Rayuwar aure

Bincike ne na musamman aka gudanar akan manyan abubuwan da suka shafi mata iyayen gida, wanda ake matukar bukatar irin shi musamman a dai dai irin wannan lokaci, an gabatar da shine a wara bita da aka yiwa mata zalla. Allah ya sakawa mawallafiyar wannan rubutu da alkhairi, malamata; Malama A’isha Ahmad Bello (Nuriyyah).
Ya ‘yan uwa bayan sallama irinta addinin Musulunci tare da fatan alkhairi, da yardar Allah SWT za ayi taqaitaccen bayani darasin ‘idaaratul Manzil’ ko ‘Home Management’ ko ‘Gudanar Da Harkokin Gida’, wanda ya qunshi abubuwa kamar haka:
1. Girki
2. Abinci
3. Tsafta
4. Zamantakewa
5. Kiwon Lafiya
Da fatan Allah SWT yayi mana jagora ya kuma sakwa malamanmu da alkhairi akan kokari da kuma jajircewa da suke yi wurin ganin sun fahimtar da al’umma ingatacciyar aqida ta Tauhidi da kuma doramu akan Sunnar Manzo SAW; da kuma wayar mana da kai akan lamarin rayuwa wanda ta hakan addininmu zai qara qarfafa da kuma samun karbuwa.
Gudanar Da Harkokin Gida
#Darasi Na 1
#Girki
Abinci ya zama dole a rayuwa, kulawa da shi yana gyara zamantakewa, rashin kulwa da shi kuma yana bata zamantakewa, dadin dadawa kuma Allah da ya haliccmu ya umarcemu da muci daga abubuwa masu dadi, Manzon Allah SAW ya tarbiyyantar damu a wurare da dama akan cin abinci, misalin hakan shine fadin Allah SWT:
“Yaku wadanda sukai imani kuci daga abubuwa masu dadi na abinda muka azurtaku dashi” (Baqara: 172)
Saboda haka ina fatan wannan taqaitaccen jawabi da zan gabatar zai zamarwa Uwargida ‘ci a hankali’ ko ‘ci ki qoshi kuma baki na marmari’ ko ‘hana mai gida fita’.
1. Iya Girki: Anan ana nufin iya sarrafa duk abinda ya sawwaqa zuwa abu mai dadi, da sanin da wanne za’a qare, da sanin irin tsawon lokacin da kowanne irin abinci ya kamata ya dauka. Misali dahuwar wake da shinkafa, ko dafa shinkafa da doya da dai sauransu.
2. Iya can-canza nau’ikan abinci: Hakan yana taimakawa wajen gujewa ginsa ko qosawa idan anan can-canza abinci daga wannan kalar zuwa wancan. Sannan zanso mutane su gane cewa ba wai sai an dafa abincin gidan sarki ba, duk abinda Allah ya hore dashi za ayi amfani.
3. Kula da yin abinci mai kyau, kuma mai tsafta: Abin misali anan shine mai gida Allah ya hore masa ya kawo shinkafa baqa kuma yace yana son ayi masa tuwon shinkafa, kinga idan tuwo ne sai ki jiqa ta tunda wuri, hakan zai taimaka wurin sanyawa shinkafar tayi haske wanda zaifi bada sha’awar aci. Kwanukan cin abincin suma su zamo a tsaftace, hakan zai taimaka wajen jawo hankalin mai cin abincin, wannan kuwa zai kasance anyi da wurwuri ba sai lokacin da za’a ci abincin za’a wanke ba.
4. Rashin bata gida: Ya kamata uwargida ta kula sosai yayin da take girki kada ta bata gidan ko rumfar girkin ko kuma kayan da take aiki dasu a lokacin girkin. Duk sanda take aiki akan wani abu wanda yake buqatar a zubar da shara daga gareshi to sai tara sharar waje daya, sannan kuma ta debe ta da zarar ta gama da wannan abin ba wai sai ta gama girkin gaba daya ba kafin ta fara gyaran gida. Hakan nan ya kamata uwargida ta kula da jikinta wajen yin girkin, ba dole ne sai jiki ya baci ba don ana girki, matan arewa sun kasance suna zama cikin datti wai saboda su suna girki kuma wannan ba dai dai bane. Dole uwargida ta tabbatar tayi amfani da duk wani abu da zai rage mata sauqin aiki a lokacin da take yin girki (kamar su wuqa mai kaifi, tsumman goge-goge, qyallen sauke tukunya, abin kwashe shara dss).
5. Kulawa da lafiyar jiki lokacin girki: Ana son uwargida tayi taka-tsantsan a lokacin yin girki wajen kula da lafiyar jikinta daga wuqa, wuta, abu mai nauyi da duk wani abu dai zai iya kawo barazana ga lafiyarta.
6. Kulawa da yara da sauran mutanen gida yayin girki: Yakamata uwargida ta kula da zirga-zirgar yara da sauran mutanen gida yayin da take aikin girki, kada ta dinga ajiye abubuwa a ko ina inda yara zasu iya wasa dashi ko kuma a inda manya zasu iyayin tuntube dashi ko su taka.
7. Gama girki akan lokaci: Yakamata uwargida ta kula da lokaci wajen kammala abinci, domin yunwa bala’ice, gama girki da wuri yana daya daga cikin abubuwan da suke jan hankalin mai gida yaso abincin kuma ya qara masa qarfin gwiwar kawo cefane mai dadi, musamman tunda akwai kwanuka masu riqe zafi yanzu (flasks).
8. Gujewa barnatar da abinci da kuma dafa isashshen abin shima abin kulawa ne.

