Hakkin ma'aurata
ce bari mu dad tsakuro wani abu game da shawarwari masu ga masu son yin auren da kuma ma'auratan mata da maza da kuma abubuwan lura ga dukkansu.
Ayoyin masu yawa ne suka zo a cikin littafi mai girma na kur'ani suna nuni zuwa ga dokokin zamantakewar aure da zamu kawo su a dunk'ule kamar haka:
1- Namiji shi ne shugaba a cikin iyali: Nisa'I:34.
2- Mace nutsuwar mijinta ce: Rum: 21.
3- Miji da mata tufafin juna ne: Bak'ara: 187.
4- Kyautata zaman tare da mata: Nisa'I: 19.
5- Kiyaye adalci tsakanin mata: Nisa'I: 3.
6- Namiji da mace daidai suke a kamalarsu ta 'yan adamtaka: Nahal: 97.
7- Kiyaye hak'k'ok'in mata: Nisa'I: 7.
8- Abin da namiji zai yi wa mace mai k'in shimfid'arsa; Na farko: Wa'azi. Sannan sai: k'auracewa shimfid'arta. Sannan sai: sanya k'arfi da duka da takurawa daidai yadda shari'a ta gindaya. Nisa'I: 34.
9- Kyautata wa mace yayin da ake ci gaba da zaman tare ko yayin da za a rabu: Bak'ara: 231.
10- Bayar da kyauta mai dacewa ga mace yayin da za a rabu: Ahzab: 49.
11- Bayar da kyauta ga mace daidai ikonsa idan za a rabu kuma ba a san juna ba a shimfid'a, kuma ba a ayyana sadak'i ba: Bak'ara: 236.
12- Bayar da rabin sadak'i ga mace yayin rabuwa kuma an ayyana sadak'i amma har suka rabu d'in ba su san juna ba a shimfid'a: Bak'ara: 237.
13- Kada a takura wa mace domin ta halatta masa sadak'inta: Nisa'I: 19.
14- Dokokin hak'k'ok'in mace bayan rabuwa, kamar wajan zamanta, da rashin k'untata mata, da ciyar da ita: D'alak': 6.
15- Rashin halaccin cin sadak'in mace ga miji yayin rabuwa: Bak'ara: 229.
16- Sulhu tsakanin miji da mata: Nisa'I: 35 .

Samun nutsuwar ruhi da abokiyar zama ba ya yiwuwa sai ta hanyar auratayya, domin idan ta fuskar fasik'anci ne ake zaune da juna wannan nutsuwar ruhi har abada ba ta samuwa, wannan kuwa abu ne sananne da d'abi'ar halittar mutum, da ilimi, suka gaskata da shi.
Saboda haka duk wanda zai yi aure ya tuna ko ta tuna cewa za ta yi aure ne da wanda zasu zauna domin gina rayuwa maras iyaka da gina gida salihi. Amma tambaya a nan ita ce: Wane mutum ne zamu zab'a domin wannan rayuwa da kuma samun nutsuwa, da soyayya, da tausasawa, da tausayawa juna?.

Ba a son a samu shak'uwa sosai sai da wanda za ku yi aure da shi, saboda haka irin soyayyar da ake yi ta al'adun da suka shigo cikin al'ummar Hausa musamman daga yammacin duniya ba ta da kyau matuk'ar ba aure za a yi ba, domin saudayawa takan kai ga aikata haram wanda zai yi tasiri a kan saurayi da budurwa har k'arshen rayuwarsu, kuma saudayawa rayuwar 'yan mata ta lalace ta hakan sakamakon irin wad'annan miyagun al'adu.
