Daren farko

Kamar yadda aka saba a al’adance, bayan ‘yan rakon Amarya sun gama ‘yan nasihohinsu suka tashi suka fita, na bi bayansu na rufe qofar gida, gabana yana faduwa haka na juyo na taho wajen Amaryata Ummul Adfal, wacce har yanzu kanta yake qunshe cikin mayafi tun lokacin da ‘yan rakon ango suke nan. Jin motshin shigowa ta yasa ta dago kai dan ta tabbatar sun riga sun tafi, ‘Assalamu Alaikum’ nace da ita ina mai murmushi a gareta, ‘amin wa alaika assalam’ ta amsa mini itama tana mai rama lallausan murmushi a gareni. Naje na zauna kusa da ita, sannan muka fara gabatar da abinda mukayi watanni muna koyawa kanmu domin wannan rana, ga maganganun da muka yi:
Ummul Adfal: O ni ‘yar gidan babana, wannan shine Daren Farko, na kasance ina mai tsoron daren da zai kaini zuwa ga wani ‘dan Adam daban, zuwa wata rayuwa sabuwa!
Abul Adfal: Daren farko kenan, na canji mai alkhairi a rayuwata, wannan shine darena da naki, saboda haka kada ki tasar mana hankalin daren, bari in sa hannuna a kan goshinki dan inyi mana addu’a kuma in roqa mana Allah SWT da addu’o’i masu yalwa, kamar yadda yazo daga Manzon Allah S.A.W inda yake cewa:
“Idan ‘dayanku ya auri mace, to ya dafa goshinta ya roqi Allah SWT kuma yayi addu’ar samun albarka, kuma yace
“ALLAHUMMA INNI AS’ALUKA MIN KHAIRIHA, WA KHAIRI MA JABALTAHA ALAYYA, WA A’UZU BIKA MIN SHARRIHA, WA SHARRI MA JABALTAHA ALAYYA”
“YA ALLAH INA ROQONKA ALKHAIRIN DA YAKE TARE DA ITA, DA ALKHAIRIN ABINDA KA DORATA A KAINA DASHI, KUMA INA NEMAN TSARINKA DA SHARRIN DAKE TARE DA ITA, DA KUMA SHARRIN ABINDA KA DORATA A KAINA DASHI”
Ummul Adfal: Ina roqonka da ka tafiyar da wannan dare tare dani cikin nutsuwa a matsayina na wacce kake qauna, kuma matarka tunda wannan dare ba irin sauran darare bane, dare ne wanda zaiyi wahala na mance dashi, kuma zanso daren yakasnce mai cike da so da qauna
Abul Adfal: Abu mafi muhimmanci a gareni shine da ki zamo cikin farin ciki, saboda haka bari in lullubeki da kalamai masu dadi, sannan in baki wannan kayan marmarin da waccan kazar, saboda haka ki nutsu kuma ki tuna fadar Allah SWT “Kuma da ambaton Allah ne zuciyoyi suke nutsuwa”
Ummul Adfal: “Kuma daga ayoyinsa ne cewa ya halitta muku matanku daga gareku, kuma ya sanya qauna da tausayi a tsakaninku, haqiqa a cikin wannan akwai ayoyi ga masu zurfin tunani” (Q. Rum 21)
Abul Adfal: Sadaqallahul Aziim. Kuma Allah ya albarkaceki gareni, ya ke wacce hankalina da zuciyata da tunanina da ruhina suka zabar min, duk abinda na mallaka ya zama mallakarki, haka ne ko? Da fatan komai zai daidaitu zuwa gareki ki samu nutsuwa. Sannan yake jarumata kuma matata, tun daga wannan dare da kuma sauran darare, za muyi Sallah raka’ biyu gajeru, kuma mu roqi Allah Mai Girma da Daukaka, dan kuwa kusanci daga Allah yake, rabuwar kai kuma daga shaidanne
Ummul Adfal : Ina neman tsari da shaidan la’ananne, wanda yake son yasa mu qi abinda Allah ya halatta mana.
Abul Adfal: Kinyi gaskiya, saboda haka tashi muyi Salah sannan muyi wannan addu’ar:
“Yaa Allah kayi albarka a gareni cikin iyalina, kuma ka albarkace ni ma iyalina”
