Sakonnin soyayya
RANAKUN BIKIN SALLA.
Wannan lokaci ne na musamman, rana ce ta farin-ciki ga dukkan masoya. Ranakun bikin salla, lokuta ne da kasantuwata a tare da ke ka iya kai wa ga sanadin ‘karuwar yalwatuwar murmushin fuskata. Rashin kasancewarmu a tare a cikin wannan rana ya haifar min da damuwa a zuciyata, amma duk da haka ba zan gaza ba wajen furta miki cewa, Ina Son Ki. Barka Da Salla.

FARIN-CIKINA.
Ana gane kyawun shuka ne idan har an gama ta da taki. Tayaya za a gane sama idan har babu ‘kasa? Kamar haka ne, farin-cikina zai yi wuyar bayyanuwa matu’kar ba ma tare da juna. Na kan shiga damuwa a dukkan lokacin da na duba gefena ban gan ki ba. Yau rana ce ta farin-ciki gare ni da kuma ke da sauran danginmu, a dangane da haka ba zan yi sanya ba wajen ‘kara tinatar da ke cewa Ina Son Ki. BaRKa Da SaLLa.

BA ZAN IYA MANTAWA DA KE BA.
Kin zamo ta musamman daga cikin mutane na musamman da na ta6a had’uwa da su a rayuwata, kin shiga zuciyata kin zauna ta yadda ba zan iya mantawa da ke ba har abada. Ina fata da burin kasancewarmu tare a daula mafi tsari da kyawun burgewa wato Aljanna. Cikin nishad’i da yalwatuwar murmushin fuska nake mai furta miki cewa Barka Da Salla!

MATSAYINKI A GARE NI.
A yayin bayyana miki adadin yadda nake jin son ki a zuciyata, zan iya yin amfani da kalmomi irin su…….ko dan ina ganin cewa babu wata kalma da za ta iya wakiltar matsayinki a gare ni. Sai dai a yau a kuma yanzu ina mai ‘kara sanar da ke cewa, ina son ki. Fatan Za A Cigaba Da Gudanar Da Bukukuwan Salla Lafiya. Barka Da Salla Masoyiyata.

KO DA A CE MUN TSUFA.
Shi so na gaskiya ba ya ta6a canjawa daga yadda ya kafu a zuciya tun asali, sai dai a samu masoyan sun canja daga yadda suke tun fari. Ko da a ce mun tsufa, idaniyata ba za ta daina ganinki a matsayin wannan kyakkyawar macen ba, zinariya mai kyawun sura. Barka Da Salla.

LAMBUN FUREN SOYAYYA.
Zan kasance cikin baki furen soyayya a dukkan lokacin da muka had’u, matu’kar na samu tukuicin murmushinki a kan haka, to fa tilas na gina mana gida cikin da’irar lambu mai cike da tarin furanni masu kyawun launi da dad’in ‘kamshi. Ina Fatan Kin Yi Salla Lafiya?

FARIN-CIKI DA DAMUWA.
Anya abu ne da zai iya faruwa, bayyanar farin-ciki da kuma damuwa a cikin zuciya guda a kuma lokaci d’aya? To ni dai a halin yanzu na kasance cikin irin wannan yanayi. Ina farin-ciki domin kasantuwar wannan lokaci na bikin salla ‘karama, ina kuma cikin damuwa ta dalilin rashin kasantuwar mu tare a daidai wannan lokaci na farin-ciki. Ina Son Ki ina kuma Fatan Kun Yi Salla Lafiya?

ARZIKINA NAKI NE.
Ina da burin mallakar tarin dukiya duk domin na yi amfani da ita wajen hidimta miki, da ganin na inganta rayuwarki, ya kasance mun rayu tare cikin jin-dad’i da walwalar rayuwa. Barka Da Salla.