Dukkan Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin Halittu, tsira da aminci su tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad tareda iyalansa da wadanda suka bi tafarkinsa har izuwa tashin Alkiyama.
Yauma gamu munda dawo muku da cigaban karantunmu na Gudanar Da Harkokin Gida (zama na biyu), wanda da yardar Allah zai kunshi darussa guda biyar kamar haka:
1. Ingantacciyar lafiya tana samuwane ta hanyar ingataccen abinci.
2. Zaman aure zaman Ibada ne ba zaman kwatar 'yanciba.
3. Mallakar miji watau (matakai).
4. Kishi kumallon mata.
5. Rainon yara.
Da yardar Allah za'a daukesu daya bayan daya aji bayani akansu.
Gudanar Da Harkokin Gida (Zama Na Biyu)

#Ana Samun Igantacciyar Lafiyane Ta Hanyar Ingantaccen Abinci
Tabbas kulawa da abinci ya zama dole kuma sanin hakan dolene da lafiyayyen abinci ga lafiyayyen mutum dolene ya hada manyan sinadirai na gina jiki kamar haka: -
1. Protein : Wannan sinadarin gina jiki anfi samunsane a jikin dabbobi ko tsuntsaye kamar su nama, kifi, nono, madara, kwai, ko ta hanyar tsiro ko shuka kamar dankali domin wadannan suna taimakawa wajen gina gababuwa da karfafasu.
2. Carbohydrate : Wadannan ana samunsu ta hanayar shinkafa, alkama, Masara da dai sauransu. Suna Haifar da karfi da lafiya da kuma haifar da zufa watau cuta zai dinga fita ta zufa.
3. Fat/Oil: Watau duk wani abinci mai maiko suma suna da nasu anfanin a jiki, kamar manja, mangyada da dai sauransu.
4. Vitamin/Minerals & Salt: Ana samunsu ta hanyar kayan marmari, ganyayyaki wasu sai an dafa wasu kuma ba sai an dafaba. Koda yake a wata sa'in kowani mutum yana da abinda ya dace dashi musamman idan aka samu lalura na ciwo, wannan kuma sai mutum yabi shawarar likita, amma idan ba haka ba ana bukatar canzawa saboda kowanne ya dinga aikinsa a inda ya kama.
Kuma kamar yadda bukatuwa ta banbanta ta fuskar girma, yara sune mafi bukatuwa akan wanda ya manyanta saboda haka sai mu gyara, don zakaga munci nama uku-hudu koma fiye da haka amma yara sai a ficincina musu. Haka kuma lokacin samartaka akwai bukatar hakan don samun karfin gabbai da dai sauransu.
Hakan yana nufin a duk lokacin da za’a dafa abinci sai a kula da irin abubuwan da za’a sa a ciki da kuma irin abincin shi kansa. Idan da hali anaso a qalla aci kowanne nau’i wadannan sinadarai a kowacce rana.