Saudayawa mace mai sauk'in hali da samari sukan iya shawo kanta ta hanyoyi daban-daban wani lokaci ma har wani shak'iyyi yakan ce da ita: Idan kika yarda da ni muka kwanta to lallai zan aure ki. Irin wannan da yake son sha'awa ne ba na Allah da Annabi ba, da zaran ya san ta a 'ya mace sai ya yi wurgi da ita, ya watsar, ba ma zata san cewa mugu ba ne mai tsananin wulak'anci sai idan ta samu cikin d'an shege ta wannan mummunar hanya, a lokacin ne zata san cewa ba ya k'aunarta koda k'wayar zarra. Saudayawa a k'asashen duniya da k'asashenmu 'yan mata suka kashe kan su saboda wannan mummunan hali da mayaudaran samari suka jefa su a ciki, rayuwa ta gurb'ace musu suka koma abin tausayi bayan da suna abin haushi, ko kuma suka gudu daga garuruwansu, ko ma suka haife d'an amma suka yarda shi a kwararo suka gudu.
Da yawa mata suna da sauk'in hali shi ya sa suka yaudaru da wuri, wasu kuma kwad'ayi ne yakan kai su ga fad'awa irin wannan mummunan hali, don haka yana kan iyaye su rik'a sanin menene 'yarsu take yi a waje, kuma da wad'anne irin k'waye ne take mu'amalannan kuma su waye suke zuwa zance wajenta da sunan suna son aurenta.
NASIHOHI
Wannna wasu tattararrun nasihohi ne da zan ba masu son aure ko miji da mata domin zamansu da rayuwarsu su kyautata, da kuma gida wanda zai zama d'aya daga asasin gina al'umma ta gari.

1Kada iyaye su yi wa 'ya'yansu auren dole.
2Nisantar auran mai miyagun halaye kamar mashayin giya.
3 Shiryar da mumini ga wata mumina don ya aureta.
4Ka yi aure don nutsuwa da kame kai, ko taimakon juna, ko gina al'umma ta gari.
5Kada a tsananta aure ya yi wahala domin wani lokaci ana samun wannan wahalhalu ta hanyar al'adu ne ko rashin sanin ya kamata daga masu ikon zartarwa.
6In za a had'u a had'u kamar yadda Allah ya ce, haka ma rabuwa, saboda haka wajan rabuwa sai da shedu da cikar sauran sharud'd'a kamar yadda suke a Addini.
7Kada a fara neman aure sai in da gaske ana so a yi auren ne.
8Babu laifi mace ta nemi namiji ya aure ta, wannan ba aibi ba ne ga mace, saboda haka mace in ta ga tana son wani tana iya shaida masa domin tarihin salihan bayi ya nuna mana haka.
9Wajan yin zance tsakanin saurayi da budurwa dole ne su kiyaye dokokin Allah kamar haramcin ganin abin da yake ganinsa haramun ne.
10Kada mai neman aure ya sanya sharud'd'a masu wahalar cika ga wacce yake son aura wad'annan saudayawa ba su sami burinsu ya cika ba.
11Kada a yi yaudara yayin neman aure haka ma a kula da kyawawan d'abi'u.
12Kyautatawa mace haka nan ita ma ta kyautata masa, kuma a rik'a godiya kan abin da ake yi wa juna na alheri, wannan kan sanya kowane b'angare ya dad'a himma kan abin da yake yi na alheri.
13Kar ka ce ai ba wajibi ba ne in yi mata kaza, domin kai ma akwai abubuwa da yawa da ba wajibi ba ne a kanta, kuma tana yinsu.
14Ku raba ayyukan kwanaki da suke hawan kanku a matsayinku na masu auratayya.
15Kada mace ta yi wa miji gorin satifiket ko wata shaida ta ilimi ko wani abin da ka iya nuna gori a kansa haka nan shi ma haka.
16Kada ki sa ran sai an yi miki abu irin na k'awarki, ya kamata ki kula da iyakar mijinki da godewa, domin rashin hakan kan iya karya masa k'arfin yi miki hidima.
17Tsafta, magana mai sanyaya zuciya, da nisantar jayayya ko bak'ar magana, suna daga cikin sirrin zama mai albarka na soyayya da gina gida na gari da salihar al'umma.
