Habiba complete hausa novel

HIBBAH
.
Cikin bacin rai yake magana "Habba mutum sai kace maye ance kufita kubarmun gida kunki fita saikace gidanku"    "Umma na gefe hawayene ke fita idonta, zuciyarta tamkar zai fito don bakin ciki da takaicin tijarar da ake musu   Sadeeq ya durkusa har kasa yana kuka "baffa don Allah kayi hakuri idan mukabarnan bamuda inda zamu   Kallo ya kare musu tare da takaici" nabaku nan da kwana biyu wallahi inbakubarmin gidaba watsamuku kayanku waje zanyi,   Aiba tare muka sai gdn dakuba.   Yana gama hayaniyarshi yayi waje  Matan gdn suna Kallo  Uwar gdn tace "mutum sai nacintsiya ance kufita kubamu waje kunkiya da hidimarshi zaiji koda hidimar naki yaran?   Dayar tace" gaya musudai ni na matsu subar dakin in dawo ciki dama nawa yamin kadan   Umma ta kwashi yaranta sukayi daki tace "kar ku yadda ku fita kujirani yanzu zanje indawo.
.
   _HIBBAH_" ummah don Allah karki jima idan kinje masifasu Mmn ahmad zasuta mana   Insha Allah barin jimaba zan dawo   Toh ummanah Allah tsare hanya ya dawo dake lfy      Ameen   Idan kannenku sundawo makaranta kubasu abinci suci kuyi wanka ku tafi islamiya ida bandawo da wuri ba.    Bayan fitar umma kai tsaye gidan kawunta ta wuce dake tsohuwar makabarta cikin garin bauchi.   Tsabar ko nisan wajen bata gani burinta kawai Allah ya kaita lfy,   Bayan isarta sun gaisada inna asabe matar kawu usman take" tambayarta ko yana gd?   "yana wajen aiki zuwa karfe hudu zai dawo insha Allah  Allah dawo dashi lfy   Nan sukayi ta hirarsu har lkcn sallar la'asar tayi suka bada farali  Sai wajen karfe biyar kawu usman ya dawo, saida ta bari y ci abinci ya huta sannan taje ta gaidashi  Ya tambayeta y lfyr yrn Fatan ba wani matsala "ba komai kawu dama so nake idan da hali mu dawo nan da zamakafin musami wani gdn koda haya ko na sayarwane mu saya,   Tunda gdn damuke ciki ya fita agadon yrn inaga kuma zamu karama kallah dawainiya Tunda shima yanada nashi iyalan.   Kawu usman yadai jitane amma kodaga yanayinta yasan halin kanin mijin nata kuma mijin y'arshi  Badamuwa, nanma ai gdn ki tattarosu ku dawonandin da zama  Da yaddar Allah abunda zamuci bazai gagaremuba fatanmu Allah karamana rufin asiri da wadatar zuci     Ameen    *.  Bayan umma tabar gdn kai tsaye gdn dillaliya ta wuce akan tazo ta sayi kujerunta da wasu tarkacen.   Sai wajen karfe shida ta koma gida lokacin su hibbah sun dawo daga islamiya, bayan sunyi sallar magrib da isha'i suka fara harda kayakinsu, saida suka gama hada komai cikin daren kafin suka kwanta.
.
Washe gari tun asuba suka tashi sukai sallah sukai wanka.    Kasancewar ranar asabarne ko islamiya basujeba don umma ta daura damarar barin gdn ayau basai gobe ba da yaddar Allah.    Wajen karfe tara mai sayan kujeru tazo harda carpet din dakinta ta hada ta sayar, dake kayan basu wani jima da sayansuba tayi sa'a an saya da mutunci ta cake mata kudinta cas ta bata aka kwashe kayan.   Mutan gdn sai tsegumi suke, itako ko kallo basu ishetaba.   Moto ta nemo akazo aka kwashe kayan tsab ta hada kan yrn su hudu suka fara gaba a moton kayan.    Sallama tayi k'ofar dakin mmns ahmad uwar gdn kallah, bayan sun gaisa da ita da maigidan tace"nazone inmuku sallama da neman afwanku da gdy agareku, Mungode sosai Allah yasaka muku da alkhairi Allah ya biyaku.   Tana kaiwanan ta tashi tayi gaba tana tafiya tana hawaye,   Dagaske yau zatabar gidannan?   Dagaske zamanta yazo karshe agidan?   Gidan da suka kafa rayuwarsu cikin soyayya, kaunar juna, kyakkyawar alaka da mutanen unguwar amma yau rana guda zatabarshi badon tasoba saidon anfi karfin ta.    Allah sarki mutuwa mairaba d'a da uwarshi,   Mairaba uba da d'anshi,   Mairaba mata da mijinta,   Mairaba miji da matanshi,   Mairaba mutum da kowa nashi  Mutuwa mai tonon silili.   *ALLAH KAMANA KYAKKYAWAR KARSHE*  Saida tashiga duk gdn mokotansu ta musu sallama tare da neman yafiyarsu.   Mutane da yawa sunyi kukan rabuwa da ita.   Don umma da mijinta mutunene masu son mutane akwaisu da barkwanci da wasa da dariya, shiyasa gidansu bai rabuwa da mutane babba da yara, gashi yau rana tsaka anrabu rabuwar da rai baisoba wannan shine     *RABUWACE SANADI* ( _QUEEN MIEEMI_)   Haka tabar cikin unguwar ranta kamar wuta.   Bayan isarta gdn kawu usman ta samu an share musu d'akin da zasu zauna ciki da taimakon 'yan matan gidan suka gyara d' akin tsaf, mazan zasu rinka kwana dakin y'anmazan gidan,"Habba"kuma suna tare da umma.    Haka suke rayuwarsu cikin kwanciyar hankali da jin dadi.   Duk kud'ad'en hannun umma ta hada da dan gadon yaranta da aka tsakura musu ta damka wa aminin mijinta ya sama musu dan gidan da zasu mak'ale don batason zama karkashin wani ta dauramai nauyinsu harsu biyar.    *
.
  *ASALIN LABARIN*
GARIN BAUCHI KARAMAR KARAMAR TAFAWA BALEWA  Garine mai tarin kauyuka, *Malam Adam*yana daya daga cikin mazauna wannan kauyen babba malamin addinine kuma manomine sosai.    Mafi yawan mutanen kauyen nasu basu damu da neman ilmi ba, yanada mata daya maisuna *Hauwa'u* da yara biyu dukkansu maza babban, sunanshi *Sa'ad* sai kaninshi maisuna *Musa*ana kiranshi da *Kallah*kasancewar sunan kakanshi na wajen uba yaci.   Tsakaninsu akwai tazarar shekara bakwai, *Sa'ad*yadau son duniya ya dora kan kaninshi duk abundaya samu na *Kallah*ne.    Suna zuwa makarantar boko awani kauye dake gaba dasu, *ALLAH*yabasu baiwar ilmi sosai.
.
