Mijina sirrina 5

*44* 
  *K*asa motsi nadiya tayi illah kawai kallo data rinka bin motar amadi dashi har ta daina hangoshi, gabanta ne taji ya tsinke yafara faduwa wanda bata san dalili ba,
Dakyar tayi ta maza taja kafarta tabar wurin ta nufi cikin gida, da amira tafara cin karo tana kokarin hada kayan wanke wanke, daf da zata wuce ta shiga daki taji maganar mama daga kofar kitchen tana yimata magana,
"Bakon naki yatafi?"
"Ehh mama yatafi.." Tafada jikinta asanyaye,
Kallonta mama tayi dakyau anan tagane cewar akwai abinda yake damunta dan haka tasake yimata magana,
"Nadiya ya kamata dai ki zauna kiyiwa kanki karatun ta nutsu domin wallahi ina jiye miki yin nadama aduk ranar da kika bari wannan yaron ya subuce miki, kiduba kiga irin dawainiyar da yake yi da yaranki, ko haka ai yasa ki saurareshi.."
Shiru tayi tana sauraren mama,itafa kowa yakasa gane matsalarta ne, ita gaba daya mazanne yanzu sun gama fita aranta, gani takeyi tunda yaya kabeer yayi mata wannan cin mutuncin to kowanne namiji ma hakan zaiyi mata,
"Kinji abinda nafada miki ko..?"
Muryar mama tadawo da ita cikin hayyacinta,
"Ehhh naji mama.." Tabawa mama amsa, juyawa Maman tayi ta nufi cikin kitchen tana cewa,
"Yawwa yadai fi miki"
Daki ta shiga nan tasamu su fadeel duk sun wargaza kayan siyayyar da amadi ya iyo musu suda su waleeda da husna,
Ko takansu bata biba ta nemi wuri ta zauna tana tunanin abinda zaije yazo nan gaba acikin rayuwarta, da ace su mama zasu barta to da ita da sake yin aure sai a lahira amma aduniya dai kam tagama,
Tadade tana tunani acikin ranta har na tsawon wani lokaci,shigowar Amira ce ta katse mata tunanin da takeyi,
"Anty nadiya wai ana sallama dake awaje.."
"Amira dan Allah ku kyaleni kaina ciwo yakeyi.."
Juyawa Amira tayi tafita,Amira bata jima da fitaba mama tashigo dakin,
"Haba nadiya ki leka mana kiga ko wanene inyaso sai kibashi hakuri tunda bakya jin dadi.."
Mikewa tayi ta fita batare da tayi magana ba,
Kamar acikin mafarki ta hangoshi tsaye yasha wani black space (no respect) kamar kada ta karasa wurin sai kuma taga cewar gara taje inyaso sai ayi wacce za ayi,
Yanda yasha kunu ya hade girar sama da kasa haka itama tasha kunun ta daure fuskarta tamau fiyeda yadda ya daure tasa,
"Lallai yaya kabeer dinnanma dan rainin wayone.." Tafada acikin zuciyarta gamida karasawa wurinda yake zuciyarta cikeda tsanarsa tareda jin haushinsa, ita sai yanzuma take nadamar kasancewarta matarsa ada,
Ko sallama bata yimasa ba ta tsaya tareda rike kugu,
"Naji ance ana sallama dani dama kaine? Idan Kaine to gani kayi kafadi abinda ya kawoka domin sauri nake.."
Mamakine ya kama kabeer ganin yanda nadiya ke faman kallonshi shekeke tana yimasa kallon hadirin kaji,
"Waye wanda naga yakai su fadeela supermarket...?" Yafada cikin kunar rai tareda gadarar cewar yaranshi ne,
Saida ta dan yimasa wani kallo mai taken ka rainawa kanka wayo sannan tace,
"Saurayina ne wanda zan aura, da magana ne?"
Wani takaici da haushine suka ziyarci kabeer lokaci guda,kallonta yayi ta cikin bakin glass dinshi,
"Saurayinki?"
"Kwarai kuwa domin ba bazawari bane saurayine sabo fil..."
Saurin dakatar da ita yayi, "ya isa haka, kina jina, kibude kunnenki dakyau kiji daga yau sai yau, kar wani wanda ya sake gigin daukar min yarana domin ba wani dan iska bane ya haifar minsu, nine na haifi abina.."
"Dakata yaya kabeer, kai har kana da bakin da zaka kira su fadeel da sunan yaranka? Yaran da kayi watsi da rayuwarsu ka banzantar dasu, yaran da harma sun manta da cewar kaine ubansu, tunda muka rabu dakai daidai da rana daya baka taba zuwa ka gansu ba bare ka dauki dawainiyarsu, kaga kuwa indai hakane to baka da bakin da zaka kirasu da 'yayanka..." Ta karashe maganar tana yin hucin bacin rai,
"Haka kikace? Nadiya ni kike fadawa haka? To tunda abin babu mutunci aciki wallahi sai kin bani yarana, zanzo zan tafi da yayana inyaso kije ki auri duk uban wanda zaki aura.."
"Wannan ne kuma baka isaba, sannan ni ba uban wani zan aura ba saurayi zan aura mai sona wanda babu abinda yasani na yaudara baima taba auren ba bare har ya zama uban wani.."
Tana gama fadin haka ta juya tafara tafiya batare data sake sauraron kabeer ba, in banda daci babu abinda makogaron kabeer yakeyi saboda yasan nadiya magana ta fada masa,sannan gashi zatayi aure zata auri wani wanda bashiba,
"To tunda kin zabi ayi rashin mutunci kisani wallahi sai na karbi yayana ko da karfin hukuma ne.."
Tana jinsa amma bata waiwayo ba saboda ita yanzu bata kaunar koda ganin fuskarsa ne, kanta kuwa in banda ciwo babu abinda yakeyi saboda tashin hankalin yaya kabeer,
"Ohh ni nadiya ko sai yaushe zan samu kwanciyar hankali?" Ta tambayi zuciyarta, ko mama bata fadawa cewar kabeer bane bare tafada mata yanda sukayi dashi ta shige daki ta kwanta.
   Tana kwance adaki har lokacin sallar isha yayi, tana jin dawowar Abba amma bata iya fita taje tayi masa sannu da zuwa ba saboda ciwon da kanta keyi mata.
Abangaren amadi kuwa abinda yafadawa nadiya kawai yafada ne saboda yana son ta amince ta aureshi amma yasan bazai iya rabuwa da itaba koda kuwa zata cigaba da fada masa bata sonshi kamar yadda ta saba,
Karfe 5 da yan mintuna ya isa gida, lokacin da yayi packing din motarshi yana kokarin fitowa yaji ihun murnar su inteesar da hamid yaran anty siyama,
Fitowa yayi ya rike da hannunsu,
"Uncle amadi tun dazu munata jiranka kadawo ka kaimu..."
"Ohhhh hamid rigima kai kullum a zuwa yawo kake ne..?"
Falo suka shiga inda su hajiya ke zaune itada anty siyama suna kallon labarai,
Zama yayi acikin kujera sharaff alamun agajiye yake,
"Anty Amadi daga ina haka?" Anty siyama ta tambayeshi tana rikeda juice a hannunta,
"Anty daga zance nake.."
Murmushi tayi ta kurbi juice din dake hannunta,
"Kaima wasa kake, yaya zakayi da zee?"
"Nidai anty mubar wannan maganar, yanzu dai yaushe zanzo nakai su inteesar yawo..?"
"Haka dai kake koda yaushe baka son maganar aure, ban saniba ko haka zaka zauna babu aure, ai tun yanzu ya kamata kafara neman kaga idan lokacin yazo shikenan sai kawai atada maganar aure.."
"To anty" yafadi tareda mikewa kasancewar agajiye yake liss, dakinsa yawuce domin watsa ruwa amma kuma zuciyarshi sai tuno masa da rabin ransa takeyi wato nadiya,
Bayan yafito daga wankan ne yaji bazai iya yin komai ba har sai ya kirata yaji muryarta,
Tana tukunkune ciwon kai na azabtar da ita taji karar wayarta sharewa tayi taki dauka duk da cewar bata san wanene mai kiran ba,
Kasancewar yasan halinta na kin daukar waya idan bata gadamaba yasashi hakura bai sake kiraba ya ajiye wayar yafita zuwa falo wurinsu hajiya, kusa da hajiya ya zauna,
"Hajiya yau me kuka dafa ne?"
"Autana ai yau girkinka nayi maka daban, abinda kafi so nasa aka dafa maka..."
"My hajiya kince yau inji dadina kenan.."
Yafada yana murmushi tareda tashi ya nufi kan dining yana jin anty siyama tana cewa,
"Kaga dan gatan hajiya"
Murmushi yayi baice komai ba saboda idan da sabo to yasaba da tsokanar da anty siyama take yimasa.
Duk da cewar ya kira nadiya bata daga ba hakan bai hanashi sake kiranta ba da misalin karfe 9 nadare, amira ce ta dauki wayar saboda ita nadiyan tayi bacci, ai amira nafada masa nadiya bata da lafiya ya gigice ya rude,
"Yanzu tana ina?"
"Gata tana bacci.."
Katse wayar yayi yazauna abakin gadonshi duk sai yake jin jikinsa yana sauya masa, bai san wanne irin so yake yiwa nadiya ba, kasa aiwatar da komai yayi ya zauna shiru har na wani lokaci,
Ganin karfe 11 saura yasa yasake kiranta, lokacin ta farka tana dafe da kanta wanda yake yimata zazzafan ciwo....