Ummul Adfal: Abinda ya kwantar min da zuciyata da raina a wanan dare shine da mijina ya kasance daga cikin muminai masu tsoron Allah, kuma shiryayyu da shiriyar Allah SWT da Manzonsa Muhammad S.A.W, kuma zuciyarsa mai umarni da hasken da baya kuma bazai gushe ba.
Abul Adfal: Godiya ta tabbata ga Ubangijin da ya sauwaqa mini al’amarina ni da matata a cikin wannan dare namu na farko, ba abinda zance daya wuce fadar Annabi S.A.W
“Idan dayanku ya tara da iyalinsa, to yayi mata adalci ya kyautata mata, idan ya biya buqatarsa kafin ta biya tata, to kada ya barta har sai itama ta biya buqatarta”
Ummul Adfal: Ya Allah ka sa wannan dare nawa DAREN FARKO a cikin rayuwata da rayuwar mijina ya zamo mai albarka, kuma shine daren da ya hada ruhinmu waje daya, kuma muna qoqarin samar da iyali masu tarbiyya da taimakonka ya Ubangjijn talikai
Abul Adfal: Ya matata mai albarka, zaki kasance cikin jin dadi a wannan dare da yardar Allah SWT, kiyi buri a tare dani na Allah ya rubuta mana farin ciki da annashuwa a cikin sauran shafukan rayuwarmu kuma ya qara kusanci da hadin kai a tsakaninmu
Ummul Adfal: Amin yaa Rabbal Aalmin, ya Allah kasa mu zama masu jure duk wani abin qi da damuwa da suke zuwa a cikin rayuwar aure, kuma ka bamu ikon kyautatawa da farantawa juna, da bada haqqoqin aure yadda ya kamata
Abul Adfal: Da taimakon Allah SWT ni dake muna kan hanyar alkhairi da so da qauna, zanyi iya qoqarina wajen ganin na tsallakar da jigin ruwan rayuwarmu zuwa gabar AMANA DA GASKIYA, kuma kin gama kyautatawa a cikin komai , Allah yayi miki albarka
Ummul Adfal: Amin!!!
Daga nan muka tashi muka yi alwala, nayi mana jagaba muka yi Sallah raka’a biyu tare da addu’o’in neman alkhairi. Daga inda nake a zaune na juyo wajen Ummul Adfal dake kan dardumar da muka idar da Sallah, a hankali na bi da hannuna ta kan dardumar na riqe hannunta; wani irin kallo mai gusar da hankali da Ummul Adfal tai mini yasa daga nan ban qara sanin abinda ke faruwa ba!
Washe gari da misalin qarfe 5:15safe na tashi na tafi masallaci domin yin Sallar Asuba, bayan na dawo na tafi da nufin in tashi Ummul Adfal dan tayi Sallah, ga mamaki na sai na ganta akan darduma, ashe ma tatashi tuntuni. ‘Abban Fareedah ina kwana?’ Haka tace dani kanta na sunkuye tana kallon qasa, ‘Lafiya qalau Maman Fareedah, kina ganin zamu iya fara Tilawar Al’qur’an kamar yadda muka tsara ko kuwa? Dan gaskiya ni har yanzu gajiyar bikin nan bata sake ni ba, zan so in koma bacci yanzu’, ‘duk abinda kace ai shi za’ayi Abban Fareedah’, ga mamaki na har yanzu kanta a sunkuye yake kamar bata so ta kalleni.
Da misalin qarfe 11:30safe na farka daga baccin safen da na koma, duk da dai banyi niyyar tashi ba amma sai na fuskanci cewa Ummul Adfal bata kusa dani, hakan yasa na daure na haqura da baccin, na tashi na fito falo dan na kasance tare da Amaryata a ranarmu ta farko bayan biki. Tun daga qofar falon na fara jiyo qamshin ‘Spanish Omelet’, nayi mamaki da Ummul Adfal bata manta da abinda na gaya mata nafi so inyi karin safe dashi ba, nan take naji wani nishadi ya kama ni, na nufi kicin din da sauri dan inyi jinjina a gareta, nan da nan na sake kidimewa a lokacin da naji qamshin ganyen shayin larabawa wanda nakanyi tattaki in tafi gidan wani abokina dan in samu in sha lokacin da ina rayuwar gwauranta. ‘To ko dai wannan shine dadin Rayuwar Aure da mutane suke fada?’ Haka na fara tunani a zuciyata. Ina dawowa daga kogin tunanin da na shiga sai naga Ummul Adfal a tsaye a gaba na, wai ashe tana ta yimin magana tana so ta shige ni kuma ina can ina tunani, na kalleta nayi mata wani lallausan murmushi, haka itama ta mayar min da murmushin sannan ta sunkuyar da kai qasa, na matsa na bata wurin dan taje ta ajiye mazubin shayin da yake hannunta zuwa kan teburin cin abinci sannan nima na bita daga baya, naje na zauna akan daya daga cikin kujerun da suke zagaye da teburin ina kallon Ummul Adfal tana ta kaiwa da komowa wajen shirya mana abin karin kumallo, har ta gama bance da ita komai ba, tazo ta zauna a kujerar da take kallon tawa, na kalleta na hada fuska, nan dan sai ta tashi ta dawo kujerar dake kusa dani dan ta gane me nake nufi.
Har ya zuwa yanzu da Ummul Adfal take kusa dani kanta a sunkuye yake, ‘wai Ummul Adfal wanda sabon salo kika fito dashi ne na jin kunyata? Duk irin shaquwar da. . .’, da kaina na katse maganar tawa a lokacin da na tuna da cewa ashe fa jiya da daddare ne muka san ragowar sirrikan da yake tsakaninmu! Lallai banga laifin Ummul Adfal ba, duk wata mace mai kunya ya kamata ace taji kunyar mijinta a safiyar wannan rana.
Haka muka cigaba da cin abincin karyawar cikin farin ciki da annashuwa, abin gwanin ban sha’awa, wani lokaci in bata abincin a baki duk da dai da qyar take karba saboda kunya, sannan da qyar ta daure nima ta bani a baki musamman da taga raina yana nema ya baci duk da dai nasan kunya ce ta hana ta.
Saboda haka Gwauraye da Tuzurai sai aje ayi aure ko ?!
Hanyoyi 60 Da Zaka Dawwamar Da Soyayyar Matarka
1. Ka zamo mai tausasa zance a gareta, kar ka zamo mai yawan fada.
2. Idan ka shiga gida kace ‘Assalamu Alaikum’, sallam tana korar Shedan daga gida
3. Annabi SAW yace mata kamar kayan qarau ne saboda haka kula dasu sosai, ka tuna akwai alkhairi a cikinsu saboda haka sai a tarairayesu.
4. Idan zaka bata shawara ko zaka yi mata fada ya zamo a cikin sirri, wato alokacin da kuke ku kadai, kada ya zamo a cikin mutane dan yin hakan muzantawa ne.
5. Ka zama mai kyautatawa matarka, hakan yana qara soyayya
6. Idan tazo zata zauna ka tashi ka bata wurin zamanka, hakan zai tausasa zuciyarta.
7. Ka guji yin fushi ta hanyar riqe al’wala a koda yaushe. Annabin Rahma SAW yace idan kayi fushi to idan a tsaye kake sai ka zauna, idan a zaune kake sai ka kwanta.
8. Ka rinqa yin ado kana sa turare saboda ita.
9. Karka zamo mai tauri, Annabi SAW yace : ‘Nine mafi kyautatawa zuwa ga iyalina’, idan kayi tauri da yawa baza ka samu kusanci zuwa ga Allah ba, haka kuma baza ka zamo namiji jarumi ba.
10. Ka dinga sauraron duk abinda matarka zata gaya maka koda kana ganin abin bashi da muhimmanci, hakan zai sa ta san ka damu da ita.
11. Ka kaucewa cin musu da matarka, yana kawo rabuwar kai.
12. Annabi SAW yace ku kira matanku da sunaye masu dadi, sunan da suke so suji ka kira su dashi.
13. Ka riqa yi mata tsarabar bazata, idan tana sha’awar wani abin marmari sai ka sayo mata ba tare da ta sani ba.