 Haka suke rayuwarsu cikinso da kaunar juna.    Bayan *Sa'ad* yagama makarantar gaba da primary aka mishi aure da masoyirshi maisuna *khadija*makarantarsu daya tayi jarabawar aji uku  shikuma lokacin ya gama aka musu aure.    Bayan fitowar jarabawar tashi ya nemi izini gun mahaifinshi yanason shiga cikin garin *Bauchi* ko Allah zaisa yasamu aikinyi,   mahaifinshi ya amince ya mishi Fatan alkhairi da samun nasara.      Da taimakon wani d'an uwanshi ya sami koyarwa awata makarar turawa, har wajen zama suka bashi dayake lokacin ba kowa ke yadda d'anshi yayi makarantar bakoba.   Kuma zasu rinka bashi albashi mai tsoka, da gudu yaje ya dauko matanshi suka dawo.    Bayan dawowarsu da da y'an watanni *ALLAH* ya azurtasu da samun d'a na miji, mai sunan *ABUBAKAR SADEEQ* yataso cikin kulawa da soyayyar iyayen shi, shekaranshi hudu ummanshi ta sami wani cikin.   Lokacin har yafara zuwa makaranta, umma na hango tanata shirye2 tafiya bikin *Kallah*wanda za'ayi a kyauye ga tsohon ciki haihuwa yau ko gobe.   Sunje sunsha biki *Yaya Sa'ad*ya taka rawargani domin shine jigon komai na bikin, angama biki lahadi suna shirin dawowa ran alhamis haihuwa tazoma *Ummah* ta sauka lafiya tasami katuwar d'iyarta, dole aka daga tafiyar sai bayan suna zasu koma.    Ranar suna ansha shagali yarinya taci sunan *HIBBATULLAH*  *Abbah yace su zauna sai bayan wata  daya zasu koma yanaso yamusu y'an gyare2 agidansu.   *Bayan wata daya*  *Abban Hibbah*yazo daukarsu asabuwar motar daya saya don yanzun Allah ya buda mishi sosai har cigaba da karatunshi, antayashi murna sosai tare da addu'a.
.
Nan yake shaidamusu yagama ganin sabon gidanshi anzuba komai yanzu ma insha Allah can zasu wuce, idan an kwana biyu kaninshi da matarshi suma zasu dawo gidan da zama, *Umma*aranta "tace gida!" Dama yana ginine?  Tayi mamaki Amma kuma saita share, iyayensu har kukan murna saida sukayi na yadda yake dawainiya dasu da yadda yakeson kaninshi hatta y'an garinsu suna yabonshi dayi mishi Fatan alkhairi.    Bayan tahowarsu *Abban*kebata hakurin rashin sanarda ita ganin da yakeyi dama so yake yamata *Bazata*_Rash kardam_ Tace "lahhhh! Bakomai ai Allah yasanya alkhairi ya kara budi.    Bayan dawowarsu sabon gidan suka nufa, balaifi gidan yayi daidai na mai karamin karfi.  Ciki da falone guda uku sai kitchen da bayan gida guda biyu, sai wani daki ciki daya sai wadataccen filin tsakar gd.   Takardun gida dana motor da duk wani kaddarar da Abban yasaya duk sunan kaninshine ajiki Tab! Wannan shine babban kuskuren daya tafka.          Da isarsu basu z'ame ko ina ba sai sabon gidansu" gidane d'an madaidaici, w'anda ya kunsha d'akuna ciki da falo guda uku, ciki d'ayan guda biyu ne, sai kitchen d'aya, bayan gida g'uda biyu, sai filin t'sakar gida.       K'afin su shiga s'aida su kayi addu'an shiga gida.   D'akin *Umma* kuwa k'omai sabo aka samata, ta zama tamkar wata amarya.
.
  Rayuwar su suke cikin jin dadi da mutunta juna girmama juna, zaman lfy da k'wanci yar hankali, zamansu g'wanin ban sha'awa.  *Abbah* yayi nacin duniya akan *Ummah* takoma makaranta, Amma sam t'aki tace gara ta z'auna tayi bautar aurenta, da kula da yaranta, da yaga taki yasata makarantar Islamiyar cikin unguwarsu.   "Haka rayuwarsu t'aci gaba da tafiya, k'ullum gidansu bai rabuwa da mutane sabida akwai suda son mutane" g'ashi sun iya zama da mutane cikin aminci, daga y'an uwansu har mutanen unguwa k'owa rubibin z'uwa yake.  *Umma* dama gwanace w'ajen ihsani shiyasa mutane keson ta.  (hummmm!  d'an adam kenan idan kanada abu kaine nasu inko bakada komai babu mai kusantarku)   *HIBBAH*  k'uwa har ribibin daukarta ake sabida k'ullum cikin gayu da kamshi t'ake, balle y'anzun data fara tafiya gata y'ar duma_ duma.  Yau *Ummah* sai gyaran gida t'ake ga bakinnan yaki rufuwa ga girke2 da akayi duk na tarbar baki ko ince masu gida *Musa Kallamu* *da matarsa *Saude*  da d'ansu *Ahmad*  Tun s'afe *Umma* aikatuwa sai wajen k'arfe 2:00MP tagama k:omai taje tai w'anka ta gyara jikinta sai d"aukar kamshi take.  *Abbah* ankasa samun nutsuwa sai shiga da fita ake yau sahibinshi zaizo" sai w'ajen k'arfe hudu suka iso tare da sauran kayansu.
.
 Bayan sun huta sunci abinci sunyi w'anka suka hau gyaran d'akin da zasu z'auna da taimakon *Umman* k'omai yayi dai-dai.  Yau tsawon wata biyu kenan da dawowarsu *Saude* ko tsintsiya bata t'aba d'auka da sunan sharan gidan ba b'alle girki da wanke wanke bata komai *Umma* ita keyi hatta wankab *Ahmad* itakeyi, *Saude* Saidai t'aci ta k'wanta kwanon dataci abincima sai anzo an d'auka, *Ummah* ko ajikinta. Gata da d'an k'aran kishi, sa ido, son kai, ko silifas *Umma* ta chanza hankalinta atashi y'ake saita saya itama hankalinta yake kwanciya.  Komai na gidan y'anzun ya dawo hannun *Kallah* don yanzu *Abban* ya koma makaranta.   *BAYAN WASU SHEKARU*   Abubuwa da dama sun faru ciki harda rasuwar *Malam Adam* da haihuwar  *Ummah* yara biyu d'uka maza, *Salman* da *Adam* anacemai *Abbah* *saude* tasake haihuwar d'a namiji  *Aliyu*  *Kallah* ya kara aure sunan matar tashi  *fauziyyah* diyar kawun *Umman su Hibbah* kayu *Usman*  gida ya cika da yara harda yaran rik'o, duk *Abban* ke daukar d'awainiya dasu makaranta su, su turarsu, komai na rayuwa shike musu don  yanzu kam  _Alhamdulillah_  akwai rufin asiri sosai *Kallah* shima yajima da samun koyarwa Saidai baya tabuka komai cikin gidan" ga matanshi kullum cikin fada ga kishin dasuke da *Ummah*  ko suda suke kishiyoyi basama junansu hakan, duk jumma'a ko ranar *Abbah* yakan debi duka yaran suje masallaci bayan sallah anyi duk gidajen y'an uwansu saisunkai ziyara,   Haka rayuwa taci gaba da tafiya da dadi ba dadi *Abbah* har mukamin kwamishina yasamu, tundaga wannan lokacin k'uma ya kamu da rashin lafiyar da aka kasa gane kanshi" har ya k'wanta asibiti, kullum asibitin baya rabuwa da mutane, kullum shalelen  *Abbah* tana makale dashi idan sundawo d'aga makaranta, bacci k'awai ke rabashi da *HIBBAH*  Satinshi uku a asibiti k'ullum *Ummah* tana wajen tareda d'an data kuma haifa maisuna *Muhammad*  Cikin wannan satin jikin yayi nauyi sosai t'sabar azabar ciwo da kyar yake iya bud'e ido, maganama saika matso k'usa da bakinshi k'afin kaji me yake cewa. k'owa yafara karaya da wannan ciwon nashi, har k'auye akaje aka d'auko mahaifiyarshi, randa tagan shi tayi kuka sosai tare da addu'ar Allah tashi kafa dunshi indan da sauran rayuwa a nan gaba.....