A taqaice tsafta kalma ce da take nufin kawar da qzanta ko dauda ko datti da kuma mummunan wari ko kawar da duk wni abinda baya da kyawun gani. Don haka tsafta ta shafi abubuwa kamar haka:

1. Jiki: Idan aka ce tsaftar jiki ana nufin wanke gangar jiki da ruwa da sabulu ko abinda zai tsaya a matsayinsu su wanda zai taimaka wajen kawar da dauda da wari.
Haka kuma akwai wata hanya da mace zata kawar da dauda daga jikinta ba tare da amfani da ruwa da sabulu ba, wannan hanyar ko ana kiranta da Dukhan wato hayaqi, ana amfani da itacen farar qaya ko magarya.
Yadda ake yin sa kuwa shine mace zata rufe dukkan jikinta da bargo a lokacin da ta tube ta zauna ta ware qafafafunta alhali wannan itacen yana qarqashinta, yana bada hayaqi a hankali, shi itacen za’a dan jikashi da ruwa sannan asa a cikin wuta, dalilin jiqawa shine domin kada ya haifar da zafi sai dai hayaqi. Yana matuqar gyarawa mace jiki da matancinta domin yana mayar da mace yarinya kuma ya ma fi wanka tsaftace jiki. Amma kafin mace ta shiga cikin bargon zata shafe jikinta da KARKAR (wani mai ne da ake hadawa in babu sai a shaf man zaitun)
<Dan Allah idan akwai wacce tasan yadda akeyin wannan hayaqi sosai sai tayi mana qarin bayani dan mu qaru>
GA YADDA AKE HADA KARKAR
Za’a samu bawon lemon zaqi a jiqa ya kwana a ruwa tare da kanunfari sai a zuba a tukunya mai tsafta tare da man simsim (Ridi) ko man zaitun ko man kwakwa ko man gyada tare da wuta mara qarfi yana dahuwa har ya tafasa za’a sauke idan aka karya kanumfari aka ga ya karye to yayi.

2. Baki: Daga cikin tsaftar jiki akwai tsaftace baki, aqalla awanke baki da maganin wanke baki ko aswaki sau biyu ko uku a kullum, kuma dadi akan haka ya kamata mace ta riqa amfani da alawa (sweet) mai dadi mai bada daddadan qamshi a duk lokacin da zata kusanci mijinta.

3. Aski: Anan ana nufin aske wurin da suke tara gashi, kamar hammata, mara da sauransu, wanda dama yana cikin fitra guda biyar da Manzon Allah S.A.W ya fada, aqalla mace ta tabbatar tana yin wannan aski duk bayan kwana arba’in.

4. Qumba (Farce): Shi ma yanke qumba yana daya daga cikin fitra guda biyar wanda shi ma jigo ne sosai a cikin duniyar tsafta. Idan so samu ne ya kamata a qalla a yanke qumba a cikin kowanne sati, amma sai kaga wata farcenta kamar ta gwagwgwan biri.

5. Kaushi: ya kamata uwar gida ta kula da kaushin qafa tabi hanyoyin da zata bi wurin kawar dashi ko magani ko wankewa ko zuwa saloon dss. Wata hanya da mace zata iyayin maganin kaushin qafa shine ta samu ruwan zafi ba sosai ba ta zuba shampoo a ciki sai ta saka qafafauwa a qalla minti goma sai ta goge qafar da dutsen goge qafa sai ta fitar ta shafa mai kamar basilin ko zaitun sai ta sanya qafar a cikin leda kamar minti biyar amma ba wai sai zata tafi unguwa ba.

Tsaftar Gida
Tsaftar gida ya hada da wurare kamar haka:
1. Bandaki: dole mace ta kula matuqar kulawa a wajen tsaftace bandaki a kullum tare da amfani da magungunan kashe qwayoyin cuta da kuma masu sa wuri qamshi in harda hali, duk da cewa basu da wata tsada, rashin dai wasu basu saba ba, idan kuma babu halin saya wankewar da kawar da yanar gizo-gizo a kullum, sai a kula tare da watsa kalanzir a wasu lokutan ko kullum musamman bandakin da yake na kowa da kowa ne.

2. Dakin Girki (Kitchen): Kitchen yana daya daga cikin wuraren da ake tantance mace mai tsafta da qazama, saboda haka dole mu riqa kulawa da tsafatar kitchen kuma kasancewar wuri ne da ake dafa abinci wanda munsan abinci yana daya daga cikin jigon rayuwar ‘dan Adam, sai muka ga ya zama wajibi a kula da wajen da ake tanadarsa.