*45*
*D*a k'yar ta iya daukar wayar tana mai runtse idanuwanta  saboda zafin ciwo,
"Sannu nadiya... Ya jikin naki?" Yafada muryarsa asanyaye kamar shine bashida lafiyar,
"Da sauki.."
"Meke damunki?"
"Kainane yake ciwo"
"Kinsha magani?"
Duk ta kosa da wadannan maganganun da sukeyi saboda sarawar da kanta keyi mata,
"Uhmmm, kinsha magani?"
"Nasha.."
"Sannu, Allah yabaki lafiya"
"Amin"
Shiru kowannensu yayi shi yana tsoron kar ya cigaba da magana ya dameta ita kuma dama duk tagama kosawa da maganar da sukeyi, ahaka suka cigaba da zaman kurame har na tsawon minti ishirin sai can ya dan saki ajiyar zuciya yayi magana,
"Baby ko kinyi bacci ne?"
"Uhm, uhm.." Ta amsa masa,
"Kinci abinci ne?"
"Uhm" tasake bashi amsa, shirun suka sake yi,
Tana rike da kanta bata iya komawa bacci ba saboda baccin da tayi dazu har dare ya raba,
Yanda batayi bacci ba haka shima amadi baiyi baccinba sai dai idan ya danji shiru yace ko tayi bacci tace a'a ahaka suka zauna har wurin karfe 4 sai lokacin tasamu barci ya dauketa, jin yayi magana shiru bata amsaba ya tabbatar masa da tayi bacci sai lokacin shima yasamu ya dan kwanta kafin asuba ta karasa.
***
A fusace kabeer yabar gidansu nadiya yana driving yana tsaki gamida masifa shi kadai,
"Harni yarinyar nan zata cewa wai saurayi zata aura? To ta auri jariri ma karewar yarinta..."
Shi gaba daya maganganunta babu abinda ya bata masa rai kamar auren da yaji zatayi nan yaji tsohuwar soyayyarta ta motsa masa take sonta ya dawo sabo fil acikin zuciyarsa yaji yanzu babu wata wadda yake son kasancewa da ita a matsayin mata sama da nadiya,
Packing yayi agefen titi ya tsaya yafara tunanin abinda yake shirin faruwa dashi, abubuwa sun hadar masa goma da ishirin nafarko saki uku yayiwa nadiya gashi yanzu Allah yasake jarabtarsa da sonta akaro na biyu a lokacin da bashida wata dabara, ga zumuncin da yayi watsi da fatali dashi gamida watsi da yaranshi da yayi wanda harma sun manta dashi sannan yanzu kuma yana son kasancewa dasu,
Tsakaninsa da iyayensa babu alaka mai kyau tsawon shekaru suna fushi dashi sannan asabe mc kullum cikin zugashi take tana cewa ya rabu dasu basai yaje wurin da sukeba sannan zasu yi masa fushin ba, koda yaushe cikin bashi gurguwar shawara take, yanzu bashida kowa sai ita, duk tabi ta kanainayeshi ta dorashi akan hanya marar bullewa.
  Kamar zaiyi kuka haka ya lallaba yaja motarsa ya nufi gida duk da cewa idan yaje babu abinda zai samu na farin ciki awurin asabe sai ko damuwa saboda bata da lokacinsa sai na kanta, bata da tsabta, babu komai atare da ita sai damuwa shi kansa akoda yaushe yana yiwa kansa ala wadarai saboda rabuwa da yayi da nadiya,
Mace mai tsabta da biyayya komai nasa tana tattali amma banda asabe,
Lokacin da ya kutsa kan motarsa cikin gidan da asabe yayi arba ta rako wasu kawayenta guda uku sai shewa sukeyi suna guda daga ita sai wata yar ficikar Riga kalar ta bacci, kullum aikin kenan yawo da kayan bacci wuni zatayi dasu ajikinta,
Ko kallonsu baiyi ba ya wuce packing space yaje ya faka motarsa ya fito yawuce ciki,
Cikin sauri tabi bayansa zuwa cikin falonta wanda yake cike da datti domin mai yimata aiki ta yi tafiya zuwa garinsu ita kuma bazatayi ba,
Akan kujera ya zauna cikeda damuwa, kusa dashi taje ta rabu tafara farfara idanuwa,
"Barka da zuwa, sannu da dawowa, nima kawayena na raka, su atika ne sukazo wai bikinta za ayi shine ta zo yimin maganar anko.."
"Yanzu me kikeso inyi miki?" Yafada akufule domin acikin haushi yake,
"50 thousands zaka bani.."
"To kibari sai naje na sato kamar yadda nasaba sai inbaki.."
Yafada cikin fada tareda mikewa, saurin shan gabansa tayi taci kwalar rigarsa....
***
  Misalin karfe 8 nasafe amadi ya fito cikin wata blue din shadda,rigar iya gwiwarsa ta tsaya mai dogon hannu, kafarsa sanye da takalmi baki, sumar kanshi yake tajewa da cumb hajiya ko fitowa batayi ba tana daki sai mai aikinta ce ke cikin kitchen tana kiciniyar hada musu break,
Ruwan tea yasha kawai ya fita, bai zame ko inaba sai kasuwa,koda yajema mutane basu firfito ba sai kalilan abinda yakaishi yayi ya fito ya nufi rano,
Lokacin da ya isa garin ba afi karfe 10 nasafe ba, gidan daga amira sai mama sai nadiya amma gaba daya yaran an shiryasu sun tafi makaranta,
Nadiya tana kwance a falon mama akan doguwar kujera amira ta shigo rikeda wayar nadiya,
"Anty nadiya yaya Ahmad ne yake kiranki.."
"Mayena kenan.." Tafada acikin zuciyarta amma afili kuma sai batayi maganaba illa kawai hannu data mika ta amshi wayar,yanda muryarta take asanyaye haka shima tashi muryar take sanyi kalau,
"Ya jikin naki?"
"Da sauki"
"To gani awaje nazo dubiya..."
Mamakine ya isheta saboda jin cewar wai yazo da wannan sanyin safiyar, amma koda ta tuno naci da juriya irin nashi sai taga wannan ba komai bane awurinshi,
"To ai ni bazan iya fitowa ba yanzu ma kaga akwance nake.."
Juyawa amira tayi ta fita saboda kiran da taji mama tana kwala mata daga cikin kitchen,
"To ya za ayi kenan?" Taji ya tambayeta, shiru tayi saboda bata san abinda zatace masa ba,
"Kodai injuya inkoma bakya son ganina?"
Nan dinma shirun tayi bata amsaba,
"Shikenan bari naje natafi.."
Dif taji ya kashe wayar tana kokarin juyawa ta gyara kwanciyarta kuma taji maganarsa atsakar gida suna gaisawa da mama,
"Ohhh wannan kowanne irin mutum ne shi oho, ban taba ganin mutum mai hakurin Ahmad ba.." Tafada acikin zuciyarta amma kuma tarasa dalilin da yasa har yanzu bataji tana sonshi ba domin ko maganar data fadawa yaya kabeer cewar zata auri amadin kawai tafada ne dan ta tura masa haushi amma bawai dan tana son amadin ba,
Tare da Amira suka shiga cikin falon inda nadiya ke kwance, hijab din dake jikinta ta sake gyarawa saboda rigar bacci ne ajikinta,
Wajen kanta yaje ya tsaya ya dafa hannun kujerar da kanta ke kai yana kallonta, tsabar naci irin na zuciyarshi sai yaji tayi masa yimasa kyau a wannan yanayin duk da fuskarta akode take babu kwalliya, idanuwanta arufe, dan sunkuyawa yayi,
"Baby...."
"Uhmm" ta amsa dakyar saboda bata son sunan nan da yake fada mata,
"Sannu..., jikinne?"
Kai ta girgiza masa,
"Kinji sauki?"
"Uhmmm"
"To Allah ya kara baki lafiya.."
"Amin.."
Haka yaci gaba da tsaiwa akanta ita kuma tana kwance ko bude idonta bata yiba bare taganshi sai dai kamshin daddadan turarenshi gaba daya ya cika mata hanci,
Sai da Amira ta shigo dauke da tiren abinci sannan tayi masa magana,
"Yaya Ahmad ka zauna mana.."
Wuri yasamu yaje ya zauna, yaci gaba da kallon gimbiyar wacce ke kwance jikinta lullube da hijabinta.....