HIBBAH Part 6-10
.
Tunda Karsu *HIBBAH*  tazo taga *KALLAH* kozaman asibitin baiyi wataran saiya kwana biyu baizoba, idan anyi maganar magungunar da za'a saya saiyace baida kudi, karshe saida akasaida moton *Abban* ba'aje ko inaba kudi sun kare, ga gidansu cike da mutane Wai sunzo dubiya Amma sun kasa tafiya Saidai suci su kwanta, da mahaifiyar *Kallah*  taga bai zama gun yayannashi tamai magana cemata yayi "ai yaga kodayaushe abokanshin suna zuwane" tace "ina ruwanshi da zuwansu shiyafi kusanci dashi, shiya kamata kodayaushe yana kusa  dashi musamman yadda yanzun jikinshi yayi nauyin nan, bai kamata yana nisaba"    Bayan kwana biyu da zance, ranar laraba Tunda ya tashi jikin da sauki sosai kowa ka gashi murna yake, dama gashi sarkin zolaya, wasa, da dariya kowa ya dubashi saiya tsikaneshi Ahaka kowa zaifita cikin farincikin da walwala, duk abunda ake *Umma* ko kadan jikinta ba kwari ko kad'an idan ta matso kusadashi idan yayi magana wani irin wari takeji kamar na gawa, karshe barin d'akin tayi tafito waje gurin mutane ta zauna, hirarsu suketayi Amma sam hankalinta baya wajen.   Juyawar da zatayi taga k'ofar gate taga wata mata rik'e da hannun *HIBBAH* idonta ya kada yayija abunka da farin mutum fuskar ma tayi ja alamar tasha kuka.  Ashe Auntynsune "yau tunda taje makaranta take kuka akawota gurin *Abbanta* wasu mutane zasu tafi mata dashi".   Tunda *Ummah* taji "haka jikinta ya k'ara sanyi".   Kamata tayi sukayi d'akinda yake, suna shiga da gudu ta d'ane gadon tana murnar ganin mahaifinta.   Haka suka yini yau jikin da sauki sosai, mutane kuwa yau kamar ana turosu.
.
Yau har wajen 11:00pm *Umma* bata tafi gidaba saida  *Kakarsu HIBBAH* tayi da gaske kafin ta tafi badon ranta yasoba, tana tafiya tana tuna wasu maganganun mijinta na yau wasu tamkar wasiyace agareta,   _"ina rokonki daki bama y'arana tarbiya ta gari"_   _"kobayan raina ki gwadamusu basuda wani uba face kanina"_  _"ban yarda arabamun kan y'a y'anaba"_  _"Kibasu ingattaciyar ilmi"_   _"ki gwada musu zumunci"_  Maganganu dai da dama, magana d'ayace ta tsaya mata arai ta wata y'ar uwansu, lokacin bakowa d'akin duk sun fita sallah *Umma* ta kama hannun k'ofar d'akin zata shiga ta d'auko hijabinta ta cire na jikinta taji matar tana cewa _"Malam sa'adu na bika ta laluma da rarrashi akan ka auri d'iyata_ *Kande* _Amma kakiya shiyasa nasa ahad'aka da ciwon da zaisa ka gangara garin da ba'a dawowa, tunda kamana kyashin cin arziki don haka dole yau kabar duniya, iyalanka kuma sunyi hannun riga dajin dadin rayuwa"_  Murmushi yayi wanda yafi kuka ciwo, yace  _"goggo Indo kenan"_ _"batun yauba nasha gaya miki banda ra'ayin mata biyu, matata ta isheni rayuwa tanamin komai, ciwo kuma dakike ikirarin kece sila wannan keda ubangijiki sannan duk abunda ya sami bawa mukaddarine daga Ubangijishi, Rayuwa da mutuwa duk tana hannunshi"._ _"bakida ikon yimin komai nida iyalaina face abunda ALLAH ya tsara mana"._  _"mikewa tayi tace nizan wuce saimunzo zaman makoki"_  Dasauri *Ummah* tabar wajen ta shige bayan gida taci kukanta tasake alola ta fito, tana fitowa taga matarnan cikin jama'a sai rafsa kuka take kamar ba'ita ta gama Maganganunnanba.   Haka ta isa gida tanata tunani iri_iri Tana shiga ta sake *Muhammad* d'an wata uku aduniya taje ta dauro alwala sallah ta kwanayi ko gajiya bataji har asuba tayi tagabatar da sallar asuba bata tsaya komaiba ta chanzama *Muhammad* kayan jikanshi ta tashi yaran suyi sallah sannan ta fice sai asibiti kasan cewar ba wani nisa sosai dasu da kafa suke zuwa, tun kafin ta isa taki kirjita sai bugawa yake, gashiyau asibitin yamata nisa.   Lokacin data iso taji kirjita ya tsananta bugewa, sai _Innalillahiwa'inna'ilaihirraju'un_ taketa fadi a zuciyarta, tana isa kofar d'akin taji sautin kukan Surukar ta, da sauri ta murd'a k'ofar tashiga abunda tayani yasata daskarewa a wajen, hawayene ya ziraro daga idonta.   _Waime *Umman Hibbah* taganine yasata hawaye haka?_ _nayi kokarin lekawa Amma ta tare kofar_
.
 Dak'ar na samu na shige ta gefen *Umma* na wuce, abunda nagani yasa na juyo nima ba ashiri,  *Ummah* kam tagama mutuwar tsaye.   *Abban Hibbah* nagani kwance anrufe jikanshi tundaga k'afarshi har kanshi, ashe tun cikin dare wajen k'arfe uku *ALLAH* ya amshi abunshi.  Saida surukarta ta tab'ata ta dawo daidai  *KALLAH* ne yata basu hakuri kafin suka samu nutsuwa, angama komai asibiti tabasu gawar, suntattara  kayan da sukazodashi Saidai *Ummah* tayi mamakin rashin ganin wasu kayan mijin nata, batadai yi maganaba kuma bata zargi kowama.  Lokacin da ta d'aga pillown da yake kwance taji nauyi ta bud'e zip d'in rigar pillown kudi tagani ciki da wani guntun takarda da sauri ta maida ta rufe kasancewar ba kowa a d'akin, sun koma gida ankai *Abbah* makwancinsa na gaskiya _saimuce Allah jikanshi da rahma ya gafarta mishi yasa Aljannah makimarshi_           *HIBBAH* kam lokacin zazzabi ya rufeta dukda tana da k'arancin shekaru, tanada shekara 8 a duniya,  *Umma* tashiga takaba saimuce Allah fiddata lafiya yabada ladan ibada.   _Bayan kwana biyu_ da rasuwar  *Abban*  da dare *Umma* ta d'auko wannan pillown ta bud'e ta d'auko ta kardan rubutu tagani kamar haka:  
.
 _ki hakuri khadija, nasan kinji maganar goggo inda ta fad'a, inarokonki da karkisa abun aranki, ciwona kuma ku dauka *ubangijina* ya saukarminda bawa bazaitaba yin abunda Allah bai kaddaroshiba Saidai yazama shine silar abun, kizama mai yarda da k'addara maikyau ko marakyau don hakan yana d'aya daga cikin halayen musulmai na kwarai yadda da k'addara._  _Sannan bazan gaji da rokonki daki kulamin da yaranaba kibasu tarbiya da ilmi domin shine kawai gatan dazaki musu, iya tsawon zamanmu dake baki ta'ba sabaminba Allah ya miki albarka idan na miki ba daidai ba ina rok'inki daki yafemin, ga kudinan 20k nabakishi halak malak_  _Bana tunanin wannin ciwon zan tashi duk sanda mutuwata ta riskeku ina rok'onku daku zama masu addu'a domin addu'arku nafi bukata ba kukaba_        *Wassalam*  *ALLAH HADA FUSKOKINMU GIDAN ALJANNAH*  Tana kaiwanan taji wani sabon ciwo akirjinta kayi hakuri fitar hawayena shine samun saukin zuciyarta, nayafeka bakamin komaiba Allah ya gafartamaka ya had'a fuskokinmu gidan Aljannah, insha Allah zan zama mai cikama burinka a rayuwa,  haka tayita sambatu batasan iya tsawon lokacin data d'auka awajenba daga karshe ta tashi ta d'auro alwala tayita jera sallolindaba iyaka, washegari akayi addu'ar uku kowa ya watse harda y'an garinsu don bazasu iya zama da  *KALLAH*  bah sam baida hali.   Haka rayuwar tacigaba da tafiya *Ummah* da yaranta sunga chanjin rayuwa sosai da sosai domin *Baffan*  nasu ya kankame komai  Bayan wata da rayuwarsshi mahaifiyarshima Allah yamata rasuwa, gida yazama abunda yazama kayanda akabari  *Kallah*  yayi kane kane akai hatta da suturarshi sawa yake, sanda akai rabon gado kuwa shafama idonshi toka yayi yace basuda wani gado don komai nashine Tunda duk wani kadara sunashine ajiki basu wani sami abun arziki ba, haka sukaci gaba da zama wataran abincima sai anga dama ake basu da ummah taga haka bashiri ta kafa murhu d'an kud'in dake hannunta take saya musu kayan abinci, ad'ad'are sukakai shekara agidan tundaga lokacin yatada fi'ilin afita abarmai gida tunda bamuda gado, wulakancin yau daban na gobe daban har abun yakai makura inda ummah ta tattara shirginta sukayi gaba yazauna ya tabbata agidan tunda wanda yayi silar samuwar gidanma yabar duniyan  _muje zuwa donjin yadda rayuwarsu HIBBAH zai kasance_    
.
    *Cigaban Labari*
Tsawon shekara d'aya kenan da rasuwar mahaifinsu *Hibbah*   abun mamaki duk abokan arzikin  *Abban* kowa ya kama gabanshi hatta wasu daga cikin y'an'uwanshi ba wanda yayi tunanin d'aukarma  *Ummah*  yaro ko d'aya duk yara biyard'in d'awainiyarsu na kanta lokacin  *Sadeeq*  na aji shida a primary,  *HIBBAH* tana aji uku,  *Salman* na aji d'aya, sai  *Adam* da yake nursery 1,sai Auta *Muhammad* dake zaman gida, Allah ya taimaka makarantar ta d'auki nauyin karatunsu har sugama dakuma littafan rubutunsu.   Kawu Umman shike basu kud'in abun hawa na zuwa idan antashi su tako da k'afarsu kasancewar shima nashi iyalan suna makarantar.   Ummah ta yanke shawarar fara sana'a don taragema Kawun nata wani nauyin, kasancewar yanada tarin iyalai yara da manyan matasa wasu sunyi aure wasu shike ciyar dasu ga girma ya kamashi masinjane a babban asibitin bauchi.   D'anyen kayan miya ta saro da wake kasancewar ranar asabarne bayan mun dawo daga islamiya ta k'ulla kayan miya d'a ur amin, ya Sadeeq kuma aka izamar kwanon wake Umma tace "maza ku d'an zazzaga dashi cikin unguwa ku dawo, don Allah karkuje ku zauna"   "Toh Umma"   Muka d'au kayan tallanmu mukayi gaba sanda muka fito kowa yafara raba idanuwa nace "Ya Sadeeq ina zamuje yanzun?"   Yace "gidajen zamushiga, Amma ke zaki rinka magana"   "tam nayarda muje."  Haka muka ta shiga gidaje tallah wasu su saya subamu kud'i wasu suce muje mudawo muna fita shikenan ba dawowa, haka muka rabarda kayan ba wani kud'in kirki tare damu, da yunwar ta ishemu muka garzaya gida.
.
  Sanda muka isa k'ofar gida sai akabarmu da ra'be ra'be don kud'in hannunmu ba yawa munma manta gidajenda mukabada bashi, Hibbah tace "yayah kazo mushiga,"  "idan munshiga mezamucema Ummah?" kafin sukara magana saiga Ummah kamar anjefota da hijab a hannu tana shirin sakawa, tana ganinsu ta fasa sa hijabin tace "kuzanje nema tund'azu, kunfita ba labarinku kundawokuma kun tsaya raka'be raka'be lafiya daiko?  " lafiya Umma"   "toh kuwuce muje ciki."  Wucewa sukayi ciki, bayan sunshiga sunba Umma kud'in da kayan miyar da wake tace "ya haka? Ina sauran kud'in?"  Kallon kallo suka farayima junansu  Ummata harzuka "Tambayarkufa nake Amma kunmin banza! Nace ina sauran kudin?"  "uhm, uhm, asan siya akace muje mu dawo mu kuma mun manta gidan,"  "shine maimakon kudawo gida tun d'azun sai kuje ku zauna?"  "ba zama mukayiba muna zazzagawane."  "kun kyauta kuci abinci kuje kuyi wanka kuyi sallah ku tafi islamiya.   Haka washe gari Ummah ta d'aura musu tallah baifi gida biyu suka zagaba suka sami waje suka zauna wasunsu, sanda suka gaji suka koma gida ba tare da wani abun karkiba, Tunda taga haka tace ta hakurada sana'ar don ko cikin gidanma ba wani saya akeshigowa yiba.   *Bayan shakara d'aya*   Lokacin ya Sadeeq ya tafi J. S. S one a makarantar gwamnati dake cikin barikin sojoji yakanje a abun haya ya tako da k'afarshi ga makarantar da d'an karan nisa ba ba yadda zaiyi haka yake fama.