3. Tsakar Gida: Dole mu riqa kulawa da tsaftar tsakar gida, domin hakan zai taimaka wurin tabbatar da tsaftar sauran wurare kamar kicin, bayi, dakin kwana dss, dadin dadawa duk wanda ya shigo gidan zaiga gidan fes-fes wanda da ma a matsayinki na mace ana buqata a kowanne lokaci ki kyautata ganin Maigida da sauran jama’a a matsayinki na makaranta mai tarbiyyantarwa, da kuma tattara kayayyaki ko wane a sa shi a muhallinsa, na kicin akai kicin, na bayi a kai bayi, na daki kuma a shigar dasu daki, ba wai a barsu a tsakar gida ba ko da an wanke bare ace ba’a wanke ba.

4. Dakin Kwana: ‘Dakin kwana dole ne mu kula da gyaranshi fiye da ko’ina a cikin gida, domin nanne wurin da Maidiga yake samun cikakken nutsuwa da hutawa da samun kwanciyar hankali da dai sauransu. Saboda haka dole ne mu riqa kula da gyaranshi qwarai da gaske, da kuma qoqarin qawatashi da duk abinda Allah ya hore, da qoqarin sanya turare da abubuwa masu sa qamshi a kowannen lokaci musamman lokacin kwanciya. In har Allah ya hore yana da kyau ayi amfani da turare na ruwa ko na hayaqi kala daban-daban, kina iya amfani da kala hudu ko biyar a lokaci daya kowannen ki sa shi a bangare daban. Misali na zanin gado daban, na filo daban, idan filon yafi daya kowanne ki sa masa nashi daban, na labule daban, na tsakar daki daban, na kujeru daban dss. Hakan zai bada wani irin qamshi mai tada hakalin Maigida ya rasa wanne irin qamshi ne wannan kuma daga ina yake fitowa !!!

Tufafi

1. Tsaftar Tufafi: Dole ne mace ta kula da tsaftar tufafinta da na ‘ya’yanta da na Maigidanta, mu sani cewa yawan kayan sawa wata baiwa ce daga Allah, amma tsafta da wanki da guga da fesa turare idan ana gida shi ake nufi da tsafta, da wannan ne mace zata amsa sunanta na mace.

2. Kwalliya: Ya kamata mace ta kasance mai yawan kwalliya da cancanja salo kala-kala ta zamani domin Maigidanta, ba abin kunya bane dan mace taje koyon kwalliya, ka da ta tsaya ga sa hoda da jagira kawai, akwai yanayin kwalliya kala-kala, hatta su kansu kayan akwai yadda zaki sa su su birge Maigida.