TAURARUWA.
Na kan ga wani haske ya gifta a dukkan lokacin da na rintse idanuna. Haske ne irin na tauraruwar da haskenta ke haske maraya da karkara. Wannan tauraruwa ba kowa bace face KE! Ina son ki, ina kuma cike da burin son kasancewa a raye, a tare da ke har abada. Barka Da Salla.

RANAR GAMO.
So wani abu ne da……..ko don ba sai na bayyana miki hakan ta hanyar amfani da harufan rubutu ba, da sannu za ki fahimci hakan a dukkan lokacin da idanuwanmu suka yi gamo da juna. Ina Son Ki kuma Ina K’aunar ki. Ki sha shagulgulan salla lafiya. Barka Da Salla.

NA MATA:
INA SON KA!
Sonka na haskawa a cikin zuciyata tamkar yadda tauraro ke haske a bisan sama. Ina sonka fiye da yadda kalmomi za su kwatanta hakan a rubuce. Fatan ka yi salla lafiya?

KAI NE A CIKIN BACCINA.
Tun bayan had’uwata da kai na manta da wani abu mai suna damuwa. Shin wai tayaya ma zan kasance cikin damuwa bayan kai ne a cikin furucina, kai nake gani a cikin baccina, da kai nake kwana a cikin zuciyata da kai nake tashi. Ina son ka masoyina. Barka Da Salla.

ZAN WADATA KA DA JIN DA’DI.
Ka kusanta da ni, zan wadatar da murmushi a saman fuskarka, zan yi ‘ko’karin wadata ka da jin dad’i daga cikin nau’ikan ababen jin dad’in rayuwar duniya. Ina sonka. Barka Da Salla.

TSANTSAR SOYAYYA.
A halin yanzu kawai kana ganin kaso ne mafi ‘kan’kanta daga cikin irin son da nake yi maka, amma lokaci na nan zuwa da zan nuna maka tsantsar soyayya mara misaltuwa, bayan mun yi aure. Ba zan ta6a mantawa da kai ba daidai da ‘kiftawar ido, saboda INA SON KA! Barka Da Salla.

KAI NE MURADINA.
Kamar yadda furanni ke bu’katar ruwa domin su tsira, mutum ke bu’katar abinci domin ya rayu, dare ke bu’katar duhu domin bayyanar da kansa, kamar haka ne nake son kasancewa tare da kai domin na yi rayuwar farin-ciki. Kai Ne Muradina. Ina Fatan ka yi Salla Lafiya? Barka Da Salla.

NA MAGIDANTA:
FARKON GANINKI.
A farkon fara ganinki kin d’auki hankalina ta yadda na kwana ina tinani da mafarke-mafarke a kanki. Bayan na isa gare ki, sai rayuwata ta canja izuwa ta musamman mai cike da farin-ciki. Bayan na mallake ki, kin zama matata na zamo miji a gare ki, sai ya kasance bana son nesanta da ke daidai da kowace motsawa ta agogo. Ina son ki matata, burina mu mutu tare, mu tashi mu rayu tare a Aljanna. Barka Da Salla.

NA YI BACCI A GEFENKI.
Ni abun da na d’auka so shi ne, yadda nake kwana shimfid’e a bisa kafad’unki na yi bacci kwance a gefenki, na rintse idanuwana na kuma ganki cikin baccina. Hmm! Kar da ki damu da wannan azancin nawa matata. Yau rana ce ta farin-ciki da nake ‘ko’karin ‘kara bayyana miki adadin yadda nake son ki. Barka Da Salla.

NUTSUWATA.
A dukkan lokacin da duhu ya mamaye idanuwana, ya kore ganina, kallonki a kusa da ni, ko jin sautin muryarki, shi ne abun da ke dawo min da dukkan abun da na rasa na daga nutsuwata. Ina son ki matata fiye da yadda baki ko wani sashe na jiki zai iya bayyana hakan. Ina Mai Yi Miki Barka Da Salla.