18Kada a yi wa juna nasiha a gaban yara ko mutane, a bari sai hanakali ya kwanta an huta sannan sai a yi wa juna nasiha cikin wasa da dariya hakan yakan fi tasiri ga ma'aurata.
19A jawo k'aunar juna da aiki ba da magani ba ko barazana.
20Kowa ya yi mu'amala da abokin zama da tausasawa ba da tsanantawa ba, domin ba ta magani sai dagula al'amuran zamantakewa.
21Kada mace ta sake ta bayar da fuska sai ga mijinta, haka ma kada ta sake ta tsananta wa mijinta, kuma ta sani kullum dole ta bujuro da kanta ga mijinta.
22Ba wa 'ya'ya isasshen lokaci da zama da su, da hira da su, da saita tunaninsu kan rayuwa.
23Girmama na gaba kamar uwar miji ko uwar mata yana daga kyawun zamantakewa da k'argonta, wato girmama iyayen juna.
24Ba wa juna isasshen lokaci na tattaunawa da hira da warware matsalarsu.
25Tanadar kyauta ta musamman ga juna ta bazata ko kuma ga iyayen juna.
26Wani lokaci matar mutum ta kan cutar da shi wajan ta taimaka masa ko makamancin haka, wannan wani abin yafewa ne da kauda kai saboda yana faruwa ne daga k'auna da son taimakawa daga mata.

Nasihohin Wata Mata Ga 'Yarta
yayin tarewar 'yarta a gidan miji, matar ta yi wa 'yar nasiha ne kamar haka tana mai cewa da ita:

27Ki zama baiwarsa zai zama bawanki [wannan magana tana da hikima sosai domin duk wanda kake jin dad'insa to shi kake kyautatawa]
28Ki k'ask'antar da kai gareshi.
29Ki ji ki bi.
30Ki bi idanunsa [wato ki duba duk abin da yake k'ayatar da shi ki yi abin da ba ya so ko yake k'insa to ki bari]
31Ki kuma bi hancinsa [wato abin da yake so na k'anshi ki yi wanda ba ya so ya ji na daga wari ki nisance shi]
32Ki bi lokacin baccinsa [wato ki kula a lokacin bacci kada ki nisanci wajan baccinsa, wato shimfidarku d'aya, zaninku d'aya, kuma ki yi masa tabarruji]
33Ki bi abincinsa da abin shansa [wato kada lokacin cin abinci ya yi ya nema ya rasa ko ba ki dafa masa ba]
34Ki kiyaye masa dukiyarsa da kula da 'ya'yansa da tarbiyyarsu, da iyalansa, da uwayansa.
35Kada ki sab'a masa umarni ko ki yad'a sirrinsa, domin idan kika sab'a masa ya yi bak'in ciki da ke, idan kuma kina yad'a sirrinsa ya yi miki kaidi ta inda ba kya tsammani.
36Kada ki yi farin ciki a gabansa lokacin da yake bak'in ciki ko abin bak'in ciki ya same shi, haka nan kada ki rik'a bak'in ciki lokacin da farin ciki ya same shi.
.
GA WASU DAG CIKIN HAKKOKIN MATA DA MIJI
.
Hakkin Mace A Kan Mijinta
Daga cikin hakkin mace a kan mijinta shi ne ya girmamata, kuma ya tausaya mata da tausasawa, ya ciyar da ita, idan ta yi laifi ya yafe mata, kada ya la'ance ta ko ya zage ta ko ya doke ta, kada ya muzanta ta ko ya kunyata ta ko ya daidaita mata asiri.
Haka nan akwai hadisai da dama da suka zo game da falalar mutumen da yake taya matarsa aikin gida, don haka bai kamata ba al'ada ta rinjayi Addini, don wasu sukan ki hakan saboda wani dalili maras ma'ana na al'ada.