14. Ka kula da harshenka zuwa gareta, wato ka guji abubuwan da zasu sa ta fushi.
15. Mutum tara yake bai cika goma ba, kayi haquri da duk wani aibun da take dashi sai Allah SWT ya sa albarka a cikin auren naka.
16. Ka dinga nuna mata yabo da godiya idan tayi maka abu mai kyau.
17. Ka dinga taimaka mata wajen ganin ta kula da dangantakar ‘yan’uwanta da iyayenta.
18. Ka yawaita janta da hira akan abinda take so.
19. Idan kaga ‘yan’uwanta suna kusa, ka dinga yabonta, kana kambamata, kana tabbatar musu da kirkinta da kyautatawarta.
20. Ku dinga yiwa junanku kyaututtuka. Manzon Allah SAW yace kyauta tana qara soyayya.
21. Idan kayi mata laifi sai ka samu wani abu ka kyautata mata dashi dan ya goge laifin.
22. Ka rinqa kyautata zato a gareta, banda zargi!
23. Karka dinga kulawa da qananan laifukanta, kayi kamar baka gani/ji ba. Yana daga cikin ‘dabi’un Sayyidina Aliyyu (RA).
24. Ka nin-ninka haqurinka da ita musamman a lokacin da take jinin al’ada.
25. Ka ringa sauraron zuwan kishinta, kuma ka ringa yabon kishin nata, ko manta Manzon Allah SAW suna kishi!
26. Ka zamo mai qasqantar da kai, idan ka zamo mai tunani to ka tuna cewa tana kula da ‘ya’yanka, itace mai kula da gida!
27. Karka dauki abokanka sama da matarka!
28. Ka ringa taimaka mata da ayyukan gida. Manzon Allah SAW ya kasance yana taimakon matansa.
29. Ka taimaka mata wajen girmama iyayenka, baza ka iya takura mata taso su ba amma zaka iya taimaka mata dan ta cimma hakan.
30. Ka dinga nuna mata cewa itace irin matar da kake ta addu’ar ka samu.
31. Karinga tunawa da matarka a cikin addu’o’inka, hakan zai qara qarfin soyayyar taku.
32. Kada ka dinga tunawa da baya, babu abinda hakan zai jawo sai damuwa, abinda ya riga ya wuce a barwa Allah.
33. Karka taba nuna mata cewa taimaka mata kake idan kana mata wani abin kamar sayan abincin gida, saboda a zahirin gaskiya mu ‘yan aikatarwa ne kawai, Allah shine yake azurtawa da ciyarwa. Wannan kuma wata hanya ce ta qasqantar da kai ga Allah SWT da kuma gode masa.
34. Ka gane cewa Shaidan maqiyinka ne amma ba matarka ba, wani lokaci idan mata da miji suna magana idan suka samu sabani sai Shaidan ya shiga tsakani. Kayi iya qoqarinka wajen ganin Shaidan bai shiga tsakaninka da matarka ba.
35. Ka ringa bata abinci a baki, Annabin tsira SAW ya koya mana hakan, abincin ba wai iya cikinta zai tafi ba idan ka bata a baki, har zuwa cikin zuciyarta.
36. Ka kare matarka daga duk wani sharri ta hanyar yi mata addu’o’in neman tsari.
37. Ka zamo mai yawan yi mata murmushi.
38. Ka guji duk abinda bata so ko mai qanqantarsa, idan baka kula ba ta haka ne zai girma har ya zama babba.
39. Ka guji yin fushi da fada a gareta, yin hakan yana rage shaquwa.
40. Ka dinga yin maraba da shawarta.
41. Ka taimaka mata wajen samun nasara a harkokinta na rayuwa.
42. Kullum ka zamo mai qara kusantuwa zuwa gareta.
43. Ka taimaka mata wajen kula da yara. Wasu mazan suna ganin kamar ba aikin su bane kula da yara, basu san cewa yin hakan ne ma zai sa su qara kima da daraja a idon matan da yaran ba.
44. Ka ringa yi mata dadin baki da magana mai taushi.