NA IYAYEN-GIJI:
IDAN KA NESANTA DA NI.
Mijina uban ‘ya’yana. Da yawan mutane na sanar da ni cewa na bika sau da ‘kafa, suna furta min na yi maka biyayya domin na samu Aljannata, amma me ya sanya ba sa tinatar da ni kan cewa rayuwar farin-ciki da walwala zata yi min wuyar samu matu’kar na rasa ka a rayuwata? Na gane hakan ne ta yadda idan ka nesanta da ni nake shiga cikin damuwa har sai zuwa lokacin da ka dawo gare ni na gan ka, sai na samu farin-ciki. A yau cikin wannan lokaci na bikin salla nake ‘kara sanar da kai cewa, Ina Son Ka! Ina Son Ka!! Maigidana. Barka Da Salla.

MATSAYINKA A WAJENA.
A yau a cikin wannan lokaci na farin-ciki da walwala ga Musulman duniya, nake son bayyana maka adadin yadda nake son ka ta hanyar yin amfani da kalmomi na musamman kamar……ko don dukkan abun da zan furta maka na san ka riga ka sani. Kalma ta yi kad’an ta bayyana cikakken matsayinka a wajena. Ina son ka mijina tamkar yadda kake so na. Ina kuma yi maka, Barka Da Salla.
ZUWA GA MASOYIYA TA.
AMINCE MU RAYU TARE.
Ke tauraruwa ce a cikin duniya, haka kuma ke duniya ce ga wani tauraro, zan so ki amince mu rayu a tare cikin shau’ki da ‘kaunar juna. Hmm! Zan kuma zo na kar6i nawa naman sallar. Barka Da Babbar Salla.

ABUBUWA UKU.
Ina son wasu abubuwa guda uku: Rana da wata sai kuma mafi soyuwa daga cikinsu a gare ni shi ne KE. Ina son rana ne domin ta haskaka mini safiya, ina son wata domin ya haskaka min dare, ina son ki ne domin mu rayu tare har abada. Barka Da Babbar Salla Masoyiya ta.

KE TA DABAN CE.
A lokacin da na fara ganinki, sai da na rintse idanuwa na domin fahimtar cewa, shin a zahiri na ke ganin ki, ko kuma kawai kin gifta ne ta cikin tinani na. Lallai ke d’in ta daban ce, kina da wata baiwa wadda ba kowa ne zai gane hakan ba, daga ciki akwai ta zazza’kar murya da tattausan murmushi. Barka Da Babbar Salla.

KO KIN SAN DA CEWA
A lokuta da yawa, kalmomi sukan gagari furtawa, domin bayyanar miki da adadin yadda sonki yake ‘kara mamaye zuciya ta a kullum. Bana fatan zuwan ranar da zan gaza wajen nemo kalmomin da zan furta miki cewa INA SON KI. Hmm! Karda Ki Manta Da Ni a Rabon Naman Salla. Barka Da Babbar Salla Masoyiya ta.

MU KASANCE A TARE DA JUNA.
A duk inda kika je ki tabbatar da cewa ina biye da ke, ko da ban zo a zahiri ba to kuwa zan zo miki a cikin bacci, ke ma za ki bayyana a cikin mafarki na, mu kasance a tare da juna, cikin wani lambu mai cike da furanni mabambanta launi. Begenki shi ne abun yi na a kullum. Barka Da Babbar Salla.

NA SHAK’U DA SONKI.
A lokacin da gari ya yi duhu, iska mai dad’i ta fara kad’awa, rassan bishiyu suka fara rangaji, a lokacin da mutane suka kwanta bacci, a dai-dai lokacin da dare ya tsala a wannan lokacin nake fara aikin begenki, na zauna ina tinaninki, na yi ta rera baitukan ‘kaunarki. Tabbas na sha’ku da sonki, idan na rasa ki ban san yanayin da zan shiga ba. Barka Da Babbar Salla.