3. Wajen Girki: Ana buqatar mace ta kula da tufafinta a lokacin da take girki dan haka shi zai qara tabbatar da tsaftarta. Saboda haka sai ta riqa amfani da qyalle ko tusmma na goge-goge, hakan zai taimaka qwarai wurin zama da kwalliyarta ko da tana girki kamar yadda bayani ya gabata, in kuma ta gama girkin sai tayi wanka idan akwai buqatar hakan amma bada ruwan qanzo ba!
ZAMANTAKEWA
Abinda ake nufi da zamantakewa shine mace ta zama mata ta gari, mutuniyar kirki wacce duk al’umma suka shaideta da mutuntaka a zamanta na aure. Kula da Maigida, yara, iyayen miji da kuma malamanta da ma sauran mutane baki daya.
Daga cikin abubuwan da zasu taimakawa mace ta zama ta gari sun hada da :
1. Bin dokokin aure
2. Bayar da haqqoqin aure
3. Kyakykyawar mu’amala da miji, ‘ya’ya, iyayen miji, dangin miji da sauran jama’a, mu sani duk wanda ya auri mace to fa ya aureta ne harda danginta, kamar yadda itama ta aure shi ne harda danginsa.
4. Haquri da yawan yafiya tare da kawar da ido akan wadansu abubuwa.
5. Neman shawara daga mutanen kirki, masu hangen nesa da nutsuwa da kuma aiki da shawarar da aka bata.
6. Baiwa Maigida shawara a kebance, ma’ana ba a cikin jama’a ba, kinga ko da bai karbi shawarar ba abin ba zai zamo matsala ba.
7. Rashin saurin fushi da kuma qoqarin kawar da fushi, kamar yadda yake a maganar Mazon Allah S.A.W : Idan kayi fushi idan kana tsaye to ka zauna, idan kuma a zaune kake sai ka kwanta, kuma kayi alwala.
8. Baiwa Maigida cikakken saurare, ki zama mai kyakykyawan saurare.
9. Sallamawa ga shawararsa matuqar bai sabawa Allah da Manzonsa ba, da kuma rashin jayayya da shi, sabanin wasu da qawayensu ne kadai keyi musu jagora da zuga.
10. Kiran Maigida da suna mai dadi ko kuma sunan da yafi so (kamar su sweety, darling, honey, angona, maigidana, nawan, my only one, Sahibina, sirrin zuciyata, hasken idona dss), kamar yadda Manzon Allah S.A.W yake kiran Nana A’isha da Ayish !
11. Yiwa Maigida kyautar bazata, kamar tufafi, abinci, abinsha, ‘greeting card’, turare da kuma yafiya akan laifi mafi girma wanda yake zaton za’ai tashin hankali akai.
12. Ki zama kina kiyaye harshe, tare da lura da abinda zaki fada, domin Manzon Allah S.A.W yace harshe zai jefa mutane a cikin wuta.
13. Yiwa Maigida uziri a inda ya gaza da nuna masa godiya ga duk abinda yayi ko ya kawo.
14. Qarfafa masa gwiwa wajen qulla zumunci da ‘yan uwansa, kamar iyaye dss.
15. Yawaita hira da shi da irin abinda kika san yafi daukar masa hankali ko kuma yafi so.
16. Yabonsa a gaban iyaye, ‘yan uwa tare da jinjina masa
17. Taimaka masa a gurin girmama iyayensa da naki
18. Kyautata zato a gareshi da kuma rashin dogon bincike a gareshi, kamar bincike a wayarsa (handset) da shiga cikin saqonninsa (messages) dss.
19. Karki fifita abokan miji akan miji, ballantana qawayenki!
20. Ki riqa nunawa Maigida cewa yana da hikima da dabara a cikin al’amuransa.
21. Mantawa da abinda ya wuce don baya jawo komai sai bacin rai
22. Tunawa da shi a cikin addu’a
23. Kulawa da ‘ya’yansa wadanda ba ke kika haifesu ba.
24. Ba da kyauta ta mamaki ga iyayensa ko wadanda suke a matsayinsu
25. Kulawa da wurin kwanciyarsa da kuma koyan salo daban-daban na kwanciyar aure, tare da tausaya masa idan kina al’ada, in har kina da abokiyar zama ki bashi damar ya tafi koda bai nema ba, in kuma ke kadai ce to ki bi hanyoyin da zaki kawar masa da sha’awa wadanda shari’a ta yarda da su.
LAFIYA
Ana buqatar mace ta kula da kiwon lafiyar kanta, dana Maigidanta da kuma ‘ya’yanta dai-dai iyawarta. Wannan kulawar kuwa ta shafi duk abubuwan da muka ambata a baya, kamar na babin tsafta dss. Saboda haka Uwargida ta guji yin sakaci akan abinda ya shafi lafiya don yin hakan zai taimaka qwarai wurin habakar arzikin Maigida da kuma samun nutsuwa da kwanciyar hankali.
Abubuwan da za’a kula dasu sun hada da:
1. Yawan tsafta
2. Nisanta da kawar da duk wani abu da zai jiwa yara ciwo
3. Rashin sakaci da kayan wutar lantarki kamar su ‘heater’, ‘electric stove’, dss, ka da asa su a jikin wuta kuma a kwanta bacci ko a fita wajen hira dss.
4. Duk abinda zai kawo hatsari a nisanci ajiyeshi a wajenda yara zasu iya dauka, kamar su ashana, kalanzir, fetur dss.
5. Kulawa da yanayin abinci
6. Gudun shan kowanne irin magani musamma idan ba qwararren likita ne ya rubuta ba
