Karin magana 7
1. Wanda za a kashe don an karairaya shi ba kome.
2. Gudu da waiwaya shi ya kawo mugun zato.
3. Am fado daga kan dabino an zarce cikin rijiya.
4. Duhun damina maganin mai kwadayi.
5. Mai kafa hudu ya kan fadi bare mai biyu.
6. Wanda ya ci ka, ya mallake ka duka da kai da iyalinka.
7. Mutum fari ne, shi ke rina kansa ya zama baki.
8. A daga sama! An yi wa wata kwace.
9. Ba a so ba, ƙanen miji ya fi miji kyau.
10. Mai farce shi ya ke susa.
11. Mai hali, mai sabo.
12. Mai nema yana tare da samu.
13. Kowa ya ci ladan kuturu, dole ne ya yi masa aski.
14. Inda aka san darajar goro, nan a kan nema masa ganye.
15. Kowa ya hana ka ‘dakin kwana, da safe sai ya ganka.
16. Tashinku tashina, in ji mai jiran gawa.
17. Kada ka yi tsammanin alheri inda ba ka ga haske ba.
18. Ina zan zauna, matsegunci ya je kasuwa.
19. Kome ya yi tsawo, im bai yi kyau ba, gara gajere mai kyau.
20. Wai kunama da ta harbi kasko, ta ce, “shegen duniya, ko motsi ba ka yi.”
21. Yaro ya san matan nemansa.
22. Harbi ga ‘dan jaki, gado ne.
23. Sai an da’de a kan san hali.
24. Banza girman ‘kashi ba tsoka.
25. Murnar mata tana ga tafi.
26. An ce da akuya Sarkin Fawa ya mutu, ta ce, “Oho, ya mutu da wu’kar yanka ne ?
27. Kowa ya ji hushi ya gaji ne.
28. Haka aka ce in ji mai ba da labarin ‘karya.
29. Tsutsar nama ita ma nama ce.
30. Ha’korin dariya shi kan yi cizo.
31. In ka ji a zuba miya , cinikin tuwo ya ‘kare.
32. Abin da wancan ya ce shi na ce, kirarin mai tsoro.
33. Kome ya yi yawa ya yi ginsa amma ban da lafiya
34. Kowa ya yi wanka da dare, ya yi kyau da rana.
35. Da na sani, ta kan kashe malam da boka.
36. Im ba ruwanka cikin magana, ka bi ta da mhmm.
37. Ranar tsafi bunsuru ke ku’di.
38. Wani tsuntsu na gudun ruwa agwagwa a ciki ta ke kwana.
39. Ko ina mai aro za shi, da sanin mai riga.
40. Mutum fari ne, shi ke rina kansa ya zama ba’ki.
41. Ba a ‘kwace wa kuturu zobensa.
42. Mai da ruwa rijiya, ba ‘barna ba ne.
43. Kowa ya rena tsayuwar wata ya hau ya gyara.
44. Ba a raba harshe da ha’kori.
45. Muguwar miya ba ta ‘karewa a tukunya.
46. Mai tsegumi ba shi rabuwa da waiwaiye.
47. Karya a ke yi, tusa ba ta hura wuta.
48. Zama lafiya ya fi zama sarki.
49. In an ga macijiya a kwance sai a ce ba za ta yi sara ba.
50. A kan mutu bare lalacewa.
51. Cinikin duniya, ‘diban nono.
52. In ka ji ‘na ‘kiya’ samun dama ne.
53. Sai hali ya yi daidai a kan yi abota.
54. Mutum ba ya cewa kansa matsiyaci
55. Mai bawa ba ya bauta.
56. Kome ka ha’kura da shi ka ga bayansa.
57. Ba’kon munafuki ba na mutum ‘daya ba ne.
58. Gaskiya ta fi dokin ‘karfe ‘karfi.
59. In rana ta fito tafin hannu ba ya kare ta.
60. Kowa ya raina gajere, bai taka kunama ba
61. Abin da aka gasa, shi ya ga wuta.
62. Abin Allah! Budurwa da ciki; gwauro da yaye.
63. A bar ganin allura kankanuwa, karfe ce.
64. A bakin tsoho ne, goro kan tsufa.
65. Kowa ka gani da abu Allah ne ya ba shi.
66. Amfanin hankali aiki da shi.
67. A daÉ—e ana yi, wata rana sai gaskiya.
68. Ciki da gaskiya wuƙa ba ta huda shi.
69. Tuba na muzuru: kaza na bakinsa, bai sako ba, ya ce : na tuba
70. Arziki ba riga ba ne, balle a tuɓe.
71. Ƙamshin arziki ya fi ƙamshin waina.
72. Ana ganin wuyan biri a kan É—aure shi a gindi.
73. Bayan ci sai tsegumi.
74. Da kunne ya ji, da jiki ya tsira.
75. Cin daÉ—i sabo ne.
76. Kowa yana so ya gaji ubansa ban da É—an matsiyaci.
77. Kowa ya rufa asirin wani, Allah ya rufa masa.
78. Hali kowa da irin nasa.
79. Duniya mace da ciki ce.
80. Duniya rawar ‘yan mata, na gaba ya koma baya.
81. , in ba rabonka ba ne, banza ne.
82. Kome na duniya wani na gaba da wani.
83. Cinikin duniya É—iban nono.