KE CE MAGANIN DAMUWA TA.
Da akwai wata da ganinta ko jin muryarta ke zamowa maganin da ke warkar da dukkan damuwa ta. Ba kowa bace ba face KE, hasken idaniya ta. Ina Yi Miki Barka Da Babbar Salla.

BURI NA, MU RAYU TARE HAR ABADA.
Bana fatan ci-gaba da kasancewa cikin irin yanayin da nake ciki na kad’aita ba tare da ke ba. Ni dai buri na a kullum mu rayu tare har abada. Tini na yi wa sonki d’aki da shimfid’a mai kyau a cikin zuciya ta, kodan na san kin riga kin san da hakan. Barka Da Babbar Salla.

ZAN ZAMO MIKI FARIN-CIKI.
Idan har ya kasance kin zamo hamada, to ni zan zamo teku domin na kwaranya a bisanki na samar miki da sanyin da zai sanyaya ki domin raba ki da zafi. A lokacin da kika kasance cikin jin yunwa, ni ne zan zamo miki ‘koshi. Zan zamo miki farin-ciki a lokacin da kike cikin damuwa. Ki huta lafiya masoyiya ta. Barka Da Babbar Salla.

…..ZAN SO…..
A wani lokaci, tsautsayi ka iya sanyawa ki fad’a cikin wani waje da ka iya sanya ki a cikin damuwa, tabbas ni ma ba zan so hakan ba, amma fad’awa mafi soyuwar son ganin kin yi, a gare ni ita ce, ki fad’a cikin tarkon SO na, ya ri’ke miki ‘kafafuwa ta yadda ba za ki iya ko da motsi ba. Hmm! Ina Son Ki. Barka Da Babbar Salla.

ZUWA GA MASOYI NA.
KAI NE ABUN ALFAHARI NA.
Karda ka d’auki batun son da na ce ina yi maka a matsayin wasa. Akwai bu’katar ka raba zuciyarka da kokwanto ko shakku a kan hakan. Kai ne abun so na abun alfahari na a dare ko rana. Ina Son Ka. Barka Da Babbar Salla.

INA JIN FARIN-CIKI IDAN MUNA TARE.
A kullum buri na a ce gani ga ka. Ina jin farin-ciki mara misaltuwa a dukkan lokacin da na gan mu a tare ko na ji muryarka. Ina son ka masoyi na. Barka Da Babbar Salla.

BURI NA.
Da ma a ce mafarki na zai zama gaskiya. Da ma a ce zan bud’e idanuwa na, na ganni zau ne a kusa da kai cikin d’akinka a matsayin matarka, uwar ‘ya’yanka mai lura da dikan walwalarka, tabbas da a wannan rana farin-ciki mara misaltuwa ya cika zuciya ta. Barka Da Babbar Salla.

INA CIKIN BEGENKA.
So abu ne da yake jigatar da zuciya, ya cika ta da damuwa a wasu lokuta, amma tunda na same ka, ka zamo mini maganin warakar dukkan wata damuwa ta a so. Ina cikin begenka a kullum. Ka huta lafiya. Barka Da Babbar Salla.

INA CIKIN KEWAR RASHIN GANIN KA.
Duk inda na shiga a duk yanayin da nake ciki ina tare da tinaninka, na kan yi kewar rashin ganinka a kusa da ni. Amma dai a kullum fatana bai wuce na zuwan ranar da ni ce zan kasance cikin shirya maka abincin da za ka ci da kuma yi maka shimfid’a wajen kwana. Ina cikin kewar rashin ganin ka masoyi na. Barka Da Babbar Salla.