7. Bin dokokin da aka bayar akan magani
8. Qoqarin amfani da maganin kashe qwari kamar su sauro, kyankyaso, quda dss.
9. Lura da yara wajen qoqarin yanke musu farce, aski, kitso, wanke kai dss.
A taqaicen taqaitawa wannan shine ‘dan abinda Allah ya nufa a rubuta, kura-kurai masu dimbin yawa Allah ya gafarta mana ya kuma sa mu dace da bin Sunnah, abinda aka yi dai-dai kuma Allah ya bamu ladan shi amin thumma amin.
Siffofi 20 na mace tagari
Samun nagartaccen gida abu ne mai matukar muhimmanci a zamantakewar iyali.   Shi kuwa gida ba ya zama nagartacce sai da mace tagari, wacce take tattare da siffofi abin koyi da za su taimaka mata wajen tafiyar da gidan yadda yakamata.  Don haka ga wadansu daga cikin siffofin da yakamata mu yi nazari a kansu don gane wacce mace tagari? Siffofin sun hada da:
1. Ta kasance mai riko da addini, ba mai sakaci da shi ba.
2. Ta kasance mai gaskiya da rikon amana a kodayaushe.
3. Ta sanya Allah a ranta a duk al’amuranta na yau da kullum
4. Ta zama mai shigar mutunci, misali sanya hijabin da zai rufe mata jikinta yayin da ta fita zuwa unguwa.
5. Ta kasance mai girmama iyaye da ’yan uwa da abokan mijinta.
6. Ta kasance mai yawan kwalliya da ado ga mijinta
7. Ta kasance kwararriya wajen iya girki.
8. Ta kasance mai godiya ga abin da mijinta zai kawo mata, kada ta rika raina abin da mijinta zai kawo mata .
9. Ta kasance mai gaggawar amsa kira yayin da maigida ya kira ta zuwa shimfidarsa.
10. Ta kasance mai kiyaye dukiyarsa da duk wasu kayayyaki da yake amfani da su.
11. Ta kasance mai rufa wa mijinta asiri, ba mai watsa sirrinsa ba.
12. Ta kasance mai ba shi hakuri cikin lalama yayin da ta yi masa laifi.
13. Ta kasance mai nuna farin ciki idan abin farin ciki ya same shi, da nuna bakin ciki idan abin bakin ciki ya same shi.
14. Kada ta yabi mijin wata alhali tana tare da mijinta.
15. Ta kasance mai kwantarwa mijinta hankali yayin da yake cikin damuwa.
16. Kada ta ba wata ko wani dama ya ji sirrinsu  (ita da mijinta).
17. Ta kasance mai kokarin neman ilimi da aiki da shi.
18. Ta kasance mai nisantar abin da ba ya so, ta kuma rika kusantar abin da yake so.
19. Ta kasance mai bin umarnin yi ko bari wajen nuna masa so da kauna a fili, ba a boye ba.
20. Ta kasance mai tausayi, ba mai jawo masa bukatun da ba zai iya biya mata ba. 
Babu shakka da bincike na tsanaki ne ake samun mace mai siffofi nagari abin koyi, gaggawa da kwadayi kuwa a harkar neman aure, babu abin da suke janyowa face da- na- sani, ita kuwa da- na- sani aka ce keya ce.
Da sunan Allah mai rahma mai jinkai. Allah (SWT) yana fada a Suratul Rum cikin Alkur’ani mai girma, “Kuma daga ayarSa ne ya halitta daga gare ku mataye domin ku samu natsuwa daga gare su kuma ya sanya tsakaninku kauna da tausayi hakika wannan aya ce ga ma’abota hankali.”
Wannan aya ta tattare duk wani ma’ana na aure a cikinta saura namu mu farfasa mu auna mu gani shin ma’anar aure da abin da yake cikinsa kuwa kaman yanda Allah ya nuna mana hakan muke yi.
Da farko Allah ya ambaci Ma’aurata da ababen samun nutsuwa duk da a nan Ya kawo jinsin mata ne. To amma ai mun sani idan har macen ba ta samu natsuwa ba, shi kansa namijin natsuwarsa ragaggiya ce. Tambaya a nan TA INA MA’AURATA ZA SU SAMI KWANCIYAR HANKALI?
Na farko a samun natsuwar aure shi ne hadafin yinsa. Bai taba yiwuwa aure ya kasance an gina shi kan wani hadafi sannan ya zamo dorarre. Wannan shi ya sa Annabi (SAW) bayan ya zayyano kaso na matan da ake aure, karshe ya ce “Na hore ku da ma’abociyar addini.”
To hakika abun nufi a nan shi ne ba wani hadafin da zai haifar maka da cikakkiyar kwanciyar hankalin aure sai hadafin tarayya domin Allah. Gina auren don Allah, zaman auren don Allah. Hakuri da juriya da tabbatar da cewa ibada ce daga bangaren miji har mata idan ta batama ka tuna matan Annabi (SAW) sun bata masa sai ka danne. Haka ita ma mace komai za ta gani a aure ta sa ibada take, ta hakure domin Allah to hakika wannan shi ne jigon samun natsuwar Aure.
Sanin Hakkin juna: Jigo na biyu a cikin aure mai kawo natsuwa kenan. Hakika a yau mun yi sake tare da wasarairai da hakkin junanmu ta yanda ta kai har wasu abubuwan ma an shafe su daga rayuwar aure sai a wajen mutane jefi-jefi. Daga hakkokin auren kuwa shi ne:

