Karin magana 6

1. Keh kuma a su wa ki'ashi a jirgi
2. Ni shegiya na ji dan daudu
3. Wanda aka haifa 29 ga wannan watan ba ya kara shekaru sai ko wane shekara hudu kenan? Ko ya
4. muna marhaba da gashashe wai kura taga bakin jaki.
5. ‘’ abun kunya nama na jan kare"
 
 
6. "Ya na iya da abin da ya gagari wuta? inji kishiyar konanniya"
7. Ko ruwa ta karewa dan kada, akwai na watsal-watsal!!!
8. MAGANA JARI CE, YARO BA DA KUDI A GAYA MAKA
9. Kwana na nawa ne?...Maye yayi amarya zai cinye ta
10. Wannan na dabam ne malami da ku’din ki’da.
 
 
11. Ma’kiyinka ba shi yabonka ko da ka kama damisa ka ba shi
12. Mai ‘kafa hudu ya kan fa’di bare mai biyu
13. Kome ka ha’kura da shi ka ga bayansa
14. Ba’kon munafuki ba na mutum ‘daya ba ne
15. Mutanen duniya su kai mutum inda Allah bai kai shi ba su wahalshe shi
 
 
16. In ka ji mutum na tsoron kira ya yi laifi
17. Allah ya sauwa’ke wahala, tsohuwa ta ga ajalinta ya kusa
18. Kowa ya ‘ki tsotse hannu bai ji za’kin miya ba
19. Gaskiya ta fi dokin karfe karfi
20. Idan gamba tana da dadi a nono, nono ma yana da dadi a wuri'n gamba
 
 
21. iska tana wahalshe da mai kayan kara
22. Shirin zaune ya fi na tsaye
23. Ranar tsafi bunsuru ke ku’di
24. Naman da ke kusa da wuta ya fi gasuwa
25. Biri bai ‘ki muruci ba wuyar gina ya ke ji
 
 
26. Kibiyar ajali sulke ba ya tsare ta sai ta wuce
27. Mai suna ya san sunansa, an ce barawo Ga shi nan
28. Im ba ruwanka cikin magana, ka bi ta da mhm
29. Shan tabar kwa’do da baki da hanci
30. Da dama , sarki a bisa jaki
 
 
31. Da na sani, ta kan kashe malam da boka
32. Kowa ya yi kashi a inuwa ya bar ta
33. Kowa ya yi wanka da dare, ya yi kyau da rana
34. Kome ya yi yawa ya yi ginsa amma ban da lafiya
35. Abin da wancan ya ce shi na ce, kirarin mai tsoro
 
 
36. In ka ji a zuba miya , cinikin tuwo ya ‘kare
37. Sarautar Allah kare a bakin zomo
38. Tsutsar nama ita ma nama ce
39. Barawon da ba a gani ba sunansa mamman
40. Kome lalacewar mutum, ba ya rasa rana tasa
 
 
41. An ce da akuya Sarkin Fawa ya mutu, ta ce, “Oho, ya mutu da wu’kar yanka ne ?
42. Aure ya tashi wai an doke bora da kaya
43. Banza girman ‘kashi ba tsoka
44. Sai an da’de a kan san hali.
45. Mutum bai fi ni tsumma ba, kar ya zuba min ‘kwar’kwata
 
 
46. Yaro ya san matan nemansa
47. Mai hushi ba shi rama gayya
48. Mai hankali shi kan ba kaza ruwa da damina
49. Izza na Kano, sarauta na Sakkwato, ya’ki na Zariya, karin magana na Bauchi
50. Inda wuta ta kama, nan a bi ta a ji
 
 
51. Zama da mai turare yafi zama da makeri ko bai ba ka turare ka shafa ba ka ji kamshi Amma makeri ko bai cuce ka ba tartsatsin wuta ya cuce ka
52. Ba ka ba mutum kibiya ya komo ya harbe ka da ita.
53. In ka bari sauran tuwo ya ‘konaka kai ka so
54. In ka ga baki da tsawo na mai musu ne
55. Masoyinka ba shi ganin aibinka
 
follow me on facebook follow me on twitter follow me on instagram

Fitattun labarai

Habiba complete hausa novel

Alqawarin da ciwo

Amfanin cin qafar kaza

Budurwar Roba

Amfanin lemon tsami

Afanin Zogale

Adam A. Zango

Amfanin namijin Goro (bitter kola)

Tona asiri

Yanda zaka duba sunanka a Npower