KIN YI WA SAURA NISA.
Son ki ya mamaye dikan zuciyata. Ina kallon ki ne tamkar tauraruwar nan da ta yi wa saura nisa. Ki huta lafiya.
BANI DA KAMAR KI.
Kalmomin da a kowane lokaci nake farin-cikin furta su gare ki su ne….. Kodan na san tini kin dad’e da sanin adadin yadda nake son ki, nake kuma ‘kaunar ki sai dai kawai na ce bani da kamar ki. Burina a kullum bai wuce na ganin na mallake ki ba har abada.
KIN ZAMO FITILAR….
Na kan ji wani abu a cikin zuciyata, ba komai bane face fitila wadda ke kunnuwa a dukkan lokacin da na sanya idanuwana a cikin naki. Ina son ki fiye da yadda alamun hakan ke bayyana a saman fuskata. Ki huta lafiya.
KIN ZAMO CIKIN TINANINA.
Kina daga cikin mutanen da ba zan ta6a mantawa da su ba a rayuwata. Kin zamo cikin tinanina. Bana fatan zuwan wani abu da zai zamo silar rabuwarmu, ko da a ce mutuwa ce. Ina Son Ki.
KI KALLI SAMANIYA.
Ki kasance mai d’aga kanki ki kalli sararin samaniya a cikin kowane dare, karda ki furgita a lokacin da kika hango wata mai tsananin haske, ni ma na yi hakan kuma na samu ganin wata tauraruwa mai haske idaniya da kore damuwar zuciya wato ke. Ina Son Ki.
KE CE A ZAHIRI KUMA KE CE CIKIN BACCINA.
A kullum na kan kwanta da tinaninki, na kuma farka a cikin mafarkina, na gan ki zaune kusa da ni, a cikin wani lambu ma’abocin tsintsaye da furanni. Tabbas a lokacin murmushinki ya fi komai jan hankalina, muryarki kuma ke samar da nutsuwata. Ki Huta Lafiya.
KO KIN SAN HAKAN NA FARUWA A KANSA SABODA KE?
Duk inda ya tafi, ko me yake yi yana tinaninki. Ko bacci yake yi ko a farke yake, yana hasaso murmushinki. A dukkan lokacin da kika yi nesa da shi, wajen ganin fuskarki ba ya bukatar hotonki. Karda ki yi tinanin wani ne na daban face ni. Ina Matu’kar son ki kamar yadda kika dad’e da sanin hakan.
BURINA, KI KUSANTA DA NI.
Da akwai wata ‘kaya a cikin zuciyata, wadda ta kasance cikin sukana a dukkan lokacin da na tina tazarar da ke tsakaninmu. Da ma a ce zaki mayar da ni wani sashe na zuciyarki na tabbata da na samu sassauci. Abu mafi soyuwar furtawa a gare ni zuwa gare ki shi ne, Ina Son Ki.
KALMOMI SUN YI KA’DAN WAJEN BAYYANA YADDA NAKE SON KI.
Masoyiyata, ina son na sanar da ke adadin yadda nake son ki a cikin zuciyata, sai dai kuma, na rasa samun kalaman da zan yi amfani da su wajen bayyana hakan a gare ki. Ina son ki. Ki kula min da kanki.
KARDA KI ‘DAUKI HAKAN A MATSAYIN ALMARA.
Da a ce a yau zan samu fukafukan tashi, na tashi izuwa sararin samaniya, na je na gano taurari, na sauko izuwa doron duniya, bana fatan ki tsunduma cikin matsanancin mamaki a lokacin da na bayyana miki cewa kin yi kama da d’ayarsu wato Zara.
Zuwa Ga Masoyina:
ZAN YI RAYUWAR K’UNCI IDAN BABU KAI.
A dukkan lokacin da ka furta baka so na, babu inda ya fi dacewa da na ci gaba da rayuwa a cikinsa face kabari, domin kuwa na san daga ranar duniya za ta zamo wajen zubar hawayena. Ina Son Ka.
AKWAI WANI SIRRI CIKIN IDANUWANKA.
Rayuwata ta kasance rataye cikin tarkon soyayyarka, ka d’ana kuma ya kama ni. A dukkan lokacin da na kalli ‘kwayar idanuwanka, na kan ji wani shau’ki mara misaltuwa. Ina Son Ka.
KAI NE ABUN SON KALLON IDANIYATA.
Ina cikin kewarka…. ina cike da d’aukin son ganin ka…. a cikin kowace rana son ka na lunkuwa a cikin zuciyata, fiye da yadda fatar bakina za ta iya furta hakan. Ka huta lafiya.
BANA FATAN CANJUWAR RA’AYINKA A KAINA.
Abu mafi tsanani wajen sanya zuciya a damuwa shi ne, ka samu wanda kake so shi kuma a lokacin ya fad’a a son wata. Bana fatan hakan ya kasance a tsakanina da kai. Ina Son Ka! Ina Son Ka!! Ina Son Ka!!! Masoyina.
FATANA MU KASANCE TARE HAR ABADA.
So abu ne mai wahalar da zuciya da kuma sanya ta nishad’i. Zan so ka kasance cikin bani kulawa domin gujewa fad’awa wahalar ta so. Ba zan ta6a canja ra’ayina a kan ka ba har abada. Ina Son Ka.
Zuwa Ga Mijina:
SHIN KO KA LURA DA HAKAN?
Zuciyata ta riga ta saba da kai, ta yadda nake iya jin tamkar na zamo cikin jakarka a dukkan lokacin da ka tashi fita. Da tinaninka nake wuni idan ka fita, sai kuma ka dawo nake samun sukunin yin murmushi. Ina Son Ka Mijina.
HM! HMM!! HMMM!!!
