Tona asiri

Surukar Marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu Tana Kotu Bisa Tuhumar Wawurar Dukiyar Gwamnati 





Maimuna Aliyu, mahaifiyar Maryam wacce ake zargin ta kashe mijin ta Bilyaminu Halliru tana cikin jadawalin wadanda hukumomin rashawa ke nema ruwa a jallo.

Idan ba'a manta ba dai, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbanjo ya mika sunan Maimuna a matsayin zabin fadar shugaban kasa na kujerar shugabancin hukumar kiyaye rashawa (ICPC). To amma bayyanan sunan Maimuna ke da wuya sai hukumomin rashawa suka yi cha a kan zabin nata, inda hujjoji bayyanannu suka fito ana tuhumar ta da yin sama da fadi da kudi Niara miliyan 57.

A daidai lokacin da hukumar ICPC ke kokarin maka ta a kotu ne aka ji sunan ta ya bayyana zata jagoranci hukumar, lamarin da ya sanya fadar shugaban kasa ta janye sunan Maimunan.

Hukumar ICPC ta maka Maimuna a kotu, inda  ta ke kalubalantar ta da laifuka uku wandanda ke da alaka da rashawa.

Wadannan laifukan da hukumar ke zargin Maimuna da faruwa sun auku ne a lokacin da take jagorantar kamfanin ajiya da basussuka na Aso.

Ko a watan Mayu, rahoton wani kwamitin bincike da 'yan sanda ta kafa karkashin sufritanda Taiwo Oyewale ya tuhumi Mimamuna da wawurar wadannan kudade, inda rahoton ya nemi a gurfanar da ita a gaban hukuma.

Sai dai Maimuna tace bita da kulli ne kawai ake mata, kuma duka zargin da ake mata ba su da tushe. Ta ce wadanda ta fallasa su yayin da take Darakta a kamfanin ajiya da basussuka na Aso ne suka shirya mata makarkashiya.


follow me on facebook follow me on twitter follow me on instagram

Fitattun labarai

Habiba complete hausa novel

Alqawarin da ciwo

Amfanin cin qafar kaza

Budurwar Roba

Amfanin lemon tsami

Afanin Zogale

Adam A. Zango

Amfanin namijin Goro (bitter kola)

Yanda zaka duba sunanka a Npower