*46*
 *Z*ama yayi akan kujera ya zubawa gimbiyar ido wacce ke kwance ta lulluba da hijabinta,
"Yaya Ahmad ga breakfast.." Amira tace dashi tana ajiye masa tiren agabanshi,
"Amira ita nadiya din taci abinci ne?" Ya tambayi amira muryarsa asanyaye,
"A'a bata ciba amma ai zata ci"
"To ai ita yakamata afara bawa baniba"
"Tom bari naje nakawo mata nata"
Fita amira tayi shikuma yaci gaba da kallon nadiya wadda ke kwance tana jin duk abinda ke faruwa,
Babu jimawa amira ta dawo rikeda cup mai dauke da ruwan zafi sai filet wanda aka doro soyayyen kwai akai,
"Anty nadiya gashi tashi kici.."
Ko motsi batayi ba bare asaka ran zata tashi,
"Anty nadiya..." Amira tasake kiran sunanta, tashi amadi yayi yaje ya karbi cup din da filet din dake hannun amira,
"Kawo amira jeki kawai.."
Bashi amira tayi ta juya ta fita, magana yafara yimata ahankali cikin sanyin muryarshi,
"Baby.."
"Uhm.."
"Tashi kisha tea din kinji.."
Shiru tayi masa sannan batayi ko motsi ba,
"Yi hakuri baby kitashi, ko bazaki iya tashiba?"
Sake yin shiru tayi har lokacin idanuwanta suna rufe,
"Tashi kinji.."
"Zan tashi"
"To tashi.."
Hijabinta ta gyara sannan ta tashi ta zauna sai lokacin ta kalleshi gaba daya haushinsa takeji saboda ya takurawa rayuwarta karfi da yaji yana neman ya rusa mata plan dinta da ta shirya,
Akusa da ita ya zauna ya mika mata tea din nan ta karba fuska adaure kamar dole,
Shikam murmushi yakeyi ganin ta tashi sai wani cin magani take, idan da sabo yasaba ganin wannan cin maganin nata sai dai kuma shi yadau alwashi bazai taba barinta ba har sai ya mallaketa ya koyar da ita sonshi sannan sai ta kamu da tsananin sonshi fiyeda yanda yake sonta duk da zuciyarshi tana fada masa cewar tana sonshi kawai damuwarta ce ta rinjayi son shiyasa takasa bayyanar mishi,
Yanda take shan tea din kamar magani takesha,
"Baby bazaki ci kwan ba?"
"Zanci.."
"To ci"
Karba tayi tafara gutsira ahankali tana ci har ya isheta,
Mamace ta shigo, ganin amadi baici breakfast dinba yasata fara fadin,
"Yaya kuma zakazo ka zauna baka ci abincin ba, dan Allah rabu da ita kaje kaci abincinka, ita ai ba karamar yarinya bace da sai an lallabata.."
Murmushi yayi saida mama tawuce sannan yayi magana ahankali wanda iya nadiyan ne kadai taji abinda yace,
"Mama bata san ni lallabaki nake yiba fiyeda yadda ake lallaba karamin yaro ko jariri..."
Sake daure fuska tayi ta kawar da kanta, tashi yayi daga kusa da ita yaje ya zauna akujerar dake fuskantarta yafara shan tea din data rage yana cin guntun wainar kwan da ta bari,
Iya Wanda ta rage yaci ya ajiye cup din da filet din nan amira ta shigo tace masa mama tace yaje su gaisa da Abba saboda abban fita zaiyi,
Tashi yayi yabi bayan amira zuwa falon Abba, suna zaune shida mama amadi ya shiga suka gaisa har zai tashi Abba ya dakatar dashi,
"Ahmad dama ina son zanyi magana dakai.."
"To Abba"
"Ahmad kasan da cewar nadiya dai ba budurwa bace dan haka babu bukatar ayi dogon nema akanta saboda yanzu tawuce wannan lokacin, kasancewar ta taba yin aure harda arzikin yara guda biyu sannan dan uwanta ta aura wanda dani da mahaifinsa uwarmu daya ubanmu daya"
"Hakane Abba"
"To idan har dagaske ka shirya auren nadiya ina son ka turo magabatanka duk da cewar ban san yanda kukayi da itaba, amma naji komai awurin mahaifiyarta dan haka yanzu abinda nake so dakai shine ka turo magabatanka, amma kaji ka amince zaka aureta ahaka?"
"Ehh Abba zan aureta ahaka kuma insha Allah magabata na zasuzo, nagode madallah, Allah yakara girma"
"Amin, Allah yasanya albarka acikin neman, zaka iya tafiya"
Tashi amadi yayi yafita zuciyarsa tayi masa wani irin sanyi duk da yasan akwai matsalar da zai fuskanta daga ita yar rigimar tasa amma yasan insha Allah wannan mai saukine domin zai jure komai indai daga gareta ne.
Tana zaune a inda yabarta bata san abinda yake faruwa ba saboda koda wasa bata zaci mama zata kaiwa Abba maganarba, shiga falon amadi yayi ya dan saci kallonta nan yaga ta hade rai kamar zatayi me,
"Baby banfa kawo miki kayan dubiya ba"
"Dama ai ban nemaba"
Murmushi yayi yaje kusa da ita ya sunkuya saitin fuskarta,
"Allah ya huci zuciyarci da wasa nake nakawo miki me zaki sha aciki? Lemo ko ayaba?"
Kawar da kanta tayi tayi banza dashi,
"Baby bazaki amsa minba? To bari naje na shigo miki dasu saboda yanzu zan koma gida akwai abu muhimmi da naci karo dashi da sanyin safiyar nan.."
Nan dinma shirun tayi dan haka yafita yaje wurin motarsa ya bude yafara fito da siyayyar da ya iyo mata, kayan marmari babu abinda babu, lemon kwali da na gwangwani da malt, ga madara, da kanshi ya shigar da kayan cikin gidan nan amira ta tayashi kasancewar amir baya nan yatafi sumaila hutu gidan umman sumaila,
Atare mama da Abba suka fito,lekawa falon Abba yayi yai mata sannu nan ta gaisheshi ya fita yatafi wurin aiki bayan yayiwa amadi godiyar wahalar da ya iyo ta siyayya,
"Baby bari naje nakoma sai munyi waya ko? Allah yabaki lafiya kinji"
"Amin" tafada fuskarta aturbune, duk sai amira dake tsaye taji babu dadi saboda ita bataga laifin amadi ba,saurayi mai class irinshi kyakkyawa mai ilmi komai nashi na classic guys amma sai faman wahalar dashi nadiya take,
"To baby bye"
Fita yayi yana yiwa amira sallama, "amira sai anjima Allah yakara sauki"
"Amin yaya Ahmad Allah ya kiyaye hanya angode madalla"
Kallon nadiya Amira tayi, "Anty nadiya gaskiya wallahi abinda kike yiwa yaya Ahmad yayi yawa, kiri kiri fa kike nuna bakya sonsa gashi yayita yimiki magana amma kiyi banza dashi sai kin gadama zaki amsa masa..."
"Ke ina wasa dake? Ni sa'arki ce? Karki yimin rashin kunya wallahi yanzun nan jikinki zai gaya miki.."
"Idan kuwa kika kuskura kika dakar min'ya nima sai na yimiki dan banzan duka" mama tafada bayan ta shigo cikin Falon saboda taji duk abubuwan da suka fada,
Fada mama taci gaba dayi,
"Haba abubuwan naki sun wuce hankali, narasa wanne irin kafiya da shegen taurin kai Allah yabaki, yarinya sai kace mutanen farko ataurin kai, shi wannan yaron meye nashi aciki da zaki rinka wulakantashi, sai kace shine yaje yace kabeer din ya sakeki? Akanki aka fara rabuwar aure da zakibi ki tsangwami yaro kamar shine yayi miki silar mutuwar auren, to bari kiji abinda amira tafada miki gaskiya tafada sannan wallahi mutukar baki so mai sonki ba to kuwa zakiso makiyinki, haba kaji min yarinya mai masifar taurin kai kamar baki san kaddara ba?"
Hawayene sharrrr suka fara bin kumatun nadiya ita bacin ranta wato harsu mama summa manta da bakar azabar da tasha da damuwar da ta tsinci kanta ashekarun baya ata sanadiyyar da namiji, har ciwon hawan jini sai da yakamata da tazo da karar kwana ma tana iya mutuwa amma shine yanzu tun ba aje ko inaba har sun manta suna ganin laifinta saboda kawai wannan yar karamar yaudarar da amadi ya shiryo mata,
"Yanzu mama laifina kuka gani kenan? Kun manta halin da nashiga abaya, kun manta damuwar da yaya kabeer ya jefani?"
"To ai nadiya mutane basu taru sun zama dayaba, kowa da halinsa, kimanta da kabeer ki fuskanci Ahmad mai sonki nagaskiya.."
"Wallahi nidai mama bana sonshi, ni bana sonshi, bana sonshi, haka yaya kabeer ma sai da nace bana sonshi amma aka matsanta min har sai da na aureshi daga karshe yayi min butulci,ni bazan yi aure yanzu ba.."
Tafada cikin kuka tareda kifa kanta ahannun kujera tana kuka....