Karda ka so 1, kuma karda ka so 2, amma dai ka ci-gaba da son 1 wadda ta mace a kan son ka. Mijina kai ne abun alfaharina da kuma ‘ya’yana. Ina Fatan Dawowarka Gida lafiya.
WANNAN SAK’ON ZUCIYATA NE ZUWA GA MALLAKINTA.
Kalmomi na kasancewa ma’abota sau’ki wajen furtawa a dukkan lokacin da SO ya kasance shi ne harshen furtawar. Zuciyata na yin haske a dukkan lokacin da muke tare, na kan shiga damuwa idan ka nesanta da ni. Duk da ka zamo mallakina amma zan so ka kasance mai kare min kanka daga harin da sauran mata zasu ke kawo maka a duk inda kake. A dawo lafiya.
Zuwa Ga Matata:
KIN HASKA DUNIYATA.
Samuwarki a rayuwata ne ya koyar da ni har na san zahirin siffa ta SO. Sai bayan da muka yi aure na ‘kara fahimtar soyayya ta gaskiya. Ina fatan mu kasance a tare da juna na tsawan rayuwa har zuwa gidan Aljanna. Ina matu’kar son ki matata. Amma a lokacin da na dawo gida za ki ‘kara tabbatar da hakan. Hmm! Ina nan cike da zumud’in son zuwa cin girkinki mai dad’i.
‘DAYA TAMKAR DA GOMA.
Da akwai wata mace a cikin wannan duniya, wadda ta yi daban da sauran matan dake a gidajensu na aure. Ita ta kasance ta daban ce, halayanta kuma ababen so ne. Ba kowa bace face ke, a saboda haka nake ‘kara son ki a kullum. Ki kula min da kan ki, har zuwa lokacin da zan dawo gida kulawarki ta dawo hannuna. Ina Son Ki Matata.
Tarin kalaman soyayya, masu k’unshe da tulin gwala-gwalan kalmomin so da k’auna, domin samun sanyayar ruhin ma’abota tsinkar fure. Ku zaÉ“i wanda ranku yake so, ku aikawa da masoyanku domin nuna musu yadda kuke ji a kansu a cikin zuk’atanku.
NA MAZA:
MAI SA’AR RAYUWA.
Wannan rana ce ta musamman kamar yadda kike ta musamman a wurina. A saboda haka nake son bayyana miki cewa, da akwai wani sirri da yake tare da ke, wanda shi ke sa wa na manta da dukkan wata damuwa na ji ni a matsayin mai sa’ar rayuwa, a dukkan lokacin da muke tare. Tabbas kina da baiwa. Na gode Allah da samun ki a cikin rayuwata, domin kuwa kin haskaka duniyata. Barka Da Babbar Salla.
MU RAYU TARE.
Ba zan taÉ“a mantawa da sautin zazzak’ar muryarki, wadda jin ta ke sanyaya zuciyata ba. Ina muradin kasancewa cikin jin ta na tsawon rayuwata. A saboda haka, ki aminta mu rayu tare, mu kasance tare a cikin kowane irin yanayi tun daga hudowar rana har izuwa faÉ—uwarta. Ina Son Ki.
ABUN DA NAKE TINAWA.
A dukkan lokacin da na kalli sararin samaniya, na ga tarin taurari sun yi wa samaniya ado, suna ta faman haske, babu abun da nake tinawa face, tattausan murmushinki da ke haska fuskata a dukkan lokacin da muke tare. Fatan kina nan lafiya? Barka Da Babbar Salla.
SASHEN JIKINA.
Ki kasance cikin da’irar soyayyata shi ne fatana. Ki sakaya ni a cikin wani É“angare na cikin zuciyarki hakan zai haskaka rayuwata. Idan kika bar ni, zuciyata zata shiga damuwa, saboda kin zamo wani sashe na jikina. A saboda haka, kar da ki yi tinanin ficewa daga cikin rayuwata, domin kuwa duhu zai maye gurbin hasken da ke a cikinta matuk’ar bana tare da ke.
MAFARKINKI.
Babu wani dare da ya kan zo ya wuce ba tare da kin bayyana a cikin baccina ba. Ki kan yi min gizo na gan ki a lokacin da idanuwana ke rufe ko suke a buÉ—e. Na kan yi mafarkinki a cikin dare da rana, daga farkon kowane sati zuwa k’arshensa. Mafarki ne da nake fatan tabbatuwarsa a zahiri, saboda ina ganin mun zamo ma’auratan juna a cikinsa. Ina son ki.
MATUK’AR SO.
Zan kula da ke, zan share hawayenki, zan kawar da damuwar zuciyarki, zan nuna miki matuk’ar so a zamammu na tare idan kin shiga gidana. Ina son ki fiye da yadda nake furtawa a fatar bakina. Zan cigaba da son ki har abada. Barka Da Babbar Salla.
KE CE TINANINA.
Ke ce a cikin mafarkina, da nake yi a kowane dare. Ke ce a cikin tinanina, da nake fara yi a kowace safiya. Ke ce farin-cikina, da nake ji a kowane lokaci. Ke ce nutsuwata da bana fatan na rasa ta a tsawon rayuwata. Ina son ki.
KYAKKYAWAR FUSKARKI.
Babbar kyauta mafi girma da muhimmanci a gare ni ita ce, samun ganin kyakkyawar fuskarki da ke É—auke da tattausan murmushi a lokacin da zuciyata ke cike da damuwa, domin ganin hakan zai kore dikan damuwata. Saboda na san kina yin murmushi ne a lokacin da kike tsaka da tinanina. Ina Son Ki Ni Ma Kamar Yadda Kike So Na.

