke, na kasance mai yin fatan kasancewar farin ciki a cikin zuciyar ki a safiya ko rana, amma shin zaki iya tinawa da wani abu wanda zuciyata ke muradin samu daga gare ki? Ba komai bane face ki mallaka min zuciyar ki ta hanyar sanya ni a cikinta ni kadai ba tare da kin hada ni da kowa ba. Ina son ki.
BARKA DA SALLAH.
HADUWAR MU TA FARKO.
Tun daren jiya da na dawo gida nake ta faman sak’a tinani ta yadda aka yi wata ta sace mini zuciyata, to amma dama hakan shi ne burina. Faruwar hakan sai ya zamto tamkar wani al’amarin mafarki ne a gare ni to amma a duk lokacin da na nutsu na zurfafa a tinani ina ji a cikin zuciyata watarana zata zamo mallakina, kin kuwa san wace ce wannan hmm! To ba kowa bace face ke zumar zuciyata, farin cikin raina. A yau sallah nake son na bayyana miki cewa ina son ki.
BARKA DA SALLAH.
KI DAURE KI AMSA KIRANA.
Na shiga damuwa a lokacin da kika nesanta da ni, ki taimaka ki dawo gare ni tun kafin zuciyata ta kara afkawa cikin hali na damuwa, yau ranar farin ciki ce a gare ni da dukkan sauran musulmin duniya gimbiyata a saboda haka nake kara jaddada miki cewa, ina kaunar ki.
BARKA DA SALLAH.
SAKE-SAKEN ZUCI.
A cikin dukkan mafarkan da nake yi bayan haduwata da ke, ban taba ganin wata rana da ta zo ta kuma wuce ba tare da na gambu tare a cikin lambu mai sanyaya zuciyar masoya ba, rayuwa ce mai dadi ke gudana a tsakanin mu, ina fatan wannan rana ta bayyana a gare ni a zahiri ba a cikin mafarki ba kawai. Ina son ki.
BARKA DA SALLAH.
KI RIKE ALKAWARINA.
Salimat, ina son ki san cewa shi so da kike gani tamkar tab’o ne, adadin yadda ka yi tsalle ka fad’a a cikin shi tofa adadin hakane zai baka wahala a lokacin da ka tashi fitowa, ina fatan mu rik’e juna da amana har abada. Ina fatan dorewar farin cikin ki.
BARKA DA SALLAH.
SARAUNIYAR BIRNIN MASOYA.
A duk lokacin da na zauna ina yin nazari a dangane da soyayyar mu, sai na hasaso cewa dama a ce fikafikai za su bayyana a jikina da na nausa da ke izuwa kayatacciyar fadar dake can babban birnin masoya na sabuwar duniyar mu domin sada ki da kujerar alfarma ta mukamin sarauniyar ‘yan matan duniya da na dade da baki. Shin Rukayya kin kuwa lura da cewa ina neman na zama zautacce a cikin soyayyar ki? Na nitse a cikin son ki ta yadda ba zan iya fita ba. Soyayyar mu ta dabance a cikin wannan duniya ta mu da muke ciki. Soyayyar mu ta zamto tamkar wani rubutaccen labari ne wanda masoya za su shekara suna nazari a kanta. Fatana dai mafarkina ya zamo gaskiya a dangane da ke.
BARKA DA SALLAH.
ZAN ZAMO MIKI GARKUWA.
Alkawari ne na dauka, ba zan taba barin damuwa ta wanzu a cikin zuciyar ki ba matukar muna a tare da juna, ina fatan nan da wani dan lokaci ki tabbatar da hakan bayan kin zamo mata a gare ni, ke kadai zuciyata ta amincewa Fatima, ki huta lafiya. Ki kula min da kanki. Ina son ki.
BARKA DA SALLAH.
KINA DA KYAU MASOYIYATA.
Shin wani ya taba sanar da ke cewa murmushin ki abin so ne? Sannan kuma a duk lokacin da kike yin murmushi ya kan mayar da fuskar ki tamkar wata fitila mai haske? Ke kyakkyawa ce, hakan ya sanya kwakwalwata ta zana mini kyakkyawar fuskar ki a cikin zuciyata wadda ta zamo abar nazarta a gare ni a duk lokacin da nake zaune ni d’aya cikin kad’aici a dare ko safiya. Ke ce abar so na.
BARKA DA SALLAH.
ZAN BAYYANA MAKA SIRRINA.
Amincin Allah ya tabbata a gare ka sahibina, a yau ne nake son na kara bayyana maka matsayin ka a gare ni, tabbas Abba ka zamo wani jigo na dorewar farin ciki a zuciyata. Fuskar ka ce abun da nake kallo na samu farin ciki cikin gaggawa. Karda ka damu ‘Dan-Hausa da rashin bayyana maka gaskiyar al’amari amma a yau ranar sallah kuma ranar farin ciki da murna nake son furta maka cewa ina son ka! Ina son ka!! Ina son ka Abba!!! Daga masoyiyarka Rukayya.
BARKA DA SALLAH.
DAMA A CE HAKAN YA KASANCE A ZAHIRI.
A kullum na kan yi mafarkin ga mu a tare cikin d’aki tare da ‘ya’yan mu, shin ko hakan yana nufin za mu mallaki juna kenan? Tabbas idan hakan ya kasance bani da wani sauran buri a rayuwata face na yi fatan kasancewa a tare da kai a gidan aljanna. Ina son ka, ka kula min da kanka karda ka bari kowace kazamar yarinya ta rabe ka. Ni ce taka Mardiya.