*47*
   *T*sayawa kawai mama tayi tana kallonta amma acan k'asan zuciyarta tausayinta take ji saboda tasan tsoron sake shiga irin halin data shiga abaya take yi sai dai amma kuma tunda ta samu mai sonta da gaskiya ai bazasu zuba mata ido har ya sub'uce mata ba,
Juyawa mama tayi ta fita bata sake magana ba tabar nadiya tanata faman shasshekar kuka, Amira ce taje kusa da ita ta zauna tafara bata baki,
"Anty nadiya dan Allah kiyi shiru, Allah ya baki hakuri amma wallahi yaya Ahmad yana sonki ni tausayinshi ma nake ji saboda gaba d'aya bashida buri sai na kyautata miki, baya son b'acin ranki nasan ma wallahi ko auren ma kukayi sai yanda kikayi dashi tunda yana son farin cikinki.."
D'agowa nadiya tayi fuskarta shabe shabe da hawaye,
"Haba Amira ai bai kamata yanzu ace dole sai nayi aureba tunda nayi auren nan naji abinda ke cikinsa, yanzu dan Allah ko a mafarki kin tab'a zaton cewar yaya kabeer zaiyi min haka? To shi da yake dan uwanama jinina ga abinda yayi min inaga wanda yake bare banida hadin komai dashi? Yaya kabeer fa jiya yazo gidan nan yace min wai dole sai nabashi yaranshi har da su zancen zai kaink kotu akai.."
Baki bude dan tsananin mamaki Amira ta kalleta, "yaya kabeer din? Dan rashin mutunci ko dan me? Mutumin da bai sake bi takan yaranba amma shike ikirarin abashi su?"
"Wallahi Amira dagaske nake ba karya ba, tsabar bacin ranshine da fargaba ya haifar min da rashin lafiyar da nake ciki yanzu"
"Allah ya rufa asiri amma ai babu alkalin da zai bashi su fadeel yanzu.."
Mama dake waje tana jin duk abinda suke fada amma batace komai ba sai dai ta cika da mamakin kokari irin na kabeer.
   Lokacin da Amadi ya koma gida yayi niyyar sanar da hajiya maganar aurenshi da nadiya amma sai yaji ta tareshi da maganar cewar gobe yayyunshi zasu zo saboda dama sukan ware lokaci na musamman suzo gidan gaba dayansu su dan tattauna su sada zumunci bayan kamar sati biyu sai kowa yakoma inda ya fito jin haka yasashi yin shiru har sai yan uwan nashi sunzo sannan zaiyi maganar,kiran nadiya kuwa tunda ya dawo yake kiranta duk da idan ta dauka bata yimasa magana da yawa daga uhm sai um um amma hakan bai hanashi sake kiranta yaji jikinta ba, kowacce rana yana yi mata waya sau 8 koma fiyeda haka.
  Washe gari tunda safe baki suka fara sauka, anty dija itace tafara zuwa itada yaranta guda uku biyu maza mansur da muhsin sai mace guda daya Amal, hajiya rasa inda zata saka jikokinta tayi dan murna, dakin amadi sukaje suka tasheshi daga baccin da yake ta hanyar yin tsalle akansa dole babu shiri ya tashi, zuwan anty Dija da kamar minti 20 Anty siyama tazo domin ita agari take tana zuwa yaya yaseen na zuwa shima amma shi baizo da matarshi da yaranshi ba shi kadai yazo nan gidan ya gauraye da hirarsu da shewarsu yaran anty Dija da anty siyama kuwa sai wasansu suke suna tsalle ajikin amadi,
Girke girke kala kala hajiya tasa aka shirya musu amma kuma duk da murnar ganinsu bai sa ta manta da shalelenta amadi ba domin komai tace autanta komai autanta.
  Sai bayan sallar azahar sannan anty hamida tazo wacce ita amadi ke bi nan gida yasake hargitsewa da murna, cikeda murnar ganin juna suka shiga gaggaisawa kafin su hau table domin diban garar da hajiya tasa aka shirya musu, kowa acikinsu tsokanar amadi yake yi sai kace wani kakansu daga kowa ya debo tsokanarsa sai yace autan hajiya ko anty amadi kaza,
Har dare suna tare afalon hajiya suna shan hirar yaushe gamo sai misalin karfe 11 sannan suka fara kokarin neman makwanci,
"Anty amadi adakinka fa zamu kwana yau sai dai ka dawo falo kan doguwar kujera.." Anty Dija ta fada tana rikeda amal akan kafadarta,
"A'a babu mai kawo min auta falo yana dakinsa kuje ku k'ak'aba adakina kuda 'yayanku" hajiya ta fada,
"To hajiya" anty Dija ta amsa mata tawuce dakinta, dakinshi shima amadi yawuce yaje yayi shirin bacci yana son ya kira nadiya yana tsoron ko tayi bacci kar ya tasheta daga karshe dai yayi hakuri ya kyaleta bai kirata ba.
  Kamar koda yaushe yanda suka saba suna tattauna abubuwan da suka shafesu akowanne zama yauma sunyi irin wannan tattaunarwa saida amadi yaji kowa ya gama fadin abinda yake son fada sannan yace yanada magana,
"To autan hajiya muna jinka meya faru?" Yaseen yace dashi,
"Yaya dama wata yarinyace nake so kuma iyayenta sunce naturo magabata na.."
Shiru dukkaninsu suka yi babu wanda yayi magana shi kuwa yaseen zubawa amadi ido yayi kawai yana kallonsa,
"Kai anty amadi me yakaika nemo aure tun yanzu?" Anty Dija ta fada tana mamakinsa,
"Anty wacce nake so Nagani shiyasa.."
"Ai ko zakayi aure sai kabari ka cika 30 years tukunna ko" anty hamida ta fada,
"Nifa badake nake ba" yace da hamida saboda ita yake bi sakonshi ce,
"Kar dai kayi min rashin kunya" tafada tana harararshi,
"Waima duk ba wannan ba kai yanzu ko ance za ayi maka aure sai ka yarda? Iya masters fa gareka kadai, sannan baka da gida bakayi gida ba, baka jima da fara aiki ba, haba anty amadi kadai sauya shawara" anty siyama ta fada,
"Anty nidai ko banida gida zanyi aure yanzu"
"Baza kayiba, babu wanda zaiyi maka aure yanzu, ka bude kunnenka dakyau ma kaji karatu zaka koma nanda next month dan haka karka sake yimin maganar aure yanzu.." Yaseen yace dashi cikin fada, jin babu wanda ya goya masa baya yasa idanuwanshi kadawa suka yi jajur zuciyarshi ta soma radadi...