SO NA GASKIYA.
Abun da nake son samu a rayuwata shi ne SO, so na gaskiya. Samun so na gaskiya daga wurin kyakkyawar mace zinariya wato ke. Ina matuk’ar so da k’aunarki. Ki Huta Lafiya. Barka Da Babbar Salla.
NA MATA:
NA MATA:
BUGUN ZUCIYATA.
Kai ne sirrin rayuwata, masoyina na gaskiya, kai ne bugun zuciyata, da kai zan É“ata lokaci mafi muhimmanci a rayuwata. Ina son ka, so na gaskiya. Barka Da Babbar Salla.
INA SON KA.
INA SON KA.
Karda ka nesanta da wadda son ka ya dasu a cikin zuciyarta. Babu buk’atar ka ce komai a lokacin da na ce ina son ka, domin kuwa na san kai ma kana so na. Ka Huta Lafiya.
ABUN ALFAHARINA.
ABUN ALFAHARINA.
Da akwai wani guda wanda zuciyata ke marari, wanda ke a cikin tinanina da idanuwana, wanda nake fatan ya kasance a cikin rayuwata har abada. Kai ne abun son zuciyata, masoyina abun alfaharina. Ina Son Ka. Barka Da Babbar Salla.
KYAKKYAWAR ZUCIYA.
Ban tashi sanin mece ce rayuwa da farin-ciki ba, sai bayan da na haÉ—u da kai. Na yi sa’a da na same ka a rayuwata. Ina son ka. Ba kawai ina son ka bane saboda kyakkyawar surarka, ina son ka ne saboda kyakkyawar zuciyar da take dashe a k’irjinka, wadda take k’okarin sanya ni farin-ciki a dare ko rana. Ina Son Ka.
ZUMAR SOYAYYA.

