Atiku yabar APC
Atiku Ya Fita Daga Jam'iyyar APC
A yau Juma'a ne, Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya bayar da sanarwar ficewa daga jam'iyyar APC amma kuma bai bayyana sabuwar jam'iyyar da yake shirin komawa ba.
A cikin sanarwar da ya fitar, tsohon Mataimakin shugaban ya jaddada cewa " Ba zan iya zama a jam'iyyar da ba su damu da matasa ba da ci gaban kasa. Saboda haka bayan na gama duk shawarwari na na ga ba zan iya ci gaba da zama dan jam'iyyar APC ba." Ana dai sa ran zai koma PDP ne, jam'iyyar da ya taka rawa wajen kafawa kuma ya tsaya takara a karkashinta.