Dole ne miji ya yi adalci ga matarsa da tsakanin 'ya'yansa da matansa, kamar yadda yake wajibi a kansa ya nuna mata soyayyarsa, kuma ya nuna mata wannan a fili ta yadda zata zama abokiyarsa a komai. Kuma ya rika yi mata maganganu irin na soyayya da nuna kauna ga juna, bai isa ba ya ba ta kudi kawai don yana da shi, wannan ba ya isa ga bukatun mace. Shi ya sa Allah (S.W.T) ya fada a cikin littafinsa cewa: "Ya sanya soyayya (kauna) da tausayi (rahama) a tsakaninku"[39].
Haka nan ba shi da kyau ga miji ya munana zato ga matarsa, ko ba komai munana zato ga musulmi haramun ne, idan mace ta san mijinta yana munana mata zato alhalin tana mai kame kanta wannan yana iya rusa alakar soyayya da girmama juna da ke tsakaninsu har ya kai su ga rabuwa.

Hakkin Miji A Kan Matarsa
Daga cikin hakkin miji a kan matarsa shi ne: Kada ta ki shimfidarsa in ya neme ta, kada ta bayar da izinin shiga gidansa ga wanda ba ya son shigarsu, kada ta yada sirrinsa ko ta yi masa barnar dukiya, ta kula da yaransa da kuma ayyukansa na gida da suka shafeta, kada ta kausasa masa harshe, ta yi kokarin faranta masa rai. Sannan ta rika ba shi uzuri a kan wasu al'amuran, kada ta yi abin da zai sa shi ya ji baya son zama da ita a gida ko abin da zai sanya shi nisantar hira da ita ko kaurace mata.
Wasu ruwayoyi sun kawo hakkin miji kan matarsa kamar haka: Yayin da wani sahabi ya ba wa Manzon Allah (S.A.W) labari cewa: Yana da mata da idan ya kalle ta sai ta faranta masa rai, idan ya shiga gida da bakin ciki sai ta yaye masa shi, idan kuwa ba ya nan tana kare shimfidarsa ba ta ha'intarsa, kuma ta kare dukiyarsa da kula da tarbiyyar 'ya'yansa. Sai Manzon Rahama (S.A.W) ya ba shi amsa da cewa: "Allah yana da ma'aikata, kuma wannan matar tana daga cikin masu aikin Allah, kuma tana da rabin ladan shahidi"[40]. Haka nan wata ruwaya ta nuna cewa: "Mace mai aiki a gidan miji daidai take da wanda yake Jihadi a tafarkin Allah"[41].
Haka nan dole ne ta yi biyayya a gare shi[42] domin shi shugaba ne a gida babu kuma yadda mutane biyu zasu hadu a wuri ba tare da shugaba ba, ta sani rashin biyayya a gare shi yana rusa masa ruhinsa da karya masa zuciya, sai ya fara tunanin daukar fansa sai gaba ta faru, kuma zamansu ya gurbace, ko kuma wannan fushin ya tura shi ga miyagun halaye da kuma yawan fusata da fada.
Kada wata mata ta rika gasa da wasu mata ta ce: An saya wa kawata kaza kai ma sai ka yi min kaza wannan ko kadan ba shi da kyau. Yana da kyau mata su dauki samfurin rayuwar zamantakewa daga Imam Ali (A.S) da sayyida Zahara (A.S), ga wani misali daga irin wannan; Wata rana Imam Ali (A.S) ya shiga wajan Fadima (A.S) sai ya tambaye ta ko tana da wani abu sai ta ce: "Wallahi kwana uku ke nan ya Dan Ammina ba mu da komai". Sai ya ce: "Me ya sa ba ki gaya min ba" Sai ta ce: "Manzon Allah ya hana ta tambayarsa, ya gaya mata cewa: Kada ki tambayi Dan Amminki (Imam Ali) komai, idan ya kawo, in ba haka ba, kada ki tambaye shi".[43]
Duba ki ga irin wannan rayuwa ta gidan Ahlul Bait (A.S) wacce hatta abin da yake wajibi a kan miji ba ta tambaya sai idan ya kawo, saboda haka yana da kyau mata su kamanta daidai gwargwado, kamar yadda maza su kuma su kiyaye ba kwauro ba barna.
