General buratai da mahaifinsa

Shugaban sojoji Lt Gen. Tukur Buratai tare da mahaifinshi Dattijon arziki, 'yan mazan jiya, kuma tsohon soja Malam Yusuf Buratai Allah Ya kara mishi lafiya.

Dattijon arziki Malam Yusuf Buratai shima tsohon soja ne wanda ya halarci yakin duniya na biyu a kasar Burma, yana daya daga cikin dakarun sojoji da sukayi yaki suka kwantar da tarzoman yakin duniya na biyu.

Aikin soja gado ne a gurin Lt Gen. Tukur Buratai, tarihi bazai manta ba; mahaifinshi Dattijo Yusuf ya baiwa majalisar dinkin duniya nashi taimakon don tabbatar da zaman lafiya a duniya.

Kamar yanda har abada tarihi bazai manta ba Lt Gen. Tukur Yusuf Buratai ya bada gudunmuwa wa gwamnatin Nigeria wajen kakkabe ayyukan 'yan ta'adda, ma6arnata da masu taka dokar kasa wadanda ada suke mafarkin sunfi karfin hukuma.

Gen Buratai da Mahaifinshi hakika rayuwansu tayi albarka, tsakaninmu dasu sai dai fatan Alkhairi Allah Ya sa su gama da duniya lafiya.

Har yanzu dai muna cigaba da addu'ah Allah Ya kaimana Maigida Lt Gen. Tukur Yusuf Buratai matsayin FIELD MARSHAL na farko a tarihin Nijeriya.


follow me on facebook follow me on twitter follow me on instagram

Fitattun labarai

Habiba complete hausa novel

Alqawarin da ciwo

Amfanin cin qafar kaza

Budurwar Roba

Amfanin lemon tsami

Afanin Zogale

Adam A. Zango

Amfanin namijin Goro (bitter kola)

Yanda zaka duba sunanka a Npower

Tona asiri