WAKAR ZINARU.
MARUBUCI: Abba Muhd ‘Dan-Hausa.
Bismillahi Allah Ubangijin kowa.
Bani basira a wakar da zan tsarawa.
Na yi baiti ya zamma gwanin birgewa.
Ka sanya wakar ta zamo hanya ta gyarawa.
Karo salati ga Annabi baban Fatima.
Soyayyata gare ki na yi damkawa.
Ina sonki ki so ni mu yi zaunawa.
Kin zamo farin ciki hasken rayuwa.
Kina da kyau da tsari na nuna wa.
Akan sonki bana taba yin nadama.
‘yan’uwa ku taho ku duba.
Wata na hango mai kyan duba.
Kowa na sonta ‘ya har da uba.
Har da Kanawa ban cire Zazzau ba.
A wajen gata ku kira ta da ‘yar mama.
Nasan yanzu kun nutsu kuna ta jira.
Ku ji sunanta Maryam ko Amira.
To amma ita sunanta…. Kai ku jira.
Zan fada muku a nan gaba cikin hira.
Ta fuskar zubi da tsarin waka ma.
To amma barima kawai na nuna ta.
Duk da na san kowa ya san siffarta.
Ita ce HAUSA da ba a kushe ta.
Adabi da harshe da al’ada duk nata.
Bako da d’an gari kai kowa nata nema.
Kai Bahaushe mai kishi ka birge ni.
Da ka hau tudu ka bar o’o da taka tsini.
Wanda ya yada al’ada tasa banda ni.
Ya kama gaibu da muka gano tuntini.
Makiyan addininmu da al’adunmu ne ma.
Ni bance karda ka zamo dan boko ba.
Kaima bai kamata ka zamo kamar baidu ba.
Da ya hangi gafiya ya jefe ta bai same ta ba.
Wadda ya jefa da wadda ya jefa bai samu ba.
kunga ya yi biyu babu nadama zai yi ma.
Dan’uwa duba Hausa ta zaga duniya.
Ta shiga Ghana da Cana babbar nahiya.
Ta shiga Kamaru da Cadi da Saudi Arebiya.
Ta shiga Amurka da Farisa da Misira a duniya.
Ta shiga Jamus da Libiya da Najeriya ma.
Fatan mu a duniya ki yi zarcewa.
Ya zamo baki da sa’a ta jerawa.
Hasken ki a duniya ya yi ta zagawa.
Ki zamo inuwa rumfa ta hutawa.
Da ruwan sanyi mai kore ‘kishima.
K`ungiyar marubuta na yi barka.
ANA a yau ke ce na dauka.
Ki zamo min sanda ta duka.
Ga makiyan al’aduna dika.
Kin zamo fitila a gare ni nima.
Wannan wakar ni ne na tsara ta.
Abba Muhd masoyin ta.
‘Danhausa nake maso Binta.
‘Ya ga Annabi mai jarumta.
Masoyina masoyinka kaima.

