SHUGABAN YAN DAUDA A DUNIYA

ƊAN DUƘUNUNU
(Shugaban ƴan Dauɗa na duniya)

Amou haji, wani mutum ne ɗan asalin ƙasar iran wanda akache shine mutum mafi rashin wanka da ɗauɗa a duniya inda ya shafe tsawon shekara sittin baiyi wanka ba.

Anche wannan ɗabi'ar tashi ta samo asali tun shekarun kuruchiyarsa inda yayi ikirarin cewa yin wanka yana sakashi rashin lafiya, sannan yatsani sabulu da soso, yana kan haka ya tattara yanashi yanashi ya koma cikin wani ɗan kogon dutse kusa da kauyenshi yana rayuwar kaɗaichi, daga bayane mutan kauyensa suka gina masa wani ɗan ɗaki a saman dutse.

Wani ƙarin abun mamaki ga ɗan duƙununu shine ba a iya rashin wanka ya tsaya ba, abinchin dayafi so shine mushen bakin hanya da mota ta kaɗe ko wani mushe daya tsinta a hanya,baya son lafiyayyen abinchi, ruwan sha kuwa yana sha ne a cikin wani robar lalatacchen baƙin mai, sannan koda yaushe a cikin shan lofe yake, ko ya jera kararen sigari samada da uku yayita busawa abunshi.

Wata tawaga ta likitochi sun taɓa kai masa ziyara inda aka ɗauki jininsa domin gwajin chutar hanta, ƙoda, da sauran cututtukan, amma abin al'ajabi aka sami ɗan duƙununu lafiya garau!, illa cewa kawai da sukayi yana fama da kaɗaichi a ƙwaƙwalwarsa.

A karshe dai da abun ya ishi mutan ƙauyensa shine suka taru watarana suka wanke shi da sabulu da soso duk da sune abunda yafi tsana a rayuwarsa, bayan wasu kwanaki da yi masa wanka yana kwanche haka siddan yarasa rauwarsa.

DAUƊA ƘARIN ƘARFI, WANDA BE SANI BA SHIKE WANKA!
follow me on facebook follow me on twitter follow me on instagram

Fitattun labarai

Habiba complete hausa novel

Alqawarin da ciwo

Amfanin cin qafar kaza

Budurwar Roba

Amfanin lemon tsami

Afanin Zogale

Adam A. Zango

Amfanin namijin Goro (bitter kola)

Yanda zaka duba sunanka a Npower

Tona asiri