HIBBAH Part 11-15
.
Lokacin Ummah tayi shirin tafiya k'auyensu don duba mahaifiyarta ba lfy, kwana biyu da tafiyarta matar Baffah tazo ta d'aukeni Wai idan Ummanah ta dawo zata dawo dani Lokacin dana koma gidan da zama ba laifi ina samun kulawa duk inda zata tare muke zuwa kullum cikin ado nake.   Lokacin da Umma ta dawo bata taga ana kula dani bata nemi indawo garetaba Tunda taga banda wata matsala.   Kud'in data kaima aminin mijinta dubu talatin da biyar ya cika dubu biyar yazama arba'in yasamusu gida Saidai unguwar ba mutane sosai kuma yawancinsu ba musulmai bane, tace bazasu koma yanzunba sai wajen ya cika da mutane,tasami Kawu Usman akan tanaso ta nemi gidan haya ta koma sabida nauyi yayi yawa a kanshi, ba yadda baiyiba da ita akan ta hakura taci gaba da zama Amma taki tace "gara yaje ko wankin kud'i da wanke_wanke zatayi don rik'e yaranta"  haka ya hakura ta nemi gidan haya a unguwar Dutsen Tanshi, ta kwashi yaranta suka koma chan da zama.   Bayan komawarsu tasamama Sadeeq wajen gyaran mashin idan yadawo makarantar boko yakanje wajen gyaranshi da yammaci kuma su tafi Islamiya, ita kuma tana d'an sana'arta tana samin abunda zasusa abaka.  