Da fatan mun amfani, Amin.
Hakkokin miji a kan matarsa
(1) Dole ne ta yi masa biyayya, ga abin da yake ba sabo ba ne, Annabi (SAW) ya ce: “babu biyayya a cikin sabon Allah, abin sani, da’a tana cikin abin da shari’a ta sani ne.” (Bukhari 7257, Muslim 1840).
(2) Ta zauna a gida ban da yawace-yawace, ban da fita sai da miji.
(3) Ta amsa masa idan ya nema ta, ba tare da matsala ba.
(4) Kada ta bar wata ko wani ya shiga gidansa sai da yardarsa. Manzon Allah (SAW) ya ce: “ka da wata mata ta bayar da izinin (shiga) gidan mijinta, alhali yana nan, sai da yardarsa.” (Muslim 1026), amma idan bai yarda ba, ko ba ya nan bai halatta ta bar wata ko wani ya shigo gidan ba.
(5) Ba za ta yi azumin nafila ba, idan yana nan, sai ya yarda, saboda hadisin da ya hana haka.
(6) Ba za ta dauki wani abu daga dukiyar miji ta bayar ba, sai ya amince, Annabi (SAW) ya ce: “Kada mace ta bayar da wani abu daga gidan mijinta sai ya yarda” (Abu Dawud).
(7) Za ta yi wa mijinta hidima, ta kula da al’amuran ‘ya’yansa, kamar abinci, wanki, share-share da sauransu daidai gwargwado, tun da zaman aure zama ne na cude-ni-in-cude-ka. Nana Fatimah (RA) ’yar Annabi (SAW) tana aikin wahala ainun a gidan mijinta Aliyu bin Ali dalib (RA) (Bukhari 5361, Muslim 2182).
Nana Asma’u (RA) ’yar Abubakar (RA), ita ma tana hidima ainun, har kulawa sosai take yi da dokin mijinta (Bukhari 5224, Muslim 2182). Idan miji ya samu dama sai ya sauwake wa matansa, ko ya rika taya su, don Annabi (SAW) ya kasance yana taya matansa aikace-aikacen gida, idan an yi kiran sallah sai ya fita, ya tafi masallaci, kamar yadda hadisin Nana A’ishatu (RA) ya nuna. (Bukhari 676).
(8) Wajibi ne ta kare mutuncinta, na mijinta da na ‘ya’yansa da kuma dukiyarsa, ban da almubazaranci, Allah (SAW) ya ce: “Matan kwarai, masu kaskantar da kai ne, masu kiyaye (mutunci da dukiya ne) ga gaibin da Allah Ya kiyaye.” (Nisa’i 34).
(9) Ta gode masa idan ya yi abin kirki, ka da ta muzunta masa, ko ta yi masa gori, kuma duk abin da ya samo ya kawo gwargwodon halinsa, ta karba hannu bibbiyu, don Annabi (SAW) ya ce: “Allah ba Ya yi wa matar da ba ta gode wa mijinta kallon rahama ba, kuma ba ta wadatuwa daga gare shi (da duk abin da Ya yi) (Nisa’i 249).
(10) Yi wa miji ado da gyara jiki shi ma babban hakki ne, Annabi (SAW) cewa ya yi: “Fiyayyar mace, ita ce wadda za ta faranta wa mijinta idan ya dube ta” (Nisa’i da Ahmad).
(11) Kada ta cutar da shi ko ta bakanta masa rai, saboda idan ta yi haka, matansa na aljanna wadanda suke jiransa za su tsine mata, su la’ance ta, su ce: “...ya shigo wajenki ne fa kawai! kwanan nan zai rabu da ke ya dawo wurinmu” (Tirmizy 1184, Ibnu Majah 2014).