Bangaren Namiji:
Hakkin ciyarwa dole ne ya fita ya nema ya ciyar da iyalinsa tare da adalci abun nufi ba ya kasance don an ce ya ciyar da su ba ya fita ya ci mai dadi, ya kawo musu ci-kar-ka-mutu.
Na biyu hakkin tufatarwa wannan Musulunci ya masa rangwame da ya kawo daidai karfinsa kuma ba a ce tilas koyaushe ba, amma akalla kar ya bar iyali cikin tsiraici. Na uku, hakkin matsuguni hakkinsa ne ya nemawa iyalinsa matsuguni mai aminci abin nufi wanda za su rayu ciki da aminci ba tare da tunanin za a iya cutar da su cikin sauki ba.

Bangaren Mace:
Na daya kula da gida, kula da yara, yi masa biyayya gwargwadon yadda ba za ta sabi Allah a ciki ba, wato duk abin da yake so, ta so shi, kuma duk abin da yake ki ta ki shi, matukar bai sabawa Ubangiji ba.

Bangaren Tarayyarsu: Kiyaye hakkin juna ta wajen ayyuka. Da yawa mu kan yi ayyukan da muka san abokin zama bai so amma muna ganin bai wani abu ba ne mu sani cewa ire-iren wadannan ayyukan duk kankantarsu kan jawo rikici, wanda ke sabbaba rashin natsuwa a rayuwar aure ba tare da mun ankara ba.
Misali maigida kan dauki al’adar zaman waje hirar dare wanda da yawa yakan taba zuciyar iyalinsa domin yawancin mata ba su cika son wannan ba. Hakika irin wannan kan haifar da rashin natsuwar mace tattare da mijinta wanda ke haifar da shaidan yai ta mata kulle-kulle sai ka ga kananan sauyi na bullowa a zamantakewa har ya jawo abin da ba a fata.
Haka bangaren mace da yawa za ka ga miji bai cika son ta fita ta kai dare ba, amma wata duk sanda ta fita sai ta kai, wanda hakan ma kan jawo kace nace har ka ga aure ya rasa hadafin da Allah ya halatta shi domin sa wato natsuwa.
Amma na biyu a bangaren tarayya shi ne: Hakkin lafazi, hakika mun manta da wannan a zamantakewar aure na yanzu. Za ka ga namiji da mace ta yi kuskure kadan ya kama fada tare da furta kalmar da duk ta zo bakinsa yayin da ita ma dan ta rama sai ta yi kokarin kwabo mara dadi wadda in ba a yi sa’a ba, ko da an gama fadan nan ma’ana an huce, shaidan zai yi ta tariyo masu maganganun juna sai ka ga an kullaci juna daga haka sai ka ga aure ya rasa natsuwa da kyakkyawan matsaya.
Hakkin kwanciya ko mu’amalar aure: Na taba jin wani shaihun malami yana bayani a kan haka ya ce ka so mafi yawa na aure na mutuwa ne sakamakon take hakkin juna wajen mu’amalar aure. Wanda shi ma dole ya zamo yana da kaso kamar haka: Hakkin juna wajen kula da yanayin lokacin mu’amalar musamman ga bangaren maza. Da yawa ba su lura da yanayin da matar ke ciki kan su kawo bukatarsu domin akwai lokutan da mace kan tsinci kanta cikin rashin lafiya ba jiki ko rashin kuzari ko bacin rai musamman yayin da take cikin satin da al’ada za ta zo mata wasu matan kan kasance cikin yanayi na fushi ko kasala. Wanda a irin haka in ba a yi sa’a ba, in namiji ya zo da bukatarsa, sai ta ki, a nan idan aka yi rashin sa’a sai ka ga an samu matsala, daga haka aure ya rasa kyawun yanayi.
Halin da za a kasance kafin mu’amalar ma’ana a nan kula da tsabta daga dukkansu su biyun dole su tabbatar da sun kauda duk wani abu da zai cutar da dayansu yayin mu’amalar. Misali kula da wanke baki hammata kyakkyawan tsarki da sanya turare mai sanyi ba mai karfi ba domin karya cutar da abokin mu’amala. Hakika rashin kula da wannan zai iya jawo a rika dardar wajen nuna bukata wanda kuma shi ma hakan wani wawakeken gibi ne a rayuwar aure wanda ke tarwatsa nutsuwar cikinsa.
