Karin magana 3

  • Haka aka ce IN JI mai bada labarin karya,

  • Shege yafi shiru IN JI mata,

  • Kamar da kasa IN JI mai ciwon ido,

  • Bansa aka IN JI barawon tagiya,

  • Yi yafi bari tsarki da manja IN JI kazama,

  • Haka tara IN JI maso goma,

  • Hayya ratata IN JI mai mata tara,

  • Daminar bana ba kamar ta bara ba IN JI kwado da ya fada ruwan zafi.

  • Sai an kula kashi yake wari

  • Barewa tayi gudu danta yayi rarrafe.

  • Mugu yasan makwantar mugu.

  • Da wasa ake fadawa wawa magana

  • Gobara daga kogi, maganinta Allah

  • Kada dai a sha ruwa da ciyawa.

  • Tafiya da wuri tafi tafiya da wurwuri

  • Mun gaji da kyau, hali mu ke nema.

  • An ce da akuya Sarkin Fawa ya mutu, ta ce, “Oho, ya mutu da wu’kar yanka ne ?

  • In Allah ya ki addu'ar biri, sai ya mutu a gonar arna.

  • kwana nawa ne .... maye yayi amarya zai cinye ta

  • Ana raba ka da ciwon kyalle .... kana kyalle ta haihu

  • abun nema ya samu ..... matar dan sanda ta haifi barawo

  • a dade ana yi ..... wataran sai gaskiya

  • zani ce ta tadda muje mu

  • A rina .... an saci zanen mahaukaciya

  • A bari ya huce .... shi ke kawo rabon wani

  • Abun mamaki .... kare da tallan tsire

  • Ba'a ba kura ajiyar nama

  • Abu mai sauki .... fidda wando taka

  • Aikin banza .... kiba a kunne

  • Albarkacin kaza .... kadangare kan sha ruwan kasko

  • Ba'a hada gudu da tsusar duwawu

  • so ba samu ba ne
  • ban chi nanin ba, bare nanin ta chi ni                          
  • bari ba shegiya ba che, da ubanta, wai shi da na sani
  • ban kasa da kai ba balle ka dauka                         
  • baki shi ke yanka wuya 
  • abin da ya kora bera chikin wuta ya fi wutar zafi                              

  • A bari ya huche shi ke kawo rabon wani                          
  • abun da dama ta jure, hagun ba ta jure ba
  • abin da mutum ya shuka , shi zai girba
follow me on facebook follow me on twitter follow me on instagram

Fitattun labarai

Habiba complete hausa novel

Alqawarin da ciwo

Amfanin cin qafar kaza

Budurwar Roba

Amfanin lemon tsami

Afanin Zogale

Adam A. Zango

Amfanin namijin Goro (bitter kola)

Tona asiri

Yanda zaka duba sunanka a Npower