45. Ka ringa cin abinci tare da ita.
46. Duk lokacin da zaka yi tafiya ka sanar da ita, haka kuma ka gaya mata rana da lokacin da zaka dawo.
47. Kada ka fita daga gida a lokacin da kuka samu sabani.
48. Gida yana da sirri kala-kala, idan ka zamo mai fadan sirrin gidanka a cikin mutane to kana yi wa kanka zaqon qasa ne. Sirrin gida ya tsaya a cikin gida.
49. Ku dinga qarfafawa junanku wajen yin ibada, ku dinga shirya zuwa Hajji ko Umrah a lokacin da kowa bai takura ba (misali a lokacin da bata da ciki kuma bata shayarwa) idan Allah ya baku iko.
50. Ka kula da haqqoqinta na aure
51. Allah SWT yace : « ku zauna da matanku cikin kyautatawa », ka dinga riritata kamar qwai.
52. Idan aka zo kwanciyar aure kada kayi mata ‘hawan qawara’, kuyi wasan tayar da sha’awa tukuna.
53. Idan kun samu sabani da matarka, kada ka gayawa kowa, idan kayi haka kamar kabar ciwo ne a bude quda ya hau.
54. Ka nunawa matarka cewa ka damu da lafiyarta. Lafiyar matarka lafiyarka ce. Idan ka kula da lafiyarta hakan ya nuna kana sonta.
55. Karka dinga tunanin ko yaushe kana da gaskiya, mutum tara yake bai cika goma ba.
56. Ka ringa sanar da ita lokacin da kake cikin matsala, farin ciki ko damuwa.
57. Ka dinga yafe mata idan tayi ba dai dai ba.
58. Kake yawan tuna cewa kaine bango wajen jinginarta a lokutan wahala ko qa-qa nakayi
59. Ka karbi matarka da duk halin da take tashi, Mazon Allah SAW yace an hallicci mata ne daga qashin qirji tanqwararre, idan kayi qoqarin ka tayar dashi zai karye!
60. Ka zamo mai kyakykyawan zato ga matarka a koda yaushe, Allah yana kula da niyyarka zuwa gareta a koda yaushe. Allah madaukaki yace:
“Kuma daga ayoyinsa ne cewa ya halitta muku matanku daga gareku, kuma ya sanya qauna da tausayi a tsakaninku, haqiqa a cikin wannan akwai ayoyi ga masu zurfin tunani” (Q. Rum 21)
Ya Allah ka bamu abokan zama nagari, masu tsoronka da yi maka da’a, kuma masu kyawun gani.
Hikimomi da dabarun da maigida zai bi ya kyautata wa matarsa
Babu macen da ba ta son mijinta ya rika ji da ita, yana nuna mata soyayya da girmamawa. Yin haka na kara wa mace jin ta fi kowace mace ko jin ta a saman duniya, sannan duk yarintar mace ko tsufanta tana son mijinta ya rika daukarta a matsayin ’yar karamar yarinya, wadda na taba bayani a kan hakan. Ma’ana ya rika kula da ita kamar yadda zai kula da karamar yarinya, ya rika tunawa da kuruciyarta da ya sani a da kafin ya aure ta.
Saboda haka idan ba ka yin haka, to daga yau ka fara, don matarka ta rika jin ita ma ta kai mace, ta samu farin ciki da jin dadin zaman aure. Na tabbata yin hakan na bayar da kwanciyar hankali a cikin gida, sannan yana kara dankon soyayya sosai.
Ka rika kula da irin sabon kayan da take sa wa ko wani sabon abu da ta canja, kamar yin kitso, kunshi da kwalliya sai ka yaba da nuna burgewa a tare da kai. Duk wani sabon canji da ka gani yana da kyau ka san da shi, idan na yabawa ne, ka yaba, idan kuma na magana ne ka yi. Wannan shi ne zai kara tabbatar mata da cewa kana damuwa da ita.