*48*
*Z*uciyarshi na wani irin rad'ad'i ya dubi yayan nashi idanuwanshi jajur,
"Yaya to idan banyi aure yanzu ba sai yaushe zanyi?"
"Sai lokacin da ka girma ka isa aure, kai bama tun dadewa nayi maka gargadin kula yan mata ba? Wato sai da ka kula su ko har wata tayi nasarar janye hankalinka, to bari kaji in fada maka wani abu kai da yin aure sai nan da 5 ko 6 years amma banda yanzu"
"Yaya ni wallahi bazan iya kara ko nanda shekara daya batare da nayi aure ba"
Jin abinda yace yasasu dukkaninsu kallonsa cike da mamaki,
"Kai yanzu har ka isa aure? Lallai amma wallahi kayi kankanta da yin aure yanzu.." Anty hamida ta fada tana jijjiga kai,
"Idan nayi kankanta da aure amma ai banyi kankanta da yin iskanci ba..."
Wata tsawa yaseen ya daka masa, "wallahi karka kuskura, idan har ka kuskura kayi abinda bakinka yake fada wallahi sai na raunata ka sai nayi maka illa, harmu zaka duba kace ka isa yin iskanci? To bismillah ga wurin nan kaje kayi, tunda abin naka ma hakane to wallahi kasar zaka bari karatu zaka koma.."
"Yaya ni bance zan zama dan iska ba amma maganin hakan kawai ayi min auren nan kuma ko karatun zan koma to afara yimin aure tukunna"
"Idan bakinka yasake ambaton kalmar nan sai na fasa maka baki, wai yaron nan yaushe ka zama haka ohhhh lallai kam kaje jami'a kaga yan mata dole kazo gaban idona kana fada min haka amma to kasani bamu shirya yi maka aure yanzu ba karka ji da wai" yaseen yafada cikin fad'a,
Tashi amadi yayi ya wuce dakinsa idonshi yana kokarin kawo kwalla,
Ita dai hajiya tunda aka fara maganar batace ko k'ala ba saboda yaseen shine babba kuma yanzu shine kamar uba ga amadi shiyasa bazata goyi bayan amadin ba gudun kar wata matsala kuma ta kunno kai amma ita tana jin zata goya masa baya tunda auren yake so gashi da bakinsa yana cewa idan ba ayi masa ba zai zama dan iska,
Tunda Amadi yabar wurin su anty Dija suke tattauna maganar da yayansu yaseen amma ita anty hameeda ta dan sauko tana ganin gara ayi masa auren tunda ya nuna yana so sai dai yaseen ya kafe kai da fata yace ko zai yi masa aure sai ya shekara 35.
  Tunda amadi ya shiga daki ya zauna yake kuka rabon da yayi kuka har ya manta domin tun rasuwar mahaifinsu amma yau akan nadiya ya zauna yana kuka, har hajiya ta shigo kukan yake hakan yabata mamaki,
"Autana kuka? Kuka kamar ba namiji ba, haba auta yi shiru akan auren ne? Indai aurene za ayi maka daina kuka"
"Hajiya amma kinaji ai yaya yace wai sai dai inkoma makaranta amma bazai yimin aure yanzu ba, ni babu karatun da zan koma wallahi har sai anyi min auren nan"
"To ya isa ai nace za ayi maka ba shikenan ba"
"Hajiya tunda yaya yace bazaiyi ba ai nasan bayi min zaiyi ba"
"Ai ni nace za ayi maka kama daina damuwa akan wannan kaji, share hawayenka"
Jin hajiya ta goyi da bayansa sai yaji hankalinsa ya kwanta zuciyarshi tayi sanyi nan ya saki jikinsa saboda yasan yanzu bashida matsala,nan takama hannunshi zuwa kan dining.
  Washe gari da safe bayan sun gama yin breakfast yaseen ya kalleshi,
"Na turo maka link din da zaka cike foam din makarantar da zaka koma ka duba email dinka"
"Yaya baki nayiba amma nifa bazan koma karatu ba har sai nayi aure.."
Azuciye yaseen ya tashi zaiyi kansa Anty siyama tayi gaggawar shiga gabansa,
"Yaron nan naga alamun duka kake so inyi maka wallahi, ni kake fadawa cewar bazaka koma karatu ba har sai kayi aure? Kai har wani karatun kirki kayi? Masters din da kayi shine har kake ganin karanka yakai tseko? Mata nawane masu masters yanzu, banza shashasha"
"Nidai ko secondary gareni ya isheni inyi aure,kuma indai ba lalata yaran mutane akeso infara ba to abarni inyi aure"
"Karka fasa kaje kayi duk abinda zakayi" yaseen ya fada azuciye,
"Kai yaya amadi wai bakinka bazai yi shiru ba?" Anty Dija ta fada,
"Anty ai ni ba rashin kunya nake yi masa ba, ni kawai aure nake so, wallahi idan har banyi aure ba komai yana iya faruwa..."
"Auta tashi kaje" hajiya tace da dashi saboda jin yana kokarin yimusu tabargaza,
"Matsalar yan auta kenan wallahi basu da kunya ga shegiyar shagwaba" anty hameeda ta fada,
"Ai wanda kikaji kadanne nifa daga cemasa baya yawo sai cemin yayi wai to zai fara zuwa hotel da clubs yana hutawa" anty siyama tafada tana dariya,
"Zanyi maganinsa ai, wallahi karatu zai koma nanda wani month din.."
"Yaya abinda nakeso dakai tunda yaron nan ya nuna auren yake so to muyi masa saboda mu kare masa mutunci sannan mu karewa kanmu, domin indai bamu yimasa aure ba kuma yana so to fa shaidan bazai barshi ba zai ta ingizashi daga karshe azo ashiga halin da ba aso,dan haka kayi hakuri muyi masa auren tunda yanuna yanada bukatarsa kuma karatu yace zai koma amma sai anyi masa aure" hajiya tace dasu tana rikeda kumatunta,
"To hajiya shikenan za ayi kamar yadda kikace amma kifa tuna shekarun yaron nan kwata kwata 28 ne kacal fa ko 30 baiyi ba" inji yaseen,
"Ehh babu komai mudai yimasa shikenan mun fita hakkinsa" hajiya tabashi amsa,
"To shikenan hajiya"
Akan haka suka tsaya na za ayiwa amadi aure amma har lokacin yaseen bai huceba haushin amadi yakeji saboda duk barazanar da ya dade yana yimasa akan cewar babu shi babu kula yanmata amma shine sai da ya kula su.
  Amadi kuwa duk da bai san abinda su hajiya suka tattauna ba bayan tafiyarsa hakan bai saka yaji son auren nadiya ya ragu acikin ranshi ba shi yanzu ne ma yake jin wani shaukin sonta acikin zuciyarshi,wayarshi ya dauka ya kirata, fitowarta kenan daga wanka kamar ba zata daga ba ta daure ta dauka,
"Baby nah.., ya jikin?"
"Da sauki"
Shiru yayi yana sauraren muryarta har yaji tayi shiru,
"Yanzu me kikeyi? Uhmmm?"
Sai da yafi minti miyar da tambayarta sannan tabashi amsa,
"Abu nake yi?"
"Menene shi? Fada min sai inzo in tayaki"
Shiru tayi masa har sai da yasake maimaitawa, "daga wanka na fito zan shirya, sai anjima"
"Dan Allah tsaya kiji, karki kashe dan Allah, kinga da ina kusa nine zanyi miki wankan,nine zan shiryak..."
K'ittt ta kashe wayar acikin zuciyarta tana mamakinsa dama haka yake shima, afuska kamar salihi ashe ashe, shika A ne,
Murmushi yayi saboda shi kansa bai san lokacin da ya soma sakin layiba.
  Kwana uku da tsayar da maganar yiwa amadi aure yaseen yasake tarasu yafara tambayar amadi wacece yarinyar da yake so,
"Sunanta nadiya"
"A ina gidansu yake?"
"A rano suke"
Dukkaninsu mamaki ne ya kamasu saboda sun zaci zaice a abuja sai sukaji sabanin haka,
"Good, wacece ita sannan waye mahaifinta?"
"Mahaifinta babban dan kasuwa ne sannan yana aiki a state government, ita kuma dalibata ce a KUT amma bazawara ce ta tab'a aure kuma tanada yara biyu"
Atsorace yaseen ya kalleshi yayinda yayunshi Mata suka hau salati da sallallami,
"Auta bazawara?" Hajiya tace dashi cikin mamaki,
"Anty amadi bazawara fa kace, kanada hankali kuwa?",anty Dija ta fada cikin zaro ido,
"Da hankalina anty, ai ba haramun bane, ni wallahi ita nakeso kuma ita zan aura"
"To kuwa bazaka aureta ba koda kuwa zaka mutu, kaji yaro da shashanci, sai kace marar mafadi? Karasa wacce zaka so sai bazawara?" Yaseen yafada cikeda mamaki,
"Gaskiya auta nima anan ban goyi bayanka ba, kaje ka sauya shawara saboda nima bazan goyi bayan da ka auri bazawara ba, ai sai ta rinka yi maka wayo.." Hajiya ta dora nata jawabin,
"Hajiya..."
"Kai tashi ka fita daga nan, tashi ka fice ko inzo inyi ball dakai.." Yaseen yafada azuciye, tashi amadi yayi ya fita hankalinsa yakai kololuwar tashi, ransa kuwa idan yayi dubu to ya b'aci.....