(12) Ta yi wa iyayensa da ‘yan uwansa mu’amala mai kyau, don haka zai sa ta samu karbuwa a wurinsu, su rika yi mata addu’ar fatan alheri. Mu’amala mai kyawu, ita ce: sake musu fuska, maraba da su, ba su abinci, kyautata musu da sauransu.
(13) Kada ta kuskura ta nemi saki, sai idan abu ya gagara, kuma ta hanyar da ta dace, Annabi (SAW) ya ce: “Duk matar da ta tambayi mijinta saki ba tare da wani laifi ba, to haramun ne ta ji kamshin aljanna.” (Tirmizy 1199, Abu Dawud 2209)
Wadannan su ne hakkokin da aka dora wa mace dangane da mijinta, idan ta kiyaye su, za ta zama ta kwarai, kuma daya daga cikin manyan matan aljannah, kamar yadda Annabi (SAW) ya bayyana cewa: “Idan mace ta sallaci (salloli) biyar dinta (na farilla), ta yi azumin watanta (na ramadan), ta kiyaye farjinta (daga lalata), ta yi biyayya ga mijinta, sai a ce mata “ki shiga aljanna ta kofofin da kika ga dama.” (Ibnu Hibban 41630).
Wannan mata ita ce mace saliha, mai samar da annashuwa da albarkar duniya da lahira, don Annabi (SAW) ya ce: “Duniya jin dadi ne dan kadan, amma fiyayyen jin dadinta ita ce mace saliha.
Idan ma’aurata suka kiyaye wadannan hakkoki, za su samu zaman lafiya da natsuwa a duniyar aure gaba daya, kuma da lahirar ma ta yi kyau.

Mata su ne duniya!
Masana halayyar dan Adam da malaman addini da likitoci sun yi ta kai- kawo da kokarin ganin sun fitar da bayanai na abin da suka fahimta daga iliminsu akan hikimar da Allah ke nufin bayyanawa a cikin bambancin jinsi da ke tsakanin mace da namiji, don fahimtar yanayinsu da kuma sanin irin rawar da kowannensu zai iya takawa a rayuwar mu ta yau da kullum.
Sun ce, “a tsarin halitta, idan muka dauki mafi girman jiki da tsawo; to namiji kenan, mafi yawan mata kananan jiki ne da su, kuma yawancin mata gajejjeru ne akan maza. Sautin muryar namiji tana da girma, ita kuma mace muryarta siririya ce.To mene ne abin mamaki don jin haka ga wanda ya san hikimar Allah da ke cikin yin hakan; watau da Allah Ya sa namiji da mace duk girma da tsawon su da sautin maganarsu daya ne, da ba wanda halittar daya za ta burgeshi, sai ma dai a rika gwabzuwa da juna idan aka samu bambamcin ra’ayi.
Mace ta fi namiji saurin girma,domin tun tana cikin mahaifa zuwa waje mace tafi yawan kwayoyin halittar garkuwar kamuwa da cututtuka. Mace tana riga namiji saurin balaga, kuma tana riga namiji daina haihuwa. Idan muka kalli wannan gabar da kyau, wannanma kamar ta fassara kanta ne da kanta, tun da mace ta fi kwayar halittar garkuwar jiki ai ko za ta fi sauri girma ,tun da jikinta ba ya fuskantar wani kalubale mai yawa da zai tauye mata habakar girmanta.
Shi ma saurin balagar ya samo asali ne daga bunkasar garkuwan jikinta ne, shi ya sa matan da ke cikin wadata da hutu su kan fi na karkara saurin balaga, da dadewa cikin shekarun al’ada da kuma saurin fara al’adar. Mace, shi ke sa kwayayen haihuwarta sukan riga na namiji saurin karewa.
Sai dai bincike ya nuna huhun namiji ya fi na mace zukar iska. Haka ma kwakwalwar namiji ta fi ta mace girma. Zuciyar namiji ta fi saurin bugawa akan ta mace. Shi ma wannan bambanci ya samo asali ne daga fifikon girman jikin na zahiri da na badini da namiji yake da shi fiye da na mace.