SAKONNIN SOYAYYA DOMIN MASOYA.
MAZA
IDAN BABU KE RAYUWA ZATA YI MIN K`UNCI.
A dukkan lokacin da na rasa ki, zan rayu ne cikin ‘kunci da damuwa, hakan ya sanya a kullum nake cewa, idan babu ke ba zan iya rayuwa ba, karda ki gwada ni a kan haka dan Allah, domin kuwa yin hakan ka iya targwatsa farin-cikina. Ina Son Ki.
KINA DA KWARJINI.
A dukkan lokacin da na hango ki sai nake jin fargaba da tsoron tinkarar ki, saboda kwarjininki, hakan ke sanya wa na gaza furta miki cewa Ina Son Ki, duk da dai har yanzu na gaza bayyana miki fuskata, amma ina son fara ganin sa’kon amincewarki ga tayin soyayyar tawa kafin faruwar hakan. Na san kin sha ganin sa’konnina, zan kuma ci-gaba da baki kulawa, domin samun farin-cikinki. Ki huta lafiya. Ina Son Ki.
RUHINMU YA ZAMO GUDA.
SO ka iya had’a ruhi da ruhi su rayu a jikin gangar jiki guda d’aya, kamar yadda ya had’a nawa da naki. Tabbas a dukkan yanayin da kike ciki na farin-ciki ko damuwa, nima na kan kasance cikin yanayi irin wannan. Ki sani cewa da sonki nake kwana da shi nake tashi. Ki huta lafiya.
SON KI NE LINZAMIN SARRAFA TINANINA.
Had’uwata da ke, wata babbar nasara ce a rayuwata. Son ki a cikin zuciyata ya zamto tamkar wani linzami ne da yake sarrafa tinanina, a saboda haka, da ke nake fatan na rayu har abada. Ina fatan kuma zaki ci-gaba da raya soyayyata a cikin zuciyarki. Ina Son Ki.
INA SON KI FIYE DA YADDA KIKE SON KANKI.
An ce kowace ‘kwarya tana da abokin burminta, haka kuwa yake, ni da ke tamkar zara da wata ne, mun dace da juna. Na gode da irin kulawar da kike bani a soyayya, da sannu zan haska ki gane cewa, ina son ki fiye da yadda kike son kanki. Hmm! Masoyiyata, ki kwana lafiya. Sai da safe.
TINANINKI NE AIKINA.
Shin ko kin san da cewa, a cikin mafi yawancin dare bana iya kwanciya na rintsa saboda tsabar tinaninki? Na kan kwad’aitu da son ganin ki a koda yaushe, fiye da yadda kike bayyana kullum a cikin mafarkina. Ni ne dai masoyinki, mai fatan kin tashi lafiya. Ki wuni lafiya, farin cikin raina.
MATA
KAI NE WANDA NAKE K`AUNA.
Shin wai haka ne cewa, SOYAYYA na daga cikin abubuwan da ba a iya gwanancewa a kan su? Matu’kar kuwa haka ne, ni zan yi iya ‘ko’karina wajen ganin na shayar da kai madarar soyayya mai tsananin dad’i. Kai ne farin-cikin raina, kuma kai ne wanda nake ‘kauna, kai ne wanda kuma zan ci-gaba da so har abada. Ina Son Ka.
NI NA SAN NA YI BABBAN DACE DA SAMUN KA.
A lokacin da ka kamu da son wani, bai zama lallai shi ma ya so ka ba, amma ni na yi dace da samun wanda ya bani ikon mulkar zuciyarsa cikin ta’kama da izza, wanda kuma ya kasance cikin soyayyar zuciyata wato ya kasance nima na kamu da son shi. Kai ne wanda ke kore damuwar zuciyata. Ina son ka sosai abun alfaharina.
SON KA TAMKAR HASKEN FARIN WATA YAKE A GARE NI.
Kasantuwar sonka a cikin zuciyata, ya zamto tamkar hasken farin watan da haskensa ke kore duhun duniya. Son ka, ya haske zuciya da saman fuskata, ya haska gangar jiki da saman fatata. Ina Son Ka.
SON KA NA YAWO KULLUM A CIKIN ZUCIYATA.
Masoyina abun alfahira, na kamu da son ka fiye da yadda kake tinani, duk da kasantuwar SO tamkar iska yake da ba a iya gani ko ta6a shi, amma akan iya jin shi a cikin zuciya, tamkar yadda son ka ya kasance cikin sukar zuciyata a dare ko rana. Ina fatan ka yi bacci cikin farin-ciki da nishad’i. Ina Son Ka.

KIRA GA MASOYA A WATAN RAMADANA.
Yi wa masoyiyarka kyauta da kayan shan-ruwa hakan zai ‘kara janyo maka martaba da ‘karin girmamawa daga wajen ta da kuma ‘yan’uwanta.
Tabbas, wannan al’ada ce da ta shahara wajen ‘kara dan’kon soyayya a tsakanin saurayi da budurwa a ‘kasar Hausa. Wannan ita ake kira da ‘Toshin barka da shan-ruwa’.
Ke ma kuma za ki iya bawa saurayin naki kayan shan ruwa, domin samun lada da ‘karuwar soyayya a tsakani, ta hanyar faranta ransa.
Kar da ku manta ana fara aikawa da kayan shan-ruwan ne tun goma ga azumi. Ana kuma bada abubuwa ne nau’in su kayan marmari ko abubuwan sa wa a baka. Misali: Ayaba da gwanda da lemo da abarba da madara da bambita da sauransu.
Allah ya bar soyayya har ya zuwa bayan aure.
follow me on facebook follow me on twitter follow me on instagram

Fitattun labarai

Habiba complete hausa novel

Alqawarin da ciwo

Amfanin cin qafar kaza

Budurwar Roba

Amfanin lemon tsami

Afanin Zogale

Adam A. Zango

Amfanin namijin Goro (bitter kola)

Tona asiri

Yanda zaka duba sunanka a Npower