*49*
   *K*o gabansa dak'yar yake gani saboda tsananin damuwa da b'acin rai, dakinsa ya shiga ya zauna zuciyarsa tana faman yimasa zugi da zafi, gaba daya yama rasa abinda zaiyi kuka ko me? Tagumi yayi jikinsa sai tsuma yake,
Gaba daya babu wanda ya goyi bayan amadi ya auri bazawara har hajiya wannan karon taki bin bayansa, anty siyama kuwa cewa tayi ai ga kanwar mijinta nan zee dake mutuwar sonshi a aura masa ita kawai anan ne kuma hajiya bata bada goyon baya ba tace adai kyaleshi yasake nemowa da kanshi.
Tunda amadi ya shiga daki bai fitoba su hajiya sunyi tsammanin ko fushin ne har lokacin bai huce ba ashe ba haka bane zazzabi ne mai zafi ya rufeshi dan haka babu shiri ya kwanta ya lulluba da bargo, yana nan kwance har la'asar tayi ganin bai fitoba yasa hajiya lekawa dakin nasa nan ta hangoshi kwance cikin bargo,
Hankali atashe hajiya taje gaban gadon tana kiransa, "auta..!!! Auta na, meya sameka?"
Jin jikinsa tayi zafi zau lokacin data yaye bargon,
"Baka da lafiya shine baka fada min ba auta? Meyasa?"
Kamar hajiya zatayi kuka ta fita ta kira yayunsa nan ta taho masa da abinci da magani, kamar karamin yaro haka ta sakashi agaba ta bashi ya dan ci yasha magani, wani irin ciwo kansa yake yi masa kamar zai bar gangar jikinsa.
Kasancewar autane shalele kowa sai da ya nuna damuwarsa akan rashin lafiyar amadi nan aka manta da batun maganar auren da yace zaiyi amma shi abin yana nan acikin ransa, har dare yayi dukkaninsu suna dakinsa ana hira shikam yana kwance kansa akan cinyar hajiya tana shafar kansa kamar wani jariri,
Lokacin da yaga kowa yafice sai iya hajiya yasamu damar yimata magana,
"Yanzu hajiya kun k'wammace inje inyi zina akan ku aura min wacce nake so? Hajiya idan fa bakuyi min auren nan ba tunda ina son yarinyar nan kuma ace itama tana sona to fa shaidan zai iya ribatarmu mu aikata abinda bashi kenan ba,saboda zamu rinka ganin ai tunda baza abarmu mu mallaki junanmu ba gara mu aikata komai, amma idan har kuka amince na aureta hajiya kun taimakawa rayuwata sannan kun tamaka mata itama, kuma ni banga abin gudu a auren bazawara ba tunda annabinmu ma da ita yafara alhalin shima bai taba yin aure ba, dan Allah hajiya kiyi min wannan alfarmar a matsayinki na mahaifiya ta, ku barni na auri nadiya.."
Shiru hajiya tayi na wani dan lokaci sannan ta shafi sumar kansa,
"To autana kabari zan duba Nagani kasan nafi kowa sonka shiyasa bazan taba bari wani abu ya cutar dakai ba, zanyi maka istihara nagani idan har aurenka da ita alkhairi ne Allah ya tabbatar idan kuma ba alkhairi bane Allah ya sauya maka da wacce tafita alkhairi"
"Yawwa hajiyata, insha Allah ma alkhairi ne.."
"Allah yasa haka"
Sallama hajiya tayi masa ta tashi tafita ta ja masa kofar, shiru amadi yayi yana tunanin nadiya acikin ransa, shi ko zai koma karatu to yafi son sai andaura aurensa da ita saboda gani yake muddin ya tafi bai aureta ba to kafin yadawo wani ya aure masa ita.
***
   Kallon asabe kabeer yayi zuciyarsa cike da jin haushinta nan ya fincike hannunta daga jikin kwalar rigarsa amma bata hakura ba sai da ta sake cakumar wuyar rigar tasa,
"Sakeni.., sakeni nace ko jikinki ya fada miki yanzun nan.." Yafada cikin karaji, maimakon ta sakeshi sai jan rigar tasa tayi ta ketata nan ya rufeta da duka itama tana ramawa amma da yake karfinsa da nata ba d'aya bane yasa yayi mata lilisss, zaginsa ta hau yi tana cewa dole dai sai ya zauna da ita ko yana so ko baya so,
Cikeda bakin ciki yaje ya sauya kayan jikinsa yabar gidan, kusan koda yaushe hakace take faruwa, kullum acikin fada suke ta zageshi tass shikuma ya nada mata na jaki, shi kansa idan ya zauna sai ya rasa gane wacce irin musiba ce ta sauka akansa, nadiya ce ta fado masa nan kuma yaji hankalinsa ya sake karkata agareta take zuciyarsa tafara aiyana masa wani abu...
***
A b'angaren nadiya kuwa tun tana fushi akan fadan da mama tayi mata har ta hakura ta ware amma bata taba sanin cewa Abba yayi magana da amadi akanta ba,
Yau da safe misalin karfe 9 amira tazo ta kirata tace taje Abba na kiranta, fita tayi daga cikin bargonta ta dauki hijab dinta ta nufi falon Abba,
Yana zaune shida mama ya kammala karyawa,
Zama tayi ta gaidashi, cikin fara'a ya amsa sannan ya dubeta duba irin na maganar da za ayi mai muhimmanci ce,
"Nadiya wannan yaron Ahmad tun yaushe yake zuwa wurinki?"
Gabanta ne ya fadi ras rass domin jikinta yafara bata cewar Abba maganar aure zaiyi mata,
"Abba bamu dade tareda shi ba kuma ni wallahi bani nafada masa gidanmu ba haka kawai naganshi yazo.."
"To nadiya in banda abinki ai mai sonka shi yake zuwa Inda kake,sannan agaskiya ni na yaba da nutsuwar yaron wannan dalilinne ma yasa nabashi dama domin ya turo magabatansa ayi maganar aurenku tunda kedai yanzu ba karamar yarinya bace.."
Hawaye ne suka fara bin kumatun nadiya wanda takasa magana,
"Kiyi hakuri nadiya nasan ke mai biyayya ce sannan mai hakuri ce akan komai, to yanzun ma wannan biyayyar taki da nasanki da ita zaki yimin ki auri wannan yaron domin nagari ne, nasan abaya kinyi mana biyayya kin auri kabeeru wanda bakiji dadin zama dashi ba to yanzu kuma insha Allah zakiji dadi ko dan biyayyar da kike yimana.."
"To Abba" shine kawai abinda nadiya ta iya cewa sai ko hawaye dake faman bulbula daga idanuwanta,
"Allah yayi miki albarka nadiya, Allah yasa yaranki kema suyi miki irin biyayyar da kike yimana,kiyita hakuri kinji"
"To Abba"
"Allah yayi albarka,shikenan tashi kije.."
Tashi tayi tafita tana faman hawaye, tana zuwa daki ta zauna ta shiga kuka, kuka take sosai kamar wacce aka rafkawa mutuwa, ita bakin cikinta ma amadi fa ko ta bakinta baiji ba amma shine zai tafi wurin Abba kai tsaye kenan auren dole yakeso ayi mata ko me??
Ta dade tana rusar kuka kafin ta dauki wayarta ta tura masa text massage,
  _Yaushe mukayi haka dakai, yaushe nace zan aureka da har zakaje wurin Abba kace zaka turo Manyanka,ka tab'a ganin inda aka yiwa bazawara auren dole? Ni nafada maka bana sonka ka rabu dani ko dole ne auren? Nidai kasani muddin na aureka to auren dole akayi min domin ban taba jin sonka acikin raina ba..._
Ganin massage dinta yasa amadi shiga cikin mamaki domin bata taba tura masa da text massage ba, yana karantawa yaji hankalinsa yatashi nan yayita kiran wayarta amma taki dauka daga karshe ma sai ta kashe wayar gaba daya, duk da cewa bashi da lafiya yana zazzabi haka ya figi mota ya tafi rano saboda fushin nadiya agareshi babban abune ko kadan baya son fushinta,
Karfe 11 nasafe ya isa kofar gidansu sai dai yau baizo da niyyar shiga cikiba domin kananan kayane ma ajikinsa ga zazzabi dake damunsa,
Wayarta ya kira taki dauka domin ta bude wayar lokacin, text ya tura mata cewar yana kofar gida tayi hakuri ta fito, dama kamar wadda take jira nan ta dauki hijabi ta fita afusace domin sai ta tsattsageshi sannan zataji dadi, kofar motar ta bude ta shiga yana zaune ya dora kansa ajikin sitiyarin motar saboda wahalar da yakeji,kansa ya daga ya kalleta yasake dorashi akan sitiyarin yana kallonta,
"Baby meyake faruwa ne, laifin me kuma nayi?"
"Au ba kasanma abinda kayiba kenan? Yanzu kayi min adalci da har zakaje wurin Abba ka kai kanka kace zaka turo ayi maganar aurenmu bayan bani nabaka wannan damar ba? Ka taba jin nace ina sonka bare har nace zan aureka? Ni ba sonka nakeba,wancan auren ma da nayi shima ba son mijin nakeba ko ahaka zan kare a auren mazajen da bana so basa sona? Ni shikenan bazanji dadin aure ba kowanne aure da akwai matsalar da zan fuskanta?"
Kallonta kawai yake yi da jajayen idanuwansa wadanda suka yi ja saboda wahalar zazzabi  har lokacin kansa yana bisa sitayarin motar akwance, sai da yaji ta tsagaita daga masifar da take balbala masa sannan yayi magana cikin muryarsa mai masifar sanyi,
"Allah yabaki hakuri baby, wallahi bani nakai kaina wurin Abba ba, shine ya kirani yace inturo manyana amma kiyi hakuri, sannan idan kikace wai bana sonki bakiyi min adalci ba, da ace yanzu kin san halin da nake ciki saboda ke wallahi da sai kin tausaya min"
"Wanne so kake min? So ko sha'awa? Babu wani sona da kake kawai kai dai kana sone kasamu wani abu daban atare dani daga nan kuma wulakanci ya biyo baya.."
Murmushi yayi ya kalleta, "sha'awa fa kikace? Haba baby idan sha'awace ke damuna ba so ba ai da sai in nemi budurwa  in magance sha'awata shikenan.."
"To koma dai menene bari kaji koda ace zan aureka sai munyi yarjejeniya dakai sannan sai kayi min alk'awai guda daya.."
Har lokacin fuskarsa dauke take da murmushi, jijjiga mata kai yayi, "yarjejeniyar me zamuyi sannan wanne alkawari kike so inyi miki? Zanyi miki shi ko na menene mutukar atare dani abun yake".