Babban hakki na kula da gamsuwar juna. Bana tantama cewar zaa iya yarda da maganata in na ce a cikin kaso 100 na auren dake mutuwa sakamakon nakasu na mu’amalar aure, kaso 99 rashin sanin hakkin juna ne ta fannin gamsuwa. Duk da mata sun fi kokawa wajen rashin kula da hakkinsu na gamsuwa amma mazan ma na kokawa ta wannan fannin. Dole ne hakkine a kanka da kanki ku zauna ku fayyacewa juna nakasun da kuke fuskanta yayin mu’amalar aure. kai namiji karkace inka samu biyan bukata ka gama haka ma macen kar tace kunya take ji ba za ta fada masa ba ta samu biyan bukatarta ba. Domin in har za a tafi a haka, to tabbas wannan aure ba zai samu daidato ba bare natsuwa.
Amma bangare na uku a samun natsuwar aure shi ne tarbiyyar yara: Hakika duk gidan da yaran cikinsa suka zamo masu nakasu wajen tarbiyya to wannan gida natsuwarsa mai karanci ce. Dalili akan hakan shi ne da yawa gida in yaran gidan ba su samu kyawun tarbiyya ba za a rika zargin juna tsakanin iyayen shi uba ya rika ganin laifin uwa ne. Ita ma tana ganin nasa. Da sannu za ka ga kwanciyar hankali da natsuwa ta kaura daga wannan iyali.
Hakuri da jarabawar da aka tsinci kai a zaman aure daga namijin har mace. Tabbas wannan ma wani jijjige ne a samar da natsuwar aure. Allah zai iya jarabtar auratayyarku da samun matsaloli na karancin abun hannu ko rashin lafiya daga daya bangaren ko daga yaranku ko matsalar dangi ta kowane bangare walau na mijin kona matar. Hakika idan ya kasance ba a samu hakuri da tawakkali ba. Aure zai zama kawai zamane ake yi ba natsuwa tare da shi.
A kalami na gana sai ubangiji  (SWT) Ya ce: “..kuma muka sanya tsakanin kauna da tausayi…” To mun ga a nan ashe natsuwa ita ke jagortar kauna da tausayi har a samu zaman lafiya a aure.
Hakika ‘yan’uwa muna tafka kuskure wajen daukan wasu abubuwa a aure a kan suke samar da zaman lafiya. Mu sani a cewa ba wani zamananci ko al’ada da zai wanzar maka da zaman lafiya a auratayya face an gina shi a kan tsarin da za a samu natsuwa a cikinsa. Natsuwar kuwa dole ta kasance daga kowane bangare ma’ana duka bangaren biyu sun hada kai don samar da ita.
Inda za mu koma mu kalli zaman magabatanmu za mu fuskanci ba komai muke ba a zaman aure face dambarwa. A yau ‘yan bana-bakwai sun dage a kan cewa aurensu shi ne auren ‘yanci ka-ganni-kana-so, na-ganka-ina so!
An yi aure irin na soyayya kaman a lashe juna to amma sai ka ji ko shekara ba a rufa ba, an fara gajiyawa da juna kowanne ka zaunar da shi sai ya rubuta maka littafi guda na laifin dan’uwansa. Mace-macen aure sun yawaita har ya kasance duk wanda ka raba, sai ya ce ma yana tsoron aure. Shin ina yancin? Amsa ita ce an manta tsari da hujjar auren ne an tafi ga abu daya wato jin dadi. Kowanne bangare na ganin dole dan’uwansa ya kyautata masa ba tare da tunanin shi ma hakki ne a kansa ya kyautata din ba.
Fatana Ubangiji (SWT) Ya ba mu zaman lafiya, Ya kuma ba mu ikon kiyaye hakkin juna a wannan Sunna mai karfi. Ya kuma ba mu zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikinta domin mu samu lagwadar samun natsuwa da junanmu.
follow me on facebook follow me on twitter follow me on instagram

Fitattun labarai

Habiba complete hausa novel

Alqawarin da ciwo

Amfanin cin qafar kaza

Budurwar Roba

Amfanin lemon tsami

Afanin Zogale

Adam A. Zango

Amfanin namijin Goro (bitter kola)

Tona asiri

Yanda zaka duba sunanka a Npower