Kalmar yarinta kada ta rabu da bakinka, kamar Bebita, ka rika sa wa tana jin a kullum ita ’yar karamar yarinya ce a wurinka. Wani lokacin ma ka kira ta da sunan da ka san babanta ko babarta suke kiran ta da shi a lokacin da take karamar yarinya, sannan ka fada mata kalaman yabawa masu dadi da cewa tana da kyan tsari.
Sai kira in ka fita ofis, ka kira matarka duk lokacin da ka kai ofis. Sai ka fada mata cewa: “Na kira ne don in tabbatar da jin lafiyarki.” Yin hakan na sa ta san cewa tana da muhimmancin gaske a wurinka sosai.
Wata rana ka ba ta hutun shiga kicin, kamar ranar da babu aiki, sai ka shiga ka dafa abincin da za ku ci ko in ba zai yiwu ba sai ka fitar da iyalinka wani wurin birgewar da za su dade suna tunawa. Zuwa sayayya tare ko zuwa wurin hutu da shakatawa, ka rika kulawa da ita kamar kwanan nan ka hadu da ita, wato kamar wata sabuwar budurwarka.
Kulawa ta musamman, idan tana son yin magana da kai, ka juya ka saurare ta da kyau. In kana karatun jarida ko kallon talabijin sai ka rufe. Haka in an bugo waya kuna cikin tattaunawa, kar ka dauka ko kuma ka kashe kafin ku fara tattaunawa. Ka saurare ta da kunnen basira kamar yadda kake yi da in ka je zance. Sannan ka rika nuna alamun kana ji da kyau ta alamun gyada kai, murmishi ko amsawa. Sauraren abin da mace ta fada na daya daga cikin abin da ke sa wa ta kara girmama ka.
Ka matso da ita kusa da kai balle ma lokacin da ka san ta tara gajiya ko lokacin da take fushi ko take cikin bacin rai, kwantar da ita a kirjinka na iya sa wa ta dan huce ko ta samu sauki. Ka sanya ta ji kamar ’yar yarinya karama a kirjinka. Ka bar ta har ta yi barci daga nan ne za ka gane irin baiwar da Allah Ya yi mata da kyanta da kai kanka baiwar da Allah Ya ba ka.
Zama a gida ranar da babu aiki don kawai ka kasance tare da ita, sannan ta san kana tare da ita ne ba don kamai ba sai dan kana son ka zauna da ita. Ka yi hira, wasanni, maganganun da za su sa ta ji dadin wannan kasancewar da ka yi da ita, tun da na sha ganin matan da ba su son mijinsu yana gida sai in lokacin da zai yi barci.
Yana da kyau wata rana ma ka kulle ta a daki, don kar yara su dame ta sannan kar ka bar su su shiga har na kamar tsawon awa shida, kawai don kana son ta yi barci ta huta. Sai kai ka kula da yara na dan wannan lokacin, ka fahimtar da su cewa innarsu na bukatar hutu, bari ita ma ta dan ji dadin rayuwarta. Sai ka yi girki ka kai mata daki ta ci gaba da hutawarta, babu abin da yake sa a ji dadin soyayya face irin wadannan abubuwan. Na san wani zai ce shi yaushe yake da lokacin hakan, ko ya ce in ya yi haka ai ya bayar da kansa ga matarsa, za ta raina shi. Wallahi babu maganar raini, tun da wanda aka yi duniyar ma dominsa na tabbata kowa ya sami labarin irin was an da yake da iyalinsa. Saboda haka ka zama miji nagari.
 
Ka matso da ita kusa da kai balle ma lokacin da ka san ta tara gajiya ko lokacin da take fushi ko take cikin bacin rai, kwantar da ita a kirjinka na iya sa wa ta dan huce ko ta samu sauki.
follow me on facebook follow me on twitter follow me on instagram

Fitattun labarai

Habiba complete hausa novel

Alqawarin da ciwo

Amfanin cin qafar kaza

Budurwar Roba

Amfanin lemon tsami

Afanin Zogale

Adam A. Zango

Amfanin namijin Goro (bitter kola)

Tona asiri

Yanda zaka duba sunanka a Npower