*50*
*S*ai da ta hade rai sannan tace,
"Koda na amince munyi aure to ba zaka kusanceni ta karfi ba har sai da yardata da amincewata.."
Duk da cewar yaji maganar tata wata iri amma sai yaji tazo masa da sauki saboda bai zaci wannan maganar zata fada ba,
Shiru yayi yana nazari amma kuma zuciyarshi tana ta tausarshi ta hanyar cemishi,
"Tunda kana sonta kawai ka amince da kanta zata nemeka badai mace bace ai mata akwai rauni.."
Ganin yaki yayi mata magana yanata murmushi shi kadai yasata yin magana,
"Kai nake jira fa kayi magana"
"Ni ai na amince karki samu damuwa..."
Galala tayi tana kallonsa domin koda wasa bata dauka zai amince acikin sauki ba duba da cewar shi saurayine ba taba yin auren yayiba,
"Shikenan tunda ka amince amma kasani alkawari fa ka dauka.."
"Nasani.." Yabata amsa,
"Shikenan yayi kyau" tafada tana kokarin bude kofar motar domin fita,
"Baby zan samu maganin zazzabi agidanku? Wallahi zazzabi ke damuna yanzu ma ba kiji jikina ba"
"Za a iya samu bari naje na duba.."
Fita tayi yabita da kallo "baby riigima" yafada acikin zuciyarsa.
  Paracetamol ta dauko masa sachet daya sannan taje falon abba ta dauko bottle watar guda daya marar sanyi tafito,
Yana nan kamar yadda ta tafi tabarshi haka ta dawo ta sameshi,mika mishi tayi yatashi ya karba ya balli maganin guda biyu yasha yana yamutsa fuska,
Sake kwanciya yayi ajikin sitiyarin, dukkaninsu sunyi shiru babu wanda yake cewa komai da haka har bacci ya dan fara daukarshi sama sama,
Juyawa tayi ta kalleshi da niyyar tayi masa sallama ta koma gida amma kamar da wasa sai taga wai yayi bacci, zuba masa ido tayi tana kallonsa, hakika duk inda ake neman cikakken namiji to amadi yakai matsalar kawai ita har yanzu bata sake dashi bane gudun kar akuma sake maimaita abinda yafaru abaya.
Sai da yashaki baccinsa ya more sannan ya bude idonsa bai zaci zai ganta ba amma sai yaganta zaune,
"Baby yi hakuri wallahi ban ma san time din da baccin ya daukeni ba"
Shiru tayi bata tanka ba dama kuma yasan ba tankawar zatayi ba,
"Bari naje na tafi.."
"Allah ya kiyaye hanya" tafada tareda bude kofar motar ta fita, ko akwalar rigarsa abin da tayi, tashin motarsa yayi yakara mai ya nufi gida.
  Kwana biyu da faruwar haka hajiya tace masa ta amince ya auri bazawara mutukar hakan zai samar masa da kwanciyar hankali duk da bata so tayi nesa dashi,
Tara yayunshi hajiya tayi tace musu subar amadi ya auri nadiya kamar yadda yake so kuma itama yanzu taji auren ya kwanta mata arai, babu wanda yayi magana acikinsu saboda dama sun san hakace zata faru tunda dan gaban goshi ne.
Murnar da amadi yayi kamar zaiyi me, nan yaseen yace duk da haka dai zai koma karatu, amadi bai damuba saboda yasan idan har aka aura masa nadiya angama mai wahalar ko bata tare ba.
Lokacin da yayi mata waya yace manyanshi zasu zo bata yi wani murna ba shi kadaine kawai ke murna, nan ta kashe wayar ta ajiye gefe tana dan karamin tsaki,
"Anty nadiya nifa ina jiye miki wani abu guda daya, karfa yanzu yaya Ahmad kawai lallabaki yake sai kunyi aure yazo ya rama duk wadannan abubuwan da kike yimasa ko kuma yabari sai kin kamu da sonshi sannan ya rama koma har yayi doubling.." Amira dake gefe tana yin sak'a da kwarashi ta fada,
"Amira kenan idan har yayi min haka ko fiye da haka zan barshi ne da Allah kawai kamar yadda nabar yaya kabeer da Allah, nasan haushina kukeji kuna ganin kamar bana kyautawa Ahmad saboda abubuwan da nake yi masa, Amira shi so yanada wahalar gaske sannan duk zuciyar da ta samu kanta acikin halin da na samu kaina dole ta tsani soyayya, Amira banida wani labari mai dadi da zan bayar Wanda na tsinta acikin auren da nayi abaya, kawai dai bautar Allah nayi amma bawai samun farin cikiba.."
"To amma anty nadiya ai shi yaya Ahmad yanada banbanci da yaya kabeer, halayensu ma ba iri daya bane.."
"Amira kenan ke yarinya ce, to bari kiji su maza gaba daya halayensu iri dayane sunane kawai ya banbanta su.."
"A'a anty nadiya ni yanzu inada kwakkwaran dalilin da Zan iya fada wanda ya banbance yaya Ahmad da yaya kabeer"
"Menene shi?"
"Son yanmata, yaya Ahmad bashi da kule kulen yanmata, amma shi kuwa yaya kabeer kamar na mamajo"
"Shi Ahmad din waye yafada miki baya kula yanmata? Ai ni yanzu banida yakini akan namiji domin bashida tabbas"
"Da yana kulawa ai da zaki sani"
"Tayaya Zan sani Amira? Gidanmu daya dashi?"
Dariya Amira tayi "kai anty nadiya kina bani dariya.. Amma dai ya kamata ai ki sani"
"Hakane" nadiya tafada,acikin ranta kuma wani tunani takeyi.
  Ranar asabar da safe yayan amadi yaseen da kanin mahaifinsu da yayan hajiya sukaje gidansu nadiya domin nemawa amadi aurenta, abba baiyi doguwar magana ba yace kawai yabashi sannan iya sadaki kawai zai kawo nan da karshen wata mai Kamawa sai adaura aure duk da sunyi yarjejeniyar cewar ba yanzu zata tareba har sai yadawo daga karatunshi wanda zai tafi zuwa London,
Batare da matsalar komai ba baki sukayi sallama suka tafi, tunda su yaya yaseen sukace an bashi nadiya harma an tsayar da ranar aure ya rasa inda zai saka kanshi dan farin ciki.
Ita kuwa nadiya tana gida babu yabo babu fallasa, tana kwance a tsakar gida da yamma tana karatun littafin Hausa kissa ko magani yaro yayi sallama yace wai ana kiranta awaje, hijabinta ta dauka ta fita duk da bata san waye yazo ba,
Gabanta ne ya yanke yafadi saboda ganin yaya kabeer da tayi domin yau bata san da wacce yazo ba....