A halayya kuwa; masana sun yi ammana da cewa,namiji ya fi ta mace son aikin karfi, da gwagwarmaya, mace kuwa ta fi son tafiyar da komai a hankali cikin natsuwa. A nan za mu iya gane cewa saboda gabobinsa sun fi nata karfi ne, amma ita ma yanayin da aka yi ta na son yin komi a hankali cikin natsuwa ba illa ba ne a gare ta. Dalili kuwa shi ne, idan muka duba da kyau za mu iya gane cewa ita ce take da alhakin renon ciki da renon yara, za mu gane cewa hakan ne daidai da ita,domin da ta zama mai son yin aikin karfi da yin abu cikin gaggawa da cikin haihuwa bai zauna a jikinta ba,shi ya sa za ku ji a asibiti ana yi wa mata gargadin su daina yin aikin karfi ko aikin gaggawa idan suna da juna biyu, domin yin hakan zai iya haddasa musu yin bari.
Sannan kowa ya san yara sun fi son a rika tafiyar da lamarinsu a hankali, saboda su ma a hankali girma da wayonsu ke shigarsu, kuma mace ce mai renon su,don haka idan mun fahimci yanayi da take da shi, shi ma abin so ne ba nakasu ba ne.
Mace ba ta iya yanke shawara a gurguje,kamar yadda namiji kan yanke nan take. Eh, kasancewar mace da wannan dabi’ar shi ma wata baiwa ce a gareta ba wai nakasu ba ne, kamar yadda wasu maza ke gani. Domin idan muka duba muka ga aikin da take da shi na kula da iyali da gida da jama’ar gidan, za mu gane cewar lallai an yi hikima da aka halicce ta hakan, sabili da hakan ne ke ba ta dama ta dubi al’amurra,ta auna su ta gani kafin ta yanke hukuncin da ya dace,saboda ita ce ta fi sanin halin kowa a ckin iyali,kuma ta kan ji nauyinsu a kanta. Wannan dalilin ne ya sa da wuya ka ji an ce mace ta rataye kanta, ko ta kashe kanta.
Mace ta fi son kwalliya da duk wani abin da zai kayatar da ita da kuma son ta yi yanga fiye da namiji. Haka ne domin ai ita aka halittawa kirar yin kwalliya da kayan yanga,irin su gashin kai mai tsawo da sauransu. da cika, aka hura kirjinta da mamuna, aka yi mata baya da kugu mai dauke da kira mai ma’ana, saboda Allah (SWT)Ya san ita abin sha’awa ce ga abokin jinsinta namij, to me ye nakasu gareta don tana dauke da ababen sha’awar da ke dauke hankalin namiji?
Da Allah bai yi wannan hikimar ba ya yaya za a samu bambancinta da namiji, kuma da ya za ta zama abin sha’awa da neman biyan bukata ga mijinta, har ya zama dalilin samar da zuriyya? Da kila sai dai mu zauna tamkar Mala’iku watau ba maza ba mata.
Haka nan mace ta fi namiji surutu, kuma ta fi namiji iya kula da harkar yara; ita a kullum hankalinta na akan cigaban iyali. Hakan kan faru ne a dalilin barinta gida da maza kan yi da iyali su tafi neman abinc, itace kullum suke tare da yara a gida cikin surutu da bari-bari,shi yasa ta kware a cikin yi musu hidima, kuma a lura mace ko da yarinya ce za ka ga ta iya hidimar iyali, domin ita uwarta ke koyawa ba ‘ya’yanta maza ba, don ta san ita ce za ta gajeta a gidan wani.
A takaice a game da dan bayanin da na gabatar a sama, za a iya gane wa mace ita ce sirrin zaman duniya. Ita ce wacce uba da ’ya’ya suka dogara da ita wajen gudanar da harkokin gida da na yau da kullum a kodayaushe.