JININ AL'ADA
ZUBAR JINI GUDAJI-GUDAJI KO KUMA WANI ABU MAI KAMA DA TSOKAR NAMA A LOKACIN JININ AL’ADA (MENSTRUAL CLOT)
Jinin al’ada yana fita ne daga al’aurar mace wacce ta balaga, a duk bayan wasu kidayayyun kwanaki. Fitar jinin yana nufin mace ta kai munzalin da zata iya daukar juna biyu matukar namiji ya sadu da ita a lokacin da ya dace. Abinda yake kawo fitar jinin shine, jikin bangon mahaifar mace yana kumbura kuma ya cika da jijiyoyin jini. Wannan shiri ne na musamman domin karbar kyankyasasshen kwai na haihuwa (fertilized ovum) bayan saduwar aure. Kumburin da mahaifa take yi yana matsayin wata shimfida ce mai laushi domin samar wa kyankyasasshen kwan makwanci mai kyau da kuma abinci. Idan ba’a dace da samun kyankyasasshen kwai ya shiga cikin mahaifar ba, to, shimfidar zata zagwanye ta lalace, sai ta fita daga cikin mahaifa a matsayin jinin al’ada. Wannan abin zai rika faruwa lokaci bayan lokaci gwargwadon yadda Allah ya tsara halittar jikin mace. Ma’ana wasu matan ala’darsu takan zagayo duk bayan kowane kwana 14, ko 20, ko 30 da makamantan haka, wanda likitoci suke kira “menstrual cycle”. Wasu matan kuma basu ganin zuban jini, sai dai suga digon jini kwai wanda ake kira “spotting”.
Sa’annan mafiyawan mata suna ganin wasu alamomi idan al’adarsu ta kusa zuwa (premenstrual syndrome), wadanda suka hada da:
1. Ciwon mara mai tsanani ko maras tsanani
2. Ciwon baya ko kugu
3. Ciccikowar nono ko ciwon nono
4. Bacin rai da rashin walwala
5. Zafin jiki ba tare da zazzabi ba
6. Tashin zuciya ko yin amai
7. Ciwon kai ko yawan mutuwar jiki
*YANAYIN JININ AL’ADA*
Launin jinin al’ada yakan bambanta tsakanin mata. Mafi yawanci yakan kasance jazur (red), amma wasu sukan ganshi baki-baki (dark). Idan kuma ya kusa daukewa sai ya koma kamar ruwan nama (brown). Jinin al’ada mai launi jazur yana nuna cewa bai dade sosai a cikin mahaifa ba. Mai launin baki-baki kuma yana nuna cewa ya dade a cikin mahaifa. Amma idan ya kasance ruwan kwai (orange), ko ruwan toka (grey), to, yana nuna alamar cewa kila matar tana da ciwon sanyi (infection), wanda gwaji ne zai tabbatar da hakan ko kuma akasin haka. Idan launin ja mai haske ne (bright red), ko ruwan hoda (pink), to, yana nuna cewa jinin ya gauraya da ruwan mahaifa (cervical fluid). Amma ya kamata mu san cewa ko ma menene launin jinin al’ada, ba abin tashin hankali bane matukar bai haddasa wata bakuwar rashin lafiya ba.
Game da sunsuna (smell ko odour) kuwa, ya kamata mu fahimci cewa jini a karan kansa baya da kamshi ko wari. Amma jinin al’ada zai iya sauya sunsunarsa ta koma mai karni kadan. Wannan baya rasa nasaba da cudanyarsa da sinadarai na wurin da yake fitowa, ko kuma dadewarsa a cikin mahaifa. Amma duk da haka bai kamata jinin al’ada ya zama mai wari ba. Idan kuma ya zamanto yana wari, to, yana alamta cewa mace tana da ciwon sanyi (infection), ko bata tsabtace al’aurarta yadda ya kamata, ko sinadan da farjinta yake fitarwa domin samar da kariya daga kwayoyin cuta ko ni’ima (vaginal pH level) yayi yawa sosai. Ana so vagina pH level ya kasance tsakanin 3.8 zuwa 4.5 na ma’aunin dakin bincike (laboratory).
Abinda ya shafi kaurin jini (blood texture) kuma shine, jini asalinsa ba tsululu bane kamar ruwa. Yana da danko da kuma kauri kadan. Don haka jinin al’ada ba a tsammanin ya saba ma wannan yanayin. Hasali ma kasancewar wurin da yake fitowa, da sinadaran da yake cudanya dasu, da dadewar da yakan yi kafin ya fito ta sanya idan yana fitowa da gudaji, to, ba matsala bace. Sa’annan mata da yawa a wannan group din suna tambayar cewa menene mahangar likita game da wani abu mai kama da tsokar nama da yake fita daga al’aurarsu a lokacin jinin al’ada. To, a gaskiya wannan shima ba matsala bane. Abinda yakan faru shine, lokacin da bangon mahaifa ya zagwanye sakamakon rashin shigar kyanykyasasshen kwai a cikinta, kamar yadda nayi bayani da farko, to, wani bangare na naman jikin bangon mahaifar (endometrium wall) shima yana bambarowa ya hade da jini. Saboda haka idan ya fito sai a ganshi kamar tsokar nama.
*ABINDA YAKAMATA AYI A LOKACIN JININ AL’ADA*
Hikimar Allah ce ta sanya mace take fitar da jinin al’ada. Don haka, idan ana cikin wannan yanayin, ga kadan daga cikin abubuwan da ya kamata a lizimta:
1. Tsabtar jiki, tufafi da abinci
2. Kauce ma shan magunguna domin tsayar al’ada ko kuma hanata zuwa
3. Rage cin kayan gwangwani, ko lemun kwalba, ko kayan zaki, ko shan coffee, ko duk wani abinci da abin sha wanda aka lura cewa yana kara tsananin laulayin al’ada
4. Samun isasshen hutu
5. Daina yinwanka da ruwan sanyi, tsarki da ruwan sanyi, ko shan ruwan sanyi
6. Canza audugar kunzugu (sanitary pad) akai-akai, da kuma daina maimaita amfani da ita