*51*
*T*unda nadiya tafito kabeer ya zuba mata ido yana jin wani irin sonta yana yawo acikin jinin jikinsa, fatan shi daya Allah dai yasa ta amincewa bukatarsa,
Yau ganinshi tayi fuska asake ba kamar wancan lokacin da yazo ba dan haka ta dan saki fuskarta babu yabo babu fallasa,
"Barka da fitowa.." Taji yace da ita wanda wannan ya haifar mata da tsananin mamaki domin bata zaci maganar kirki daga gareshi ba,
"Kina mamakine nadiya? Bai kamata kiyi mamaki ba saboda duba da irin matsayinki da muhimmancinki acikin rayuwata da kuma rayuwar 'yayanmu.."
"Hakane" tafada tana kallonsa har lokacin fuskarta tana dauke da mamaki,
"Nadiya nasake shawara, naga kamar bai daceba in rabaki da yaranki adaidai lokacin da suke bukatar kulawarki shiyasa ma nafasa karbarsu zan bar miki su amma kuma ni ina ganin yanada kyau muyiwa kanmu adalci mu koma yadda muke ada"
"Ban fahimceka ba yaya kabeer.."
"Yawwa, nadiya abinda nakeso dake shine ni ina ganin mai zai hana mu rufawa kanmu da yaranmu asiri muce saki biyu nayi miki mukoma muci gaba da rayuwarmu da bawa yaranmu kulawa"
Wani murmushin takaici nadiya tayi sannan ta kalleshi,
"Lallai yaya kabeer, wato dai so kake mu jefa kanmu acikin halaka, mukoma muci gaba da zaman zina domin ba zaman aure zamuyi ba.."
"Nadiya ba nufina kenan ba, dan Allah kiyi hakuri ki amince da wannan bukatar tawa,bafa wani abu bane sabo,da yawa daga cikin ma'aurata wadanda suka samu matsala irin tamu suna yin haka su rufawa junansu asiri su koma suci gaba da rayuwarsu..."
"Yaya kabeer dan Allah mubar wannan maganar domin ba mai yiyuwa bace saboda ni ahalin yanzu ma da ranar auren wani akaina.."
Ido kabeer ya kwalalo take fuskarshi ta sauya ya dubeta cikin tsantsar kishi,
"Yanzu nadiya kinfi son ki auri wani daban baniba, nadiya kiyi hakuri ki yarda mu maida aurenmu"
"Yaya kabeer idan mun ha'inci mutane da iyayenmu mun maida aurenmu ai bamu isa mu ha'inci Allah ba domin yasan komai, sannan kuma nifa yanzu bana yimaka tsananin son da har zan aikata babban sab'o.."
"Nadiya...." Yakira sunanta cikin danuwa,
"Sai anjima...."
Bata sake sauraronsa ba tayi tafiyarta ta shige cikin gida tana mai jin tsanar kabeer tana sake shiga cikin zuciyarta domin inbanda ma ya rainawa kansa hankali yaushe zai tunkareta da wannan maganar,babu wanda ta fadawa ko mama bata fadawa ba tabar abin aranta ita kadai.
  Cikin satittikan da basu wuce 2 zuwa 3 ba Amadi ya kammala komai nashi na tafiya karatun da zai koma lokacin saura sati 2 daurin aurensa da nadiya wacce har yanzu tana nan akan dokin rigimarta bata sauko ba,
Duk da mahaifinta yace sadaki kawai amadi zai bayar amma hakan bai hanashi niyyar yi mata lefe ba idan taje gidanshi.
Ita kuwa nadiya tana can agida tafara shirye shiryen komawa makaranta domin hutunsu yakusa yakare saura kadan,ga damun da kabeer yaketa yimata akan dole sai sun hada baki sunce saki biyu yayi mata ba ukuba takoma gidansa,
Ita sam bata shirin biki takeyi ba ta shirin komawa makarantarta take,
Ana saura kwana biyar daurin auren amadi yaje gidan da yamma, babu yabo babu fallasa ta karbeshi, kaya yakai mata masu aji da matsayi swiss lace da material wai ta dinka tasa ranar biki,
Adakile tayi godiya ta karbi kayan ta koma gida shikuma ya shiga ya debi su fadeel ya fita dasu, mama takaiwa kayan nan mama tahau cewa,
"Ohh wannan yaro ai da kokari yake duk da abba yace sadaki kawai zai kawo amma bai hakura ba har saida ya kashe kudinsa ya siyo wadannan kayan, bai san mu ba taro zamuyi ba, aure kawai za adaura babu wanda zan gayyata, nida sake yin taro kuma sai Allah yakaimu bikin Amira.."
Murmushi nadiya tayi "wallahi mama nima hakan yayi min daidai dama bana son ni aji ma zan sake auren..."
"Allah dai yasa ayi cikin nasara"
"Amin" nadiya ta amsa tareda daukar ledar kayan tashiga daki.
  Tunda kwanakin bikin suka karato nadiya take jin gabanta yana faduwa Wanda ko a lokacin aurenta nafarko bataji irin haka ba, har saida ta kasa daurewa ta fadawa mama irin faduwar gaban da take ji nan mama tace mata tayita addu'a insha Allah babu komai sai alkhairi.
  Ranar daurin auren kuwa nadiya tana kwance bata da niyyar tashi domin dama tace babu abinda zatayi ko kunshi baza tayiba bare wani kitso, dama kuma a masallacin kofar gidan abbansu kabeer za adaura auren domin shine waliyinta,amma tunda safe mamansu kabeer da kannenshi suka zo gidan sannan umman sumaila itama tazo da sauran dangi na kusa, shiyasa gidan ya danyi mutane sai shewarsu kakeji,
Duk da bata so sai da Amira tayi mata kunshi domin dama ta iya babu kalar kunshin da bata iyaba daga kan baki har zuwa ja,
Lallabata mama tayi tace ta daure tayi kitson ma tunda dai abune na lokaci guda sannan gashi gidan da mutane, haka ta zauna badan taso ba Amira tayi mata kitson, shuku biyu sannan anzubo wani tagaba wanda yabada style mai kyau,fati kanwar yaya kabeer sai tsokanarta take,
Wanka tayi ta shirya tasaka wani leshi golden tasa sarka da dan kunne, karfe 2:30 amadi ya kirata dama kuma amir yashigo yana guda yana cewa "ina Anty amarya take? Mun dawo daga daurin aure har andauro,sadakinki dubu 50.."
Gabanta ne yasake tsananta bugu nan ta tashi tayi salla raka'a biyu tazauna tana addu'a, shikuma amadi yasha kwalliya domin komai fari yasaka, farar shadda, farin takalmi, farar hula da Agogon azurfa, sai kiranta yake awaya saboda yana son yazo yaganta amma bata dauka ba gashi a can gidansu biki akeyi sosai, yayunshi sun hada mishi dinner ta musamman a ni'ima guest palace domin tayashi murna, duk danginshi na uwa da na uba sunzo dan haka gidan acike yake da baki,
Bai hakura ba yaci gaba da kiranta saboda yana son taje dinner din amma yasan dakyar idan zata amince, jin ta daga wayar yasashi maida hankali kan wayar,
"Baby ina kika shigane?"
"Meya faru?"
"Babu komai, kawai dai naga inata kiranki ne shiru bakiyi picking ba"
"Bana kusa ne"
"To shikenan, alhamdulillah yau dai gashi burina ya cika nazama mijin nadiya, yanzu alfarma daya zaki yimin ki shirya za azo adaukeki saboda da akwai dinner da..."
"Wacce irin dinner? Ni ai kasan bazanje ba, kaine saurayi dan haka zuwa kai yakama"
Murmushi yayi "yi hakuri dan Allah ki shirya.."
"Nifa babu inda zanje.."
Haka yayita rarrashinta amma taki furr tace ita bazata jeba, katse wayar yayi ya kira amir yace yaturo masa da number din mama, babu bata lokaci amir ya tura masa, kiran mama amadi yayi awaya suna gaisawa yafada mata yana son zai turo adauki nadiya saboda akwai dinner din da yan uwanashi suka shirya masa, sam bai fadawa mama cewar ya kirata taki amincewa ba,
Kiranta mama tayi tace in anjima lallai lallai tazama cikin shiri itada Amira za azo adaukesu zasuje dinner,da to ta amsa takoma daki tana cije lebe gamida yin kwafa saboda jin amadi yakai kararta wurin mama.
K'arfe 6:30 na yamma Amira tagama cancada mata kwalliya kamar a shago kasancewar duk irin kwalliye kwalliyen nan na zamani ta iya, acikin kayan da ya kawo mata tasaka wani pink din leshi ba karamin kyau tayi ba amma fuskar nan murtuk babu fara'a ko kadan....
follow me on facebook follow me on twitter follow me on instagram

Fitattun labarai

Habiba complete hausa novel

Alqawarin da ciwo

Amfanin cin qafar kaza

Budurwar Roba

Amfanin lemon tsami

Afanin Zogale

Adam A. Zango

Amfanin namijin Goro (bitter kola)

Tona asiri

Yanda zaka duba sunanka a Npower