*YARAYUWAR HIBBAH YAKE CIKI*
.
 Tsawon wata biyu *HIBBAH* nashan gata   ashe duk kiwonta suke daga baya komai ya chanza ta dawo tamkar baiwa, itake share share daga d'akuna har cikin gida ga lodin wanke_wanke ga aika kamar me duk nisan aika ita kezuwa ga yaransu ba abunda suke akatawa.   Umma tana kokari sosai wajen kula da yaranta da basu tarbiya wani lokacin abunda zasucima gagararsu take, yadda Allah ya taimakesu mutanen dasuke hayar sunada kirki suna d'an taimaka musu.
.
Lokacin da yara suka sami hutu duk ta tattarasu suka tafi kyauye hutu, sanda taje taga sauyi sosai wajen mahaifinta, abun ya mugun bata mamaki Amma sam bata nunaba, bayan dare yayi sun ke'be da mahaifiyarta take tambayarta meke faruwa taga mugun sauyi gurin mahaifinta. Nan take gayamata sharrin da kishiyoyinta suka mata "iyayenkine suka sami Babanku Wai ninama yaransu asiri shiyasa sukaki auruwa, Tunda ga nawa yara mata uku sunyi aure don haka dole inje in karya asirindana na musu, namasu rantsuwar 'ba sanin gurin wani mai asiriba balle har inje in musu, munyi rikici sosai har maigari saida yashiga zancen tukunna nasamu sukuni." "Lallai mama kina cikin ukuba"  "Humm!  "kedai bari Allah ne kawai zai fiddani, domin yanzu zaman rashin y'anci nake a gidannan, ace Tunda yarantarmu bamuyi hakanba da mahaifinku saida tsufa   yazo mana, danasa abun araina Amma daga baya na cire don nasan bayin kanshibaba k'ullaliya akamai." "Amma wannan abun da tashin hankali, ina tunanin baba yaje dahar zai zauna mata su shiryama wannan kullin? Allah tona asirinsu kekuma yakara miki hakuri da juriya."           "Ameen"  Sundau lokaci mai tsawo suna hirarsu daga baya suka kwanta.   *Washe gari* Bayan umma taje gaida mahaifinta da k'ar ya amsa yana cin magani, hakadai ta bashi tsarabar data kawomai, shaddace yadi biyar da takalmi da hula ko kallonsu baiba yace ajiye acan "idan kin karya kizo zamuyi magana"  "toh"  Saidatabi kowani d'aki ta gaidasu har makwabtansu duk tashiga ta gaidasu sanda ta dawo tasamu ancikasu da abun karyawa, bayan tad'an taba ta nufi d'akin mahaifin nata, yace "takoma ta kira mahaifiyarta yanason ganinsu"  Juyawa tayi taje ta kirata sannan suka dawo, gyaran murya yayi sannan yafara magana "Hadiza!  Saida Umma taji wani iri don baisaba kiranta da sunantaba kasancewar itace d'iyarshi ta fari,  " Naam baba" Inaso yaran dake hannunki ki maidasu wa dangin mahaifinsu don anfara kawomin korafin kinabin maza acan,   Atare Umma da mahaifiyarta sukad'au salati INNALILLAHIWA'INNA'ILAIHIRRAJI'U
.
  Daga Mama har Umma kuka kawai sukayi, Wai yau mahaifintane da kanshi yake gayamata tanabin maza, yau Mahaifintane kece tana zina, mahaifindaya bata tarbiya tundaga tsumman goyonta har yazuwa yanzu Amma shike mata wannan mummunan zato. _innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un_  wannan wacce irin jarabawar rayuwace take shirin fuskanta. Haka yagama maganganunshi wani zancenma dagaji had'ine, saida yagama tsaf sannan ya sallamesu.  Abun mamaki sukagani lokacin da suka fito daga d'akin Matan Baban Umma su biyu suna la'be agefen k'ofar sai murna suka ga dukkan alamu sunji me akace.  Wucesu kawai sukayi aiko Umma suna bada baya suka kwasheda dariya sukace "kad'an kuka gani"  Mama tace "ALLAH yafiku dashi muka dogara."   Wunin ranar Umma a d'aki tayishi don data fito za'a mata habaici.   *
.
*CIKIN DARE*  Ummane da Mama ke magana Mama tace "Saidai ki hakuri don yanzun saikin toshe kunnenki don zakisha maganganu, tunda kina zaman gdn hayane ba tare da wani nakira don Allah idan kinkoma kiyi k'ok'arin fidda miji cikin manemanki ki aure hakan zaisa ki fita zargi.  " Nifa ba aurenne bansoba wanda zai rik'eni da yarana hud'u shine abun tunani tunda kinga duk dagin mahaifinsu ba wanda yakuma waiwayansu badon kuma basunan ba suna raye kuma dukkansu sunada rufin asiri daida gwargwado. " " kidainasa damuwarsu aranki kedai ki kula da yaranki koda wasa ban yarda kibasu yarankiba" "Insha Allahu zan sadauk'ar da rayuwata don kula dasu, ran Monday insha Allah zamu koma don zamanmu zai zame miki 'bacin rai tunda wunin yau bak'ak'en maganganu kawai suke jifarki dashi a dalilina" "Allah yakaimu gobe asabar da lahadi saiki zazzaga gidajen y'an' uwa"  Saida sukasha hirarsu sannan sukayi bacci dama yaran sun jima da bacci.   *Washe gari* Umma taje ta gaida mahaifinta sannan tabiya d'akin matan Baban nata biyu ta gaidasu da kyar suka amsa gaisuwar, yaranma sunje sungaida kowa, wanka sukayi sukafice ziyara gidan y'an'uwa.  Basu suka dawoba saidare suka dawo gida, washe garima haka suka sake ficewa Saidai yau da wuri suka dawo don shirye_shiryen tafiya.   'Dakin Mama cike yake da kayan abinci irinsu Wake, gyad'a, gero, dawa, masara, bushashshen ku'baiwa, Kuka,  daddawa, shinkafa, tsintsiya duk mutunene suka turo musu dashi a hakanma harda basu hak'uri.
.
 Da daddare saida Umma tabari kowa ya rufe k'ofa ta nufi d'akin Baba ahankali ta tura k'ofar tareda sallama tashiga zaune yake kan kujera yana saurarar Radi'o amsa sallamar yayi tare da fad'in "lafiya da darennan"  "lafiya lau Baba. " waja tasamu ta zauna tafara magana "nazone dama inbaka hak'uri kan abunda ake fad'a game dani, nasan sharri akamin kuma kowaye nabarshi da Allah. Da sannu Allah zaimin sakayya, nayi mamakin yarda da kayi akan maganar kafi kowa sanin wace ceni, kafikowa sanin irin tarbiyar da kamin, tunda yarintana banyi Zinaba saida girma yazomin ribar mezanci, bayan nasan girman zunubi irinna mazaunai. Tayaya zanciyar da yarana da haram bayan nasa dukkan jikin da aka raimeshi da haram bazai shiga Aljannahba."kukane yaci k'arfinta tace "gobe insha Allah zamu koma ina mai neman afwarka ka gafarceni Insha Allahu dana koma zanyi Aure domin kare kaina da zargi." batajira amsarshiba ta tashi tayi gaba shikam yayi mutuwar zaune tana fitowa taga kishiyar Mama mak'ale da alama taji duk abunda tace, wucewa tayi tare damata addu'ar shiriya ita kuma ta shige d'akin Baba.     ~
.
  *WASHE GARI*   Umma sungama shirin tafiya zuwa k'arfe takwas motarsu zai tashi, yanzu wajen karfe takwas da minti hamsin tana jiran Baba ya dawo suyi sallama amma bashi ba labarinshi, tun asuba daya fita sallah bai dawoba, k'arshe dai tafiya sukayi ba tareda sallamabah.   _
.
Su Ummah Allah kiyaye hanya, yabada hak'uri_  Tun dawowarsu Umma taje taga Hibbah takuma basu tsarabarsu, bata kuma komawa gidanba, don randa ta koma gida tayi kuka sosai yadda taga Hibbah ta dawo, duk wani aikin gidan ita keyi hatta gjrkin gidan itace bata da wani lokacin kanta, da zarar ta tashi tun asuba tayi sallah zata fara sharan gida tana gamawa ta fara abun karyawa sai ta sallami kowa sau tari haka take tafiya makaranta ba tare data karyaba, tana aji biyar na primary Allah yabata baiwar ilmi na boko da arabic.   _(ba doleba tunda Umma da Abba ba dama wajen ilmi ta kowani fanni)_  Haka rayuwa tacigaba da tafiya wani lokacin asamu wani lokacin arasa, Umma sun daidaita da wani bawan Allah yanada yara Uku biyu mata d'aya na miji, Allah yama mahaifiyarsu rasuwa.   Lokacin da suka daidai tamai maganar yaranta guda hud'u yace "ba komai d'a na kowane."   Lokacin da sukayi aure komai yana tafiya daidai daga baya kuma halinshi na asali ya nuna, ba abinci, sutura, duk wani hak'k'i daya rataya kan miji baya baya badawa, da Umma taga haka tuni ta ware ta fara wankin kud'i shima ba kullum ake samuba gashi lokacin tana da ciki, haka suke rayuwa idan tasamu tayi wankau kud'i suci abinci inbabu su hak'ura daga baya ya tsiri sabon salon iskanci idan yadawo aiki saiya siyo abinci yashige d'aki ya k'ira yaranshi suci, da Umma ta fuskanci hakan bata nuna damuwartaba don tasan ba wanda zai iya mata d'awainiya da yaranta tunda dangin ubansuma sun gaza balle wanda bai had'a jini da suba.        
.
    Haka Umma ta ware tana neman abun rufin asirinsu ita da yaranta.