Lallai na yi babbar sa’a da samun haÉ—aÉ—É—en saurayi, mai daÉ—aÉ—an kalamai da iya shayar da masoyiyarsa ruwan zumar soyayya. Na yi murna da samun ka a rayuwata. Ina Son Ka. Barka Da Babbar Salla.
NA MAGIDANTA:
NA GODE MATATA.
NA GODE MATATA.
Samun ki a rayuwata ya bani k’warin guiwar tunkarar matsalata da samun nasara a kan dukkan abun da na sa a gaba. Kulawarki a kaina na k’ara min jarumta, soyayyarki a gare ni na sanyawa na ji ni a matsayin cikakken mutum. Na gode matata, ina alfahari da samun ki a rayuwata. Ina nan cike da kewarki cikin zumuÉ—in son dawowa gida na sanya ki a idanuwana. Ki Huta Lafiya.
FATANA DA BURINA.
A gare ki nake samun bargo, a dukkan lokacin da sanyi ya rufe ni. Ina samun tsaro, a dukkan lokacin da hatsari ya tinkaro ni. Ina samun farin-ciki, a dukkan lokacin da damuwa ta lilliɓe ni. Fatana da burina mu mutu tare mu tashi tare mu rayu tare a gidan Aljanna. Ina Son Ki Matata Fiye Da Yadda Nake Son Kaina.
NI DA KE.
NI DA KE.
Ina son ki kuma zan cigaba da son ki na tsawon rayuwata matata. Ni da ke tamkar k’ashi ne mai k’warin da bana fatan ganin ranar da zai yi targaÉ—e balle har ya kai ga ya karye. Ina Son Ki. Ina Mai Kara Yi Miki, Barka Da Babbar Salla.
NA IYAYEN GIJI:
INA SON KA MIJINA.
Shi so na gaskiya ba ya taÉ“a duba tsawon lokacin da aka É—auka ana tare ko wani canji na rayuwa, a saboda haka sonka ke k’aruwa a cikin zuciyata a kowace rana. A kullum kana k’ara zama saurayi a idanuwana, kuma gwarzo abun alfaharin Ni da ‘Ya’yana. Ina Son Ka Mijina. A Dawo Lafiya.
NA YI NASARA.
Daga cikin biliyoyi da Miliyoyin samari na zaɓo ɗaya tamkar da dubu. Tabbas na yi nasara na samun ka a matsayin mijina abun alfaharina. A tsawon lokacin da zan rayu ina numfashi, ina son ka so mara iyaka. Allah Ya dawo min da kai gida lafiya mijina. Ina Mai Kara Yi Maka, Barka Da Babbar Salla.