HIBBA Part 16-20 (THE END)
.
 Umma ta haifin d'anta k'ato duk suna cikin k'oshin lafiya, yaci sunan Muktar.   Muna zaune mukaga Baffa Kalla sunshigo da wasu manyan mutane su uku da takardu ahannunsu, yanunamusu ko ina na gidan da muke ciki suka fita, mudai anbarmu da tunanin ko lfy? Ohh.  Bayan ya rakasu ya dawo yake fadima matan nashi cewar "yasai da gidan kud'i yasai wani gida a karofi nanda wata biyu zasu tashi idan angama gyaran gidan." acewarshi "yagaji da yadda mutanen wannan unguwar suke damunshi da k'ananun magana akan yakasa rik'e amanar y'ay'an d'an'uwananshi."   Umma kam zama sam yak'i dad'i gashi yanzu bata samun aikinyi sai ayi kwanaki basu sami abunda zasu sa'a bakin salatiba daga k'arshe dai ahaka auren ya rabu, ga yara har biyar awajenta tunda auren ya k'are mijin ya kwashi yaranshi suka k'ara gaba bata kumajin d'uriyarshiba, dama kuma zaman gidan haka suke, mutanen daya gwada matasu amatsayin y'an'uwanshi ashe duk k'aryane zaman mutunci kawai ya had'asu, dole tanemi alfarma wajen masu gidan sumata hak'uri zasu gyara gidansu kafin kud'in hayar ya k'are.   Su Hibbah ankoma sabuwar unguwa yau kusan watansu uku da dawowa, saidai gidan dasuke yanzu bawani fasali d'akunane guda hud'u ciki d'ai_d'ai, sai bayan gida da kitchen, sai filin tsakar gida wanda yaci a d'aga d'akuna ciki da falo da bayan gida guda biyu awajen.

 HIBBATULLAH!
 HIBBATULLAH!
HIBBATULLAH!
Sau uku tana k'wala mata kira a rikice ta fito daga wankan da take jiki duk kumfa ta d'auro zani ta fito, da sauri ta isa k'ofar d'akin ta durk'usa gabanta na dukan tara tara.  Tace "gani Mama."  Wani kallo ta mata saidata kusa zama cikin masifa tace "rami kika shigane da nake k'iranki bazaki amsaba?"   "Ahh! ki hakuri wanka nashiga"   "kin kad'amana miyanne dazaki shiga wani wanka?"
.
  "bai karasa nuna bane shiyasa nashiga wankan, naga lokacin islamiya yayi su Ahmad suntafi tun d'azun"  "ina ruwana? Idan kinga kinje Islamiya yau toh kin gama miya kin d'auramana ruwan tuwo, idan kin dawo ki k'arasa don kinsan ko wuta bamai iza miki" Kwallace ta taru a idonta don tasan yauma saitasha dukan latti, haka ta wuce kitchen ta samu wutan ya mutu ga iccen d'anye ruwa duk yagama jik'ashi, ledodi da roba tayita bankamai har ya kama miyar ya k'arasa nuna ta kad'a ta sauk'e ta d'aura ruwan tuwo da sauri ta fito sau warin hayak'i take gashi ko wankan bata gamaba, kayan makarantarta kawai tasa tafito tabiya dakunansu ta musu sallama ta wuce kamar kullum ba wacce ta takata.   Sanda tazo fita saidata lek'a k'ofar gidan taga ba kowa tayi ajiyar zuciya tajin jin dad'i sannan ta fito, sauri take tayi don tasan tagama latti bama dukan lattin take tunaniba burinta kar Allah ya had'ata da y'an cikin unguwar don tasan saitasha kuka.   Ta isa makarantarta karfe biyar dai_dai ta iso.  Tana shigowa y'an aji suka fara "Hajiya babbah" suna murnar ganinta.   HIBBAH yarince mai fara'a son mutane ga uwa uba ilmi, shiyasa malamai da d'alibai ke sonta. tana aji shida a boko, islamiya kuma tana aji biyar Malamansu na k'iranta da Mace mai kamar maza. Itace minitor, ita kecin na d'aya duk jarabawa duk lokacin da zasuyi gasar karatu ita ke cinyewa, shiyasa kowa ke sonta.
.
   Allah ya taimaketa yau malamai suna meeting bata sami kowaba, nan suka fara bitar karatunsu, bayan ta koma gida ko kayan makarantar bata cireba jaka kawai ta ajiye tayi kitchen tahau had'a wuta tana had'awa taje tai sallar magrib tana idawa koma kan girki, kafinta gama tagama shan wuya da iccen damina wanda ruwa ya gama dokarsu, ga yara sunata kukan yunwa.  Tana gamawa ko ci bataiba ta sunkuya wankin kayan makarantarsu nata dana yara biyar tagama k'arfe tara lokacin kowa na d'aki da yaranshi alola tayi aje tai sallar Isha'i, tana idarwa ko batabi takan abincinba ta d'auki yar tabarmar kwanciyarta tayi d'akin Mamansu Ahmad don kwanciya tana shiga tasamu duk sunyi bcc kan gado, gefe tasamu tashinfid'a tabarmanta ta kwanta, tama gama mantawa mai gidan anan d'akin yake, chan cikin dare taji magana sama_sama kamar masifa Mamansu Ahmad kecewa "wallahi saitabar d'akinnan"  "habba ke kuwa inaga ta mantane kibarta tunda tayi bacci" "bacci fa kace ina ruwana da baccinta" "babu ruwanki, amma amata hak'urin yau tunda kinga sauran yaran suma baki koresu a d'akinba."  "saurankam ai yaranane itako bani na haifetaba uwarta bansan wani gantalin takeyi agariba"   Hak'uri yayita bata dak'ar ta hak'ura   Hibbah dake kwance ba abunda takeyi sai kuka, Wai yau ita akema gorin wajen kwana har akema mahaifiyarta mai yawace_yawace, Allah sarki Ummanah, Allah yasa kuna cikin k'ishin lafiya da kwanciyar hankali aduk inda kuke.
.
*  Cikin dare Hibbah ta tashi da sand'uwa ta bud'e k'ofar d'akin ta fita, d'akin da da suke ajiye wasu shirgin da kayanta aciki nan ta nufa ta ciro zani cikin kayanta ta shimfid'a ta kwanta acan gefe hijabin jikinta kuma ta rufu dashi.  Asubar fari ta tashi tanayin sallah tahau gyara gidan ta nufi kitchen, sauri take tagama yau ta tafi makaranta da wuri ga yunwa Amma ko kad'an bata shawa'ar zama taci abincin zuwa shida da rabi ta gama komai saura gyara d'akin matan gidan, gashi har yanzun basu fitowa tunda sukayi sallah suka koma.     Sai wajen k'arfe bakwai suka fito lokacin duk yaransu sun shirya a gurguje ta shiga ta gyara musu d'akunan, kwanukan dasuka ci abinci ta had'a waje guda ta rufe sai ta dawo zata wanke don ta riga tayi wanke wanke.  dubawa tayi taga har bakwai da kwata da sauri taje ta kar'bi naira hamsin kud'in mashin d'inta tayi gaba yaran sun jima da tafiya makaratar gwamnati take sukuma sunata kud'i, idan anbata kud'in abun hawa na zuwa da k'afa take dawowa kafin ta iso gida duk yunwa ya gama da ita wani lokacin ma idan ta dawo sai ace abinci ya k'are anba yara, dolenta zata hak'ura ta d'aura na dare idan ta gama akayi rabo ad'an yafa mata.  
.
_wacce rayuwa su Umma suke ciki bara mu lek'asu_  Cikin yaddar Allah su Umma har sun koma gidansu dake yanzu unguwar tafara samun mutane, da taimakon Alhaji Isma'il aminin mahaifinsu Hibbah suka d'an gyara gidan.   Gidane mai d'auke da hud'u ciki d'ai_d'ai, sai bayan gida.  'Dakunan duk rufin kwanone, ko arzikin silin babu mafi yawan rufin d'akin a'bule suke, dabaraakayi aka d'an lik'esu, sai filin tsakar gida wanda zai iya fidda d'akuna kamar wad'ancan, ya fidda kitchen dakuma bayan gida.  Wad'ancan d'akunanma manyane sosai Umma ta sa kayanta a daki d'aya yaran suna d'aya ahan kali zata sami y'an haya su shiga saura biyun.  Gidan ko katanga babu sai kara aka samu aka kawaye gidan dashi, ahaka suke rayuwarsu cikin kwanciyar hankali da rufin asiri.   Hibbah nagani zaune can gefe rik'e da k'irjinata da ciki, sauran d'alibai kuwa wasu na gyad'a, wasu tambo, wasu nacin abinci, wasu na filin break, dake lokacin sun fito  break ne, kad'awa akayi don komawa aji d'alibai sai rige_rigen shiga aji suke don gudun duka, Hibbah ma mik'ewa tayi don shiga aji saida tana fara tafiya wani girine ya kwasheta ta fad'i k'asa warwas numfashinta sai sama_sama yake kafin kace me d'alibai yan'uwanta sun rufeta, Ko ganinta ba'ayi.   _Nayi iya k'okarina don ganin na kutsa tsakanin yaran na kasa,dole na koma gefe ina tunanin me yasami HIBBAH baiwar Allah_             *
.
Duk sun rufeta ko ganinta ba'ayi, wasu daga cikin d'aliban sukace "kodai aljanu gareta?" aidajin an ambaci aljanu kanemi yaran ka rasa, saiy'an kad'an, kamata sukayi suka kaita aji aka dukufa karatun (Alqur'ani), ko gezau bataiba, don abundaya ragu.
.
   Wata malamace tashigo don yimusu karatu, Saidai mafi yawan d'aliban ajin hankalinsu ya raja'a wani wajen da taga sun kewaye wajen,  Tambaya tayi "meke faruwane?"  Wata d'alibace taimata bayanin komai tace"shine zaku barta anan? Clinic yadace ku kaita baku cika akantaba da zafin ciwo zataji koda rufeta da kukayi ga zafi."    "malama bazata iya tafiyabane."    Har wajen malama tasu ta iso tana kallonta tace "dama Hibbace ba lafiya? Subhanallah! Yadda taganta rik'e da k'irji ga numfashi na fita da kyar gashi tana rik'e da ciki tasan yunwace."  Tace ma yaran "kowa ya koma wajen zamanahi ya zauna mutum d'aya ta tsaya ta mata firfita."  Fita tayi daga ajin, zuwa can sagata da y'ar k'aramin kwando d'auke da k'aramin flaks da kofuna biyu da gwangwamin madarar ruwa sai sugar.  Da kanta ta had'amata lafiyayyar shayi ta d'agota tabata abaki tanasha ta kwaro amai, ajiyewa tayi ta tafi Clinic din cikin makarantar ta ma ma'aikaciyar wajen bayani tace "ga dukkan alamu ulcer keneman samun muhalli jikin yarinyarna.
.
malama tace  "nima tunanin danake kenan." magunguna ta dauka da allurai guda biyu suka fita, allurai biyu akamata zuwa anjima in yad'an lafa  mata taci wani abun sai tasha maganin.   Ahankali takejin ciwon na tafiya ga wani zufa na sauk'omata.   Shayin aka kuma had'a mata tashi aka bata magani, kafin atashi taware kamar ba'itaba, Saidai rashin k'arfin jiki, tana tunanin yadda zata taka har zuwa gida a k'afa cikin ikon Allah malamar ta bata kud'in abun hawa.
.
  Hadarine yau sosai ya had'o cikin dare, Hibbah duk sanda ake ruwa hankalinta na gidansu wajen Ummanta tunda taje ta kwana biyu taga yadda suke ana ruwa ba karamin tausaya masu Ummah da k'annenta, yanzu haka zaune take tana tunanin idan ruwannan ya sauk'o kwana zaune zasuyi atak'ure, bata gama tunaniba taji wani iska mai k'afi had'eda ruwa ai batasan sanda ta fara kukaba tana addu'ar Allah takaita ruwan kar yayi yawa.    Nima gidansu Ummah na garzaya don ganin wani yanayi sukeciki da yasa Hibbah kuka haka.   Ummah na hango ita da yayanta mak'ale can gefen d'akinsu wajen da baya zubarda ruwa, wasu sunyi bacci wasu kuma sai gyagyad'i suke,  Fita nayi daga d'akin don idona bazai iya cigaba da kallon yanayin da suke cikiba  Allah sarki rayuwa jarabawarta takanzo ma bawa ta ko wani fanni fatanmu Allah yabamu ikon cinye jarabawar.
.
   Yau asabar ba boko Hibba sai sauri take tagama wanke_wanken datake ta tafi islamiya don yanzu wajen takwas da rabi, tana gamawa taje ta sa kayan makaranta kira taji ankwala mata matar Baffan nata da sauri ta fita taga Maman Shahida ke kiranta kudi ta mik'a mata Wai tayi sauru ta sayoma Shahida k'osai amsa tayi tana Addu'ar Allah yasa gidan ba layi fitowa tayi sai sauri take bugawa, daban y'an unguwar tagani zaune kan dakalin k'ofar wani gida, tunda ta hangosu gabanta ke fad'i jitake kamar ta juya amma bata isaba jiki sanyaye taci gaba da tafiya aiko tana isowa waje duka d'au ihu suna k'irantada sunan data tsana.        
.
*Cigaba tayida tafiya, sukuma sukaci gabada tsokanarta, kwallar data taru idonta ne ya zubo, kukan zuci kawai take zuciyarta kamar wuta take jinshi, nan  take kanta ya fara sarawa, haka ta isa gidan sayan k'osan, Allah ya taimaketa ba layi akabata tayi gaba tare da fatan kar Allah yakuma had'ata da mutanennan saidai tana isowa sukaci cigaba daga yadda suka tsaya, kukane yakuma kwanamata, tasa bayan hannunta tana sharewa.   Tana isa gidan tamik'amata ta d'au y' ar ledan littattafanta tayi gaba, ga kanta dake tsananin ciwo ta gwammace taje makarantar data zauna gida don idan ta zauna aiki saita rasa yadda zatayi idantace batada lafiya ace k'aryane aikine bataso,shiyasa ta gwammace ta tafi makarantar datai zaman gidan.   Haka rayuwa taita tafiya da jarabawa kala daban daban.   Har noman kud'i Umma keyi, wanki, surfe da daka na kud'i don kawai tasami abunda za'arufama kai asiri, daga baya tasami aiki a ma'aikatan kula da marayu da marasa galihu basuda matsala yanzu sosai, yaranta duk tamaidasu makarantar kud'i yaya Sadeeq kawai ke makarantar gwamnati, d'akuna biyun tasa haya, balaifi suna rayuwa cikin jin dad'i da kwanciyar hankali.    Cikin ikon Allah Hibbah sun zana jarabawar aji shida a primary ta fito da kyakkyawar sakamako, har anmata register a makarantar gaba primary aji d'aya, saidai k'arfe sha biyu zuwa biyar da rabi suke tashi, tundaga lokacin aikin gida ya k'aru mata don saitayi girkin rana idan ta gama ta d'aura miyar dare kafin ta dawo gida magrib yayi,sai kicin.    Haka rayuwa taci gabada tafiya, kwatsam aka rufe ma'aikatardasu Umma suke aiki, lokacin aka turo mata mahaifiyarta ba lafiya  nan take ta tafi don dubata, kwana biyu da zuwanta Allah ya kar'bi abunshi, kwana bakwai tayi ta dawo, akaci gaba daga inda aka tsaya.          ~
.
*  Rayuwa taci gaba da tafiya lokacin Umma duk sama ma yaranta wajen aiki, dagamai kafinta, d'inki,gyaran wuta, makanikanci, gakuma karatu ta ko wani fanni sunayi tukuru na addini da boko,   Hibbah ma tun wani ciwo datayi Umma tazo ta d'auketa bata kuma komawa gidanba suma basu nemetaba, haka suka Cigaba da rayuwa kowa abundaya samo wajen aikinshi dashi suke had'awa su biya buk'atunsu.
.
 *BAYAN SHEKARU MASU YAWA*
Gidan Umma nazo amma gaba 'baya na kasa gane gidan don duk layin wasu had' ad'd'un gidaje nagani, da tambaya nasami gidan.    Ummu na hango zaune kan wani rantsatsen kujera rik'eda wata yarinya dagani suna kamada yaya Sadeeq, can naga wata y'ar duma dumar mata tashigo ta kar'beta tana cewa "ai Umma Zarah akwai kuka tundaga gefenmu nake jiyo kukanta."  kafin Umma tayi magana akai sallama aka shigo wani k'aton Alhaji nagani, har gaban Umma ya wuce ya tsugunna ya gaidata sannan yace "Umma zamu wuce gidan Hibbah muduba ya jikin nata."    "toh saikun dawo Allah tsare hanya, agaidata da yaran."      "zataji insha Allah."      Maman Zarah matar ya Sadeeq tace "Umma sai mundawo, ko inbar miki abokiyar hira."      "waaa! jeki da abunki adawo lafiya."   Suka fita suna dariya Umma dariya take.   Hibbah tayi aure harda yaranata biyu, suna zaman lafiya,so da K'aunar junansu.  Ya Sadeeq ma yayi aure da y'a d'aya   Sauranko duk karatu suke.   Baffah kallah ananan anaga tarin iyalai ga gida kullum cikin rikici.   Y'an'uwa yanzu kowa rububin zuwa


follow me on facebook follow me on twitter follow me on instagram

Fitattun labarai

Alqawarin da ciwo

Amfanin cin qafar kaza

Budurwar Roba

Amfanin lemon tsami

Afanin Zogale

Adam A. Zango

Amfanin namijin Goro (bitter kola)

Tona asiri

Yanda zaka duba sunanka a Npower